Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TSUTSAR NAMA BOOK 1.txt
Chapter 99 of 264
💥💥💥💥💥
Nutsuwar data samu game da shawarar Hajiya Rubayya ya sata ajiye batun hukunta Samraah. Sai ma zuciyarta data gama tsara mata fara shirinta a yanzu. Zuciyarta fes ta fito falon. Arwa da Muhsin kawai ta samu a falon suna kallo. Sai masu aiki dake É—an kai kawo na tsaftace sa duk da babu wani datti. Komawa tayi da baya zuwa É—akin Azizat. Kwance ta sameta da waya a hannu tana charting, sai Bahijja dake cikin closet É—inta tana maida kayan data watso Æ™asa. Batare data kalla uwar tata ba ta ce, “Mammah any problems?â€.
Maimakon taji haushin yanda Azizat É—in tai magana a tsaitsaye sai ma tai murmushi. Cike da kulawa takai zaune a kusa da ita tana shafa kanta. “Babu komai Baby na. Aikenki dai zanyi sashen Yayankuâ€.
Da sauri Azizat ta É—ago fuskarta da murmushi. Sai kuma ta tura baki tana mai haÉ—iyewa. “Mammah bayan Yayan ya sake fita shi da tawagarsa. Ina kuma Æ™yautata zaton wata tafiyar ma ya sake yiâ€.
Da mamaki Hajiya Mammah ke kallonta ta ce, “Tafiya kuma? Bayan yau ya dawo?â€. Sai kuma ta dauki wayarta ta shiga daddanawa batare data jira amsa ba. Kunnenta ta kai. Batare da yin ko sallama ba ta ce, “Kuna ina?â€.
Cikin girmamawa da ga can aka bata amsa da, “Gamu a airport zamu wuce Chainaâ€.
“What! Shine ba labari?â€.
“I'am sorry Maa. Da alama tafiyar gaggawace ta tasoma Boss ne.â€
Ƙwafa tayi, tare da yanke kiran. Batare da tace komai ba kuma ta miƙe tai ficewarta. Da kallo Azizat ta bita sai kuma ta taɓe baki itama ta cigaba da charting ɗin ta.....
✨✨✨✨
A ɓangaren Paah shima hankalinsa ba'a kwance yake ba. Dan tun randa abin nan ya faru bai sake saka samun ko kallon arziƙi daga ɗan nasa ba. Ko jiyyar kwanaki uku da yay a gidan idan ya shiga dubasa sai ya ƙirƙiri barcin ƙarya. Yana samun sauƙi kuma ya tattara ya bar musu gidan. Sai yau ne matarsa ke sanar masa Awwab ɗin ya dawo gida. Shine dalilin barowarsa inda yake a gaggauce yazo gidan. Kai tsaye sashen Awwab ɗin ya nufa, amma tun kafin ma ya shiga Hayatu daya samu a compaund ke sanar masa Awwab ɗin na sashen Hajiya Babba.
Sashen Hajiya Babban yaso nufa shima. Sai dai hakan ya gagara saboda shakkar haÉ—uwar tasu. Dan yasan a rayuwa Awwab bai haÉ—a al'amarinsa dana mahaifiyarsa da komai ba. TaÉ“ashin da Hajiya Æ™arama tayi ne ya sashi dawowa a hayyacinsa firgigit. Cike da mamaki ta ce, “Lafiya kuwa Abban Awwab?â€.
Numfashi ya sauke mai Æ™arfi, sai kuma cikin damuwa ya amsa mata da, “Ba komai†yana miÆ™ewa. Da sauri ta riÆ™o hannunsa. “Ya zakace babu komai bayan ga damuwa Æ™arara a fuskarka? Nasan dai bazai wuce akan fushin da Awwab yake ba. Ni a ganina mizai hana kaje ka samesa. Sai ka lallashesa dan yaron nan ya fimu gaskiya, shiyyasa kullum nake nusar da kai illar biyema Addah a gidan nan. Dan koba komai Hajiya Babba uwar Æ´aÆ´anka ceâ€.
Wani mugun kallo ya watsa mata. Sai kuma ya fisge hannunsa batare da ya tanka mata ba yaja tsaki. Fuuu ya fice abinsa batare da ko waiwayenta ba. Da kallo kawai ta bisa itama. Sai kuma ta girgiza kanta ranta duk a dagule....
💕💕💕💕
*_INDIA_*
Kai kawo take kawai tana kuka ita kaÉ—ai a É—akin, a kallo É—aya zaka fahimci tana a cikin matsanancin tashin hankali da bai da misali. Kanta ta shiga girgizawa cike da sakin zantukan da suka zame mata sirrinta cikin sambatu. “Kai ina bazai yiwu ba. Bazan halaka yarona da hannuna ba wlhy. Saimah bazai yiwu ba. Na tafka kuskuren farko bazan bari na sake aikata na biyu baâ€. Ta Æ™are maganar tana rarumar wayarta. Number Æ™anwarta Saimah dake Dubai ta shiga lalubowa. Cikin sa'a kuwa ta sameta a sama-sama dan ko a jiya sunyi waya. Kira ta danna mata, sai dai harta fidda rai da za'a É—auka tana gab da tsinkewa aka É—aga.
Mamy da zuciyarta ke bugawa da sauri-sauri tamkar zata fito ko sallama bata tsaya yi ba ta ambaci sunan yar uwar tata kai tsaye.
“Saimah!â€.
Cike da mamaki da shiga tashin hankali ta amsa mata daga can. Sai kuma ta É—ora da faÉ—in, “Lafiya kuwa Aunty najiki cikin tashin hankali? Kar dai kice min mun rasa Mansoor ne?â€.
Wani irin suka Æ™arshen zancen Saimah yayiwa Mamy a zuciya. Dan haka a fusace ta bata amsa da, “Oh haka kuke zaman jiran ji kenan shiyyasa kika saka Æ´arki ta kirasa a waya ta tada masa da hankali da yake bata da isashiyar tarbiyya. To bai mutu ba, ba kuma zai mutu a sanadin auren shashashar É—iyarki ba in sha ALLAHU....â€
A fusace Saimah ta ce, “Wace irin magana ce wannan kuma daga tambaya Sadiyya?â€.
“Kin fini sani Saimah. Nace kin fini sani. Duk wata masifa kece ummul ana isin sakamu cikinta. Kai haba nagaji bazan iya jurewaba gaskiya. Maganar auren Mansoor da Husnah babu shi tunda baya soâ€.
Wata shegiyar dariya Saimah ta sanya daga can. Sai da tayi mai isarta sannan ta É—ora da faÉ—in, “Wannan shine kuskure mafi muni da zakiyi a rayuwarki kuwa Sadiya. Dan in har Mansoor zai ce bazai zauna da Husnah ba to kemafa ki shirya tsaff dan auren shekara talatin da takwas zai guntule shima. Zan sanarma mijinki da É—anki abinda kika aikata game da auren Mansoor na farko. Na kuma sanarma duniya komai. Ya rage naki yanke hukunci. Kin san kuma shima Maash É—in ba kanwar lasa bane dan ya tabbatar miki da hakanâ€. ÆŠit-É—it ta yanke wayarta.
A matuƙar fusace Mamy tai wani irin masifar yin cilli da wayarta. Sai kuma ta zube a saman gadon ɗakin hotel ɗin tana fashewa da kuka mai masifar ƙarfi...
“Mi kike É“oyewa Halimatu?â€.
Firgigit ta juyo tana kallonsa. Sai kuma ta mike zumbur tana goge hawayenta jikinta na karkarwa. Cikin rawar murya da kaÆ™aro murmushi take girgiza masa kanta. “Abban Attahir yaushe ka shigo? Dama kana É—akin nan? Ai ban san kana nan ba wlhy....â€
Hannu ya É—aga mata. Dole tai shiru. Cikin É“acin rai ya sake maimaita mata tambayar farko. Sake daburcewa tayi. Harshenta na sarÆ™ewa ta ce, “Ba komai. ALLAH ba komai. Ko kaji wani abu ne?â€.
Maimakon amsa mata idanunsa kawai ya dasa mata. Sai kuma ya jinjina kansa batare daya sake tanka mata ba ya juya ya fice abinsa. Gaba É—aya ji Mamy tai É—akin na juya mata tsabar tashin hankali. Birkicewa ta sake yi tamkar sabon kamun hauka. Itako idan har Abban Attahiru yaji wayar nan tata ta shiga uku. Wannan wace kalar rayuwa ce ta jefa kanta da É—anta a ciki saboda kwaÉ—ayin abin duniya. Wane irin son zuciya ne? Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un...
Da ƙyar likitoci suka iya controlling sabon yanayin da Mansoor ya shiga. Dan a baya baya aman jini sam. Gashi yanzu iyayensa sun sake jangwaɓo abinda yafi na farko. Bayan dawowa a hayyacinsa hana kowa akai shiga ganinsa har na tsawon kwanaki uku. Sai da suka tabbatar komai ya dawo normal sannan suka barsu ganinsa bayan anja musu dogon gargaɗi.
Sunji farin cikin samun lafiyar tasa. Sai dai bai kula kowa a cikinsu ba har suka gaji da zama suka fito saboda adadin lokacin da aka basu ya cika. Suna fitowa Dad yay wucewarsa, dan har yanzu babu jituwa tsakaninsa da Mamy. Ya tattarata ya watsar da al'amarin ta. Bai kuma sake mata magana akan komai ba. Itako duk wanda ya kalleta yasan bata a cikin hayyacinta a kwanakin nan. Dan komai ya gama Æ™wace mata. Ta rasa ina zata kama danta mafi soyuwa a ranta da mijinta na neman kuÉ“uce mata a dalilin son zuciyarta........âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.