Tsofaffin Hausa Novels

Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: TSUTSAR NAMA BOOK 1.txt

Chapter 96 of 264

💞💞💞💞

*_INDIA_*

Kuka take sosai da ƙoƙarin riƙe hannunsa daga haɗa kayan da yake tayi. Sai dai ko kallon inda take baiyi ba balle ya dakata da abinda yake ɗin. Cikin matsanancin takaici da fusata Attahir da ya gama harzuƙa da abinda ke faruwa ya fisge jakar yana mai dakama ƙanin nasa tsawa.
“Mansoor are you mad ne wai?”.
“Yes! I'm. Na ce I'm!. Ba haka kuke son ku ganni ba. Ko ba haka kukafi buƙatar ganina ba?. Nace muku ga wadda nake so, kun rabani da ita batare data ma wani cikinku laifin komai ba. Duk da abin yana min ciwo har yau har gobe ban taɓa ce muku komai ba. Amma hakan bai muku ba kuma sai ace min wai ga mata an ɗaura min aure da ita. Tunda nake da ku na taɓa ce muku ina son wannan yarinyar ne? Wlhy da nayi rayuwar aure da wannan yarinyar gara na shiga duniya. Na gaji da wannan rayuwar haka nan haba. Sai kace ba jininku bane ni, yaya kuke so na cigaba da rayuwa cikin salama ns wa....” kuka ya sarƙesa ya kasa cigaba da magana. Sai ma zubewa da yay a saman gadon yana mai dafe kansa dake sara masa da duka hannayensa biyu, tare da cusa hannunsa cikin sumarsa ya yamutsata.
Sosai jikinsu ya sake yin sanyi. Musamman Mamy da tafi kowa kasancewa a cikin É—imuwa. Itama zubewa tayi a gaban Mansoor É—in tare da kamo hannayensa cikin nata tana sake fashewa da kuka. Dad ne da tun É—azun baice komai ba ya furzar da iska mai kauri daga bakinsa, tare da kai hannu saman kansa ya shafo. Sosai kukan Mamy da Mansoor ke cizon zuciyarsa. Sai dai shi baima san ta inda zai fara ba game da wannan hargitsi daya rasa tushensa balle iyaka.....
Kakarin da Mansoor ya fara ne ya maidosa a hayyacinsa. Kusan a tare shi da Attahir suka zabura kansa. Yayinda Mamy ta sake ɗimaucewa. Yunƙurin amai ya fara sai ga jini bula. Ihu Mamy ta fasa, yayinda Attahir ya fita a guje yana faɗin bari yay kiran asibiti...
Kafin cikar mintuna goma ambulance ta iso. Lokacin da aka fito da Mansoor daga ɗakin hotel ɗin da suke ya gama fita a hayyacinsa. Dama yau kwana uku kenan da sallamosa baya kwanakin kusan wata guda daya kwashe yana jiyya. Samun lafiyar tasa ya saka walwala da farin cikin kowa dawowa a cikin ahalin nasa. Dan nan da kwanaki biyu ma suke shirin komawa gida Nigeria. Sai kuma aka samu akasi Husnah yarinyar Auntynsa da aka ɗaura masa aure da ita a randa aka fasa da Samraah dake Dubai ta ɓaro musu aiki tai kiransa a waya. Kalaman da tayi amfani da su a wajen gaisawar tasu ya sakashi neman fashin baƙi a wajen yayansa Attahir. Shi kuma batare da tunanin komai ba ya buɗe masa zancen cewar ai da gaske Husnah ɗin take an ɗaura mata aure da shi a randa aka fasa da Samraah. Wannan shine dalilin rikicin na yanzu, ga shi kuma da alama aiki ya koma baya.....

🌜🌟🌛

Ina nan tsaye abin duniya duk ya isheni ya buɗe ƙofar bathroom ɗin alamar zai fito. Koda gigi ban yarda na kalla wajen ba balle ma na saka kaina a uku. Har tsawon mintuna uku ina ɗan jin motsinsa cikin yanayin rashin hayaniya. Cikin ƙarfin hali da dakiyar zuciya na ce, “Ni ka buɗe min ƙofa na fita bana son taɓara”.
Shiru babu alamar zai amsa min, daurewa nai na sake maimaitawa cike da tsiwa. Nan ma banji alamar zai kulani É—in ba. Sai kawai na taune lips É—ina ina jin kamar naje na rufesa da duka. Tsahon mintuna goma ina dai wajen a tsaye ban juya ba ban kuma gusa ba. A bazata naji sautin muryarsa a bayana.
“Bani phone ɗina”.
Da sauri na juyo har ina buge hannu da ƙofa. A tsayen kuwa yake ƙyam a bayan nawa shantali guda dashi, dan duk nawa tsawon sai na ganni ɗis a gabansa. Ga fuskarsa a tsuke babu alamar wasa tattare da shi. Duk da yanda naji zuciyata ta motsa na tsorata sai na dake nima ina mai tsuke tawa fuskar tamau harda su hura hanci.........✍️

_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._

_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_

_BANK NAME:KEYSTONE_

_BANK ACC NO:6019473875_

_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_

_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_

__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_

_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_

*09033181070*

*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*

_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_🐛TSUTSAR NAMA....!!🐛_*
_(Itama nama ce)_

_𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻_

_𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐_
_𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒊𝒓𝒕𝒚 𝒇𝒐𝒖𝒓_

......Matsawa nayi baya ina kumbura fuska. “To ka buɗe min mana ba tana sashen Ummie ba. Oh Hajiya Babba”. Nai saurin gyarawa saboda kallon da naga ya wani kafeni da shi. Kamar bazai tanka min ba sai kuma a daƙile kamar an masa tilas ya ce, “Miya kaita can?”.
“To ina ruwanka, kai dai ka matsa naje na ɗakko maka”.
Shiru bai matsa ba ya dai zuba min ido kawai. Sai da ya mula dan kansa sannan ya sake furta, “Da gaske abinda Mammah ɗin ta faɗa kenan?”.
Karon farko na ɗago na kallesa. Dan yanda yay maganar a dakensa ba ƙaramin tsargani yay ba. Idanuna cike da ƙwalla har muryata na rawa ma na ce, “Miye ribata idan na aikata zalunci akan baiwar ALLAHr da bataji ba bata gani ba. Idan har zan iya cutama Ummie nima zan cutar da tawa mahaifiyar kenan idan tana raye. Ko an faɗa maka kowa ma irinka ne da kansa kawai ya sani sai kuma neman dukiya baya taɓa waiwaye da tuna bayansa. Ka saki hakƙokin wadda inda kaine a kwatankwacin halin da take ciki ko barcin mintuna bazata taɓa bari ya ɗauketa cikin daɗin rai ba saboda damuwa. Dan zata iya sallama komai da komanta dan ganin ka samu ingantacciyar rayuwa da kulawa da lafiya. Na tabbatar wlhy bazata taɓa barinka cikin yunwa ko datti ba. Bazata taɓa miƙa ragamar kulawa da kowane motsinka a hannun masu aiki ba. Koda zataje inda kake ka raunatata koma ka sumar da ita gobe bazai sakata fasa sake zuwa inda kake ba dan ta dubaka. Ina mai baka shawara a wannan gaɓar da kada kayi sakaci da damar da UBANGIJI ya baka ta neman aljannarka a ƙarƙashin kulawa da mahaifiyarka. Ku tausayama baiwar ALLAHr nan dan ALLAH ku nutsu ku fuskanci halin da take a ciki. Idan ba hakaba watarana kaine zakai kuka da dana sani mara adadi dan su waɗan nan da sukazo suka cika gida suna ci daga arziƙin da UBANGIJI ya bata suna fankama da hura hanci ko a kwalar rigarsu maybe ma basu ƙi ta kwanta ta mutu ba ko ta dawwama a haka cikin halin lalura dan komai ya zama nasu.....”
“Your are vary stupid!!”.
Ya faɗa cikin katseni da daka tsawa. A take kuma idanunsa suka jirkice ƙwayar tsakkiya ta koma siririya, zaibar ta sake duhu exactly na maguna dai musamman idan suna a cikin hasken rana. Har cikin raina naji tsawar tashi ta ratsa ni, a take kwarjininsa da shakkarsa suka sake dabaibaye ni har na gagara sake magana. Sai da ya buɗe ƙofar a fusace ya fice sannan na sauke nannauyar ajiyar zuciya ina mai rumtse idanuna. Lallai wannan mutumin yayi nisan da bai jin kira. Sannan akwai abinda ya kamata na sani dan na fahimci sam baya son abinda zai taɓa ahalinsa kenan. To lallai babbar magana. Dan ni inaji a jikina lallai akwai ɓoyayyen al'amari mai cike da darasi a ƙarƙashin ciwon mahaifiyar nan tasa. Amma in sha ALLAHU koma minene ni *_SAMRAAH ABDULL-WAHAB GWARZO_* nayi alƙawarin sai na bankaɗosa. Uban kowa sai ya kwashi kashinsa a tafin hannunasa cikin MAASH MANSION..
(Tofa babbar magana. ALLAH ya bada nasara Kandala🥱).

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.