Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TSUTSAR NAMA BOOK 1.txt
Chapter 83 of 264
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ðŸ˜ðŸ™_*
*_Typing📲_*
*_ðŸ›TSUTSAR NAMA....!!ðŸ›_*
_(Itama nama ce)_
_ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»_
_ð‘©ð’ð’𒌠ð’•ð’˜ð’_
_ð‘·ð’‚ð’ˆð’† ð’•ð’˜ð’†ð’ð’•ð’š ð’•ð’˜ð’_
___________
Toh Nazo maku
Da kayan arziki
Kudai kunsan mata sai da gyara
Macen da Bata da gyara ta zama yar kallo a gidan ta
A katafaren kamfanin mu na BEENAD HERBAL MEDICINE
Mun shahara wajen kawo maku ingattatun magunguna mata da na gyaran jiki,kayan mu guarantee ne
Muna da
Shedaniyar gumba
Gumba mai saying
Garin mai kabbara
Mai dalalan miyau
Wayyo dadi
Mai bunsuru
Dan jarida
Soyayya dole
Bakin kyalle
Tadire ta girke
Gumba mai likkafani
Maza taye
Zumar kwakwa
Zumar ridi
Zumar dabino
Zuma mai ma'ul ijaba
Farin jini
Mallakoki
Gumba kalla kalla da dai sauran su
A BEENAD HERBAL muna da turarukan wuta da humrah kalla daban daban sai Wanda kika zabba
Ga kuma maganin slimming
Gyaran nono
Maganin hips
Maganin Kara kiba
Da dai sauran su
Kayan mu tested and trusted ne
Muna maraba da masu siyan Daya ko sari
Muna Nan cikin garin kaduna
Kuma muna tura Kaya duk inda kike da yardan Allah
Ni ce taku har kullum
AMINA GACHI
07034404975
CEO BEENAD HERBAL MEDICINE &INCENCE
KADUNA
Phone no 07034404975
____________
......RiÆ™ota nayi ina girgiza kaina. Ta tsaya tana kallona. Idanuna cike da Æ™walla na ce, “Kiyi haÆ™uri Mama ki buÉ—e min zan gwada na gani. Koba komai itama mutum ce kamar mu. Muma kuma bamu san ya rayuwa zatai damu ba anan gaba. Dan ALLAH ki buÉ—e min kawai ALLAH yana tare da niâ€.
Sosai alamar sanyayar jiki ya bayyana a gareta na jin kalamai na. Dan haka ta nufi Æ™ofar dake a falon batare da ta sake cemin komai ba. Bayanta nabi ina mai jin tausayinta. Babbar mace kamila yanayin rayuwa yasa tana gurfana a gaban wadda bata wuce sa'arta ba. Lips É—ina na ciza. Kafin na furzar da iska nabi bayanta nima. Sosai tsaruwar falon farko na sashen yay matuÆ™ar É—aukar hankalina. Fes yake yana É—aukar ido saboda kayan alatun da yasha. Da alama ana gyarashi kullum. Kamar zanyi magana sai kuma nayi shiru dan ganin yanda Mama Balki ke É—ari-É—arin buÉ—e Æ™ofa ta biyu. Sai da ta runtse ido da karanto addu'a sannan ta murÉ—a handle É—in. Da sauri tayo baya tamkar mai shirin zurawa a guje. Kallonta na tsaya yi kawai cike da nazari, sai kuma na sauke numfashi. “Uhhh mama, inaga kije kawai daga nan babu damuwa zan Æ™arasa ni kaÉ—ai.â€
Waro idanu Mama tayi, sai kuma ta marairaice fuska idanunta na cika da Æ™walla. Ƴar nan dan ALLAH kiyi addu'a kinji, ko ki zauna a wannan falon sai zuwa anjima ta tashi ki gudo, Kinga shike nan an rabu lafiyaâ€.
Murmushi mai kama da yaÆ™e kawai na mata ina jinjina kaina alamar to zanyi. Numfashi ta sauke mai nauyi, sai kuma ta haÉ—iyi yawu jiki a sanyaye ta juya ta fita tana waigena. Ni dai kallonta kawai nake har sai da ta maida Æ™ofar falon ta rufe a hankali. Sai kuma ta sake buÉ—ewa. “Karki sake ko kulle kowacce Æ™ofa dan ALLAH Kandala. Ki barsu a buÉ—e yanda zaki samu damar gudowa koda an sami akasiâ€.
Kaina na jinjina mata nan ma ina murmushi. Ta sake ɗan jan ƙofar batare data rufe duka ba ta barta. Shiru nayi kawai a wajen tsaye har zuwa wani lokaci. Ni kaina a tsoracen nake. Amma inata ƙoƙarin dakewa kun dai san ɗan jarida da jarumtar wahala. Shiru sashen yake babu alamar motsin mai rai, sai ɗan yanayin kamar bashi-bashi dake bugowa daga ƙofar da Mama ta buɗe. Ƙofar na tsurama idanu na wani lokaci, kafin nayi ƙundun balar nufarta cikin sanɗa da ambaton sunan UBANGIJI......
📯📯📯📯
Farin cikin da Musaddiq yake a wannan rana bazai taÉ“a musaltuwa ba a zahiri. Sai dai ya barma UBANGIJI komai. Tsaff ya fito cikin shirinsa na shadda ruwan Æ™asa mai haske harda hula. Sai Æ™amshin turarensa yake mai sanyin daÉ—i. Hannunsa riÆ™e da takardunsa yake Æ™oÆ™arin kulle Æ™ofar. Juyowa yay da sauri jin kamar mutum ata bayansa yana kallonsa. Ilai kuwa ido huÉ—u sukai da Umma mahaifiyar Mom da alama isowarta gidan kenan. Kauda tsarguwar kallon Æ™urillar da take binsa da shi yayi, tare da sakin nutsatstsen murmushinsa ya Æ™araso inda take. Cike da girmamawa ya ce, “Sannu da zuwa Umma. Ina kwana? Anzo lafiya?â€.
Cikin ɗan daburcewa da dawowa a hayyaci ta shiga amsawa bakinta a washe. Dan harga ALLAH yaron ya gama firgita mata zuciya da guntun lissafin ta. Wani kalar mahaukacin sirrintaccen ƙyawu fa taga yayi mata da ƙiba harda haske. Ga arziƙi muraran ya nuna a jikinsa kai kace ma shine ɗan masu gidan ba ɗan riƙo ba. Dan ko mahaukaci ya kallesa ya kalla Abbas yasan akwai banbanci da tazara mai yawa ta cigaban rayuwa....
“Ki shiga Umma ai su Mom É—in suna nan cikiâ€. Ya faÉ—a cikin katse mata tunanin data lula. Firgigit kuwa ta dawo a hayyacinta. Sai kuma ta washe baki cikin in ina ta ce, “T... t.. to É—an nan nagode kaji, ALLAH ya muku albarka ya Æ™ara arziÆ™i. Bari na shiga É—in dai toâ€. Ta Æ™are maganar tana tafiya da waiwayensa a lokaci guda har taci tuntuÉ“e tana neman faÉ—uwa. Ta dai samu ta dafe gini idonta a kansa har lokacin ga baki a washe kamar sakara.
Shi dai Musaddiq cike da al'ajabinta yay ficewarsa. Kaɗan-kaɗan sai ya kalla kansa ko zaiga abinda takema kallon ƙurulla a jikin nashi. Amma sai baiga komai ba. Haka dai ya tare napep ya shiga komai na masa kai-kawo a rai da zuciya. Koda ya iso gate ɗin companyn sai da ya nuna ɗan katin da ogansa ya bashi sannan aka barshi ya shiga. Sosai yake jinjina ƙudira da rahama ta UBANGIJI. Dan gaskiya wannan Company ya matuƙar tafiya da imaninsa. Gini ne iya gini da baka iya ƙuresa da idanu. Ga ma'aikata nata faman kai-kawo da securitys. Ga kayan aikin tako ina da zai tabbatar maka da komai fa da gaske ake babu wasa. Da taimakon wani security akai masa rakiya office ɗin Manager.....
💦✨💦✨💦
Ji Abba yay tamkar ya tashi ya buga ihu da tsalle dan farin cikin hukuncin Baba. Domin ya tabbatar musu in dai Halime na son Abban zai bashi ita. Hakan yasa aka aika aka kira Halime. Koda tazo taci karo da su Abba sai da ta nuna ƙololuwar mamakinta har ta gagara yin magana sai da Babanta yay mata magana ma ta iya gaishesu muryarta na rawa. Zata ɗora da zance Abba daya san mi zata iya faɗa yay saurin katseta. Dan baya fatan ta tona asirin komai musamman akan abinda ya faru a randa ta gudo ɗin, saboda ya fahimci bata sanarma su Baban komai ba. Shirun kuwa tayi kamar ta fahimci abinda yake buƙata, daga haka mai anguwa ya sanar mata abinda ya kawo su Abba. Sake diriricewa kuwa tayi tana faman zare idanu. Da ƙyar Abba ya iya danne dariyarsa. Alhaji Jafaru da Alhaji Sadisu kuwa sai da suka dara kaɗan. Mai anguwa ma dai yayi kaɗan kafin ya ɗora da tambayarta ko tana son Abba ɗin.... Ai baima rufe baki ba suka tsinceta can ta zura a guje cikin gidan mai anguwar.
Basu Abba ba hatta da Babanta yanzu kam sai da ya dara. Fuskarsa da sauran dariyar ya dubi Abba. “Imamu kaga fa shirmen mutuniyar taka. Anya zaka iya da ita? Dan Sa'adiyya akwai wauta a tattare da ita ta Æ´aÆ´an fari. Ni kaina wani abun idan tayi a wasu lokutan Æ™uleni sukeyi. Sai dai kuma akwai himma ga biyayya. Duk abinda kaso daga Sa'adiyya zaka samesa. Gwargwado na bata ilimin addini, na zamanin ma ta fara wasu dalilai yasa dole aka yankesa....â€
Fuskar Abba da murmushi kansa a Æ™asa ya ce, “Karka damu Baba, ni É—in ita nake so ba shirmen ba. Sannan nagartattun halayen nata da tarbiyyar ta suka jani gareta. Dan wauta wataran zata daina in sha ALLAHU yanzu ma akwai Æ™uruciya neâ€.
“To Alhamdullah Imamu, naji daÉ—in jin wannan batu daga gareka. Dan haka ina sake maka albishir da baka auren Sa'adiyya. Kuma bana son kubar garin nan sai an É—aura, in har da sadaki a tare da kai da anyi sallar zuhur yanzu kawai sai ayiâ€.
Wannan furuci shi ya sake rikita Abba. Dan baba bai kammala rufe baki ba ko ya zaro kuÉ—i masu yawa a aljihunsa ya dire gaban Baban. Dariya su Alhaji Sadisu suka sanya masa. Cike da tsokana Jafaru ya ce, “Ai ka bari dai ni na biya maka Alhaji zumuÉ—inkaâ€.
Dariya su mai anguwa suka saka da Baba. Yayinda kunya ta kama Abba ya kaima Alhaji Jafaru harara yana ɗauke kansa gefe. Da ga haka suka miƙe domin haramar masallaci....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.