Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TSUTSAR NAMA BOOK 1.txt
Chapter 18 of 264
Shima da ƙyar ya iya miƙewa da ga falon ya nufi bedroom ɗinsa. Tamkar mai hasashen ganin wani abu sai da ya gama kalle kowacce kusurwa da lungu da saƙon na ɗakin sannan ya kai zaune a bakin katafaren lafiyayyen gadon. Sabon gida ne fil dan yau ne ya fara shigarsa. Anyi aikin gininsa tare da Companyn nasa ne. Bai cika son zaman hotels ba a rayuwarsa sai in har ya zama tilas a garesa. Ta wani ɓangaren kuma gorin mutane akan kullum yana cika bakin shi ɗan Kano ne amma ko gida baida a arewa ma gaba ɗaya ya sashi ginin wannan gidan da ko makaho ya laluba yasan an kashe kuɗi. Dan yanda companyn ya haɗu shima gidan haka ya haɗu matuƙa.
Yanda ya zauna shiru ya dafe kansa zaka ɗauka ciwo yake masa ne. Amma sam ba haka bane. Abubuwane kawai suke masa kai-kawo a rai da suka faru a wannan yinin. Kallon komai yake tamkar wani film ba zahiri ba. Ba yau ne ya fara cin karo da matsaloli da ƙalubalen rayuwa ba. Amma na yau ɗin na musamman ne. Dan duk sunzo masa a bazata. Hakan na nufin ya sakankance da yawa kenan. Sannan dole ne ya sake shiri in har yana buƙatar abubuwa su tafi masa a yanda yake buƙata anan batare da tangarɗa ba?. Amma dai bari ya jira P.A ɗinsa da sakamakon da yake buƙatar gani kafin ya tsara komai akan mizaninsa. Da ga haka ya miƙe yana mai fara zame kayan jikinsa domin shiga wanka...
Yaja tsahon lokaci a bayin kafin ya fito sanye da bathrobe ash color sabuwa dal. Dan yanda take wani maski-maski zai tabbatar da hakan. Ƙaramin towel da a hannunsa ya kai kan jiÆ™aƙƙiyar sumar kansa mai tsaho data kwanto masa a fuska sosai, hakama ta bayansa kai kace bai haÉ—a jini da babaÆ™en fata ba balle ma har a kirashi da suna bahaushe. Tamkar ba shi kaÉ—aine a É—akin ba. Fuskar nan a tsuke babu alamun rahama a cikinta. Duk da tun fitowarsa wayarsa ke tsuwwa alamar kira na shigowa, yay biris da ita tamkar bai ji ba. Sai ma Æ™oÆ™arin nufar Æ™aton mirrorn dake a É—akin yayi abinsa. Tuni Hayatu ya shirya masa kayan shafe-shafensa a mirrorn, dan zaiyi kamar 1week ne a cikin Kanon kamar yanda yake fata. Hand dryer da aka ajiye a saman mirror É—in sabuwa fil ya É—auka ya jona a socket, sumar tasa ya fara busarwa. Cikin Æ™anÆ™anin lokaci ya kammala gyarata alamar ya riga ya saba da hakan. Kafin ya É—an shafa mansa sama-sama tare da sprays masu shegen Æ™amshi kala har biyu sannan ya nufi doguwar wadrobe data cinye bango guda. Ta farko kawai ya buÉ—e, anan ko yaga kaya kusan kala goma duk Æ™ananu, sai Æ´ar akwatin da yazo da ita da suit kala uku a ciki. Yasan kayan dake a shiryen duk aikin Hayatu ne. Batare da yace komai ba ya ciri farin pyjamas mai shegen Æ™yau da laushi, sai boxer shima dai sabo. Tsaf yay shirinsa tare da sake komawa gaban mirrorn yay sabon wankan tsadaddun turarurrukansa na barci da Æ™amshinsu ba'a magana kamar ba dare ba. Tsaki yaja a hankali yana hararar wayarsa da ke cigaba da tsuwwa babu ko Æ™aƙƙautawa. Ya san mai kiran nasa, dan ita kaÉ—aice take karya dokarsa akan hakan. Duk wanda ya sanshi yasan yanada doka a akan kira, dokar kuwa itace in har kamasa kira 1 bai É—aga ba ka bada mintuna kamar biyar sannan ka sake. Idan nan ma aka samu akasi bai É—aga É—in ba to ka haÆ™ura kawai, idan shi ya samu lokaci zai iya ya kiraka, idan bai biyo ba kuma ka É—auka kiran naka baida muhimmanci ne. Wayoyinsa duk a hannun Hayatu suke. Wannan ce kawai yake riÆ™ewa saboda Ummien sa. Gaban gadon ya Æ™arasa in da ya yasar da wayar, cikin Æ™ara É—aure fuska ya É—auka dan yana son ta barsa. A daÆ™ile ya kai wayar kunensa sai dai yaÆ™i cewa komai. Sai da yaja kusan sakan hamsin ya ce, “Thanksâ€Â. Kawai yaja bakinsa yay shiru. Kasancewar bai sauke wayar ba zai tabbatar ma da har yanzu magana ake daga can, dan sai wani yamutsa fuska yake da sake tsuketa kamar mai jin warin mai maganar. Kusan minti biyu ya sake furta, “Zanyi barciâ€Â. Daga haka ya yanke kiran gaba É—aya. Wayar ya wurga a saman gadon tare da jan tsaki mai Æ™arfi ya haye gadon yay kwanciyarsa. Kai kace ma baida wata damuwa a rayuwa. Sai da yay addu'oi barci sannan ya lumshe idanunsa. Kafin wani dogon lokaci ya fara sauke numfashi a hankali alamar yayi barcin.....
â—´⌓`â—Ââ—´⌓`â—Ââ—´⌓`â—Â
Duk yanda nagaji na kasa barci. Sai faman juye-juye nake abubuwa na dawo min tamkar yanzu suke faruwa, dan ma ƴar wayar da mukai da Mansoor ta ɗan sani ƴar nutsuwa. Ganin ƙwaƙwalwata na neman tarwatsewa na tashi na ɗaura alwala. Salla na farayi, sai da na kwashe kusan awa ɗaya da rabi sannan na zauna ina istigifari. Kamar a mafarki naji wayata na verbration. A gogo na kalla, ƙarfe biyu da kwata. Mamaki ya kamani, dan ko Mansoor baya kirana a wannan irin lokacin, kuma ma ai munyi waya duk da dai yace zai sake kira video call amma bai kira ba, ganin lokaci haja yasa ban damu ba. Dan duk tsawon wayarmu baya wuce daga tara zuwa goma. Jin an sake kira bayan ta katse na yunƙura na ɗauka. Abin mamaki Mansoor ne. Ɗagawa nai hankali a tashe, a tunanina ko wani abu ya samesa. Amma sai naji yaymin sallama cikin taushin murya. Ajiyar zuciya na sauke a hankali, sannan na amsa masa.
“Dama naji a jikina zaki iya kasa barci, kiyi haÆ™uri Yaya ne ya É—auke hankalina shiyyasa ban sake kiran ba. Haba Babie dan ALLAH ki cirema kanki damuwar nan. Ai ko ke kika aikata laifin nan sai hakaâ€Â.
Numfashi na sauke a hankali. Cikin sanyin murya na ce, “Ni ban kasa barci ba fa, na farka ne kawaiâ€Â.
“Uhhm yau kuma halin daba naki ba kika aro, to ai bai miki Æ™yau ba dan baki iya Æ™aryarba tunda ga harshenki yana rawaâ€Â.
ÆŠan murmushin Æ™arfin hali nayi, sai kuma nakai kwance ina faÉ—in, “To amin afuwa gashi na kwanta. Amma kaima miya hanaka barci?â€Â.
“Saboda mahaÉ—in zuciyata batayi baâ€Â.
“Hummâ€Â. Na faÉ—a kawai ina murmushi. Shima ina jiyo sautin nasa murmushin. Mun É—an yi shiru na wasu sakannin kowannemu na sauraren saukar numfashin É—an uwansa. Kafin ya katse shirun da cewa, “Kin sanarma Yaya Musaddiq abinda ya faru ko?â€Â.
“A'aâ€Â.
“Miyasa?â€Â.
“Kawai daiâ€Â.
“Aiko Babie ya kamata ya sani. Dan ko zamu iya É“oyema kowa shi banda shi. Maybe ma ya Æ™aremu da shawara ai. Dan wlhy har yanzu ni kaina duk a kulle yakeâ€Â.
“Hakane zan sanar masa gobe in sha ALLAHU. Amma ni dai dan kaÆ™i ta nawane. Hukuma kawai ya kamata mu miÆ™awa aiâ€Â.
“BaÆ™i naiba Samraah. Ina son ki fahimci wani abu. Mutumin nan fa ya wuce duk inda kike tunani a Æ™asar nan. Yanzu koda mun miÆ™a video É—in nan ga hukuma kina ganin zasu hukuntashi ne. Ko kin manta yanzu a Æ™asar nan tamu KUÆŠI ne ke magana ba GASKIYA ba. Shi kuma ALLAH ya bashi su, Samraah Maash fa zai iya juya Africa a tafin hannunsa ta yanda yaso bama Nigeria ba. Ke hatta da Æ™asashen masu jajayen kunnuwan yanada Æ™arfin faÉ—a aji sosai fiye da yanda kike tunani ta wasu fannoni. Sai dai su banbancinsu damu zasu iya hukunta duk wani mai laifi koda shi wanene? Amma a Æ™asarmu ba haka bane. Ko wanda bai kama Æ™afar Maash ba zai iya shallakewa in har da kuÉ—i. Kiyi haÆ™uri dai mu nema mafita mai É“ullewa. Mu kuma samu jajirtaccen É—an sandan da zai iya yin duk abinda ya dace batare da kuÉ—i sun iya tankwarashi ba saboda gaskiyarsa. In dai Maash ne bazamu Æ™yalesa ba sai an Æ™watoma mutumin nan hakkinsaâ€Â.
“ALLAH ya tabbatar to. Na kuma gamsu da bayaninka.â€Â
“Masha ALLAH dear, yanzu dai zan shigo gobe in ALLAH ya kaimu ki biyo Yaya Musaddiq gareji mu haÉ—u acan dan ina so mu tattauna da gaggawa mu nemo mafita kafin Maash ya farga. Saboda babu yanda za'ai ace babu camaras a wajen nan duk da Companyn bai fara aiki ba sai Mondayâ€Â.
Sosai zancensa ta ratsani dan har sai da na tashi zaune dingangan. Amma na gagara cemasa komai saboda yanda zuciyata ke bugawa da sauri-sauri........âœÂï¸Â
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.