Tsutsar Nama Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: TSUTSAR NAMA BOOK 1.txt
Chapter 43 of 264
Shan maganin ya ƙara saka min jin daɗin jikina. Sai dai damuwa data kasa ɓoyuwa a kan fuskata. Sai gajiyar zama waje ɗaya daban saba ba. Nida nake yini tsaye kan ƙafafuna ina faman bautar aiki, garama idan office naje akan ɗan samu sassauci tunda shi kusan daga zaune ne. Motsin sake buɗe ƙofa da naji ya sakani tashi daga kwancen da nake cikin kujerar ɗakin, ɗan kwalin abayar naja na rufe kaina zuwa ƙirjina da ƙyau. Dai-dai nan aka ƙarasa shigowa. Mutumin ɗazu ɗinne dai, daga bakin ƙofa ya tsaya yayinda ni kuma nake kallonsa a tsiwace. Dan sai yanzu ne komai ke dawo min game da sanin da nai masa. Tabbas shine yaron mutumin nan mai kama da ƴan daudu ko nace ɗan daba ma ko sara suka oho duk ya cancanta, shine kuma ya kira da PA ɗinsa a ranar wancan taron. Nai saurin kauda kaina ina ƙoƙarin dai-daita fuskata da jikina. Tsahon mintuna kusan biyu ɗakin shiru, kafin cikin son nuna jarumta na furta,
“Dama kune kukai kidnapping É—ina?â€.
Maimakon bani amsar dana buÆ™ata sai jinai cikin bada umarni ya ce, “Zaku iya shigowaâ€. Baima ko gama rufe baki ba kuwa garadan samari biyu suka shigo. Ko namiji yaga wannan samudawan dole ya ji tsoro balle ni, amma dai nayi Æ™oÆ™arin dake zuciyata ban bari tsorona ya fito a saman fuska ba. Sai dai faman haÉ—iyar yawu nake da Æ™yar zuciyata na faman kai da kawo a cikin Æ™irjina. Umarnin tashi suka bani, bani da ikon yin musu ko dan bindugun dake a hannunsa, É—aya daga cikinsu ne ya koma ta bayana ya É—auro Æ™yalle a saman idona, zanyi magana ya ce, “Shiii!! Young Lady, inba hakaba harsashi ya rufe miki bakiâ€.
Yawu na sake haÉ—iyewa mai kauri, daga haka ban sake magana ba har suka bani umarnin tafiya bayan sun saka min wani abu a hannu na riÆ™e. Tafiya kawai naji munayi batare dana san ina muke nufa ba, amma dai baka jin hayaniyar komai ko'ina tsitt sai kukan tsuntsaye daga É—an nesa damu kaÉ—an. Da ace hannuna babu handcuffs wlhy sai na cire abinda aka rufen fuskar komai ma za'ayi ayi. A haka naji mun shigo wani waje mai shegen sanyi da Æ™amshi na musamman. Nanma mun É—an yi tafiya kafin naji mun tsaya cak a inda Æ™afata ta taka wani lallausan abu.........âœï¸
_Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa._
_GUDA DAYA:400_
_BIYU:700_
_UKU:900_
_HUDU: 1200_
_BANK NAME:KEYSTONE_
_BANK ACC NO:6019473875_
_ACC NAME:MUSAA ABDULLAH SAFIYAH_
_ATURA SHEDA ZUWA;09166221261_
__
_IDAN KATI NE KUMA MTN/VTU A BIYA DA TURA SHEDA ZUWA GA:09134848107_
_*Al'ummar NIJER kuma ku nemi wannan number don yin naku payment din*_
*09033181070*
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
_MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI... ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃_
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu ðŸ˜ðŸ™_*
*_Typing📲_*
*_ðŸ›TSUTSAR NAMA....!!ðŸ›_*
_(Itama nama ce)_
_ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»_
_ð‘·ð’‚ð’ˆð’† ð’•ð’‰ð’Šð’“ð’•ð’š ð’ð’Šð’ð’†_
......Kamar yanda d.c.o ya nema washe gari an sake kawo masa bayani akan ɗayan daya buƙata. Sai dai abin baƙin ciki shima layin na taƙaitaccen lokaci ne kamar wancan, ba kuma a taɓa kiran wani da shi ba. Nasara ɗaya da suka samu itace na shi wanda yay register ɗin layukan duk mutum ɗaya ne. Kuma a lokaci ɗaya yayisa. Sun saka a nemo musu shi a duk inda yake. Hakama abokin masu napep an samu nasarar cafkosa a safiyar yau. Bayan kamar awa biyu da kawosa police station ɗin aka kaisa office ɗin d.c.o kamar yanda ya buƙata. Sai da ya gama masa kallon tsaf daga sama har ƙasa kafin ya tura masa hoton Samraah dake gabansa.
“Kasan wannan?â€.
Ya faÉ—a kansa tsaye idanunsa Æ™yam akan saurayin. Hoton saurayin ya É—auka ya kalla na kusan sakan talatin, É—agowa yay ya kalla d.c.o sai kuma ya rissinar da kansa yana É—an jinjina kai. “Nasanta ranka ya daÉ—e. Sam-G ake kiranta, tana gabatar da shirin matasa kuma ina É—aya daga cikin fans nata da shirin baya wuceni ta redio ko shafukanta na sada zumunta musamman YouTube da ake É—ora shirin, nakan je na kalla videos É—intaâ€.
Kai d.c.o ya jinjina masa da faÉ—in, “Masha ALLAH. Minene sana'ar ka?â€.
“Direban napep ne yallaÉ“aiâ€.
“Kozan iya sanin ranar goma ga watan nan kana ina? Da ga shida na safe har zuwa Æ™arfe takwas?â€.
Jimm yay irin na mai son tunano abu. Har kusan minti É—aya sai kuma ya É—ago yana girgiza kansa. “Na manta yallaÉ“ai. Saboda kwanakin sun ja da yawaâ€.
“Uhhm yayi Æ™yau†d.c.o ya faÉ—a yana kallon yaronsa. “Azo da yaran nan su dukaâ€.
Kai yaron nasa ya jinjina cikin girmamawa. Fita yay babu jimawa sai gashi ya dawo tare da samarin farko da aka fara kamawa. Yanda suke kallon saurayin haka yake kallonsu. Duk da babu duka ko zagi da akai musu zaman waje É—aya da É—an karan Dauda yasa duk sunyi wujiga-wujiga dasu....
“Kasan waÉ—an nan?â€.
“Eh yallaÉ“ai na sansu, su duka abokaina ne. Tare ma muke harkar napep É—in ma.â€
“Kace ka manta mi kayi ranar goma ga watan nan da safe ko?â€.
“Eh yallaÉ“ai a gafarceniâ€.
D.c.o baice dashi komai ba. Sai abokinsa ya kalla ya ce, “Kai tuna masaâ€.
Kai tsaye abokin nasa ya ce, “Kazo É—akinmu ni da Æ™anina bayan sallar asuba dan gari ma bai gama haske ba. Kace na baka makulin mashin É—in Imran zakaje amso saÆ™o tasha kai taka tayar na gareji dan naka babur É—in ya samu matsala tun jiya sai barinsa ma kayi ya kwana a gareji kan yau zaka kai musu tayoyi da zasu canja maka. A gaban Æ™anina Isa akai komai kumaâ€.
Da sauri ya dafe kansa ya ce, “Tabbas anyi haka Salisu. Tabbas abinda ya faÉ—a gaskiyane yallaÉ“ai, amma a gafarceni inada yawan mantuwa ne wlhy. Na amshi mashin É—in, abinda nace kuma zanyi naje nayi da shiâ€.
“Masha ALLAH haka muke son ji ai dama. Ina ka kai yarinya to? Sannan waye ya sakaka kidnapping É—inta? Ko raÉ—in kanka ne kawai?â€.
“Ya salam kidnapping kuma? Ni banyi kidnapping kowaba ranka ya daÉ—e. Duk wanda ke tare dani kuma yasan wannan ba aikina bane ba inada sana'a. Taya ma kuma na rasa wanda zan É—auka sai Sam-Gâ€.
“Ƙarya kake yi, a waccan ranar ba gareji kaje da napep É—in abokinka ba Yakasai kaje layin gidan su Samraah. Kai zaman jiranta na kusan mintuna talatin da huÉ—u. Zata iya yiwuwa kasan dama zata fito a lokacin ne. Dan haka tana fitowa da shirin tsaida abin hawa kazo ka É—auketa. Ka tsaya a dai-dai fita anguwar ta titin bayansu gaba É—aya. Ka cire wayarta da facemask da eyeglasses É—inta ka ajiye saboda maybe kana tunanin za'a iya ganeka ko kuma wanda ya saka ka aikinne ya baka umarnin yin hakan. ÆŠan saurayi ban kawoka nan dan ka raina min hankalina ba. Amma kana da zaÉ“i guda biyu. Fitomin da komai a yanda yake dan ka samu sassauci ko cigaba da raina min hankali na saka ka faÉ—a ta dole wanne ka zaÉ“a?â€.
Ɗan jimm yay na wasu sakanni, sai kuma ya sauke numfashi da faɗin, “Zan faɗa maka gaskiya yallaɓai.......
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.