Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TSUTSAR NAMA BOOK 1.txt
Chapter 233 of 264
*_BILYN-ABDULL ONLINE SHOPPING_* _Duniyar cancaɗa ado da kwalliyar birgewa. Kar ku bari ayi babu ku😘😘😘._
*_My account on TikTok_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram_*
I'm on Instagram as @balkissaibrahimmusa. Install the app to follow my photos and videos. https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
_Ina masu son zuwa ganin likita ko yawon buÉ—e ido Æ™asar Egypt?. To ku garzayo munada hanya mai sauÆ™i ta sama muku sauÆ™in tafiya cikin Æ™a'ida da bin dokar Æ™asa. Katafi anan cikin aminci, ka dawo kuma cikin aminci. Wajen kwananka a can zamu tanada, asibitin da zakaga likita duk zamu tsaya maka da tsayawar UBANGIJI. Hakama yawon hutawa zamu zame maka jagora. Kai ko hanyar zuwa domin sayo kaya duk muna da ita. Kai dai kawai kazo garemu kaga aiki da cikawa da iznin ALLAH. 09032345899. A nememu tanan ga masu buÆ™ata, dan ALLAH serious bama son latsi ko wasa dan ba wasan muka fito ba 😂ðŸ˜ðŸ‘ðŸ»._
......A tsare motocin da muke ciki suke tafiya saman titi tamkar an zana su. Duk ta inda muka gitta sai kaga idon mutane na binmu. Ni dai ina kwance a jikinsa ina game da waya yana kallona hannunsa a saman cikina yana shafawa. Jakin babangida da muka É—an hau ya sa na cije baki da miÆ™ewa zaune da Æ™yau saboda motsin da cikina yaya babu shiri, Æ™oÆ™arin tambayata yake lafiya ni kuma hankalina nakan mai agwalina dake bakin titi cike da barrow da idona ya hango min. Har mun É—an gota nace ma TJ ya tsaya. Tsayawar kuwa yayi, ni kuma na kalla ogan nasa daya zuba min ido. Batare da damuwa ba na ce, “Ya Awwab Please bara na sayi Agwalima É—in canâ€. Nai maganar ina zaro 1k a handbag É—ina. ƘoÆ™arin buÉ—e Æ™ofar motar nake ya riÆ™o hannuna. A marairaice na juyo na kallesa kamar zanyi kuka. Baice komai ba ya É—auke kansa tare da sakin hannuna ya buÉ—e side É—in da yake ya fita. Cikin rawar jiki TJ ya fita shima yana faÉ—in ya bari ya sayo amma ya É—aga masa hannu. Hakama Hayat da su Fahad ganin ya fito duk suka fito suma amma sai bai kalla kowa a cikinsu ba ya tsallaka wajen mai agwalima É—in. Tashin bal, gaba É—aya mutane sun zuba masa ido musamman ganin yanda yaje gaban mai agwalima ya tsaya. Shi kansa mai agwalima duk ya rikice dan duk wanda dai ya kalla wannan É—an gayen yasan baiyi kalar shan abun titi irin wannan ba, barema wai agwalima. Hannu ya bama mai agwalima alamar busabaha. Jikinsa na rawa ya waro idanunsa waje zai É“oye hannun, amma sai bai damuba ya riÆ™o hannun nasa shi kuma. Cikin dakewar nan tasa da silent voice ga hausa bai cika ba ya ce, “Ina son shi duka saka a ledaâ€.
“Agwalima É—in ranka ya daÉ—e?â€.
Mai agwalima ya faɗa cikin waro idanunsa waje fiye da ɗazun. Cikin halin ko'in kula ya jinjina masa kai. Sake ruɗewa mai agwalima yayi ya shiga kwasheta yana zubawa a bako. Yayinda masu wayoyi aka samu abin ɗauka kasancewar wani ya ambaci sunan Maash ɗin a wajen. Yana gamawa ya laluba aljihun farar shaddarsa da yau ma Samraah ta dage sai ya saka ya zaro kuɗi. Bai wani damu da dubawa ba ya ajiyema mai agwalima ya ɗauka bako ɗin zai wuce. Cikin sauri TJ da Hayat, Fahad, Hafizzullah suka zo dan su amsa amma nan ma ya hanasu sai da ya kawota har mota ya saka a sit ɗin gaba ya cira guda biyu ya buɗe side da nake ya ɗauka roban ruwa ɗaya ni dai ina binsa da kallo kamar wata sakara ya wanke a gwalimar fes sannan ya miƙo min.
Kasa koda motsawa nayi, sai idanuna na ne da suka cika da hawaye ke binsa da kallo, ɗan duƙowa yay ya hure min idanun tare da kamo hannuna ya ɗaura a gwalimar sanan ya rufe murfin ya zagaya nasa side ya shiga. TJ na gama rufewa na faɗa jikinsa kawai na ƙanƙamesa hawayen da nake riƙewa na gangaro min. Ku gane bawai yayi abinda maza da yawa bazasu iya bane ba ko basu taɓa yi ba, kawai dole ne abin ya bani shock musamman da na sani kuma da kuke biye da labarin nan kuka sani Maash yayi makamancin hakan abun mamaki ne.
“ShagwaÉ“a baâ€.
Naji saukar soft muryarsa cikin kunnena dai-dai yana É—agoni zaune da Æ™yau. ÆŠagowa nai na kallesa idanuna na sake cika da hawayen zanyi magana. Kansa ya girgiza min tare da kai yatsarsa ya É—auke hawayen. Sai kuma ya É—ago hannuna dake É—auke da agwaliman ya ce, “Ya ake ci?â€.
Murmushi na sakar masa ina É—an langaÉ“e kai na ce, “Bafa ci ake ba sha, bari ka ganiâ€.
Ban jira amsarsa ba na luguyguyta agwalima É—in yay ruwa sannan na sha shi, wani irin lumshe idanu nayi dan jinai tamun daÉ—i fiye da koyaushe. Jin an riÆ™o hannuna yasa na buÉ—e idanun, kan bakinsa ya kai agwalimar dana sha É—in shima ya sha. Da sauri ya saki hannun nawa yana dafe bakinsa. Cikin É—an waro idanu na ce, “Miya faru?â€.
“Tsamiâ€.
Ya faÉ—a fuska a yamutse kamar zai fasa ihu.
Bamma san dariya ya kwace min ba. Sai da ya dungure min kai yana faÉ—in, “Mugunta baâ€. Sannan na tsagaita. A haka muka iso gidan Abba. Tarba muka samu fiye data jiya. Dan yau iya danginmune kawai sai na Aunty Halima amaryar Abba dake shirin tafiya gida, dan har suyar namansu sun kusa kammalawa. Cike da farin ciki auta yazo ya Æ™adandaneni harda kukansa yana faÉ—a min yayi missing É—ina, miyyasa na tafi na barsa Bibaa nata dukansa. Bata masa homework bata masa wanka. Murmushi nayi ina mai lallashinsa, na kalla Bibaa da tai sumar tsaye kawai tana kallonmu. Hannunta na kamo itama na rungumeta a jikina. A mamakin kowa sai kawai ta saki kuka da babu wanda yasan dalilinsa.
Haka dai bayan an nutsu a falon baƙi iya manyan damu aka gaggaisa ni da Falaq muka fito, dama su Fahad basu shigo ba suna ɗakin Yaya Musaddiq abinsu. Sashen Mom muka shiga gaisheta. Dan tunda ta fito taga mune ta koma. Tana kwance a kujera ta juya ma ƙofa baya. Koda muka gaisheta Ummanta ta amsa wai barci take. Dariyama abin ya bani ni kam. Dan na fahimci bata san na ganta ne kawai, alhalin sanda muke shigowa suka fito suma, daga baya ne suka koma dakin. Ban wani damu ba muka fito. Sashen Aunty Halima muka shiga. Nan ne kam muka baje anata shan hira har ƙanwar mijin Aunty Zakiyya da tai min ƙunshi biki tai mana ƙunshi ni da Aunty Falaq. Sai ga Hafizzullah ya shigo da waya a hannu ya nuna mana wai mutane sun yi video ɗazun wajen sayen agwalimar da Yaya Awwab yayi gashi nan yanata tranding anata comments. Ni abun ma sai ya bani mamaki irin wannan rashin aikinyi haka har ina. Kowa yaji da sabgar gidansa amma sun zauna damuwa da abinda bai shafesu ba. Wannan nunawa ta Hafiz tasa ƴan uwa da basu san abinda ke faruwa ba suma duk suka gani. Nanfa abokan wasa suka tasani da shaƙiyanci aunty Falaq na kare ni da Aunty Halima.
Sosai kasancewa a gidan Abba yau ta sakamu a farin ciki, bayan sallar azhar sai ga Yaya Musaddiq ya iso. Fahad da Hafizzullah sunje airport sun É—akkosa. Sosai gidan ya sake rikicewa da farin ciki, sai lokacin ma nasan ashe su Yaya Awwab meeting sukayi akan batun auren Yaya Musaddiq É—in. Shi Abba da bai san Yaya Musaddiq nada budurwa ba yace ya bashi Bibaa. Sai da Yaya Musaddiq ya iso aka tambayesa kafin a sanar masa batun Bibaa yace ai yanada matar aure. Gaba É—aya sai jikin Abba yay sanyi, Gwaggo Gudidi zatai batun Bibaa yay mata alamar ta bari. Haka dole tai shiru. Bayan la'asar muka bar gidan. Companyn sa mukaje. Daga inda labarin Muhammad Awwab El-Mu'azz Maash da Samraah Abdul-wahab Gwarzo Sam-G ya fara kenan. Sai da naji hawaye sun cika min ido. Dan komai dawo min ya dinga yi tamkar yanzun ne yake faruwa, barema da muka shiga hall na meeting aka saka mana footage na ranar taron. Hatta da inda nake É—aukar video a wajen gawar Jaga da bai mutu ba. Rungumeni Ummie tayi tana hawaye. Yayinda Maash ya haÉ—amu gaba É—aya ya rungume shi kuma. Bamu baro cikin company ba sai goma da kusan rabi na dare. Muna fitowa daga Company tafiyar tamu ta rabu. Su Ummie akai gida da su mu kuma wata hanyar daban. ƘoÆ™arin tambayarsa nayi ya hana, dole naja bakin nai shiru har muka iso. Wani irin mugun waro idanu nayi ganin gidan da aka fara kawoni amarya matsayin matar Maash, ni kuma ina É—auka matar Mansoor. Rasama abinda zance masa nayi, na saki baki da hanci kawai ina kallonsa. Ido ya É—an kashe min tare da jan mayafina ya rufe min fuska sannan ya ranÆ™wafo ta bayana hannayensa duk saman kafaÉ—ata cikin kunne ya furta, “Idan za'a kawo amarya rufe fuskarta akeyiâ€. Ban iya nace masa komai ba. Face murmushi dana saki ta cikin mayafin. Hannuna ya kama har ciki, bai ajiyeni a falo ba ya kaini har bedroom É—in nan da tarihi bazai taÉ“a mantawa da shi ba. Sai da ya zaunar da ni a saman gadon sannan ya furta, “One minute†ya juya ya fita. Mayafin na É—aga ina bin bedroom É—in da kallo idanuna cike da hawaye komai na dawo min tamkar yanzu yake faruwa. Sai da naji motsin zai shigo mai maza na maida mayafin yanda yake. Abinda ya shigo da shi ya ajiye, na fahimci hakanne saboda Æ™amshin daya cika É—akin. Cikin nutsuwar nan tasa ya kai zaune kusa da ni, batare da yayi magana ba ya kamo hannayena cikin nashi, kaÉ—an ya murza yatsun da suka sha lalle yau wajen Æ™anwar mijin aunty Zakiyya, sai kuma ya É—agosu duk ya kai mitsitsin bakinsa ya sumbata. Hannayen ya saki ya kama gyalen ya buÉ—eni ya saka kansa ciki shima, sannan ya sake maidawa ya lulluÉ“e mu. Cikin wata irin murya mai taushi da sanyi ya furta,
“Mrs Muhammad Awwab!â€.
Har cikin tsakkiyar kaina naji wannan kira. A wani irin slowly na É—ago manyan idanuna da ruwan hawaye ya jiÆ™e na zubasu cikin dara-dara É—in cat É—in nasa da blue É—in ya fito sosai da É—igo-É—igon gold. Idan har kaga idanunsa haka to yana cikin matuÆ™ar farin ciki ne babu wata damuwa a tattare da shi........âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.