Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TSUTSAR NAMA BOOK 1.txt
Chapter 246 of 264
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ðŸ˜ðŸ™_*
*_Typing📲_*
*_ðŸ›TSUTSAR NAMA....!!ðŸ›_*
_(Itama nama ce)_
_ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»_
_ð‘©ð’ð’𒌠ð’•ð’‰ð’“ð’†ð’†_
_ð‘·ð’‚ð’ˆð’† ð’‰ð’–ð’ð’…ð’“ð’†ð’… & ð’•ð’†ð’_
.......Mun iso gida babu mai iya cewa ko uffan. Ni dai harga ALLAH banji daɗin abinda sukai ma Paah ɗin ba. Koba komai mahaifinsu ne. Anji yayi kurkure, babban kuskure kuwa da magana ta ALLAH yafe masa ga ɗan da yasan zafin mahaifiya abune mai wahala. Sai dai kuma idan duk aka tattara akai haƙuri sai komai ya wuce. Koda muka kasance daga ni sai shi naso na masa maganar su ɗan sautama Paah ɗin, su kuma bashi damar neman afuwar Ummie, idan ta yafe masa suma suyi haƙuri su yafe masa. Tunda dai babu hannunsa a cikin manyan laifukan. Koda yake shima nashin babban laifi ne. Amma sai naji tsoron hakan. Dan kallo ɗaya kaima fuskarsa ta isa sakaka ka shiga hankalinka.
★★
A asibiti sun wuce sun bar cakwakiya. Dan Prof dai bakinsa yaƙi rufuwa sai tsinema su Fahad yake. A fusace Paah ya furta, “Ƴaƴana ba tsinannu bane ba baba. Kuma in sha ALLAHU bazasu kasance hakan ba. In dai kai baka kasance da tsinuwar ALLAH a kanka ba su mi sukai maka da kake aibanta min su?. Baba ka cutar da mu. Ka wulaƙanta rayuwarmu ta hanyar kasa godema ni'imar da UBANGIJI yay maka. Abie ya maka dukkan gata na rayuwa batare da kun haɗa komai ba. Ya tallafeka ya tallafi mahaifiyarka, ya tallafi matarka damu ƴaƴanka. Amma ka zaɓi sakashi a rana kai ka maye gurbin inuwarsa. Shin baba kai wane irin mutum ne? Bakaji komai ba a yayin salwantar da rayuka har shida saboda buƙatar DUNIYA mai yankewa? Bakayi tunanin kaima wataran zakaje inda suka tafi ba? Bakayi tunanin sune da nasara ba kai ne mai faɗuwa koda ace ka mallaki kuɗin daka salwantar da rayukansu a kansu. Kaicon mahaifi irinka, kaicon jini irin naka, kai cin zuciya irin taka Bab.....†kuka mai cin rai ya sarƙe Paah, hakama su Uncle Abdullahi kuka suke sosai a wannan gaɓar. Su dukansu suna maimaita masa inama ace ba shine mahaifinsu ba. Inama zasu iya canja ƙaddararsu. Wani irin ratsa zuciyar Baba prof kalaman yaran nasa sukeyi matuƙa, kodan basu taɓa haɗe kai sun masa hakan ba a tare ne oho. Komai fa yayi ne domin su, domin jin daɗinsu, amma a ƙarshe ma gashi suna kaico da kasancewarsa mahaifinsu. Kokuwa anzo gaɓar da shima zai ɗanɗani ɗacin hakanne oho. Sai kawai ya fara jijjiga kamar ɗazun, dole dai aka sakasu suka fito likitoci suka ƙara rufuwa a kansa. Kafin wani dogon lokaci abin ya rincaɓe matuƙa. Sai aman jini ta hanci ta baki. Haka suka kusa kwana a kansa, sai dai kuma babu tsumi babu dabara. Lokaci yayi. Prof an tafi ba'a nema gafarar kowa ba, zuciyar ma batayi nadama da yarda ta aikata ɓarna ba. Hatta ƴaƴansa kaico suke da kasancewarsa mahaifinsu, babu kokarin da ba'ai ba na ya kama kalmar shahada da suke karanta masa sai ma saɓanin hakan ke fita a bakinsa.
Su kansu likitoci da jami'an tsaron dake tare da shi jikinsu yayi sanyi. Yayinda kowa ke jifansa da ALLAH wada rai. Babu wanda za'a ambatawa mutuwarsa ya faÉ—i alkairi ko nema masa rahama. Sai dai a ce halinsa ya bisa. Wasu ma cewa suke sai kuma aje a tarar da abinda aka shuka.
Cikin matuÆ™ar kuka Uncle Abdullahi ya ce, “Kaicon mu Æ´an uwa, Kaicon mu. ALLAH yasa muyi dawwamammen tuba kafin mu koma garesa. Wlhy Æ´an uwa ba'ata yaya rayuwarka ta Æ™are ba ko yaya Æ™arshenka ya kasance ne abu mai sauÆ™i. Ka cutar da mutane ka kwanta jiyya ko fuskantar wani iftila'i na rayuwa ne sakamakon ba ko Æ™addarar laifunka. Babban tashin hankali da bawa zai fuskanta a rayuwarsa bayan shuka mugayen ayyuka shine ya bar duniya batare da neman gafarar kowa ba kamar yanda mahaifinmu ya kasance a yau. Ya bar duniya ZUCIYARSA na mai kasancewa a bushe batare da rinisa ga UBANGIJI ba. Ya bar duniya jama'ar dake zagaye da shi a kusa ko nesa suna mai jifansa da ALLAH wadarai da murnar an rage musu mugun iri irin. Yabar duniya kowa naji a ransa shari'ar UBANGIJI tafi wadda za'a kwatanta yimasa anan duniya. Ya bar duniya ana ALLAH wadai da gagara nema masa gafarar UBANGIJINSAðŸ˜ðŸ˜. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, Æ´an uwa mun san minene raÉ—aÉ—in FITAR RAI kuwa? Mun san MINENE KWANCIYAR KABARI KUWA? Mun san MINENE TASHIN KIYAMA kuwa? Munsan MINENE WUTA DA ALJANNA kuwa? Ƴan UWA ni da ku duk bamu sani ba faðŸ˜. Amma UBANGIJI ya mana nuni da su a cikin littafinsa mai tsarki a ayoyi daban-daban, MANZON ALLAH ya isar mana da saÆ™on tabbatattu ne kuma zamu kai garesu ko mun shirya, ko bamu shirya ba. Ko mun yarda, ko bamu yarda ba. Mi muke kallo Æ´an uwa? Mi muke jira? Mi muke tsammani? Mi muke hange? Ina muke tunanin kaiwa?. Itafa duniya sunanta kawai DUNIYA. Ribarka da ita kawai ka BAUTAMA UBANGIJI, kayi biyayya ga MANZON ALLAH. Sai UBANGIJI ya baka Æ™yaÆ™yÆ™yawar makoma domin RAHAMARSA da GAFARARSA. Dan ALLAH, dan ALLAH, dan girman ALLAH Æ´an uwa mu tuba mana. Mu zubda mugayen ayyukanmu mu koma ga ALLAH. Kin san kina bin Bokaye domin biyan buÆ™atar duniya mara amfani a gareki, akan KISHIYA, ko Mallakar MIJI, ko Mallakar abokan zama, ko Mallakar Æ´an uwanki, mahaifiyarki, oganki a wajen aiki, ogarki a wajen aiki ko kasuwa, family É—inki ko na mijinki. Kin san kina ZINA, kin san kina MAÆŠIGO, kin san kina amfani da kanki wajen biyama kanki buÆ™ata, kin san kina shaye-shaye, kin san kina gulma, kin san kina annamimanci, kin san kina zunÉ—e, kin san kina muguwar kissa wa miji dan ya tozarta abokiyar zamanki, kin san kina yaudara, kin san kina zamba cikin aminci, kin san kina cin bashin mutane, kin san kina kawalci, kin san kina cin amanar mijinki, kin san kina sata, kin san kina sakaci da tarbiyyar Æ´aÆ´anki subi maza dan su samo miki kuÉ—i, kin san kina cutar mutane ta hanyoyi da dama, kin san kina! Kin san kina! Kin san kinaðŸ˜. Ya kai É—an uwa aikinka shine É“ata tarbiyan É—iyan mutane. Kana matashi ko mai aure kasan yanda zaka yaudari yarinya da kuÉ—i ka aikata ZINA da ita. Ko ka bita ta Æ™arfi, ko yara Æ™anana da bama su gama sanin kansu ba. Kasan kana bin bokaye domin asiri yara su bika su soka. Kana bin bokaye dan oganka na office ko kasuwa. Kana bin bokaye dan neman mulkin duniya. Kasan kana LIWAÆŠI, kasan kana gallazama matarka a cikin gidan aurenka. Duk hakkin da ALLAH yace ka sauke nata kana tauyeta, bata isa kuma tace ka tauyeta ba sai kaci zarafinta. Kasan kayi sakaci da tarbiyyar É—iyan da ALLAH ya baka matsayinka na mahaifi. Kasan kana sata, kasan kana gulma, munafunci, annamimanci, zunÉ—e, fallasa sirrin gidanka a majalisa, zamba cikin aminci, durÆ™usar da makwafcinka na kasuwa ko wajen aiki saboda kai ka tashi. Amsar cin hanci da rashawa ka bama wanda bai cancanci aiki ba ka hana wanda ya cancanta. Shaye-shaye, siyar da kayan maye, kawalci, neman matan mutane a social media, kune munafukan anguwa anzo neman auren yarinya ku É“ata saboda son zuciya, aboki ya kawo muku damuwar gidansa dan ku bashi shawarar banza ku É—ora shi bisa mummunar aÆ™ida. Duk wani munafunce-munafunce a harkar siyasa kana gaba-gaba. Kaine! Kaine! Kaine. To kafa shirya, akwai babban aiki a gabanmu wanda baka san ranar da zai zama MAFARI gare ka ba. Akwai É—an É—anar raÉ—aÉ—in zafin fitar RAI. akwai kwanciyar KABARI da amsa tambayoyin cikinsa. Akwai tashin alÆ™iyama, akwai HISABI, akwai makoma mafi girman tashin hankali. Sune guda biyu, dole, dole, dolene a cikin biyu sai kin/ka kasance a cikin É—aya. Wato WUTA ko ALJANNAHðŸ˜ðŸ˜. ZaÉ“i ya rage tsakanin ni da kai. Dan haka mu kasance masu sassautama zukatanmu. Mu guji duk wasu mugayen ayyuka da ruÉ—anin duniya fa shaiÉ—an ke É—ibarmu garesu komai Æ™anÆ™antarsu. Mu zauna da mutane lafiya dan bamu san randa malaki'an mutuwa zai Æ™wanÆ™wasa mana Æ™ofofinmu ba. Mu sauke hakkin na Æ™asa da mu, mu kiyaye cin hakkin koda iyalanmu ne. Mu bama Æ´aÆ´anmu tarbiyya ta Æ™warai, mu nema daga hankalinmu, muyi haÆ™uri da kaÉ—an, wataran sai UBANGIJI ya bamu mai yawa ta hanyar da bamuyi zato ko tsammani ba. Ba sai munyi shirka, ko tauye hakkin wasu zamu samu arziÆ™i ko É—aukakar duniya ba. Daga É—aukaka har dukiyar ba masu amfanar damu komai bane idan har bamubi ALLAH da MANZONSA ba. Domin ita DUNIYA ba nan bane gidan GUMURZUN. LAHIRA itace kankat, sai mai RABO kuma ke samun tagomashi da ROMON dake can. Mu yawaita istigfari, mu yawaita istigfari, mu yawaita istigfari. ALLAH ka gafarta mana ka gafartama iyayenmu. Ya rabbi kasa muyi dawwamammen tuba kafin mu koma gareka. Ya rabbi kasa ranar mutuwar mu ta kasance ranar farin cikin mu, ya rabbi kasa kwanciyar kabari ta zama hutu a garemu, ya rabbi kasa mu kasance a cikin tawagar da MANZON ALLAH zai ceta yayi kuma alfahari damu ranar TSAIWA matsayin al'ummarsa. Ya rabbi kasa duniya a tafukan hannayenmu kada ta kasance a cikin zukatanmu. Ya rabbi kasa kar muje da arziÆ™i gaban UBANGIJI, hakkokin MUTANEN da muka zalunta a duniya ya cinyesu mu koma MATSIYATA. dan arziÆ™in DUNIYA É—an uwa, Æ´ar uwa ba shine arziÆ™i ba. ArziÆ™in tashi da ayyuka Æ™yawawa a ranar sakamako, amma haƙƙokin mutane ya cinyesu bayan an gama biyansu mu tashi taskarmu babu komai sai zunubansu da namu shine babban talauciðŸ˜. To ALLAH ka bamu ikon sauke hakkin mutane da ke a kammu, mu kuma nema gafararsu kafin mu koma garesa. Ya rabbi kasa mu karÉ“i LITTAFINMU da hannun DAMAðŸ˜ðŸ˜. Ya UBANGIJI, ya RABBI, ya ALLAH kasa ALJANNA ta kasance makomarmu ni da ku da iyayenmu baki É—aya ðŸ˜ðŸ˜ðŸ˜ðŸ™â€......âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.