Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TSUTSAR NAMA BOOK 1.txt
Chapter 141 of 264
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ðŸ˜ðŸ™_*
*_Typing📲_*
*_ðŸ›TSUTSAR NAMA....!!ðŸ›_*
_(Itama nama ce)_
_ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»_
_ð‘©ð’ð’𒌠ð’•ð’‰ð’“ð’†ð’†_
_ð‘·ð’‚ð’ˆð’† ð’ð’Šð’ð’†ð’•ð’†ð’†ð’_
.......Kayane ɗinkakku har kala biyar, sai kayan ciki b&p 12-12. Sosai naji kunya ta kamani. Wani gefe na zuciyata kuma na mamakin inda yasan seize ɗina. Hatta da ɗinkunan dai-dai jikina cif. Zumuɗin tafiya wajen Ummie ya sani ajiye komai gefe na shirya cikin doguwar rigar lass pink mai ƙyau mara nauyi kuma. Komawa nayi gaban mirror ɗin ina kallon kaina fuskata cike da murmushi. Na dawo Samraah ta ƴar jarida ƴar gayu. A take yaya Musaddiq yazo min a rai. Hawaye naji sun cika min ido na kewarsu. Tunda abin nan ya faru bamuyi waya ba. Dolene idan na dawo wajen Ummie na roƙesa aron waya nayi kiransu har su aunty Zakiyya ma. Da wannan tunanin na ɗauki turarensa na fesa tare da ɗaukar ɗankwalin nai simple ɗauri. Mayafin cikin akwatin guda uku na ɗauka ɗaya nayi salla dan babu hujjab. Ina idarwa na miƙe cike da zumuɗi na tattare duk kayayyakin dana baza na maida bathrobe ɗin danai amfani da ita da towels ɗin daya cire na maida bayin. Sake ɗan gyara fuskata nayi da faran fauda ɗin dana gani sannan na fice.
Nayi mamakin ganin falon ƙal yanzu yana zuba ƙamshi ga sanyin ac duk da dai ɗazun ma ba wani datti bane. Amma daga gani yanzu kasan an sake gyarashi. Kaina tsaye na fito batare da jin damuwar idan na haɗu da wani yaya zanyi ba. Koda na shiga sai da na sauke ajiyar zuciyar jin daɗin ganin babu kowa a falon. Dama ba lallai na samu masu aiki ba, dan yanzu lokacin hutu ne an gama na safe sai kuma azhar tayi. Kaina tsaye na haye sama harda ɗan guduna.
Naji matuÆ™ar farin cikin samun sashen Ummie fes da shi, ga Æ™amshi na tashi tako ina. Da alama aikin Mama Balki ne kuwa. Ilai kuwa a ciki na sameta tana bama Ummie abinci. Da gudu na naje na faÉ—a jikin Ummie ina mai sakin kuka. Dariya Mama Balki ta sanya min, niko ko'a jikina murnar ganin Ummie kawai nakeyi. Sai da na gama murnata na É—ago ina kallonta. Itama kallona kawai takeyi kamar ta samu television. Murmushi na sakar mata idanuna cike da Æ™walla na ce, “Ummie na i miss youâ€.
A bazatar da ta bamu matuÆ™ar mamaki mukaga ta saki murmushi tare da kai hannu ta shafa kaina. Sai kuma ta saki kuka. RuÉ—ewa mukai mu duka. ƘoÆ™arin miÆ™ewa nake a jikinta amma sai ta riÆ™eni da Æ™yau, sai kawai na sake rungumeta nima ina kukan. Mun jima a haka kafin na É—ago jin kamar jikinta ya saki. Mama na kalla, ta sakar min murmushi itama tana share Æ™wallar idonta. A raunane ta ce, “Tayi barci. Dan tasha maganinta bayan na gama bata abinci. Gani nayi ga sake jawo kwanon sai nayi zaton bata Æ™oshi ba shine na sake zaman bata kika shigo.â€
Nawa hawayen nima na share. Sai kuma na tashi a jikinta muka taimaka mata ta kwanta. Zama nayi a kusa da ita hannunta cikin nawa ina jin matuƙar farin ciki da ganinta. Sai matuƙar tausayinta dake cimun rai da zuciya dan duk ta rame min a ido alamar ciwon ya bugeta sosai wannan karon...
🩸🩸🩸🩸
“Kamar ya an sallamesu? Waye ya sallame sun?â€. Ta faÉ—a cikin daka tsawa. ƘanÆ™ame jiki nurse É—in tayi jikinta na rawa. Cike da tsorata da birkicewar Hajiya Æ™aramar ta ce, “Am sorry Maa. Wlhy ni ban san wanda ya sallamesu ba, naga kawai sun fito ne amma Dr Larai ce ta musu rakiya har mota. Muma ganin haka yasa muka rakasuâ€.
Wani irin tashi sama jijiyoyin Hajiya Æ™arama sukayi, a fusace ta sake dakama Nurse É—in tsawa. “Get out of my side!!â€.
Ai da gudu Nurse É—in ta fice kuwa. Har neman faÉ—uwa take, ALLAH dai ya taimaketa ta dafe bango. Tana fita itama Hajiya Ƙarama ta fice a fusace. Sai da taje Æ™ofar office É—in Dr Larai sai kuma ta gyara yanayinta cikin jan numfashi da saukewa. Knocking Æ™ofar tayi, aka bata iznin shiga. Dr Larai na zaune da waya a hannunta da alama akwai abinda take yi. Shigowar Hajiya Æ™aramar ya sata ajiye wayar tana murmushi. Da girmamawa matsayin Hajiya Æ™arama na shugaba a asibitin ta ce, “Welcome Doctor ashe kin shigo? Yanzu nake tunanin zuwa na duba kafin na wuce gida ai damaâ€.
Murmushin yaÆ™e Hajiya Æ™arama tayi, tare da jan kujera ta zauna. Hakan yasa itama Dr Larai komawa ta zauna. Gaisuwa sukai a mutunce. Kafin Hajiya Æ™arama ta tambayi bataga petient É—inta ba. Kota canja musu É—aki ne?. Da É—an mamaki Dr Larai ta ce, “Kunyi saÉ“ani kenan? Dan sun wuce gida. Yaron nan naku rigimamme ne na bugawa a jarida. Dan har office É—in nan yazo ta tirkeni sai na bama yarinyar nan sallama. Babu irin son fahimtar da shi É—in da banyi ba dan ya barta ta Æ™ara samun sauÆ™i sosai amma fir yaÆ™i. Wai a dinga zuwa gida ana dubata. Ko kuma ya kawota asibitin kullum. Rikitaccen mutum ne na lura mai ra'ayin riÆ™au gaskiya.â€
Da Æ™yar Hajiya Æ™arama ta Æ™aÆ™aro murmushi. Sai kuma ta miÆ™e tana faÉ—in, “Ai in dai Awwab ne Æ™yaga da yawa wlhy. Shike nan bari zanje gidan mu haÉ—u ai.â€
Murmushi itama Dr Larai tayi da faÉ—in, “To shike nan hakan ma yayi, amma ina tausayama matarsa dan zata sha fama. Stubborn namiji irin wannan idan baka karancesa ba wahalar zamane da su. Dan su abinda suke so kawai za'ayi tilas.â€
Murmushi kawai Hajiya Æ™arama tayi dan ita abinda ya dameta shi ya dameta. Cikin wayancewa dai tace bara taje taga petient sun taru. MiÆ™ewa itama Dr Larai tayi tana tattara kayanta. “Okay nima ai wucewa zanyi. Nasan Alhaji bazai wuce ba sai na koma.â€
💦🩸💦🩸💦
Tuni ganin Ummie yasa na manta da dokarsa ta kar na daɗe. Na shagala sosai da kwance mata gashinta bayan nayi sallar azhar, kanta na a saman cinyata ƙamshin turarensa ya cika ɗakin. Da farko ban maida hankali ba saboda nasan na saka wani a jikina. Sai da naji alamun mutum na nufoni sannan na farga. Shi ɗinne dai sanye cikin brown wando da ash ɗin riga mai gajeren hannu. Gashin nan a ɗaure ta can ƙasa sosai dan har yana taɓa bayansa. Saukar iska a cikin idanuna ya sani jan numfashi da ƙarfi na lumshe idanun, sai kuma duk kunya ta kamani irin wannan abin kunya haka na kure bawan ALLAH da ido. A zatona zaiyi maganar kallon sai naji baice komai ba. Sai ma hannunsa da ya ɗaura saman nawa dake tsefe kan Ummie. A hankali na ɗan ɗago na kallesa. Shima ni ɗin yake kallo. Ƙure juna mukai da ido ga hannayenmu akan Ummie.
“Kinga mamanki kin manta da umarni na ko?â€.
Ya faÉ—a a hankali kamar mai raÉ—a. Fuska na É—an marairaice masa da karyar da kaina gefe a shagwaÉ“e na ce, “Kanta ne fa ya tsufaâ€.
Idanunsa ya É—an ja luuu kamar zai lumshe sai kuma ya buÉ—esu tar akan nawa. Bazan iya jurar salon kallon nasa ba a yanzu dan haka na janye nawa a hankali na duÆ™ar da kan. Shima sai bai sake cewa komai ba ya É—an janye hannun nawa ya Æ™arasa tsefema Ummien. Dama É—ayan da nake yinne ya rage. Dan bana mata kitson da yawa. Koda ya kammala cumb dake saman cinyata ya É—auka ya taje mata kamar yanda naima sauran. Sannan ya tattare gashin cikin hannunsa. Kallona yay a hankali ya furta, “Cire band É—in kaina, idan kin dawo kwayi kitsonâ€.
Kai kawai na jinjina masa. Kafin a kunyace na kai hannuna saman gashinsa dake kwance luff yana Æ™yalli kona wata macen albarka na zame sililin baÆ™in band É—in daya haÉ—e da gashin sai ma ka Æ™ura ido kake ganewa. Koda yaushe kuma zakaga da irinsa yake É—aure gashinsa. Ina gama zarewa gashin nasa ya tarwatse a baya. Sai kawai na shagala da kallonsa har sai da naji saukar hannunsa cikin nawa zai zare band É—in sannan na dawo hankalina. DuÆ™ar da kaina nayi kunya duk ta isan. Yau dai na kula kamar ina sakin layi da yawa. Sai dai yanda ya basar yasa na É—an ji nutsuwa. Yana gama É—aure mata ya gyara mata kwanciya shima ya miÆ™e yana faÉ—in, “Lets goâ€.
Dole na mike a hankali ina gyara mayafin jikina. Wani kallo ya dinga bina da shi daga sama zuwa ƙasa. Sai kawai nai gaba da sauri. A falo muka samu mama Balki ashe bata fita ba. Tana ganinmu ta saki murmushi da faɗin, “Har kun fito.†a kunyace na jinjina mata kaina. Shi kuma ya sanar mata akwai baƙi a gidan zuwa anjima zai kira wayarta tazo su gaisa. Ya kuma roƙeta ta rufe ƙofar falon ko Paah ne yazo karta barsa ya shigo. Maganar tasa ta ɗan ban mamaki, har na kasa haƙuri sai da na kallesa. Amma sai ya ɗauke kansa kamar ma bashi ne yay maganar ba...
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.