Complete Hausa Novels

Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Bazan Barshi Ba Part 1 Complete Hausa Novel.docx

Chapter 13 of 56

_*page*_ *```31```*

Malika tayi tsaye sororo sbd tsananin mamaki,mohd kuwa kallon Rynt yake kmr wanda yaga abin burgiewa a tare da ita, sbd a cikin kwanciyar hnkli ta saki mgnr kmr ma ba ita ba.

Rynt kuwa na gama fad'ar mgnr ta juyawar ta zuwa d'aki ,sae a lokacin malika ta saki wani irin zagi ta tafi fuuu!tabi Rynt tana fad'in"cabd'i lallai yau sae kinsan wa kika ta6o,har ni zaki zaga ki kwashe lfy!

Koda ta isa d'akin Rynt tuni Rynt ta rufe d'akinta tasa makulli ta kuma je tayi kwanciyarta akan bed, malika ta shiga sirfa bala'i tana dukan qofa kmr zata 6alle qofa, duk Rynt na jinta tayi banza da ita.

Mohd ne yazo yaja malika yana fad'in"don't mind her xo mu tafi kawai"tace"banni da er iska tambadaddiya idan ba tsoro ba ta fito mana,wlh ta fito!taga yanda ake quliqulin kubra da mutum.

Da qyar dae mohd ya samu ya jata suka bar gurin .

2 days a go

Kwata kwata mohd ya daina zuwa d'akin Rynt dmn zuwa duba lfyrta kmr yanda Abbansa ya tilasta mai, haka kuma bai qara ganin ta fito ba, sam bai damu ba sbd a cewar shi dokar da yasa mata ce tabi.

Malika kuwa tun a rnr da abin ya faru tayi tafiya da yamma zuwa garin kd gun bikin wata qawarta yayinda ta tafi d'auke da alwashin duk ta dawo sae tayi ma Rynt dukan ftr hnkli.

Kwance yake a falo shi kad'ai yana hutawa sae ga mami tazo ta same shi tace"dan Allah yaya ina son naci chocolate"sae da ya kalleta snn

ya tashi zaune tare da zaunar da ita kusa dashi yace"to bari na byr a siyo miki"um um yaya inada shi a d'aki amma hannu na bazai kai inda Anti ta ajiye min ba, to kice Antin ta d'auko miki mana, ai bazata iya bane, meyasa bayan ita ta ajiye? Anti bata da lfy fa, ko abinci ma ta daina ci,kullum sae kuka take tayi ,gashi kai baka zuwa kullum bare ma kasani ynx haka ma tun dazu take son ta tashi amma ta kasa sbd jiri ke d'ibar ta"man yayi shiru yana kallon mami can yace"naji jeki zanzo na duba ta.

Ya jima kafin yake zuwa d'akin don koda ma yaje ya samu har mami tayi bacci sbd dama dare ne, ya sami Rynt zaune kan bed ta had'e kai da guiwa,sallamar sa yasa ta d'ago wanda kallo d'aya ya mata ya fhmci tana jin jiki,

fararen idanuwnta duk sunyi jajir yayinda eyelashes d'inta sukayi warawara sbd hawayen da suka ta6a su ,

snn fuskarta fayau ba kwalliya kmr kullum,maida kanta ta koma yi tsakiyar qafafuwanta shi kuma yaje kusa da ita ya zauna kan bedside drawer yace"me yake damunki ne?tayi shiru kmr bata jinsa yace"kina jina fa"tace"nima ban sani ba"yace"to ki shirya zan miki allura ne"tace"bana so"baice mata komai ba sae tashi yayi yabar d'akin,Rynt kuwa sae tashi take sonyi amma ta kasa sbd jiri wacce dama idan tana zazza6i haka yake mata.

Can ta samu ta tashi tsaye se kawai jiri ya d'ebe taje zuwa fad'uwa,bata fad'in ba sae jin tayi an kamata, a firgice ta juyo tare da fad'in"baffa"sae kawai taga ashe mohd ne riqe da ledar magunguna a hannun shi, wani irin baqinci taji don ta d'auka ko Baffanta ne ya dawo gareta kmr yanda take mafarki a kowane dare,hawaye ne suka zubo mata bata damu da ta share ba sae jaye jikinta daga nashi tayi snn ta koma ta zauna, mohd kuwa ya d'aura ledar magunguna kan bedside drawer yaje ya d'auko gorar ruwa da cup snn yaje ya zauna kan gadon tare da tsiyaya mata ruwa a cup, ya bata ta kar6a shi kuma ya shiga 6alle magunguna ,ya bata taqi kar6a sae ruwa takai a bakinta tana sha, tayi saurin ajiye ruwan sbd wani irin abu da taji cikinta nayi na rashin abinci ga ruwa ta kora akai, nn take taji amai ta yunqura zata tashi amma jiri bai barta ba tayi saurin dafa kan gadon gudun kar ta fad'i, mohd yakai hannu zai taimaka mata, tayi saurin dakatar dashi ta hnyr cewa"bana so"bai kula ta ba sae janta yayi suka tafi bayi don ya fhmci gab take da kwaro aman, suna shiga ta warce hannunta daga nashi ta dafa washbasin tana kwara amai a ciki,kalar aman ya soma tsorata mohd yace"ke wnn aman fa? wani kallon takaici ta watsa mai tare da fad'in" juna biyu nake d'auke dashi ko da wata matsala ne!

d'an shu'umin murmushi mohd yayi tare da kauda kansa gefe nn idon sa ya hango masa bayan hijabin Rynt da yayi staining da jini, yakai hannu ya riqo hijabin ya nuna ma Rynt snn yace"ya haka kuma keda ke d'auke da juna biyu sae na sami wnn qazantar a hijabinki ko kuma jin ciwo ne? Kunya Rynt taji sosai tayi saurin kauda kanta tare da fizge hijabinta ta 6oye gurin da yayi staining,murmushi yayi tare da fita bayin.

Hannu takai kan mixer tap ta kunna famfo ta kuskure bakinta ta wanke washbasin taje

a daddafe ta saka key a qofa snn ta cire hijabi har kayan jikinta, ta saka su a bucket ta zuba ruwa da klin bata iya wanke wa ba sae wanka tayi koshi da qyar taga ta samu ta kammala ta d'aura towel ta fito toilet corner ta jawo qaton hijab d'inta har qasa ta zuba snn ta fito,ta sami mohd zaune yana jiran fitowarta wanda baiji fitowarta ba sae qamshin sabulun da yaji sosai hkn yasa ya d'ago ya ganta,ya tashi tare da fad'in "idan kin shirya zan dawo"bata bar sun had'a ido ba ta kauda kanta gefe har sae da taji ya fita snn ta nufi wardrobe ta shirya taje tayi kwance tare da jan blanket ta rufe jikinta har kanta, sae ga mohd ya shigo d'akin d'auke da freshmilk da kuma plate d'in abinci don ya fhmci aman da tayi na yunwa ne.

Yaje tare da ajiye abincin kan bedside drawer snn yace"ga abinci nn kici snn kisha magani"

Nn ya juya zai bar d'akin tace"ni bana cin abinci ka koma dashi"

Ya dawo tare da fad'in "dolen ki kici don ba ajiye ni kikayi ba da zan kawo maki abu na koma dashi"

Nn ya tilasta ta kan dole ta tashi zaune, ya dungura mata plate d'in a jikinta ,takai hannu ta ture plate d'in tace"nifa na gaya ma bazan ci ba" kallonta kawai yayi bai ce mata komai ba sae hannuwan rgrsa da ya shiga linkewa shaye da toka yayinda Rynt ke kallon sa da mamaki kaddai d'ura mata abincin zai yi ta qarfi,tana kallo ya d'auki plate d'in ya d'ibi abincin a spoon ya nufo bakinta dashi kmr zatayi kuka tace"nace maka bana so dan Allah ka barni"daga nn kawai ta fara kukanta a hnkli ba don komai ba sae don tuna baffanta da tayi wanda sam baya takura ta akan komai. Haqiqa tayi rashi babba wanda har abada bazata sami kmr sa ba.

Tayi minti biyar tana kukanta mai ban tausayi mohd sae kallonta yake wanda ga dukkan alama ta fara bashi tausayi ,a hnkli ya sauke numfashi snn yace"idan kinci zan barki ki koma islamiyya kuma zan barki kije gidan inna"da sauri ta kalle shi snn tayi magana cikin muryarta ta marasa lafiya tace"dagaske kake?ya gyad'a mata kai snn takai hannu takar6i plate d'in abinci tana mai kallon shi tace"ka tafi kawai zanci"

ba musu ya tashi ya fita don ya fhmci bata iya cin abinci a gaban idon sa ne.

Sae da yayi wanka ya kuma yi shirin bacci snn ya dawo d'akin ya samu taci abinci kmr yanda tace ta kuma sha duk wasu magunguna da ya 6alle mata,yakai hannu ya d'auki plate wanda ke d'auke da ragowar abinci snn ya kalleta sae sharar baccin ta take cikin natsuwa.

Wayar sa ce tayi qara ya saka ta a silent snn ya d'aga had'e da fita d'akin.

Washe gari Alhmdlh jiki ya fara yiwa Rynt sauqi don da taje wanka har kayan da ta jiqa cikin bucket jiya ta wanke abinta tas taje ta shanya.

Byn ta shirya snn tayi breakfast ta koma ta kwanta sbd zazza6in bai qarasa sakinta ba,ba jimawa bacci ya kwasheta sae ga mohd ya shigo d'akin riqe da hannun mami,yaje kan bedside drawer ya zauna mami kuwa ta hau kan gadon tana fad'in"anti ma tayi bacci"

Komai mohd bai ce ba sae hannun sa ya d'ora kan goshin Rynt,sae kawai yaga ta bud'e idanuwanta a hnkali ta sauke su akan nashi, ba tare da ya sauke hannun sa da ke kan goshinta ba yake tambayar ta "jikin fa?

Billy giro

🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮🔮

[10:00PM, 5/2/2017] Billy giro😊: [1/20/2017]

🔮```BAZAN BARSHI BA!```🔮

🔮🔮🔮

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.