Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TSUTSAR NAMA BOOK 1.txt
Chapter 201 of 264
Zazzabi ya tasani gaba posting yanzu sai a slow. Ayi hakuri dai in sha ALLAHU muna gab da tsargewa kowa ya huta🥲.
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ðŸ˜ðŸ™_*
*_Typing📲_*
*_ðŸ›TSUTSAR NAMA....!!ðŸ›_*
_(Itama nama ce)_
_ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»_
_ð‘©ð’ð’𒌠ð’•ð’‰ð’“ð’†ð’†_
_ð‘·ð’‚ð’ˆð’† ð’”ð’†ð’—ð’†ð’ð’•ð’š-ð’ð’ð’†_
.......Washe gari tunda Baba prof da Hajiya ƙarama suka dawo hayyacinsu duk sai suka matsa a sallamesu a safiyar. Iya ƙoƙari doctors ɗin sunyi dan ganin sun fahimcesu musamman ma Baba prof da tai masa illa a inda ya kamata ya samu kulawa amma sam hakan yaƙi yiwuwa. Dole suka haƙura suka sallamesun. Dama shi Paah tun a daren Maash yasa aka sallamesa saboda Ummie ta tada hankalinta akan zataje asibitin zaman jiyyarsa. Shiko bai amince da hakan ba. Shiyyasa ya yarda da a dawo da Paah ɗin gida likitan ya cigaba da zuwa dubashi anan.
Kai tsaye sashen Maash ɗin aka kaisa ɗakin da Ummie take. Sai ganinsu kawai tayi. Sosai ta nuna farin cikinta taita sanya musu albarka. Su dai basu ce komai ba musamman ma Maash da ke matuƙar jin zafin Paah har yanzun. Isma'il ne yay kiran Maash ya sanar masa ai an sallamo Baba prof gashi a gida. Baiyi mamakin hakan ba, dan haka baice komai ba sai murmushi. Lokacin da kuma yake fitowa ya shiga ya duba Paah ya fito zasuyi break fast su Fahad ke sanar da itama Hajiya ƙarama ta dawo gida yanzun nan. Dama su su Hajiya Mammah tun jiya aka sallamosu. Uffan shi dai Maash baice ba, sun kuma san bazai ce ɗin ba daman....
✨✨✨✨
Iya faÉ—in yanayin da Baba prof ke ciki kawai sai dai kintace, dan a matuÆ™ar harmutse yake. Duk da yanda yake jin rashin Æ™arfi a jikinsa suna isowa gida wanka yay tare da yin shiri cikin manyan kaya. Sai da ya fito sannan ya tuna babu drivernsa fa a gidan yanzu. Gashi bai san ina Commondo ya kaisa ba. Zaune ya kai cikin kujerar falon kawai yay shiru. Sai da yaja tsahon lokaci a haka kafin ya É—auka waya yay kira. Ana É—agawa da ga can batare da ko sallamar da akai masa ya amsa ba cikin bada umarni ya furta, “Ka sameni a gida yanzun nanâ€. Ƙitt ya yanke kiran.
Sake zabga tagumi yayi na wani lokaci, sai kuma ya miƙe ya fara safa da marwa a falon cikin rashin ƙarfin jiki. Tsahon awa ɗaya ciff sannan Uncle Abdullahi ya iso gidan. Ya nuna mamakin ganin mahaifin nasa a gida, kasancewar duk sun san bai isa a sallamesa ba haka da wuri dan jikin nasa da saura. Ga Doctors ɗin ma sun tabbatar da yana buƙatar hutu..
“Baba ina kwana? Yaya Æ™arfin jikin?â€.
Ya faɗa cikin ƙoƙarin danne komai dake a ransa. Shiru Baba prof bai amsa ba, sai da yaja lokaci mai tsaho sannan ya juyo a wani irin yanayin mai wahalar fassara yake kallon sa. Kasa jurewa Uncle Abdullahi yay ya duƙar da kansa ƙasa, ya san minene laifinsa, ya kuma shirya amsa komai da za'a tuhumesa da shi. Kamar ko yanda yay zato a zafafe Baba prof ya furta,
“Abdullahi!! Wanene ni a wajenka?â€.
Sosai tambayar ta bama Uncle Abdullahi mamaki, amma ya daure kansa a Æ™asa ya amsa da, “Baba mahaifina ne kai, wanda yay sanadin kawoni duniya, ya tarbiyyace ni ya tufatar da ni da ciyar dani a lokacin Æ™uruciya da kula da ilimina duk bisa amincewar UBANGIJIâ€.
“Ban yarda da hakan ba Abdullahi. Ƙarya kake yi!. Da ace ni É—in mahaifinka ne da baka zaÉ“i wata rayuwa bayan idanuna ba. Da ace ka yarda ni Adamu ni na ciyar da kai, na tufatar da kai, na biya maka kuÉ—in makarantar da har kayi kaurin wuyan aikata abinda ka aikata to lallai fa da baka kasance wani abu a bayan ganina ba. Abdullahi idan ban manta ba ni da kaina na hana É—an uwanka aikin interpol a sanda ya Æ™wallafa ransa. Amma shine kai ka zagaye ka zama jami'in sirri bada sani na ba. Hakan na nufin akwai wani abu a ranka ke nan ko kake shiryawaâ€.
Hankali tashe Uncle Abdullahi ya ke girgiza ma Baba kai. “Wlhy Baba sam ba abinda kake zargi bane ba. Kuma a lokacin daka hana Yaya Mu'azz zama jami'in interpol na É—auka wannan aikinne kawai baka ra'ayin muyi. Zama wannan jami'in kuwa wasu dalilai ne suka kaini ga zama hakan. Ban kuma É“oye ba domin wata manufa tawa sai dan yanayin aikina kenan. A jiyan ma dole ce ta tilasta ni fitowa har duniya ta sanni da wannan matsayin. Amma idan har na É“ata maka rai ka gafarceni dan ALLAHâ€.
Shiru Baba prof kamar bazai tanka masa ba. Sai da ya mula dan kansa kafin cikin bada umarni ya furta, “Bazan taÉ“a aminta da kai ba Abdullahi a yanzu sai na tabbatar. Sai dai a matsayina na mahaifi ina baka umarnin ka saki wannan yaron Commondo....â€
A bala'in firgice Uncle Abdullahi ya É—ago yana kallonsa. Har bai san sanda ya furta, “Baba saboda mi? Akan mi kuma zanyi hakan bayan shi É—in mai laifi ne. Dukkan bincikenmu ya tabbatar mana da cewar da hannunsa a yin kidnapping É—in Yaya Mu'azz. To wai kai minene ma haÉ—inka da shi da har kake so a sakesa Baba?â€.
“Babu ruwanka da alaÆ™ar dake tsakanina da shi. Kidnapping Mu'azz kuwa ni da kaina zan hukunta shi na kuma ji ba'asinsa nayin hakanâ€.
Wani murmushin É“acin Rai Uncle Abdullahi yay da faÉ—in, “Baba to ai kai ba jami'in tsaro bane. Dan mi zan barka kayi hakan? Sannan babu ta inda dokar Æ™asata ko aikina suka bani damar sakin Commondo a halin yanzu. Saboda yanzu haka ana kan binciken mugayen ayyukansa ne ma. Shawarar dazan baka ma shine Baba kai gaggawar barranta kanka da shi idan ma wata alaÆ™a ta taÉ“a alaÆ™antaku. Dan wannan mutumin mugayen ayyukansa zasu iya kaisa Æ™asa dama duk wanda yake tare da shi. Ka gafarceni Baba na barka lafiyaâ€. Ya Æ™are maganar yana miÆ™ewa ya fice. Dan gaba É—aya kansa juya masa yake. Idan bai bar gaban Mahaifin nasa ba zai iya rasa control É—insa ne gaba É—aya...
Ko sau ɗaya Baba prof ya kasa motsi. Sai kalaman Uncle Abdullahi ne ke masa wani irin amsa kuwwa acikin kunne har bai ma san ya fita a falon ba. Cigaba da jin sautin muryar Uncle Abdullahi na masa ihu cikin kunne ya sakashi fassa wani ihu shima yana wancakalar da Centre table ɗin gabansa. A guje wasu a cikin ma'aikatan gidan suka fara rige-rigen shigowa ciki harda Kuku da ke lafe yana jin komai. Sai dai shi kansa a yau ba ƙaramin girgiza zuciyarsa tayi ba da ganin abinda bai taɓa zato ba. Yanzu nan duk irin aibanta Baba prof da tsiyatakunsa da ya dinga yi a wajen ogan nashi ashe mahaifinsa ne. Kan bala'i jan. Wannan wace kalar cakwakiya ce haka. Sai yanzu ya fassara sunan Uncle Abdullahi da ƙyau. *_Abdullahi A.KM_* wato (Abdullahi Adams K/Mashi) kenan dai. Jiyyar gaba ɗaya haddarsa ta gama gogewa. Jiyay kawai buƙatar ganin Maash yake, shin shima yasan ogansa kawunsa ne ko kuwa sai a jiya da yay bayani?.
Da ƙyar suka samu Baba prof ya zauna. Haka suka shiga kimtsa falon shi kuma ya shige bedroom. Giyarsa ta samu ya kwankwaɗa ya zube ƙasa sai barci. Dan inba hakan yayi zuciyarsa zata iya bugawa a yanzun nan.....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.