Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TSUTSAR NAMA BOOK 1.txt
Chapter 108 of 264
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ðŸ˜ðŸ™_*
*_Typing📲_*
*_ðŸ›TSUTSAR NAMA....!!ðŸ›_*
_(Itama nama ce)_
_ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»_
_ð‘©ð’ð’𒌠ð’•ð’˜ð’_
_ð‘·ð’‚ð’ˆð’† ð’‡ð’ð’“ð’•ð’š ð’‡ð’ð’–ð’“_
......ÆŠan jimm Mama Balki tayi alamar tunani, kafin ta jinjina kanta. “Za'a samu hotonsa, amma sai dai a wajen Alhaji Æ™arami. Dan lokacin da muka dawo rai a É“ace daga garinsu abinda danginsa sukai mana ya sakani a damuwa sosai harna kwanta ciwo. Bani da aiki sai kallon hotonsa ina kuka. Ga kuma halin da Ummie take ciki itama duk na haÉ—u na Æ™ara hargitsewa. Shine Ummie ta saka Alhaji Ƙarami ya tattare hotunan duka daga wajena, ni kuma ban sake amsa ba bayan komai ya lafa na samu nutsuwa. Amma ina ganin zan tambayesa yanzu, ko kuma na saka Hayatu ya amsoâ€.
Kai na jinjina mata cikin gamsuwa.
✨â¤ï¸âœ¨
Yau kwanaki biyu kenan Mom bata saka Abba a idanunta ba. Dan tun jifar da tai masa a washe garin angwancinsa bai sake shiga inda take ba. Hakama amaryar tasa taƙi fitowa. A tunaninta dana yaƴanta harma da Ummanta ai tsoro ya hana amarya fitowa. Dan haka suka fara jin alfahari a ransu musamman ma Mom. Haka zata fito tsakar gida tana habaici da yada magana. Daga Gwaggo Gudidi har Halime da Gwaggon ce ta kwaɓeta babu mai kulata. Hakama Abba yayi watsin ruwan tsarki da ita shan shagalinsa kawai yake da amaryarsa. Gaba ɗaya ya ajiye shekarun girmansa gefe yana koyama Halime salo-salo da tabbatar mata ita ɗin ma fa mace ce. Itako banda raki da taɓara babu abinda take ɓarar masa. Gaba ɗaya ta susuce bawan ALLAH baya ganin komai da tuna kowa a gabansa sai ita. Hatta kasuwa a kwani biyun nan babu inda yake zuwa a gidan yake yini salla kawai ke fidda shi. Dole kuma akayi abinci Gwaggo Gudidi taje ta ɗiba musu tasa Bibaa na kumbure-kumbure takai musu har falo.
Yau dai zaman ɗaki ya ishi Halime. Tana ganin Abba ya fita sallar la'asar ta fito. Tsaff take cikin kwalliya, duk kwalliyar ba'a yi ta yanda ya kamata ba kaya data saka sun fiddo jikinta tsaff da yi mata ƙyau. Ga uban turare ta bulbula. Tun a gaban mirror ake gwada tafiyar da za'ayi, dan haka koda aka fito taku ake ɗaɗɗaya ana juya jiki su adole amare. Nan ko a cikin ɗaki raki takema Abba😂. Gwaggo Gudidi tai shirin fara gaidawa. Dan haka kai tsaye ɗakin da take ta shiga. Ta samu Gwaggon na haɗa kayan tafiya, dan magana ta gaskiya taɓarar da Abba ke zuba musu a gidan na kasa kimtsa bakinsa ya fara isarta itama. Bata ji na daren farko ba amma jiya da rana da yau gabannin asuba fes a kunnenta. Wannan taɓara da rashin sanin ciwon kai har ina. Gara dai ta gusa taɗan basu waje ai ita uwa ce. Maybe ma idan ta wuce ɗin waccan mahaukaciyar surukar tashi itama tayima kanta faɗa ta shirya ta tafi, dan har yanzu Umma na gidan ta fake da jiyyar Mom duk da itama fa abinda Abban keyi na damunta.
Cike da farin cikin ganin Halime Gwaggo ke faÉ—in, “Oyoyo oyoyo É—iyata amaryaâ€.
Kunya ce sosai ta kama Halime. Tai Æ™asa da kanta tana wasa da yatsun hannunta. A ran Gwaggo tace (ashe ke da sauranki Imamu bai ida kakkaÉ“e sauran taki kunyar ba). A fili kam sai ta riÆ™o hannun Halime cikin nata. DurÆ™usawa Halimen tayi Æ™asa cike da girmamawa da kunya tana gaida Gwaggo. Sai Gwaggo taji hawaye sun ciko mata. Dan abune da bata taÉ“a gani ga Mom ba. Ko sanda tana amarya fingai-fingai tazo musu babu alamar kunya tattare da ita. Amma ita wannan jiba dai yarinya Æ™arama amma Alhamdullah. Bayan sun gaisa Gwaggo taita jan Halime da Æ´ar hira. Wani ta amsa wani tayi murmushi kawai cikin kunya. Sunfi mintuna ashirin a haka suka fara jin hayaniya na tashi. A tare suka fita, dan muryar Umman Mom suke jiyowa. Cak bakin Mom dake Æ™oÆ™arin yin magana ya maÆ™ale, tun daga bakinta da hanci da idanu duk akan Halime. Kasa haÆ™uri tayi ta nufo inda suke da sauri. Gaban Halime ta tsaya sai kuma ta nunata da yatsa lips É—inta na rawa. Amma mi a mamakin kowa sai gani sukai Halimen ta saki murmushi tare da rissinawa a girmame ta ce, “Yaya ina yini? Fatan duk kuna lahiya ke da yara? Ya gajiyar bik.....â€
“Wacece ke? Miya dawo dake gidana dan ubanki?â€. Mom ta katse Halime jikinta har É“ari yake. Murmushi Halime ta sake saki da É—an bin Mom da kallo daga sama zuwa Æ™asa. Sai kuma ta sake murmusawa da yin fari da ido tana wani watsa hannuwa gaba da baya cikin iyayi ta ce, “Halime mana nasan kin gane ai. Na dawo matsayin da kema kike a gidan, wato MATAR ABBA IMAMâ€.
Wani shegen tsalle Mom tayi gefe tamkar wadda taci karo da baÆ™in maciji. Yayinda Gwaggo Gudidi da abin ya bama dariya ta saki murmushi da gyara tsaiwar ta. Wani irin zaburowa Mom tayi kan Halime tana faÉ—in, “Shegiya munafuka algunguma Æ™arya kike wlhy, mi mijina zaiyi da kucaka Æ´ar aiki irin ki. Dan ubanki faÉ—a min miya kawo ki?â€.
Murmushi Halime ta saki, tare da ja baya kaɗan ta kaucewa cakumar da Mom ke ƙoƙarin kawo mata. Cike da fari da sake yarfar da hannu. Sai kuma ta ɗan duƙo cikin raɗa-raɗa ta furta, “Abinda mijin naki yake yi dake nima shi yake yi dani a cikin ɗaki†ta ƙare maganar da kashe mata ido ɗaya cike da son sake bata haushi ta gittata ta wuce cikin takun da aka gama kowa a gaban mirror.
Gaba É—aya Mom tai baya zata zube bakinta a hangane sai da Ummanta da itama tayi sumar tsaye ta tarota....
â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸â¤ï¸
Sosai abubuwan da naji a bakin Mama Balki suka sakani a cikin damuwa da ɗimuwa musamman akan mijinta daya rasu, dan gaba ɗaya suffofin data ambacesa dasu kama suke dana Babbanmu. Idan kuma ban manta ba Mom ta taɓa min gugar zana da cewar ai ubanmu har karuwa garesa a Lagos. Lallai tabbas ina buƙatar ganin hoton nan nashi.
Damuwa tamun yawa sai dai ina matuƙar daurewa dan kada kowa ya gane min. Musamman Bahijja sarkin tambaya. Data ganni shiru tata nacin son jin mike damuna. Har cikin rai nima ina ƙaunar yarinyar, sai yanayinta ke ɗauke min kewar Auta. Kwanki biyun nan jikin Ummie da sauƙi sosai, dan na duƙufa addu'a. Yanzu hatta a ruwan wankanta da Mama Balki ke shiga a ɓoye tai mata safe da yamma sai nayi addu'a. Abincin ta da ruwan shanta duka. Dan na daina bata abinci gidan sai wanda nasan ni na girka ko Mama Balki. Damuwa da yawan tunani ya sani ɗan fitowa yau ina zagaya gidan ko zan rage nauyin zuciya da kewar ahalina, dan ina son kiran Yaya Musaddiq akan abinda naji amma na kwaɓi kaina har sai na tabbatar sannan. Wayar Bahijja ce a hannuna na gama magana da Yaya Musaddiq dake sanar min a wajen aikinsu sunce zasu turashi ƙasar waje ya ƙaro karatu. Farin cikin wannan magana ta sani cigaba da tsaiwa a wajen ina kallon kai kawon masu aiki maza dake sabgoginsu a garabar gidan.
A dai-dai nan naga ana ƙoƙarin buɗe ƙaton gate ɗin gidan. Ban kawo komai a raina ba na ɗauke kaina ina cigaba da game a wayar. Har motocin suka gama shigowa ban ɗago ba, dan na ɗauka normal baƙine tunda gidan baya rabo da shiga da fitar motoci. Sai da naji tsaiwar mota a inda nake sannan na ɗago, dan dama a jikin wata motar nake a rumfar ajiyesu. Haka kawai sai da naji ƙirjina ya motsa da ganin wanda banyi tsammani ba. Dan rabonsa da gidan kusan sati ɗaya kenan dama wasu kwanaki.
A hankali ya ziro Æ™afafunsa dake cikin takalma boot brown masu laushi da É—aukar idanu tamkar wani miski, gasu da É—an tsaho ta sama dan har akan wandonsa sosai suka hau. Ko maÆ™iyi ya kallesa daga sama har Æ™asa yasan yayi Æ™yau matuÆ™a cikin shigar tasa. Ga mayen Æ™amshin turarensa da tuni ya mamaye wajen kamar anyi É“arinsa. Cike da matuÆ™ar girmamawa duk masu aikin suka zube suna gaishesa, cikin lumshe idanu da sake dai-daita nutsuwarsa ya É—aga musu hannayensa alamar amsawa. Kafin ya motsa lips É—insa kaÉ—an cikin silent voice É—in nan tasa ya furta, “Kuna lafiya?â€.
Cike da jin daÉ—i da girmamawa duk suka amsa masa. Shima sai bai sake cewa komai ba ya juyo gareni. Kallon cikin ido mukaima juna, na kauda nawa da sauri ina É—an tura baki. Ganin yanda duk yaransa suka samun ido musamman Hayatu ciki-ciki na ce “Ina yiniâ€.
Bai amsa min ba, bai kuma daina kallona ba. Sai da ya mula dan kansa ya É—aga Æ™afafunsa zai bar wajen. A bazata naji shigar furucinsa cikin kunnena. “Karna sake ganinki a anan wajenâ€. Da sauri na É—ago, sai dai kafin na iya cewa wani abu yabar wajen yaran nasa na take masa baya. Sai Hayatu ne a hankali ya ce, “Good afternoon maaâ€. Harara na É—ago na watsa masa. Ya wuce yana murmushi.
Masu aiki dake durƙushe har yanzu kansu a ƙasa duk miƙewa sukayi tare da darewa suka bashi hanya. Shiko ya ratsasu cike da takun nan nasa na mazantaka da tsantsar kamala da nutsuwa. Hayatu da wanda ban san sunansa ba da ƙyamusashiyar baturiyar nan Juliet suka take masa baya. Baki na taɓe tare da raka bayansu da harara. Sai kuma naji duk tsaiwar ta gundireni. Haka na koma ciki ina ƙunƙuni.
Ban sake jin labarinsa ba dan ina sashenmu ina wanke kayan Ummie har yamma. Na kwaso kayan zanje na kai ciki aunty Zakiyya ta kirani a wayar Bahijja. Shine na ajiye na fito domin amsa wayar dan bana son su fahimci komai. Ina fara wayar Æ™amshin turarensa ya mamaye wajen. ÆŠagowa nai da sauri, sai na hangesa É—an nesa da ni kaÉ—an ya nufi gate É—ayan mutumin nan daban san sunansa ba (TJ) biye da shi. Da alama masallaci zasu je dan sanye yake cikin blue jallabiya data fiddo da shi tamkar wani balaraben yankin sudani. ÆŠauke idanuna nayi da sauri saboda hararar daya watsomin da ban san ta miye ba. Wayata na cigaba dayi da aunty Zakiyya ina dariya har sai da na kammala sannan na koma na É—auki kayan Ummie na shiga ciki. Labarin data bani na É—irkama Halime kayan mata dan ta rikita Abba yasa na kasa daina murmushi. Na samu ummie tana barci, dan yanzu abinda tafi yi kenan. Sai uban Æ™amshin turarensa daya tabbatar min daya shigo sashen. Baki na taÉ“e na ajiye kayan na fita........âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.