Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TSUTSAR NAMA BOOK 1.txt
Chapter 33 of 264
Washe gari koda na kammala aikina na shirya na fito na samu Abba a falo na gaishesa bai amsa min ba. Ko'a kwalar rigata nai ficewata. Yaya ga É—aukan muka wuce ina bashi labari ina dariya. Shi kam murmushi kawai yayi yace “ALLAH ya Æ™yautaâ€. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya gidan Abba babu daÉ—i sai haÆ™urin UBANGIJI kawai. Yayinda a waje aiki ke caja kai kuma. Kamar yanda mukai shiri ranar asabar muka tafi Katsina ganin Hafizzullah. Ƙiri-Æ™iri Mom ta nuna baÆ™in cikinta akan hakan. Ta shiga zuga Abba wai ya hanamu zuwa. Sai dai Yaya ya nuna musu babu abinda zai sakamu fasawar. Haka dai muka tafi Mom na banbaminta na rashin gaskiya. Hafizzullah yayi matuÆ™ar farin ciki da ganinmu. Dan harda kukansa na murna. Ya rame saboda karatu, naita tsokanarsa nikuwa muna faÉ—anmu da muka saba. Tare da shi muka yini. Da zamu wuce masauki kuma ya bimu akan shi tare damu zai kwana. Nan ma raba dare mukai muna hira kafin su koma É—akin Yaya Musaddiq su kwanta ni kuma nai kwanciyata ni kaÉ—ai muka sha waya da Mansoor dake bani labarin an shirya komai tsaf gobe in sha ALLAHU za'a tsaida date. Jinai duk wani iri, amma a Æ™asan raina ina farin ciki da hakan. Koba komai ai zan samu Æ´ancin kaina. Na kuma samawa Æ´an uwana. Dan insha ALLAHU Hafizzullah gidana zai koma, Yaya kuwa zan cigaba da dagewa akan yay aure..........âœï¸
_Kandala ta malam Mansoor 😘_
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ðŸ˜ðŸ™_*
*_Typing📲_*
*_ðŸ›TSUTSAR NAMA....!!ðŸ›_*
_(Itama nama ce)_
_ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»_
_ð‘·ð’‚ð’ˆð’† ð’•ð’˜ð’†ð’ð’•ð’š ð’ð’Šð’ð’†_
........Washe gari kamar yanda Mansoor ya faɗa muna a hanyar dawowa gida ya turamin saƙo na jerarrun kalaman godiya ga ALLAH. Tare da sanar min an tsaida wata ɗaya kacal, nanda kwana talatin in sha ALLAHU na zama mallakinsa. A gidansa zanyi azumin watan Ramadan. Duk da naji farin ciki ban maida masa reply ba, dan ina cikin mood mara daɗi na rabuwa da Hafizzullah. Shima mun barosa harda hawayensa. Munko samu gida cike da kayan sweet, biscuits da drinks a falo. Harda su goro sai akwatina guda biyu. Yanda babu wanda yay min magana akan kayan nima banma kowa ba. Sai auta ne ke faɗamin Uncle Mansoor ya gaya masa kayana ne. Sai kuma habaicin da Baby keta saki ranta a ɓace. A kallo ɗaya da nai mata kuma na fahimci tasha kuka. Ban kulata ba dan ba itace a gabana ba. Washe gari Monday na wuce aiki da wuri. Bayan mun dawo na tarar da Gwaggo Gudidi tazo daga Dawanau. Kakace a wajenmu, dan ƙanwar kakarmu ce, mahaifiyar su Abba da mamanmu kenan. Ba sosai take zuwa gidan ba saboda wulaƙancin da Mom ke musu. Mu kuma Abba baya barinmu zuwa wajenta, garama Yaya yanzu daya mallaki hankalin kansa yana zuwa abinsa. Yanzun ma shine ya kirata ya gaya mata komai ganin Abba baida niyyar saka danginsa ko ɗaya a batun auren nawa. Ƴan Gwarzo kuwa sun kwashi nasu kason kayan da za'a rabama mutane sun wuce dasu tun jiyan, dan bamu samesu ma a gidan ba. Nayi murna ƙwarai da ganin Gwaggo Gudidi. A take na shiga hidima da ita dan naga babu alamar ko abincin kirki ma an bata. Duk da hararar da Mom ke mun banbi takanta ba na shiga hidima da kakarmu. Bayan sallar isha'i kuma Yaya ya sayo mata kayan ƙwaɗayi yazo ga zauna muka sha hira. Dan dole Abba ma yazo ya zauna akayi da shi shima. Mom da ƴaƴanta kuwa kowa yay shigewarsa ɗaki sai Auta da uwar gulma Bibaa kawai a wajen. Bamu tashi a falon ba sai sha biyu. Abba ko tun sha ɗaya matarsa tazo ta tasashi suka shige ko kunyar Gwaggo Gudidi bata ji ba balle mu ƴaƴa. Shimfiɗata na barma Gwaggo, dan Yaya Musaddiq ya kawo mata babban bargonsa. Zan kwanta a ƙasa tace na hawo kan bargon. Badan naso hakan ba na hau dole. Sabuwar hira muka buɗe da ita har sai ɗaya sannan barci ya kwasheta. Niko alwala na tashi nayi nai nafilfilina kamar yanda na saba sannan na kwanta. Hakan kuma bai hanani tashi uku da rabi ba na shiga ayyukana. Kafin kace mi na kammala, dan har abinci naima Gwaggo na saka mata a kula nakai ɗaki dan nasan ba lallai da rana a bata na kirki ba. Gashi ban dawoba lokacin. Kalacin ma isashe na ɗiba mata. Itako tanata mitar yanda nake wannan uban aiki ga fitar safe kuma. Ni dai bance komai ba face murmushi kawai. Yau kam Yaya Musaddiq ya shigo gidan domin gaisheta. Ya ajiye mata kayan shayi da ƙaton bread ɗin ta harda soyayyan ƙwai. Albarka ta dinga saka mana sannan mukai mata sallama muka wuce dan kar mu makara.
Gwaggo Gudidi itace ta raba komai na kayan sa ranar nan. Har maƙwafta sai da tasa Auta ya kai ma kowa gida-gida. Sannan dangin su ta ƙulla na kowa daki-daki. Wanda ke anan cikin Kano ta saka Yaya Musaddiq ya kaita ta kai ma kowa. Na Gwarzo ma tare sukaje takai duk na ɓangaren danginsu dai. Yaya Musaddiq ma da Hafizzullah ta ɗiba musu. Nima komai sai da ta ɗiba min. Hakama jama'ar gidan kowa da nashi. Kuma kowa zai iya rabama abokan arziƙinsa idan yaso. Amma sai Mom tai biris da nata anan falo har Gwaggo ta wuce bata ɗauke ba daga ita har ƴaƴanta. Abba dai ganin Gwaggon yasa shi zama ya ƙuƙƙula ya fita dasu wai zai rabama abokansa da ƴan wajen aikinsu. Ya raba ko bai raba ba oho masa.
A ranar da nakai ma ƴan office ɗinmu kowa ya sake sanin alaƙata da Mansoor, dan wasu basu ɗauka gaske soyayya muke ba saboda yanda muke komai cikin taku. MD kuwa ai kamar zai mutu. Dan masifa yayta zubama kowa a wannan yinin babu gaira babu sabar. Har dai ƴan uwana ma'aikata suka fahimci kishi yake yi. Ni dariyama ya bani wlhy. Mansoor kam yaji daɗin abinda nayi, dan bai ɓoye ba sai da ya sanar min. Murmushi kawai na masa nidai. Bayan an tashi aiki ya buƙaci kaini naga aikin gida da ake ƙarasawa. Amma sai nace masa ba yau ba ya bari weekend zai fi. Shima ya yarda da shawarar tawa. Dan haka ya maidani gida. A ranar ne kuma na fahimci wata farar mota na binmu a baya. Duk da naji tsoro sai banyi magana ba, nace bari dai na tabbatar. Ganin munzo titin shiga layinmu motar ta wuce yasa na sauke ajiyar zuciya har Mansoor na kallona.
“Lafiya irin wannan ajiyar zuciya haka kamar wadda nai shirin sacewa. Ko tsoro kike kada na wuce dake ne?â€.
“Ai kaima bazaka fara hakan ba sai an bakaâ€. Na faÉ—a cikin kauda kai ina murmushi. Shima Æ™aramar dariya yay da sake faÉ—in, “Hakane. Amma da zama a taimaka a banin yau zanfi kowa farin ciki. Maybe ma na Æ™ara samun Æ™arfin aikin yanda ya kamataâ€.
“Humm†kawai nace na buɗe motar na fice ina murmushi. Godiya na masa kamar kullum. Yanata son mu haɗa ido amma naƙi yarda da hakan. Sai ma na wuce da sauri na shige gida abina. Amma na maƙale jikin gate ina leƙansa. Yaja kusan minti ɗaya idonsa a gate ɗin fuskarsa da murmushi kafin ya tada motar ya wuce...
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.