Tsofaffin Hausa Novels

Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: TSUTSAR NAMA BOOK 1.txt

Chapter 209 of 264

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒔𝒆𝒗𝒆𝒏𝒕𝒚-𝒏𝒊𝒏𝒆_

.......Mu dukanmu salati kawai mukeyi da mamakin hatsabibanci irin na wannan mata. Sai kace ba mace da aka sani da taushin zuciya da tausayi ba. Lallai al'amarin na matar nan babbane. Tsahon lokaci babu wanda ya iya cewa komai hatta shi mai gayya da aikin. Sai da Jaga ya ce, “Humm ai dama na faɗa maka babban yaya. Akwai abinda take yi a asibitin nan shiyyasa ta bashi muhimmanci sosai. Dan matar nan ANGULU ce wlhy bata jewar banza. Shi kansa Commondo ɗin amfani kawai take yi da shi. Ai ko yanda kuɗaɗe ke shigar mata duk da tana ɓoyewa tuni ya kamata a zarge ta da hakan”
Cikin jinjina kai Hayatu ya ce, “Tabbas maganarka haka take Jaga. Dan ko shi kansa Baba yanzu na fara tunanin anya matar nan ba itace ke amfani da shi ba”.
“Zata yiyu bazata yiwu ba oga Hayatu. Saboda magana ta gaskiya shima tsohon nan hatsabibin kansa ne. Ko maganar saka yara a containers ɗin babban yaya na kwanaki wlhy ina da tabbacin yana da hannu a ciki. Dan ni na faɗa muku wannan Mr Paul fa abokin huɗarsa ne sosai. Sune ma suketa son jansa ya shiga siyasa yana ƙi, bakuga yanda aketa jan shari'ar ba ma. Yanzu dai gasu can na barsu a halin ruɗani da ƙaulanin kasa banbance ni fatalwar ne ko kuwa ina raye. Duk da dai nasan zuciyarsu tafi karkata ne a ni fatalwa ne. Amma a taron sunan nan na gobe zan tabbatar musu ni mutum ne. Ruɗanin da zasu shiga shi zai sa su fara neman hanyar tabbatar da gaskiya, babban Yaya kuma sai yay amfani da wannan damar. Ni wlhy so nake ma Babban yaya yasa a saki Commondo nifa nafi son na kashesa da hannun....”
Ya kasa ƙarasawa saboda kallon da Maash ya masa. Murmushi na ɗan yi da girgiza kai. Hakama Hayatu sai da ya murmusa kaɗan. Sai TJ ne ya furta, “In sha ALLAHU bazaka sake aikata wani mummunan aiki ba Muntari. Na baya ma ALLAH ya yafe maka tunda Alhamdullah bama ka taɓa yin kisan ba dai”.
“Hakane kuma Yaya Tijjani”.
Jaga É—in ya faÉ—a fuska a marairaice kamar zai yi kuka.. Ni sai ma abin nasa ya bani dariya......

💦⭐💦⭐💦

Gaba ɗaya lissafin Baba prof ya gama rincaɓewa. Dan tunda Isma'il daya kawosa ya rakashi har Bathroom ya fita sai ma ya gagara yin wankan. Ga warin gudawar da yay a jikinsa na matuƙar damunsa. Amma ruɗanin ganin Jaga ya mantar da shi komai. Tabbas da farko zuciyarsa ta bashi Jaga fatalwa yay musu. Sai dai yanzu daya haɗa lissafi ya fahimci maganar Hajiya ƙarama gaskiyace kenan. Commondo na son cimma wata manufa shiyyasa bai kashe Jaga ba. Shiyyasa a yanzu ma da yake a hannun hukuma bai damuba, saboda yanada wanda zai masa aiki a waje. To amma Jaga sunan Awwab ya ambata ai. Ya ilahil alami. Shin ko dai Commondo shima ya koma ɓangaren Awwab ɗin ne? Tabbas idan hakanne zama fa bai gansa ba. Dole ne a gobe ayita ta ƙare kawai. Zaiyi amfani da taron da Nafisa ta sanar masa za'ayi a Mansion. Ƙasaitacen murmushi ya saki a hankali tare da sauke nannauyan ajiyar zuciya. Sai yanzu ne yaji ƴar nutsuwa na dawo masa. A gurguje yay wankan duk da jikinsa babu wani ƙarfi. Yau babu zancen shan barasa. Ɗakin sirrinsa ya shiga ya dinga haɗa duk wasu abubuwansa masu muhimmanci waje guda. Haka ya raba dare, sai da ya gama tsaff sannan ya bincika jirgin da zai iya tashi koma na wane ƙasa ne a gobe idan ALLAH ya kaimu ƙarfe huɗu. Yako samu mai zuwa Saudiyya, a take ya sayi ticket ta online ɗin. Bindigarsa daya jima bai yi amfani da ita ba ya ɗauka yayma zubin bullet taf sannan yay zaman yin dogon rubutu a takarda daban-daban kowanne da sunan ƴaƴansa. Suma ya kammala gab da asuba ya haɗasu ya ajiye. Sai lokacin ya samu giyarsa ya kwankaɗa son ransa sannan ya haye gado yay male-male.....

🌿✨🌿✨🌿

A lokacin da Baba prof ke wancan shiri anan Maash Mansion ma Hajiya ƙarama tunda ta samu ta sheƙama kanta ruwa akan batun Jaga sai ta fara samun ƴar nutsuwa. Ita dai tunaninta na nan akan Jaga fatalwa yay musu. Dan haka ta tabbatar ma kanta yin abinda ya dace kafin komai ya buɗe. Dan ta fahimci a yanzu Madam Jannifer da Commondo komai zai iya fita daga bakinsu. Hakama Baba prof a shirye yake da yin komai a kansu. Idan ko haka ne to batun ta kwanta a barci baima taso ba. Ita dama ta kammala dukkan shirinta game da kaf dukiyarta da harƙallolinta ta shirya ta yanda kota bar ƙasar zata cigaba da gudanar da komai a maɓoyarta. Hatta da sace Samraah ta gama da wannan matsalar, dan bazata taɓa barma Awwab ba, babu ruwanta da batun wani ƴar Abdul-wahab jirgin mota ce har yanzu tana sonta da kwaɗayin kasancewa da ita, ko cikin jikinta bai dameta ba zata zubar da shi da zarar sun bar ƙasar. Arwa kuwa da abarta zata tafi. Itama dai ticket ta siya ta online amma na ƙasar Dubai, daga can zata wuce ƙasar data gama tsarama kanta rayuwa da wani bazai taɓa tunanin tana a can ba saboda ƙasar ba wani wajen yawan zuwan mutane bane. Gaba ɗaya yaranta da ta gama shiryawa domin wannan yaƙi ta kira. Sai Marcel da shine uban tafiya. Abinda kawia ya banbanta shirinta da Baba prof ita sai nan da kwana biyu take shirin wucewa. Amma dai a gobe take son ai mata kidnapping duk wani wanda ke cikin list ɗinta. Saƙonta daga wajen Dr Khunal kuwa a daren yau zai iso Nigeria kamar yanda ya tabbatar mata. Dan tun ɗazu da sukai waya yace mata bazai ƙara minti goma da shi ba a hannu amma ya sake ninka mata kuɗin kuma a haka ta biya. Jirgin da ya taho da saƙon kuma da ayanzu haka yana a bisa hanya na tashi yay mata text da _Done_. Wannan ne ma ya bata ƙwarin gwiwar tunkarar Baba prof a ɗazun....

🤍💫🤍💫🤍

A nan ɓangaren Fahad da Hafizzullah kuwa su shirin shagalin sunan gobe in sha ALLAHU sukeyi hankalinsu kwance. Dan su kawai a rakwashe a ƙwalle a girgije shine nasu shirin. Ga mutanen Kano su Abba da wasu a cikin ƴan gwarzo na a hanyar zuwa a goben domin ganin Falaq da kuma halartar bikin suna duk da taso ace itace ta fara ziyartarsu amma sun dai ce sune zasu zo domin neman afuwar mama Balki. Dan hakama suka kwaɓeta gaya mata, hatta da Samraah ma bata san da zuwan nasu ba. Amma Maash da Hayatu duk sun sani, a jirgi ma zasu zo.
Abin da farko kamar wasa sai gashi dai gagarumin taron suna na niyyar haɗuwa. Dan daga abincin mutane ɗari da sukai niyyar yi sai Ummie tace a ninkashi ya zama na mutane dubu ɗaya za'a bada wani sadaka. Duk da ma bata san da zuwan baƙi daga Kano ba kasancewar har yanzu bata san alaƙar Hafizzullah da Samraah ba. Ba kuma tasan Samraah ɗiyar Jirgin Mota bace. Su Hayatu sun tsara sai a gobe zata sani in sha ALLAHU wajen taro. Koda Hajiya Mammah ta zagi Samraah da sunan ɗiyar driver a jiya kawai ta ɗauka hakanne amma hawai ta ɗauki abun da muhimmanci ba. Dan ko ɗiyar mai bara Awwab da Fahad suka kawo mata matsayin matansu zata goya musu baya kuma taso matan musamman idan sun kasance mutanen kirki masu tarbiyya.
Bayanin likitanta akan ba komai zai dawo mata kanta lokaci É—aya ba kamar da, ba kuma komai zata zurfafa nazari ko maida hankali akansa ba yasa yanda take É—aukar Hafizzullah É—an Mama Balki yasa suka barta a hakan kawai. Dama kuma bata tambayi kowa ba akan hakan ma.....

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.