Complete Hausa Novels

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx

Chapter 44 of 56

*page 82*

Cikin hikima da dabara mohd ya janye malika daga kan jikin sa ya soma ciyadda kanshi sbd ya fahimci tana yi ne kawae don ta 6ata ran Ryynt wacce yaji dad'in ganin yanda ta nuna ko oho duk da yasan dole a ranta xata ji wani abu.

Suna kammala cin abincin Mohd yakai hannu zae d'auki briefcase d'insa dake ajiye gefe malika ta rigashi d'auka ta rataya jakar ta tafi dashi rungume a jikin ta sae kwarkwasa take still Ryynt bata bi ta kanta ba sae hannun mami taja suka tafi d'aki.

Da dare bayan isha'i Ryynt ce zaune a d'akin ta tana koyarda su Alawiyya da mami karatun qur'ani yanda ake fitar da harafi da komai su kuma suna saurarenta idan ta gama su karanto inda duk sukayi kuren fitar da harafi ta gyara musu.

Tsawon lokaci Man na tsaye a bakin qofar d'akin yana sauraren yanda qira'ar Ryynt ke shiga kunnen sa mai dad'i sae duk ya qara jin sonta a ransa yana kuma jin shi kam ya gama yin sa'ar uwar 'ya'yansa a duniya.

Gyaran murya yayi had'e da yin sallama Ryynt ta kai aya snn ta amsa masa sallama tana mai kallon sa sae murmushi yake mata har ya qaraso gurin su yazo gab da ita ya zauna nn qasa kan dardaumar sallah inda take zaune akai nn mami da alawiyya suka gaida shi, ya amsa musu yayinda alawiyya taja hannun mami suka fita.

Ryynt ta gaida shi cikin sakin fuska,

Shima fuskar sa a sake ya amsa mata had'e da riqo hannun ta yana mae kallon fuskarta yace"karatun ki da dad'i Ryynt?

Ryynt tayi murmushi tace"uhm zolaya koh?

A hnkli yaja hancinta yace"ba wani nn aikin san gaskiya na fad'a,don haka yau sae kin koya min qira'ar nn taki mae dad'i.

Ya fad'i hakane tare da janyo ta zuwa jikinsa ya d'auki qur'anin da ke ajiye kusa da ita ya bud'e,

Yace"oya karanta min ina jin ki"

Tace"hm Mk knn ni bance ka koya min taka qira'ar ba sae kai"

Yace"yaushe kika ta6a jin karatuna da zaki ce haka"

Tace"a mumbae mana idan muna sllr asuba"

Yayi murmushi kawae dmn haqiqanin gaskiya shi kaina yasan karatun sa nada dad'i sosai amma na Ryynt dabanne da zaka ji kmr kar ta daina idan tana yi dmn har wata irin natsuwa mutum ke jin kansa a ciki.

Yace"karanta min to ko aya biyar ne inji kinji"

Tasan da gaske yake zancen hkn yasa bata sa wasa ba ta kalli qur'ani ta fara karanta wa mohd yayi tsit had'e da lumshe ido yana saurarenta har sae da yaji ta tsaya snn ya bud'e ido, Ryynt tace"bacci kake ji?

Mohd dake kallon ta cike da so yace"bacci jin dad'in karatun ki ba"

Ya fad'i hakane tare da rufe qur'ani ya ajiye ya riqo hannun ta yace"ya naji jikin naki da kamar zafi?

Ryynt tayi shiru dan ita kanta bata san me ke damunta ba kawae dae taji jikin nata nayin zafi.

Mohd yace"kinyi shiru gaya min baki da lafiya ne"

Tace"lafiyata qalau"

ya shafo cikinta yace"babyna fa?

Tace"shima haka"

Yace"that's gud bari naje na d'an watsa ruwa bcs dawowa ta knn nace bari nazo na ganki tukun"

Tace"ba dae tun fitar ka ta safe ba"

Yace"eh wlh aiki ne ya riqe ni"

Tace"eyyah sannu ni na d'auka ko ka dawo ba kai dae sami fitowa bane"

yace"inafa aiki bae bar na dawo ba yanzu gabad'aya jikina ma sae ciwo yake min ga kuma bacci da nake ji sosai"

Ryynt tace"idan ka watsa ruwa mana sae kasha magani koda zaka tashi jikin naka ya sake maka ae koh"

Hakane my ryynt bari na tashi naje.

Nan ya tashi ya fita Ryynt ta bisa da kallo har ya fita snn taje ta kirawo mami da alawiyya suka ci gaba da karatun su.

Bayan sun gama karatun ne alawiyya ta tafi d'akinta Ryynt kuwa tayi wa mami wanka ta mata shirin bacci snn itama taje tayi wanka wacce koda ta fito tuni mami tayi bacci hkn yasa tana gama shirinta na bacci itama ta kwanta tare da kashe musu wutar d'akin.

Bayan har bacci ya kwashi Ryynt mohd ya shigo d'akin wanda yana ta6a jikinta yaji ya qara zafi fiye da yanda yaji sa a d'azun.

A hnkli ya zauna kan bedside drawer yana shafa goshin ta da yaji yafi koina zafi a jikinta sae kallonta yake yana ji kmr ya ta she ta ya bata magani sae dae kuma baya son farkadda ita hkn yasa ya tashi ya fita.

Guraren 11 sae gashi kuma ya kasa haquri ya dawo riqe da ledar magunguna a hannun shi da kuma gorar ruwa had'e da glass cup.

A nn tsayen da yake ya ajiye magungunan kan bedside drawer ya bud'e gorar ruwa ya soma tsiyaya ruwa a glass cup yana cikin hakane yaji kmr motsi tafe a bayan shi juyawar da zae yi ne glass cup ya qwace mai ya fad'i ya fashe ,qarar fashewar glass cup d'in ne yasa Ryynt ta tashi a firgice zata fasa ihu mohd yayi saurin rufe mata baki ya janyota zuwa jikin sa sae duk ta qara rud'ewa tana qoqarin qwatar kanta nn mohd yaje saitin kunnen ta yace"am sorry Ryynt nine"

Ajiyar zuciya ta fitar mae qarfi tare da qara qanqame shi sae faman sauke numfashi take kmr wacce tayi gudu sosai.

Mohd kuwa sae shafa bayanta yake a hnkli nn kawae ya soma jin saukar hawayen ta a qirjinsa yayi saurin d'ago fuskarta yana share mata hawayen yana fad'in "yi haquri na tsorata ki da yawa koh"

A hnkli ta koma kan qirjin sa ta kwanta murya can qasa tace" kaina ke ciwo kuma abu ya shige min a qafa"

Nan ya kai hannu ya kunna wutar d'akin ya riqo qafar ta zae cire mata glass d'in da ta taka tayi saurin riqe masa hannu cikin murya mae kama da ta kuka tace"zan cire da kaina"

Yace"yi haquri bari na cire maki kinji bana son kije baki cire da kyau ba ki bar saura a jikin ki"

Ba yanda ta iya ta gyada masa kai had'e da 6oye fuskarta a qirjin sa shi kuma ya kai hannu cikin hikima da dabara ya cire mata glass d'in a hnkli ba tare da ya karye a jikinta ba snn ya zaro farin handkerchief d'insa ya d'aure mata qafar sbd jinin da ke fitowa.

Sae a snn Ryynt ta d'ago daga kan qirjin sa tana share hawayen da ke kan fuskarta sbd kuka tayi a lokacin da yake cire mata glass.

Mohd ya sake maida ta kan qirjin nasa yakai hannu yana shafa bayanta had'e da yi mata sannu ita kuma ta lafe sosai tana qoqarin komawa bacci ya d'ago ta yace"kar kiyi bacci bari kisha magani tukun kinji"

Ba musu ta gyad'a masa kai shi kuma ya jawo ledar magunguna ya 6alla mata ya bata tasha daga nn ta koma abinta kan bed ta kwanta mohd kuwa na durqushe kan guiwoyinsa a gefen gadon yana shafa goshinta tana kallon sa yace"daga kanki ba inda ke maki ciwo dae koh ?

Tace"eh"

Yace"to yunwa fa ba kya ji?

Tace"um um"

Ta fad'i hakane tare da rufe idanun ta a hnkli

Shi kuma daga haka bae sake cewa komai ba sae hannun sa da ya kai kan cikinta yana shafawa har tayi bacci snn ya tashi daga durqushen da yake ya gyarawa mami kwanciyarta yasa blanket ya rufa musu jikin su.

Ya kwashe glass cup d'in da ya fashe yasa a dustbin ya goge gurin snn ya kashe musu wutar d'akin ya fita yaje d'akin sa wanda da shigar sa yayi tsaye idonsa akan malika da yaga kmr yanzu ta kwanta don ba ma yanda ya barta ba ya ganta nn dae ya basar ya kwanta had'e da kashe bedside lamp.

washe gari tun da asuba sae da yaje d'akin Ryynt ya tashe ta ta miqe tana d'an d'ingishi ta nufi bathroom mohd dake kallonta sae duk bae ji dad'i ba haka dae ya fita ya tafi zuwa masallaci.

Yana dawowa daga masallaci bae zarce koina ba sae d'akin Ryynt ya same ta zaune kan darduma riqe da qur'ani a hannun ta ta bud'e zata fara karatu.

Tana ganin sa ta rufe qur'ani tace"barka da asuba ka tashi lafiya?

Yace"lafiya lau my Ryynt ya kan naki ya daina maki ciwo?

Tace"Alhmdlh gabad'aya ya daina min ciwo"

Yace"mashaa Allah amma kuma qafar ki na damun ki sosai koh, dan naga har ba iya taka ta da kyau"

Tace"eh amma ba wani zafi sosai kmr kar nayi arwala ma sae naji ta sake min ba kmr lokacinda ka tashe ni ba"

Tana mgnr ne yayinda mohd ya riqo kafarta yana dubawa ya tashi tare da fad'in "ina zuwa"

Ya fita bae wani jima ba ya dawo riqe da wani magani ya shafa mata a qafa snn yace"bari na barki kiyi karatun ki koh"

Bata ce komai ba sae d'an guntun murmushi da tayi ta bishi da ido har ya fita.

Da dare guraren qarfe tara da rabi Ryynt ce d'aure da towel iya cinya tana neman kayan baccin da zata saka sae ga mohd ya shigo d'akin d'auke da sallama a bakin sa Ryynt ta kalle sa snn ta amsa sallamar bae qaraso ba yayi tsaye kmr mae fushi yana kallonta tace"yi haquri yanzun nn gani nn zowa kayan bacci kawae zan saka.

Bae ce komai ba har sae da ya qarosa gurinta ya rungumo ta ta baya bakin sa saitin kunnen ta yace"na qagu da yawa Ryynt amma kuma ke sae jamin aji kike kmr nayi miki wani laifin "

Tace" ni baka min laifin komai ba"

To amma shine kika bar ni tun d'azun inata faman jiranki.

Tace"yi haquri to za6a min kayan baccin da zan saka sae mu tafi"

Nan ya ciro mata wata er fincikar riga pink mae kyau wacce ita ta siyo abar ta da suka je dubai,

ya kai hannu zae zare mata towel tayi saurin riqewa ta kar6i rigar sae wani murmushi take tana kallon sa tace "bari naje bathroom na shirya"

Mohd yace"hm jeki yau naga qarewar 6oye min jiki da kike don yau bazan ma kashe wutar d'akina ba"

Tayi er dariya tace"da wasa kake kaima nn ta wuce bathroom ta sako rigar ta fito a yangace ta kama gefen rigar ta tsaya tace"ya ka gani?

Mohd da ya qaraso gurinta ya rungumota tare da d'aura mata kiss kan goshi yace"sosai my Ryynt kinyi kyau"

Kamar da shagwa6a ta kalle sa tace"uhm to rigar fa baka ce na iya za6e ba"

Sae da yaja hancinta d'auke da damurmshi yace"sosai kin iya za6e my Ryynt kuma rigar tayi miki kyau sosai"

Tace"um um fa"

Yace"Allah kuwa"

Tace"nagode bari na saka hijab to"

Yace "kema dae da wasa kike"

Nan ya d'auke ta cak zae fito da ita malika da tun d'azun take la6e a bakin qofa tana kallon su tayi saurin barin gurin.

Ryynt tace"wlh aa da gske nake rigar bata fita ka sani har dae da safe idan zan fito"

Ya sauke ta tare da fad'in "to naji je sako hijabin muje"

Nan taje ta saka hijabin suka fito mohd na rungume da ita a jikin sa har suka isa d'akin shi.

Washe gari guraren qarfe goma na safe Ryynt ce taci kwalliya abinta cikin wata atamfa riga da skirt da sukayi d'as a jikinta tayi d'aurin d'an kwalinta mae kyau tana rataye da briefcase d'in mohd dake rungume da ita a jikin sa yana sanye da milk suit dukkan sunyi kyau sae zuba qamshi suke sun fito daga d'akin shi suka wuce malika dake zaune a falo.

Suna kaiwa qofar fita falon mohd yayi tsaye cike da murmushi yana kallon Ryynt yace"my ryynt ba sae kin fita har waje ba dmn bana so ki wahala kawo jakar koma abinki kije ki kwanta ki huta kinji"

Ryynt ta lumshe ido had'e da sakar masa lallausan murmushi ta miqa masa jakar ya kar6a tare da d'aura mata kiss kan goshi snn kuma yaje kan cikinta ya mata ya d'ago tare da fad'in"sae na dawo"

bye ta mishi snn tace"Allah ya tsare min kai"

Sae da yace"amin"snn ya fita Ryynt ta

juya zata tafi d'akinta sae malika ta gani tsaye a gabanta".

Billy giro😊

[10:07PM, 5/2/2017] Billy giro😊: ```🔮BAZAN BARSHI BA!🔮```

🔮🔮🔮🔮

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.