Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TSUTSAR NAMA BOOK 1.txt
Chapter 70 of 264
â¤ï¸â˜…★★â¤ï¸
Tsakanin Halime da Dady dai tun wannan ranar ba'a sake haɗawa ba. Dan washe gari uban aiki taci kamar kurar wasa. Dan kaf girke-girken da aka tanadama Alhaji Rufa'i itace tayi su. Tayi kuma gyaran gidan musamman falon tarar baƙi da Mom ta sakata ƙalƙalewa kamar za'a canja bangonsa. Ita dai bata san dalilin uban aikin da taci ba sai da yammaci take ji a bakin auta wai Baby ce tayi baƙo. An kuma ce ta saka hijjab da niƙab takai masa abinci falon baƙi. Bata da yanda zatai dole tabi umarnin Mom tayi shigar da akace taje takai komai. Da ɗunbin mamaki ta fito mara misali. Yayinda taketa jarumtar danne dariyar dake cinta har sai da ta shiga ɗakinta. Bata tsaya a tsakar ɗakin ba ta shiga toilet ta rufe kanta duk dan kar a jita sannan ta fara kwasar dariya harda hawaye. “Kambu taƙashin nan. Yanzu ni Halime ina Baby ta samo wannan tulun giyar, wlhy cikinsa kamar an kifa masakin Baba Lauren gidanmu na Daudawa. Gashi sanƙameme kamar samudawan da suka zo mana a labari. Tab ɗi jan, daga dai ganin wannan kasan sai dai a so shi dan kuɗi duk da dai ƙyaƙyƙyawa ne a fuska.†kiran da Mom ke ƙwala mata ya sata fita a guje dan tasan idan tai na uku sai ta sha maruka a wajenta.
Gab da magrib taji ihun Bibaa da Abbas ya cika gidan. Ta kitchen ta kasa kunne sai ta jiyo ihun nasu wai duk murna ne akan Alhajin nan ya bama Baby makulin mota, tare da alƙawarin kujerar maka gareta da Mom da Dad da kuma Abbas, su kuma su Bibaa da Auta da Nabil yay musu ƙyautar wayoyi iphones. Hakan dai na nufin su duka banda Yaya Musaddiq bawan ALLAH kowa ya samu alkairi daga Alhaji Rufa'i. Baki ta yaɓe ta cigaba da aikinta. Daga haka bata sake bi takansu ba sai washe gari da kakarsu tazo take jin har ƙyautar kuɗi yay ma yaran gidanta itama wai naira miliyan ɗaya. Itama kuma kakar tasu harda ita a zuwa saudia, da yaje gidanta kuma ya bata waya mai ƙyau ƴar dubu ɗari biyu harma ta sayar da ita yau. Sosai Halime ta jinjina kwaɗayin wannan mutane da mamakin maganganun da taji suna tattaunawa. Dan sai da Mom ta farga da ita sannan tasha maruka aka korata waje, daga haka bata san mi suka ƙarasa tattaunawa ba.
WASHE GARI kuwa bata ma san lokacin da Mom ta fita a gidan ba tare da Baby. Sai Bibaa da Auta da suka wuce makaranta. Shi dama Abbas ba'a sakashi a lissafin gidan. Yaya Musaddiq kuma ta lura jiya kamar bai kwana a gida ba. Tana a falo tana shara da raira waƙarta cikin zazzaƙar muryar nan tata taji kamar ana kallonta. Ɗan jim tayi cikin nuna tsarguwa. Sai kuma ta cigaba da shararta amma ta daina waƙar da take rerawar ta (kwanana ya kusa ƙarewa a gidanmu zan tafi ɗakina. A gidan mijina zan rayu zaman kaɗaici ya kusa yankewa).
Cikin sauke ajiyar zuciya da rashin jin daÉ—in daina raira waÆ™ar tata Abba ya Æ™arasa fitowa daga jikin Æ™ofar É—akin barcinsa da yake maÆ™ale.........âœï¸
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ðŸ˜ðŸ™_*
*_Typing📲_*
*_ðŸ›TSUTSAR NAMA....!!ðŸ›_*
_(Itama nama ce)_
_ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»_
_ð‘©ð’ð’𒌠ð’•ð’˜ð’_
_ð‘·ð’‚ð’ˆð’† ð’•ð’˜ð’†ð’ð’—ð’†_
__________
Toh Nazo maku
Da kayan arziki
Kudai kunsan mata sai da gyara
Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta
A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE
Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne
Muna da
Shedaniyar gumba
Gumba mai saying
Garin mai kabbara
Mai dalalan miyau
Wayyo dadi
Mai bunsuru
Dan jarida
Soyayya dole
Bakin kyalle
Tadire ta girke
Gumba mai likkafani
Maza taye
Zumar kwakwa
Zumar ridi
Zumar dabino
Zuma mai ma'ul ijaba
Farin jini
Mallakoki
Gumba kalla kalla da dai sauran su
A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba
Ga kuma maganin slimming
Gyaran nono
Maganin hips
Maganin Kara kiba
Da dai sauran su
Kayan mu tested and trusted ne
Muna maraba da masu siyan Daya ko sari
Muna Nan cikin garin kaduna
Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah
Ni ce taku har kullum
AMINA GACHI
07034404975
CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE
KADUNA
Phone no 07034404975
____________
.......Ƙamshin turarensa mai armashi daya bigi hancin Halime ya sata ɗagowa a zabure. Hakan yay dai-dai da isowar Abba inda take. Aiko suka kusa cin karo. Tsalle tayi baya jikinta na rawa. Tako tafi zata zube ƙasa yay saurin riƙota. Rawar jikinta ce ta ƙaru sosai sai faman zazzare idanu take tamkar bazazzage a hannun kanawa (😂😜lol).
“Please kinga calm down nutsuâ€. Abba ya faÉ—a da sauri ganin yanda duk ta gigice. Kasa nutsuwar tai, sai ma mutsu-mutsun son Æ™wacewa da take kawai daga hannunsa. Sakinta yay, aiko ta kwashi tsintsiyarta ta zura da gudu hanyar kitchen dan nan ne kawai takema kallon wajen É“uya. Murmushi Abba ya saki mai haÉ—e da Æ™aramar dariya yana girgiza kansa da jinjina wawtarta. Sai kuma ya sauke ajiyar zuciya mai kauri zuciyarsa na sake tabbatar masa da yanayin dake son hawa kansa batare daya shirya ba. Dan duk yanda yake son Æ™aryata zuciyar tasa hakan ya gagara. Dole ya haÆ™ura a yau tare da tabbatar da da gaske fa son yarinyar nan da ko sunanta bai sani ba yake. Lallai yasan shima ya taro match babba, mai aikin gidansa fa. Randa Jalilah tasan wannan sirrin nasa sai abinda ALLAH yayi ai. Maybe yankan raguna zata musu shi da yarinyar nan....
📯📯📯📯📯
Zancen Bahijja ya tabbata. Dan kuwa bata dawo ba sai bayan sallar magrib. Haka ta shigo idanunta balo-balo alamar taci kuka. A take zuciyata ta motsa. Sai dai bance da ita komai ba ganin itama ta dake tana min murmushi. Dan cike da kulawa ta shiga faÉ—in, “Lah baki je falo ba bayan gasu A'i can duk sun dawo su tun É—azun. Su Mama Balki ne kawai su sai anjima saboda girkin masu gidan kowa da abinda yake so. Balle ma Uncle Boss yana gida aikin yafi tsamari kodan gayyar yaransaâ€.
Dariya sunan data faÉ—a ya bani, wai Uncle Boss. Amma sai haka kawai naji gabana ya faÉ—i, cikin Æ´ar in ina nace, “Waye Uncle Boss kuma?â€.
Numfashi ta sauke mai nauyin gaske. Sai kuma tai murmushi da faÉ—in, “Uncle boss shine gidan dama Æ™arfin ikon kidan baki É—aya. Shine babban É—a a gidan kuma. Bari dai kada na shagala da yawa banyi sallar magriba ba, har an kusa isha'i. Kuma Malam da anyi isha'i idan ka makara zuwa makarantar dare duka yake yiâ€.
Da kallo kawai na bita dan babu abinda na fahimta a zancen nata. Sai kawai na cigaba da lazimina harta fito ta kabbara salla ban sake cewa komai ba. Tana idarwa ana kiran sallar isha'i. Dan haka muka tashi a tare muka kawota. Muna idarwa ta miƙe ɗauke da Alkur'ani tace na taso muje wajen karatu. Ban musa mata ba na tashi na bita kuwa. Mun samu duk kusan ƴammatan nan sa'anninta suma sun fito, a tare muka rankaya waje. Can muka nufa cikin wajen wasannin nan dake ƙwanyar da hasken lantarki tamkar rana. Hakama tsakar gidan yake tako ina. Ga hasken ya sake ƙawata gidan tamkar ba'a duniya ake ba. Mun samu malam har ya iso, dan haka babu wani ɓata lokaci muka zazzauna a ƙatuwar dardumar dake shimfiɗe a wajen. Yayinda shi kuma yake zaune a saman kujera abinsa. Kamilun mutum dattijo. Dan shekarunsa da gashin fuskarsa zuwa kansa dake fari fat ya isa tabbatar maka da shi ɗin ba yaro bane ba. Mun gaishesa a tare, ya amsa mana da kulawa kafin a fara karatu babu ɓata lokaci dan kowa ya riga yazo. Naji daɗin karatun, duk da kuwa nayi sauka tuni. Kusan awarmu ɗaya da rabi dan sai takwas da kusan arba'in muka tashi. Sai dai yanata kallona amma baiyi magana ba balle tambayar dalilin shigowar baƙuwar fuska ajin karatunsa. Can sashen muka koma, sai dai wasu basu zauna ba suka shiga canja uniform wai zasu koma can sashen su ƙarasa ayyukansu, ciki kuwa harda Bahijja da tafi kowa rawar jikin komawa. Sun bani matuƙar tausayi, amma dai bance komai ba dan bani da abin cewar. Shiru babu wanda ya dawo a cikinsu ni dai har na fara hamma saboda sabon barcin wuri da nayi tun fil azal. Mama Balki data rigasu dawowace tace naje na kwanta. Babu musu na miƙe na wuce ɗaki kuwa, dan ni kaina nasan ina buƙatar barcin, amma ba lallai tunanin dake danƙare a zuciyata ya barni yinsa ba. Koma dai yaya ne zanyi yaƙi da zuciyata wajen ganin na yisa kodan na samu nutsuwar fuskantar abinda ke gabana. Dan Alhmdllh, ɗan zuwa islamiyyar nan ta ɗazun da nayi sai nake jin kamar yanayin da nake jin kaina sanda nake a gidan Hajiya ya fara sakina...
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.