Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TSUTSAR NAMA BOOK 1.txt
Chapter 238 of 264
Ransa a dagule ya dawo Dubai ɗin nan kamar yanda ya barta cikin ɓacin rai. Dan akwai kayansa daya kamata tun six days ago ace suna Nigeria kawai ake sanar masa wai an riƙesu a ƙasar Camaroon. Yayi iya ƙoƙarin sa ta hanyar waya dan ganin kayan sun isa saboda muhimmancinsu da mabuƙata kayan dake jira amma sai wani banza ke raina masa hankali. Gashi anan Dubai ɗin ma abu mai muhimmanci yake yi. Ga matarsa na hanyar tahowa. Duk da yaso ace da kansa yaje tararta hakan bai yiwu ba, dan yayi zaman meeting da wasu manyan ƴan kasuwa na duniya akan wasu matsaloli. Yana cikin meeting ɗin ya samu saƙo wai ana neman juyar da jirgin kayansa inda ya fito an hanashi ƙarasawa Nigeria. Dole yay excusing kansa daga wajen Meeting ɗin cikin abinda bai fi awa ɗaya ba yabar Dubai ya nufi Camaroon ɗin. Tunda yaje can bai huta ba, yanata faman kaiwa da komowa shi da lawyers nashi dan ƙulli ne babba ake neman masa da gwamnatin ƙasar. Sai a yau ya samu kansa kayan suka wuce Nigeria, ko tabbatar da tashin nasu baiyi ba ya fallo ya koma Dubai ɗin dan hankalinsa duk hana kanta. Shine ya iso da ɗokin ganinta amma ko ɗaga kai ta kallesa ma batai ba. Yaso mata uziri sai yaga kawai ta ɗago ta gaida Hayatu batare da shi ko ma kallonsa tayi ba. Wane kalar wulaƙanci ne hakan, matarsa, da ya ɗauka dukkan kansa ya bata da kowane irin matsayin girmamawa. Kai ina baya son raini kuma sam. Koda wani laifi ya mata ya kamata ta haɗiye a gaban koda Ummiensa ne sai sun keɓe ita da shi ta faɗa masa ko ta nuna fushin da shi, idan ba ban haƙuri ne zai bata, idan na ya fahimtar da ita ne zai yi ƙoƙarin hakan. Amma har yanzu bata san wanene shi ba.
Wankansa yayi ya haye gado yay kwanciyarsa. Dan kwana biyun nan sam baya ko isashen barci, ga wata yunwa da yake ji mai tsanani amma yafi buƙatar barcin dai first. Barcin kusan awa biyu yayi alerm ya tada shi, ganin lokacin salla yayi ya miƙe da ƙyar zuwa bathroom. Ruwa ya sake watsama jikinsa dan ya warware da ƙyau, yay alwala ya fito. Yana ƙoƙarin saka kaya ta shigo ɗakin, bai nuna yasan da shigowar tata ba kamar yanda itama ta nuna bata san da shi ba tai waucewarta bayi. Sai da ta shige ya zubama ƙofar cat eyes ɗinsa da suka sauya kala. Komai baice ba ya saka sallaya ya kabbara salla. Bayan ya idar tana daga gabansa tana tata ya ɗauka waya yay kira. Cikin harshen larabci yay magana da bata wuce ta sakan huɗu ba ya ajiye yana miƙewa. Bakin gadon ya koma ya zauna yana latsa wayar, mintuna kusan goma aka danna door bell ɗin gidan, tashi yay ya fita, babu jimawa ya dawo ɗauke da ƙyaƙyƙyawan kwando a hannu. Cikin set na kujerun da aka ƙawata bedroom ɗin dasu ya koma ya zauna, bayan ya mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa, dan har yanzu tana a saman sallayar bata tashi ba. Abincin da aka kawo masa ya ɗan tsakura kaɗan ya ture...
Dai-dai nan na tashi daga zaman sallayar daya ishe ni. Veil ɗin kaina na warware, yanzun ma batare dana kala inda yake ba na nufi ƙofa zan fita amma sai na jita a rufe. Mamaki ya kamani dan nasan dana shigo dai ban kulle ba. Numfashi na ɗan furzar na koma kawai saman gadon nai kwanciyata. Ina kwance kamar mai barci sai dai idanuna ne kawai a lumshe naji alamar tsaiwar mutum a kaina. Sai ƙamshin turarensa daya cika min hanci matuƙa. Kamar zan share sai dai na buɗe idanun. A kansa na sauke su, ganin yanda ya wani kafe cikina da ido yasa na yamutse fuska. Kamar na balla masa harara sai dai na daure na sake maida idanun na rufe. A matuƙar mamaki naji saukar muryarsa a kaina wai yana da buƙata..
Kutumelecy ban taɓa sanin guy ɗin nan tantiri bane sai yau. Kasa jurewa nayi na buɗe idanuna a kansa jin ya kwanto gefe na. Sai kawai na yunƙura zan bar masa gadon. Ya maida ni ya kwantar. Ƙoƙarin turesa na shigayi sai dai ko gezau. Ƙarshe takaici yasa na sakar masa kuka. Amma hakan bai sakashi fasa abinda ya ambata ɗin ba. Sai dai duk yanda yaso ya samu haɗin kai daga gareni bai samu ba. Bai kuma fasa bina a cikin nutsuwa ba. Niko tunda ya barni sai na juya masa baya kawoi ina raira kuka. (Wato bily fushin mai ciki sai addu'a kawai, dan har cikin ƙasan raina haushinsa nake ji). Yanzun ma komai baice min ba ya ma tashi ya wuce bathroom abinsa. Aiko na sake hawa fummm...
Haka yayo wankansa ya fito, sai da ya kammala gyara jikinsa cikin bada umarni ya da dakewar nan tasa a daÆ™ile ya furta, “Five thirty zamu wuceâ€. Daga haka yay ficewarsa. Yau na sake tabbatar da rayuwar aure haÆ™uri ce kawai. Duk kuma daÉ—inka da miji sai ya baka wannan maÉ—acin. Nima ji nake Æ™asar kawai nake son bari, sai kawai na miÆ™e na gyara jikina na shirya. Sai da nai sallar la'asar na Æ™arasa kimtsawa na fito duk da da sauran lokaci. Babu kowa a farlon sai television, na wuce na É—auka ruwa na koma na zauna a kujera. A haka su Aunty Falaq suka fito suka sameni suma cikin shiri. Damuwata na haÉ—iye na É—auka Awwab dake Æ™usha Æ™ushin kuka. Batare da mun zauna ba duk da saura kusan mintuna arba'in Hayatu yace muje anzo É—aukar mu. Nayi zaton shi yana waje, amma sai naga mu kaÉ—ai ne muka shiga motar, koda muka iso airport ma babu shi, sai da muka shiga jirgi bayan cikar lokaci mun zauna sai gashi ya shigo shi da Juliet. Dama a wuya nake, ga shi kuma da wannan shegiyar Æ™andararriyar baturiyar. Su duka ban kallesu ba, sai da ya zauna a kusa da ni cike da iyayi ta ce min, “Good evening†tana ranÆ™wafowa da tab a hannu wai zata nuna masa abu.â€
Ai bamma san na buga mata wata tsawa ba cikin rufewar ido na furta, “Hy bar nan!!â€.
Ba ita ba har shi uban gayyar sai da ya kalleni. Na watsa musu harara su duka yayinda ita jikinta ma ke rawa. A daburce ta shiga bani haÆ™uri da Æ™oÆ™arin mun bayanin abu zata nuna masa mai muhimmanci. Nima sai na sake fusata na ce, “Okay bazaki tafin ba kenan ko?â€.
Zata sake magana yay mata nuni data wuce. Sim-sim ta tafi har tana waigena. Na sake balla mata harara sai ta zabura da sauri ta Æ™arasa ficewa a wajen. Ƙwafa nayi da faÉ—in, “Da ki tsaya mana. ALLAH da sai an fitar da ke a karye daga jirgin nan. Ki cigaba da shiga mun hanci karki fasa ramammiyan banza jiki duk Æ™ashi ko Æ™yan kallo babu subi su nanewa mazan mutane da sunan aiki mayuâ€.
Gyaran murya ya É—an yi. A fusace na juyo ina harararsa. Na ce, “Oh ko zaka shigar mata ne?â€.
Kansa kawai ya É—an jinjina min alamar a'a, idanunsa dake wani lullumshewa a kaina Æ™yam. Cikin masifar dai nace, “Aida ka shigar mata duka zan iya dakuâ€. Na É—auke kaina nama kwanta ina wani buÉ—ewa da Æ™yau yanda zanji daÉ—i.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.