Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TSUTSAR NAMA BOOK 1.txt
Chapter 50 of 264
💢💢💢💢💢💢💢
Agogon dake bangon É—akin ta sake kallo a karo na barkatai, sai kuma ta ja sirrin tsaki. ÆŠagowa mijin nata yay ya kalleta. Ganin yanda ta É—auke kai gefe ya sashi faÉ—in, “Lafiya kuwa kike Safina?â€.
Kanta ta É—an girgiza, cikin nuna damuwa ta ce, “Ba komai. Yaron nan ne dai al'amarinsa ya fara bani tsoro. Kalla agogo maganar É—aya ake na dare amma har yanzu bai shigo gidan nan ba. Hakan na nufin a asibitin zai kwana ko mi?â€.
Agogon ya kalla shima, sai kuma ya É—auka wayarsa batare da yace mata komai ba. Kunnensa ya kai alamar kira yake bayan yay Æ´an danne-danne. Ana É—agawa kuwa bayan amsa sallama ya ce, “Ɗan uwanka bai dawo gidan nan bane har yanzu Attahiru?â€. ÆŠan jimm yay alamar saurare. Sai kuma ya janye wayar batare da ya sake cewa komai ba. Kallonsa Mamy tayi cikin Æ™agara ta ce, “Bai dawo ba ko?â€. Kansa ya jinjina mata alamar eh. Zai cigaba da aikinsa a computer ta dakatar da shi. “Ya kuma zaka cigaba da aiki ka dadynsu? Ka kirashi É—an ALLAH mana muji yana inaâ€. Kafeta yay da ido na tsawon sakanni. Sai kuma ya girgiza kansa da faÉ—in, “Mansoor yaro ne Æ™arami Safina. Karki manta shirin É—aura masa aure fa ake nan da kwanaki huÉ—u. Kinga ko ai yasan abinda yake koâ€.
“Nifa gaskiya Daddynsu bana wani jin batun auren nan a raina yanzu. Kuma dama can kaima kasan dan ya nace ne akan yarinyar nan yasa ka zuba ido da kuma dagewa da nayi nima saboda yarinyar ta shiga raina da farko. Amma magana ta gaskiya maganar matar kawunta ta É—azun ta shigeni matuÆ™a. Shiyyasa tunda na dawo gidan nan naketa auna abubuwa. Dan zancen abin a duba ne fa, musamman idan muka tsaida hankalinmu muka nazarci komai a yanda yakeâ€.
Idanu kawai ya zuba mata kamar zai cinyeta da su. Itako ta É—auke kai tana wani kum-kum da fuska tabbacin zancen nata fa tun daga zuciya ne.
“Safina kin san kuwa mi kike faÉ—a? Kin san fa yanda É—anki ke matuÆ™ar son yarinyar nan. Idan har a baya na kasa hanashi dake kanki a yanzu mi kike tunanin zan iya? Naga kece kika zaÆ™e da faÉ—ar Æ™yawawan halayyar yarinyar a baya duk da ni na nuna batai min ba. Ina baki shawarar kawai ki bisu da addu'a kamar yanda kika saba tun farko. Maganar matar kawunta kuma ai ba lallai ne ya zama gaskiya ba. Tunda ba'a san wani kalar kidnappers ne suka kamata ba.....â€
“Oh amma yallaÉ“ai su Kidnappers É—in har suna da wani banbanci da juna ne?. Ai duk wanda akace kidnapper to Kidnapper É—inne kawai babu wani ba rabe a ciki. Na kula yanzu ba gane maganata kake ba, bayan kuma ada ba son yarinyar kake ba, ban san miya canjaka a yanzu ba kuma. Amma dai ka zauna kayi nazari kaima. Wlhy sam babu alamar wahala a tattare da yarinyar nan. Sai ma uban haske da Æ™yau data Æ™ara duk da kuwa sau biyu na taÉ“a ganinta ido da ido. Amma ai biye nake da program É—inta duk sati a gidan tvn su.â€
Shi kam dai Dad É—in su Mansoor yama kasa magana. Dan mamaki ma da al'ajabi matar tasa ke bashi yau kam. Sai yake ganin kamar ma ba ita ba. Irin wannan kafiya haka har ina kuma. Anya kuwa ba wani ne ya zugata ba?. Bashi da mai bashi amsa. Dan haka ya girgiza kansa kawai yana Æ™oÆ™arin manyan abubuwan dake ransa tare da haÉ—iyesu a zuciyarsa da ga shi sai UBANGIJINSA. Gudun damuwarta saboda tanada hawan jini ya sashi sassauta nasa yanayin, cike da kulawa ya ce, “Tom naji zanyi nazari kamar yanda kika ce in sha ALLAH. Kuma zan yi bincike. Shima É—an naki bari na taÉ“asa a waya. Ki kwanta ki huta kemaâ€. Kafin ma tace wani abu ya É—auka wayarsa ya fara Æ™oÆ™arin kiran Mansoor........âœï¸
_Tofa wata sabuwa masu karatu🥱_
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ðŸ˜ðŸ™_*
*_Typing📲_*
*_ðŸ›TSUTSAR NAMA....!!ðŸ›_*
_(Itama nama ce)_
_ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»_
_ð‘·ð’‚ð’ˆð’† ð’‡ð’ð’“ð’•ð’š ð’‡ð’Šð’—ð’†_
......Yana kai wayar kunnensa dai-dai nan ma yake jin horn ɗin motar Mansoor ɗin da ƙarar buɗe gate. Wayar ya sauke tare da ajiyar zuciya ya ce, “To Alhamdullah gashi can ma ya dawo ai. Sai ki kwantar da hankalinki
Ajiyar zuciya Mamy ta sauke kuwa. Ta yunÆ™ura zata miÆ™e Dad É—in ya zuba mata ido. “Ina kuma zaki?â€. “Zanje na duba shi ne mana. Kofa abincin dare baici ba. Kasanshi kuma da abinci, inba tsaresa akai ba ba wani son ci yake baâ€.
Kai Dad É—in ya girgiza. Sai kuma ya ce, “Uhm kinga Safina zauna Pleaseâ€. Babu musu ta koma ta zauna. Sake cemata yay “Kwanta sai da safe. Tunda dai Mansoor ba jariri bane balle kice baki gama rainonsa ba.†tasan halin mijin nata dan haka bata sake magana ba kuma. Sai dai zuciyarta gaba É—aya tana akan son sanin a wane hali É—an nata yake ciki. Amma tunda yace bazata je ba to bata isa fitarba kuwa. Shima dai hankalinsa ya sake maidawa ga aikinsa bai sake bi takanta ba kuma. Ga shi ya haÉ—e fuska dan bama ya son tace zata roÆ™esa ko ta takura masa da batun auren Mansoor É—in kuma.....
💞🌟💞🌟💞🌟💞
Washe gari kamar yanda doctor ya faɗa aka sallameni. Gwaggo Gudidi taso wucewa da ni can Dawanau gidanta amma Yaya Musaddiq ya roƙeta kan ta barni na koma can gidan ɗin. Tunda har Mansoor yayi magana kan baya son a ɗaga bikin nan a yanda yake koda na kwana ɗaya ne kawai ayi a wuce wajen. Ya kamata kuma muje can gidan Abba a ƙarasa komai daya kamata kada halin Mum ya dameta. Badan Gwaggo taso hakan ba ta yarda.
Tarba muka samu babu yabo babu fallasa da ga Mum. Hakama su Baby na zaune a falo amma babu wanda yay min sannu ko nuna farin cikin dawowata garesu. Sai auta ne ya tsillo da gudu ya ruÆ™unÆ™umeni. Duk da miskilancin yaron sai da ya furta, “Adda nayi kewarki. Adda Bibaa tace kin mutu bayan sake ganinki ba ashe Æ™arya take minâ€.
Murmushi kawai na masa tare da shafa fuskarsa. Yayinda Gwaggo ta riÆ™e haÉ“a da faÉ—in, “Ta mutu kuma? To in ALLAH ya yarda ba yanzu ba, mu bazamuga mutuwa ba sai alkairi nan da kwana huÉ—u. Ke kuma baÆ™in halin naki sak na uwarki dai ashe, da wani shegen goshinki kamar jirgin tsallake ruwan bagwaiâ€. Ta Æ™are maganar tana nuna Bibaa data tura baki gaba zomomo. Na zata Mum zatayi magana. Sai naji shiru ta dai sake tsuke fuska. Ni dai sai ma na yunÆ™ura na nufi bedroom É—inmu dan so nake na É—an watsa ruwa ko zanji daÉ—in jikina. Yanda na tadda É—akin kaca-kaca sai da Æ™irjina ya buga. Abu sai kace turken dabbobi. Wai ni yaushe Bibaa zatayi hankali ni Samraah. Na jima tsaye zuciyata cike da takaici ga Æ™yanÆ™yami dan bazan iya zama a É—akin ba. Dole na juya na fita cikin Æ™arfin hali da son Æ™arfafa kaina. Har yanzu duk suna a falon, Gwaggo Gudidi tai saurin faÉ—in, “Ya kuma kika fito Samraatu lafiya dai ko?â€.
Kaina na jinjina mata a yanayin rashin Æ™arfi jiki, cikin yamutse fuska na ce, “Gwaggo zan É—akko kayan shara ne É—akin yayi datti ina jin Æ™yanÆ™yamiâ€.
Dukansu sai da suka É—ago suka kalleni. Yayinda Gwaggo ta riÆ™e haÉ“a da faÉ—in, “To kaji kuma wani sheÉ—ancin kuma, yanzu duk waÉ—an nan zagada-zagadan Æ´an matan uwa wa Æ´an matan amarya a gida ashe hotiho suke. Yo ni dama tunda na shigo naga gidan yamun wani harmutsai a ido nasan ana Æ™waÉ“a hauka dan har bashi-bashi da tsami-tsamin dauÉ—a nake shaÆ™owa ma. Yanzu ke Julaila kike ko mima oho miki bayan koyama Æ´aÆ´anki rashin kunya abinda zai taimaki rayuwar tasu ma kin tauyesu basu iya ba. Komai kun tattara akan marainiyar ALLAH. To wlhy ba mugunta kikai mata ba idan ma ke haka kike tunani, su waÉ—an nan da kike gani Æ´an hutu a gabanki su kika kashewa rayuwa, dan su zasu gurji kan ubansu nan gaba kaÉ—an. Zaku ma ki tabbatar da hakan ke da su ranar da tusa ta Æ™arewa bodari, É—iya mace bata iya komai ba ai bata cika mace ba wlhy, babu kuma namijin da zai juri zama da ita, idan ma ya haÆ™ura ya jure dan yanada kuÉ—in biyan wasu suyi to bazata taÉ“a daraja a idonsa ba dan wataran ko shine Æ™aruna akan kuÉ—i zai so matarsa ta masa hidima. Kai ai wlhy baki birgeba kuwa. Ashe ma fuggukar taki da É—aga hanci kamar Æ™ofar gora na wofine†ta Æ™are faÉ—a a fusace. Bibaa ta nuna da Baby “Ku dan ubanku Imamu ku tashi ku É—akko kayan shara, ke kuma zoki zauna anan wazai barki kiyi wani aiki kina fama da kanki. Zakiyya ma na hanya gyaran jiki zata fara miki yau É—in nan dan duk da gaki nan fes da ke ga kuma Æ™arancin lokaci bazai hana nasa a kwaskware min ke ba dan kowa ya sake tabbatar da amarya Æ´ar gata zan kaiâ€.
Sosai Bibaa da Baby ke kallonta ransu a ɓace, sai kuma su kalla Mum da taƙi cewa komai. Tsawa ta daka musu, babu shiri suka miƙe a zabure kuwa. Nayi mamakin shirun Mum dan nasan yanda suke ƴar tsama da Gwaggo Gudidi, rashin jituwar tasu ma ce tasa Gwaggon daina zuwa gidan gaba ɗaya. Amma dai dole a wannan shirun nata akwai ayar tambaya.
Su Baby naji na gani Gwaggo ta turkesu sukai gyaran ɗakin, sau biyu tana maidasu su maimaita wai bai mata ba. Bayan sun kammala sunata zungure-zunguren baki tasa Bibaa ta tattara kayanta ta maida ɗakin Baby. Shima auta aka haɗa masa nasa aka sanda shi ɗakin Mum. Acewar Gwaggo nan sune zasu zauna har sai biki ya tashi. Ni dai dariya ma abin ke ban. Dan Gwaggo Gudidi fitinanniya ce sai dai idan bataso ba zaka ga ta watsar da kai kamar mai shiru-shiru. Halin namu dai na kamanceceniya sosai, ƙila dai ita na gado ma (🤣). Fuu Mum ta tashi batare da tace mana komai ba ta bar falon, mu duka da kallo muka bita, sai dai babu wanda yace komai.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.