Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TSUTSAR NAMA BOOK 1.txt
Chapter 155 of 264
Da sauri na buÉ—e idanun a kansa. Kamar zan yi kuka na ce, “Tiger fa?â€.
Ido É—aya ya kashe min kawai yay gaba batare da ya amsa min ba. Yana buÉ—e Æ™ofar nima cikin shagwaÉ“a na ce, “Kaima Lionâ€.
Wani shegen murmushi kawai ya sakar min batare da yace komai ba ya buɗe ƙofar ya fita abinsa. Nima sai na samu kaina da sakin murmushin har haƙorana na bayyana. Sosai murmushinsa ke sakani farin ciki da nishaɗi. Dan yana bala'in ƙara ƙyau a duk lokacin da yayi sa. A gurguje na ƙarasa gyara ɗakin, nasa turare na fito falo bayan nayi salla. Fes na samu ko'ina anan alamar yasha gyara. Sashen Ummie na nufa ta hanyar da yabi da ni daren jiya. Na jima a can dan yau ma har sai da Mama Balki tace naje gasu Yaya Musaddiq nan zuwa harda Falaq. Cike da farin ciki da zumuɗi na tafin kuwa. Tuni na manta da halin da nake ciki saboda farin cikin ganin ƴan uwana duk uku. Nan fa na zauna muka buɗe sabuwar hira, har sai da Aunty Falaq ta tsareni naci abinci wai inji Yaya Awwab. Ni saima abin ya ban mamaki. Sai dai ban ja zancen ba na basar dan tunda na shigo na fahimci baya nan. Bayan sun tafi sallar la'asar nace mu shiga muma muyi a bedroom Aunty Falaq taƙi, nayi-nayi da ita tace ALLAH bazata taɓa iya shiga bedroom ɗin Yaya Awwab ba. Zata je sashen su Mama tayo. Sosai nake mamakin yanda suke mugun girmamasa, sai kuma hakan ya birgeni. Tare muka nufi sashen su Maman da ita. Bayan nama guard ɗinsa magana sun kulle sashen. A hanya muka gamu da Hajiya ƙarama ta dawo maybe daga asibiti ne oho mata. Sai dai muna gaisheta sai ga hajiyar nan data ɗakkoni da ga Abuja ta fito a mota itama. Sosai na zuba mata ido, dan tun ranar birthday ɗin nan ban sake ganinta a gidan ba. Itama kallona take kamar wata tsohuwar mayya. Dan haka na tsuke fuska ataƙaice na gaisheta naja hannun Falaq muka wuce. Har muka shige sashen Mama ina jin idanunsu a kammu su duka biyun..
Koda mukai sallar a sashen Mama Balki muka cigaba da zama. Suma su Yaya Musaddiq nan suka samemu. Sabuwar hira muka sake zamanyi yanzu kam harda Mama Balki da mijinta. Sunata bamu labarin Baba muna jin daÉ—i, sai gab da magriba Hayatu ya shigo yake cewa sun dawo. Yaya Musaddiq yazo suje ya Æ™arasa kimtsawa jirginsa na nine ne. Gaba É—aya kuma duk sai jikinmu yay sanyi, amma babu yanda muka iya tunda cigaba ne yazo mana. Sai kuma munyi haÆ™uri zamuci ribarsa. Anan mukai sallar magrib É—in, sannan muka É—an sake gyara jikinmu dan muma muna son masa rakkiya airport É—in. Ana kuwa idar da sallar isha'i sai gasu sun dawo. Nasiha sosai Mama Balki da Baba suka sake ma Yaya Musaddiq, sannan muka haÉ—u mukai masa addu'a. Ya sake kiran su Abba yay musu sallama har nima muka gaisa. Mun fito muka samu har mitsocin da zamu tafi da su airport É—in an shirya. Da farko nayi mamaki, sai da naga boss É—in ya fito alamar da shi za'ai rakkiyar sannan na fahimci dalilin shirya motocin da yawa haka. Dan kusan mota biyar. Biyu ta guards É—in sa. Sai Mama da Baba da Yaya Musaddiq suka shiga É—aya. Hayatu, Falaq, Hafizzullah suma suka shiga É—aya. Sai ni da shi a ta tsakkiya duk da ba haka naso ba. Amma Falaq ta turani a motar da tsiya-tsiya tana dariya. Waya yake sanda na shiga, dan haka muna haÉ—a ido nayi saurin kauda kaina. Sai da mukai nisa da gidan sosai sannan ya kammala wayar, batare dana kallesa ba nace, “Ina yiniâ€.
Bai amsa min ba, sai kaifin idanunsa da nake ji a kaina. Kasa jurewa nayi a hankali na É—ago na É—an kallesa. Caraf kuwa ya cafke idanun nawa a cikin nasa kamar dama mai jiran hakan. Wani irin kallo yake mun mai tada tsigar jiki da saka jini tsinkewa. Bamma san sanda cikin rawar murya da shagwaÉ“a na ce masa, “Ni ka bar kallonaâ€.
A hankali ya lumshe idanun ya sake buɗewa, sai kuma ya riƙo hannuna batare da yayi magana ba yanzu ma ya jawoni jikinsa kawai ya rungume. Luff nayi dan nima da alama abinda gangar jikin nawa ke buƙata kenan. Tuna bafa mu kaɗai bane akwai driver ya sani saurin yunƙurin tashi, amma sai ya maidani ya sake matsewa. A marairaice na buɗe baki zanyi magana ya dakatar dani.
“Bana son surutuâ€.
A hankali na sauke ajiyar zuciya tare da haɗiye abinda nake son faɗar kuwa. Dan ji nai bazan iya masa musu ba sam. A hakan muka isa airport ina a jikinsa. Munfi tsahon mintuna biyar bayan isowar tamu kuma kafin ya bari muka fita. Jinai gaba ɗaya kunya ta kamani ganin kowa ya fito ashe sai mune kaɗai a mota. Yaya Musaddiq yaja gefe sukai magana. Ban san mi suka tattauna ba dai naga Yayan nata murmushi da kallonmu. Sai kuma ya ɗan sosa kansa kamar wanda yaji kunya. Daga haka kuma naga shima Yaya Musaddiq ɗin yazo yaja Baba da Mama suka koma can. Anan ɗin ma sun ɗan jima, kowa fuskarsa ɗauke da murmushi idan ka cire uban gayyar da shi daman sai yaso yake murmushin. Shiyyasa da wahala ka gane farin cikinsa da akasinsa sai ka masa farin sani na haƙiƙa. Bayan sun gama zantukansu muma munata hirarmu suka dawo inda muke. Baifi mintuna biyar ba aka buƙaci ganin su Yaya a ciki. Tofa ai tuni kuma kuka ya tashi ni da Hafizzullah. Ganin haka itama Aunty Falaq ta fara. Mama Balki da Hayatu na ta mana dariya. Baba ko sai lallashinmu yake, shiko ai kamar ma bai san munayi ba. Haka dai muna ji muna gani Yaya Musaddiq ya wuce ya barmu da kewa.
Hafizzullah da Hayatu da Falaq can gida suka wuce. Mu kuma muka nufi gida muma inata mita dan nazata yau a wajenmu muma Hafizzullah ɗin zai kwana. Bai dai tanka min ba har muka isa gida. Hakan ya ƙara tunzurani. Dan haka nama rigashi fita a motar. Badan su Mama Balki dake wajen ba ma da bazanje sashensa ba. Nafi mintina goma da shiga sannan ya shigo. Lokacin har na shiga wanka. Na fito na sameshi zaune a bakin gado yana waya. Wucewa nai cikin closet ɗinsa na shirya. Ina fitowa yana shiga bayin shima. Sai na saka sallaya nayi shafa'i da wutri. Na idar na tashi na fita. A karo na biyu na shiga kitchen ɗin sashensa. Kai tsaye store na shiga na ɗakko catton biyu na bottle water na fito. Bedroom ɗin ba dawo dasu. Har lokacin kuma bai fito ba. Gaba ɗaya na fito da ruwan tare da buɗe musu murfi sai dai ban cire su a jiki ba sannan na ɗauka Alkur'ani na fara karatu. Surorin da duk akace suna karya sihiri nake karantowa ina tofawa a cikin ruwan bayan na ɗaɗɗaga murafan. Nayi nisa sosai a karatun sannan ya fito. Duk da nayi mamakin daɗewar tasa a ciki ban kula ba na cigaba da karatuna a nutse...
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.