Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TSUTSAR NAMA BOOK 1.txt
Chapter 101 of 264
Koda suka iso Nigeria tun a airport suka sake nema Mansoor suka rasa. Tashi hankalin Mamy ya sake yi, bata ko saurari Dad ba ta shiga taxi tace ya kaita anguwar su Sakina. Dan suna da gida anan Kano da in sunzo suke sauka. Attahir ne cikin damuwa yay ƙoƙarin tsaidata, amma sai bata ko sauraresa ba dan haka yay zuguy yana kallon motar. Sai kuma ya juyo yana kallon Dad da shima yake tsaye cikin matsanancin ɓacin rai bai ce komai ba. Rasa abin cewa Attahir ɗin yayi, sai kawai ya duƙar da kansa yay shiru zuciyarsa duk a dagule dan shi kam ya rasa mike faruwa haka kuma a tsakanin iyayen nasu cikin kwanakin nan.....
💞â💞â💞
MAASH
Har dare bai san inda hankalinsa yake ba. Sai gabannin asubahi zazzaɓin ya sakesa. Ajiyar zuciya ya ringa saukewa a jajjere. Kafin ya miƙe zaune cikin dauriya saboda kiraye-kirayen sallar asubahi da ake tayi tako ina. Cikin nauyin jiki da rashin ƙwari ya nufi bathroom yana haɗa hanya. Ruwa mai zafi ya samu ya shiga. Sai da ya tabbatar ya ratsashi tare da watsakke masa jiki sannan yay wankan da alwala ya fito. Dukkanin sallolin daya rasa jiya saboda yanayin da yake ya fara ramawa. Bayan ya idar da sallar asubahi har zai kwanta sai kuma zuciyarsa ta gargaɗesa akan hakan. Alkur'ani ya ɗauka ya fara karatu, tun yanayi da ƙyar har jikinsa ya fara sakewa nutsuwa ta fara riskarsa. A jajjere ya dinga sauke ajiyar zuciya nan ma. Sai da ya kai har inda yake buƙata kafin ya miƙe ya hau gadon ya kwanta. Shi ba ma'abocin yawan kwanciya barci bane musamman ma na safe saboda yawan uziri. Amma rashin samun na dare yana kwanciya barci mai nauyin gaske yay awon gaba da shi...
A lokacin da Maash ke a sashensa yana fama da ciwo a É“angaren Samraah tsaye take Æ™yam akan Æ™afafunta tana miÆ™ama UBANGIJI kukanta. Kaso biyu bisa ukun daren ta rayashine da Æ™iyamullail. Kafin ta É—ora da karatun Alqur'ani har asubahi. Tana idarwa duk da barcin dake a cikin idanunta haka ta É—ora shi ta cigaba dayi. Tanayi tana tofama a ruwan data ajiye botiki guda. Da yake tasa himma kafin goma tayi taci kusan izifi ashirin da wani abu. Motse-motsen da Ummie keyi ya fargar da ita, (yunwa) ta ayyana a ranta tana Æ™oÆ™arin miÆ™ewa. Ilai kuwa sai gashi tana farkawa da kiran sunan “Muhammad yunwa. Yunwa Muhammad†ta fara cin karo. Zumut ta miÆ™a ta nufeta har tana tuntuÉ“e da katifa............âœï¸
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ðŸ˜ðŸ™_*
*_Typing📲_*
*_ðŸ›TSUTSAR NAMA....!!ðŸ›_*
_(Itama nama ce)_
_ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»_
_ð‘©ð’ð’𒌠ð’•ð’˜ð’_
_ð‘·ð’‚ð’ˆð’† ð’•ð’‰ð’Šð’“ð’•ð’š ð’†ð’Šð’ˆð’‰ð’•_
........Sosai mamaki ya kama Paah jin wai Maash ya sake barin gidan. A take ya ɗaga waya yay kiran Hayatu dan yasan ko kiran Maash ɗin yay a yanzu ba lallai ya ɗaga ba. Dan a ganinsa har yanzu fushi yake akan abinda ya faru. Amsar da Hayatun ya bashi na tabbacin sun wuce ya sake tsaya masa a rai. Sai kawai yaji duk yana ƙara zargin kansa da kansa. Da sauri ya miƙe ya nufi sashen Hajiya Babba. Sai dai me ya samu sashen a kulle. Kai tsaye zargin Maash ne ya kulle yazo masa. Jiki a sanyaye ya sakko yana jin lallai dole shima ya nufi Chaina a yau ko gobe su haɗu da Maash ɗin.
🌟🌟🌟
Cikin barci ya farka da matsanancin ciwon kai. Duk da yanda yaso samun nutsuwa hakan ya gagara. Har magani yasha duk da tsanar da yay masa amma ina. Ya jima yana tsintar kansa a irin wannan halin a mabanbanta lokuta. Sai dai na yau ya tsananta sosai. Dan duk yanda yaso sake komawa ya duba Ummie ya gagara hakan. Har dare yana cikin mawuyacin hali. Salla kawai ke tada shi. Ai kusan ƙarfe ɗaya babu shiri dole yabar gidan. Dan ji ya dinga yi tamkar ana masa yayyafi da garwashin wuta. Ya tsani gidan da komai na cikinsa matuƙa. Kasancewar cikin dare sosai ya fita a gidan babu wanda ya sani da ga ALLAH sai shi sai mijin Mama Balki da ya kira ta waya. Hatta da securitys ɗin gate sanin matsayin Malam Baba agidan yasa koda zai fita da baƙo babu wanda ya iya cewa komai. Azatonsu ma ko mai magani ne tunda yau ciwon Hajiya Babba ya tashi sosai tun safe aketa fama..
Can wani gidansa ƙarami dake a wata anguwa daban dole Malam Baba ya kaisa, anan yay jiyyar kwanaki uku ya dawo ragal, sai sannan yake ji a bakin Malam Baba ai jikin Ummie ya motsa sosai amma itama dai da sauƙi. Dan baƙuwar yarinyar nan na tsaye akan al'amarin dan ma taji mata ciwo. Kasa cewa komai Maash ɗin yayi, sai guri ɗaya daya zubama idanu kawai a yanayin da baka isa tantancewa a kansa ba....
★★★★
Sam gidan babu kwanciyar hankali. Dan tun washe garin da naima Ummie kitso jikinta ya birkice. Sai ma abin ya nema fin na baya. Dan a ranar naci ɗan karan dukan da kowa sai da ya tausaya min. Dan har asibiti sai da aka kaini. Duk da azabar wahalar da naci a hannunta hankalina nakanta. Sam na kasa samun nutsuwa. Akoda yaushe cikin nazari da aune-aunen abubuwa nake. Dan motsawar ciwon nata ya tsaya min a rai. Ga duk wannan abun da akeyi banga ko giccin ɗanta ba a gida. Alamu kuma sun tabbatar da baya nan kenan. Sosai naji takaicinsa ya mamayeni. Har inaji a raina anya mutumin nan da curin hankali a brain ɗinsa kuwa. Rashin man kan yayi yawa matuƙa. Mahaifiya ai tafi gaban wasa. Amma shi duk motsinsa dai a neman kuɗi yake kawai baya tuna gabansa da bayansa. Kai dolene na saita masa layi ko zai tsireni, tunda na fahimci maganata ta ranar bata dawo dashi a hayyacinsa ba.
Bayan kwanaki uku jikinta yayi sauƙi Alhamdullah. Haka na sake komawa gareta. Ranar kuka nayi sosai ganin sun ɗaureta. Haka na kwanceta ina zubda hawaye. Na rungumeta a jikina duk da nasan komai zai iya faruwa. Sai dai alhmdllh babu abinda tai min face kukan yunwa-yunwa. Yau ma kamar ranar haka na fita na nemo mata abinci, ina bata ta ɓingire barci. Gyaran sashen na shiga yi bayan nayi kiran Mama Bilki ita kuma ta taimaka ta mata wanka. Dan sabbin masu aikin nan da aka kawo fa sun gudu tun daren da abin ya faru ta fashema ɗaya kai. Bayan Mama Balki ta mata wanka da taimakonta na ƙarasa gyaran sashen. Sai ko gashi ita da shi duk sun dawo a hayyacinsu. Duk wanda ya shigo ma sai yayi sha'awa. Nata yima Mama Balki tambayoyi akan wannan al'amari sai dai bata ce da ni komai ba. Dan haka nima na haƙura na duƙufa kula da al'amarin Ummie ɗin tare da ƙara ƙaimi. Dan yanzu ruwa na samu na ajiye na gorori a cikin kowane kwana biyu saina sauke Alkur'ani a ɗakin da tofawa cikin ruwan. Sam na hana kaina isashen barci. Nama daina fita a sashen gaba ɗaya sai neman abinci. Da farko Hajiya ƙarama taso taka min birki akan abinda nake yi ɗin, sai Hajiya Mammah tace ta barni. Duk da abin ya bani mamaki dan ita ma nai zaton zata hanani sai bance dai komai ba. Sai daga baya nakema Mama Balki zancen, shine tace ai Paah ne yace a barni na cigaba da kula da Ummie ɗin, sai dai bata san dalilin Hajiya ƙarama na son hanani ba. Kodan ita likitace tana ganin kamar Ummie zata iya cutar dani ne oho.
Na gamsu da hakan, dan haka na cigaba da sabgata. Sai dai na sakama kowa na gidan ido dan ina son sanin wanda ke É—aure Ummie É—in a duk lokacin da ciwonta ya motsa....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.