Best Hausa Novels

Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: LAYLERH MALEEK.txt

Chapter 9 of 65

*Chapter 17*

Mummunan ganin da idanunsa sukayi ne yasa lokaci ɗaya yaji wani irin abu me nauyi ya daki ƙirjinsa, wanda hakan ya tilastawa zuciyarsa bugawa da ƙarfi, idanunsa da suka zama jajaye ya rumtse tare kuma da dunƙule ƴan yatsun hannunsa, wani irin tafasa yakejin zuciyarsa nayi, ga kuma wani ɗaci da ya mamaye maƙoshinsa.

haƙiƙa wannan yanayin baƙone awajenta, irin wanda bata taɓa samun kanta acikinsa ba, tabbas a iyaka tsawon rayuwarta bata taɓa kusanci da wani namijin da ba muharraminta ba kamar yanda Najeeb ya tilasta mata yi ayau ɗin.
Yanayin yanda hucin numfashinsa ke dukan beauty face ɗinta ne yasa gaba ɗaya tsikar jikinta mimmiƙewa, ahankali ta ɗan soma jan jikinta baya, domin bazata iya jurewa kusancin nasu ba, wanda sanadin hakanne yasa taji jiri na ƙoƙarin ɗibanta.

Samun kansa cikin wata sabuwar duniya ta daban da yayi ne, yasa wani irin zazzafan shauƙi ya soma ɗibansa, sosai yanayin ya masa daɗi, kasancewar bai taɓa samun kusanci da ita har haka ba,
Jin da yayi tana ƙoƙarin nisanta kanta da shine yasa shi sake damƙe hannunta dake cikin nasa, cikin wani irin yanayin da yakejin kansa aciki yace.
"Please Laylerh faÉ—amin kina sona?"

Jin tambayan da yayi mata ne yasata buɗe tsumammun idanunta, tare da sauƙesu akansa, wani irin kallo takeyi masa wanda ke nuna kamar bata fahimci abun da yake faɗa ba, hasalima ayanayin da take ciki kamar bata gane komai.
Shi ɗinma idanunsa wanda suka juye izuwa kalan bacci ya zuba mata baya ko ƙiftawa,ahankali yakejin ƙaunarta na mamaye duk wani sassa na jikinsa.
kwata kwata batajin zata iya ci gaba da kallon cikin idanunsa, wanda yanayinsu ya riga da ya sauya, har takai ga tana hango wani abu na daban acikinsu, ahankali tayi ƙasa da kanta tare da ɗan lumshe idanunta, hakanan taji kirjinta na bugawa, yayinda wani irin abu me kama da fargaba haɗi da tsoro suka nemi mamaye dukkan sassan jikinta, sanyi da kuma iskan da taji na ratsa cikin tafin ƙafanta ne yasa zuciyarta fara yi mata wani tunani na daban.

Har zuwa yanzu idanunsa akulle suke, domin azahirance bayajin zai iya jurewa kallonsu a irin yanayin da suke ciki, har zuwa yanzu ƙuna da raɗaɗi yake ji acikin zuciyarsa, haka yakeji kamar ana caka masa mashi aƙirjinsa, haƙiƙa da ace yasan shigowarsa cikin falon zai gusar masa da ƴar nutsuwar da tayi masa saura, to tabbas da ya hana kansa ahigowa falon.
Idanunsa da sukayi jajur ya ware, yayinda tuni gashin jikinsa suka soma mimmiƙewa, lokaci ɗaya kuma fuskar sa tayi ja, kasancewar yaji tambayar da Najeeb din yayi mata ne, yasa zuciyarsa soma tafarfasa, domin jin amsar da Laylerh'n zata bashi daidai yake da hargitsewan tunani da ƙwaƙwalwansa.
Amatuƙar fusace ya saki handle ɗin ƙofar falon, wanda sanadin hakan yasa ƙofar falon rufewa da wani irin ƙarfi.
Jin ƙaran ƙofar ne yasa Laylerh da ta bawa ƙofar shigowa falon baya tayi saurin juyowa.
Ganin M.Jay dinne yasa zuciya da ƙirjinta yin wani irin tsalle kamar zasu faɗo ƙasa, cikin wani irin masifaffen tsoron daya shigeta tayi saurin janye hannunta daga cikin na Najeeb ɗin tare da ɗan matsawa gefe.

Ɗauke kansa yayi daga kallonsu tare da kawar da idanunsa da suka soma ganin dishi dishi zuwa wani waje na daban, cikin wani irin taku dake nuna zallan isa da taƙama irin na cikakkun soldiers, ya nufi hanyar part ɗinsa, sam bai yarda ya sake kallonsu ba, hasalima yi yayi kamar baisan dasu acikin falon ba.
Idanunta da sukayi raurau kana suka ciko da hawaye ta lumshe, ji tayi gaba ɗaya zuciyarta ta karye, yayinda taji wani irin haushin kanta ya kamata, hakanan taji ajikinta cewa kamar bata aikata daidai ba. " Shin meyasa tabari Najeeb ya riƙeta? Meyasa?." tayiwa kanta tambayar da babu wani me amsa mata ita.
Najeeb wanda ya zura hannayensa cikin aljihun wandon jumper'n dake jikinsa ne ya sauƙe ajiyar zuciya tare da ɗan lumshe idanunsa, sahirtaccen murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa wanda har hakan yasa fararen haƙwaransa bayyana, idanunsa ya zubawa Laylerh'n wanda ta riga da ta basa baya.
Hannunsa ya ciro ahankali ya dafa shoulder ɗinta, cikin yin ƙasa da murya yace.
"Meyasa kika juyamin baya?."

Idanunta dake cike da tarin ƙwalla ta lumshe akaro na barkatai, kaman kuwa jira hawayen nata suke ta lumshe idanun nata, ahankali suka ɗan gangaro kan fuskarta, jin hawayen nata sun zubo ne yasa cikin sauri ta kai hannun ta share, tare da ɗan jan jikinta gefe, ahankali kuma ta soma ƙoƙarin zame hannunsa daga kan kafaɗanta, dan hakanan taji duk komai ya daina yi mata daɗi. Ganin yanda take ƙoƙarin zame jikinta ne yasa Najeeb sanya hannayensa duka biyu ya juyo da ita, suka zamana suna fuskantar juna.

Cikin sauri ta rufe idanunta dan kuwa kwata kwata batason sake haɗa idanu dashi, duk da kuwa kasancewar bata gama sanin menene ainihin haƙiƙan abun dake cikin zuciyarta ba, saidai batajin zata iya bari ya fuskanci rauninta, sanin da tayi cewa ayanzu babu komai acikin ƙwayoyin idanunta face rauni.
Sauƙe idanunsa akan zara zaran eye lashes ɗinta dake ɗauke da danshin hawaye yayi.
"Laylerh!!."
Yaƙira sunanta cikin wata irin murya me ratsa jiki da zuciya.
Sanyin muryan nasa da ya ratsa kunnuwanta ne yasa ta buɗe idanunta ahankali, saidai bata yarda ta sauƙe ganinta akansa ba. Kyakkyawan fuskanta da kuma kyawawan laɓɓanta yake kallo, ahankali yakejin wani irin shauƙi na sauƙar masa, hakanne kuma yasashi ɗan lumshe idanunsa tare da jan wani dogon numfashi, ahankali ya janye hannayensa dake kan kafaɗunta tare kuma da ɗan shafa gefen fuskarta, cikin wata irin silent voice me ɗauke da sassanyan amo yace.
"Ke kyakkyawace Laylerh, salon kyaun ki na daban ne, haka zalika duk wani sirrin kyau akwaishi atattare dake, please ki kulamin da kanki kinji, sannan kuma kimin kwalliya me kyau anjima zanzo zance wajenki, kamar yanda kowani saurayi yake zuwa wajen budurwarsa!."
Idanunsa ya lumshe tare kuma da buɗesu alokaci ɗaya, hancinta ya ɗan ja cikin kulawa yace. "Take care!." Raɓawa yayi ta gefenta ya wuce, wanda sanadin hakan yasa jikinsu gogan na juna.
Idanunta ta lumshe tare da jingina bayanta ajikin bango, sam ko É—aya kalamansa basu shigeta ba, hasalima kwata kwata bata fahimci inda kalaman nasa suka dosa ba, abu É—aya kawai tasani shine yanayin da taga M.Jay É—in aciki, domin yanayin nasa, ya nuna cewar akwai zallan damuwa atattare dashi.
Jin zuciyarta na ƙara raunana ne yasa ta jan ƙafafunta da takejin sun mata nauyi ta ƙarasa bakin ƙofar shiga ɗakinta, ahankali ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shige ciki.

M.Jay
Ahankali ya maida ƙofar bedroom ɗin nasa ya rufe, cikin wani irin huci da yakejin zuciyarsa nayi ya tura duka hannayensa biyu cikin aljihun wandonsa, idanunsa dake alumshe ya ware, sakamakon yanda suka ɗauko masa hotunan Laylerh'n da kuma Najeeb riƙe da hannun juna.
"Ki na sona?" maganan da Najeeb ɗin ya faɗa kenan, dake ta yimasa yawo acikin ƙwaƙwalwa da zuciyarsa, sanadin haka kuwa ƙirjinsa ke ƙara yi masa zafi, kwata kwata yakasa fahimtar me hakan yake nufi, tunowa da wani abu da yayi ne yasa shi ɗan soma girgiza kansa, lallai ya yarda cewa gaba ɗayan rayuwa ƙaddara ce, dake iya sanjawa ako da yaushe, kana kuma yayi imani cewa shima tasa rayuwar ƙaddarace, saidai kuma tasa ƙaddaran ta banbanta dana kowa, domin sosai take hurting mind ɗinsa, akaron farko kenan da yaji yayiwa Najeeb wani irin mugun tsana, tsana mafi tsanani, kuma irin tsanar da bai taɓa yiwa kowa irinta ba.
Iska me zafi ya fesar daga bakinsa tare da É—an lumshe jajayen idanunsa, sam baya jin daÉ—in mood É—in daya samu kansa aciki.
Nan kan saman gadonsa ya faɗa tare da sanya hannu ya dafe daidai saitin zuciyarsa dake harbawa da ƙarfi.

Koda ta ƙarasa cikin ɗakin nata, asanyaye tasoma cire kayan uniform ɗin dake jikinta, haka takejin gaba ɗaya komai ba yayi mata daɗi, gefe guda kuma ga wani abu da takeji na sukan zuciyarta, sanadin hakanne kuma yasa takejin kamar ta aikata wani abun da yake ba daidai ba, tabbas har yanzu tana da buƙatar sanin meyasa takejin feeling na musamman akan M.Jay din, meyasa idan ta gansa take rasa duk wata nutsuwarta?, haka kuma takan kasa controll ɗin kanta, musamman akan abun da takeji azuciarta dangane dashi, lallai tana da buƙatar sanin haƙiƙanin menene SO da kuma yanda akeji idan ankamu dashi, lumshe idanunta tayi asakamakon tunawa da yanda zuciyarta ke matsanancin bugawa matuƙar M.Jay ɗin nakusa da ita.
"Idan wannan abun da takeji shine SO, kenan gaskiya da kuma haƙiƙanin abun da takeji acikin ranta yana nufin soyayya ne?."
Tambayar da zuciyarta tayi mata kenan, wanda hakan yasa taÉ—an zaro idanunta waje, kasancewar sam bata shiryawa tambayar ba, kanta taÉ—an girgiza kana abayyane tace.
"Idan kuma da gaske hakan shine SO, na kamu da son Yaya M.Jay kenan?" tayiwa kanta tambayar da bata da mafarin samun amsarta..
Still girgiza kanta tayi domin hakanan taji bata gamsu da tunanin nata ba, sanin cewa zuciyarta zatayi ta saƙa mata abubuwa da yawa ne yasa cikin sauri ta ƙarasa cire uniform ɗin dake jikinta, tare da ɗaura wani farin towel ajikinta wanda tsawonsa ya tsaya iyaka cinyoyinta.
Ganin da tayi cewa ankusa ƙiran sallan Magriba ne yasa kaitsaye ta wuce toilet, kasancewar yanayin garin na yau akwai ɗan zafi ne yasanya ta haɗawa kanta ruwa acikin bathtube tare da shiga ciki ta kwanta, sanyi da kuma daɗin ruwan daya ratsata ne ya sata ɗan lumshe idanunta tare kuma da sakin ajiyar zuciya, lokaci ɗaya taji duk wani damuwan dake ranta ya soma gushewa.
Samun kanta da tayi acikin wani sabon yanayi ne, yasa tayi wankan ta cikin nutsuwa, bayan kuma ta gama wankanne ta É—auro alwala.
Koda ta fito daga toilet ɗin tsane jikinta tayi da wani ɗan ƙaramin towel, wani haɗaɗɗen body lotion me daɗin ƙamshi ta shafa ajikinta, bayan lotion ɗin kuwa bata sake shafa komai ajikinta ba, domin dama yawan kwalliya ba ɗabi'arta bane, wannan yasa bata wani damu dayinsa ba.
Ƙarasawa gaban sif ɗin kayanta tayi tare da buɗewa, kayannata dake jere acikin sif ta zubawa ido, tana tunanin wanda zata saka, kasancewar idan ana yanayin zafi kwata kwata bata saka kaya me nauyi ajikinta.
Wani dogon wandon skin tight ta ciro haɗe da wata haɗaɗɗiyar farar armless, koda ta saka kuwa ba ƙaramin kyau kayan sukayi mata ba, musamman ma wandon daya kama jikinta sosai, har yakai ga ya bayyana tsararren hips ɗinta.
Koda ta gama saka kayan kuwa har anshiga sallan magriba, aɗan gurguje ta zura ƙaton hijab ajikinta, tare da shumfuɗa wani lallausan darduma ta tada sallah.
Anutse tayi sallan nata koda ta idar kuwa bata tashi akan sallayan ba, tana nan zaune har aka ƙira sallan Isha, bayan ta idar da sallan isha ɗinne tayi azkhar ɗinta haɗi da addu'o'i sannan ta miƙe tsaye, sanin cewa lokacin cin abincinsu yayi ne yasa ta cire hijab din dake jikinta, tare da ƙarasawa gaban drawer'nta, wata black kimono da aka ƙawata gaba ɗaya jikinta da adon fararen duwatsu ta ciro haɗe da sanyawa ajikinta, kasancewar kuma rigar na ɗan showing ne yasa, duk wanda ya kalleta zai hango ainihin shigar dake jikinta, ɗan kwalin rigar ta naɗa akanta, wanda kuma ya sauƙo har zuwa kan ƙirjinta.
ÆŠan kallon kanta tayi amadubi, ganin da tayi cewa shape É—in jikinta bai bayyana sosai bane, yasa anutse ta fice daga É—akin.

Acan falon kuwa Abbou Jaheed da Momy ne kaÉ—ai ke zaune akan dining table É—in, kasancewar Alhaji Ahmad Rufae ya wuce Kaduna, M.Jay kuwa tunda ya shiga É—akinsa ba wanda yasakejin motsinsa, sai kuma Najeeb da gabaki É—aya ma shi baya gidan.

Anutse ta shigo cikin falon, ganin Abbou Jaheed da kuma momy zaune dining area ne yasa duk taji jikinta yayi sanyi, tunowa da yanda taga mood ɗin Abbou Jaheed ɗin yauda safe ne yasa ta ɗanji fargaba ya ɗarsu acikin ranta, ganin cewa basu ganta bane yasa ta juyawa cikin sauri ta soma ƙoƙarin komawa ɗakinta.
"Laylerh."
Abbou Jaheed ya ƙira sunanta, wanda tun shigowarta cikin falon ya ganta.

Jin Abbou Jaheed ya ƙira sunanta ne yasa ta tsayawa, ahankali cikin yanayi na ɗan fargaban da takeji acikin ranta ta juyo, ƙasa tayi da kanta tare da soma wasa da ƴan yatsun hannunta, cikin sanyin murya tace. "Na'am."

"Kizo!." Abbou Jaheed ya faɗa yana me karantar yanayinta, tabbas yasan cewa ɓacin ran daya gwada mata ayau da safe yayi mata tsauri sosai, amma ta hakane kawai zai gujewa faruwan abun da yajima yanajin tsoron afkuwansa.
Asanyaye ta ƙaraso kan dining area ɗin, wanda har zuwa yanzu bata yarda ta ɗago kai ta kalleshi ba, saboda wani irin nauyi da kunyansa takeji.
Gane abun dake zuciyarta ne yasa Abbou Jaheed É—in sakin murmushi, cikin kulawa ya kamo hannunta, tare da cewa. "Zauna kici abinci!."

bazata iya musa masa ba domin dama yunwa takeji, kan É—aya daga cikin kujerun dining area din ta zauna, tare da É—aukan plate tayi seving É—in kanta, kasancewar tanajin yunwa sosai ne yasa ta maida hankali wajen cin abincin.
Idanu Abbou Jaheed ya zuba mata cike da matsanancin tausayinta, hakanan yakeji ajikinsa cewar yanayin dayayi mata magana É—azu da safe bai kyauta ba, wanda kuma har yanzu yanayin daya gansu aciki ita da Maleek din ya kasa barin cikin idanunsa, baisan meyasa ba yake yawan jin fargaba, akan duk wani lamari daya shefesu su biyun, duk da kuwa yasan cewar jinin Maleek ne ke gudana ajikin Laylerh'n amma yana tsoron faruwar wani abu.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare kuma da lumshe idanunsa, tabbas akwai wata rana acikin rayuwar Laylerh Maleek din wanda baya fatan zuwanta garesa, sama da shekara 7 kenan da ya ɗauka yana nisanta tsakanin Laylerh da Maleek ɗin, ba kuma ya fatan waƴannan shekarun daya ɓata su tafi abanza, wanda kuma sanadin ganinsu da yayi tare ayau ɗin, yasa zuciyarsa ta raunana, yayinda yake ganin abun da yake gudu da kuma ɓoyewa yana neman tunkarosa nan kusa batare daya shiryawa hakan ba.

Jin taƙoshi ne yasa ahankali taɗan ture plate ɗin abincin daga gabanta, duk da cewar bata wani ci abincin sosai ba amma haka take jin kanta aƙoshe, cup ɗin exotic ɗin dake gabanta ta ɗauka ahankali ta ke ɗan sipping drink ɗin, duk da ma kasancewar cikin zuciyarta ɗauke take da tarin damuwa na rashin ganin M.Jay ɗin da tayi awajen cin abincin, hakanan yasa duk taji ba daɗi aranta.

Baƙon Ƙamshin turaren daya ziyarci hancinta ne yasa ta ɗago da ɗara ɗaran idanunta, wanda kuma hakan yayi daidai da shigowarsa cikin falon, sanye yake cikin shigar tsadaddun riga da wandon da sukayi matuƙar amsar jikinsa, kana kuma suka bayyana kyawunsa, akaron farko kenan da taji ta kasa ɗauke idanunta akansa, tabbas shi ɗinma kyakkyawane, kuma yana da abubuwan burgewa da yawa ajikinsa, kallon yanda ƙawataccen sajen dake kwance akan fuskarsa ke sheƙi tayi, wanda kuma hakan yasa suka haɗa idanu dashi, da sauri tayi ƙasa da kanta, domin sam bataso ya kamata tana kallonsa ba.
Ƙarasowa dining area ɗin yayi tare da ɗan jan kujera ya zauna, fuskarsa ɗauke da murmushi yace.
"Abbou barka da dare."
Murmushi Abbou Jaheed É—in yayi, fuskarsa asake cike kuma da nuna jin daÉ—i yace.
"Yauwa Najeeb barka dai, yau kai da É—an uwanka Maleek kun mana yajin aikin cin abinci ko."
Murmushi Najeeb ɗin yayi har saida fararen haƙwaransa suka bayyana, kallonsa ya mayar gefen da Momy ke zaune, cikin nutsuwa haɗi da girmamawa yace.
"Please Momy alfarma nazo nema awajenki!."
Jin abun daya faÉ—a ne yasa Momy sakin Murmushi, kana ta faÉ—aÉ—a fari'ar dake kwance akan fuskarta, sannan cikin kulawa tace.
"FaÉ—i koma wace irin alfarma ce ka samu."
Murmushin jin daɗi yayi tare da tsaida idanunsa akan Laylerh wacce har yanzu taƙi ɗago kanta dake ƙasa.

Kansa yaɗan shafa ataƙaice yace. "Dama inasone Laylerh ta min rakiya zuwa mall."
Jin abun daya faɗa ne yasa Laylerh'n tayi saurin ɗago kai ta kalleshi, idanunsa ɗaya ya kashe mata, wanda hakan yasa ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.
Murmushin me ɗauke da ma'anoni daban daban Momy tayi, cike dason cimma manufarta akansu tace. "Laylerh ae ƙanwarka ce Najeeb, saboda haka kana da iko da ita ako da yaushe, bakomai kuje Allah Yadawo daku lafiya."
Abbou Jaheed dake jin duk abun da suke faÉ—a ne ya saki murmushi, cinin kulawa yace.
"Ni babu wanda zai tambayi izinina kenan wato nagama nawa dana ba da aure ko?."
Murmushi Momy da Najeeb din sukayi, ahankali ya miƙe tsaye cikin yin ƙasa da murya yanda Laylerh'n zataji sa yace
"Kisameni amota please."
Baijira amsawarta ba ya juya, kaitsaye ya nufi hanyar fita daga falon.
Laylerh da ta bisa da kallo ƙasa ƙasa taɗan murguɗa masa baki.

"AYSHA!."
Abbou Jaheed ya ƙira asalin sunanta murya asanyaye.
Yanayin yanda taji muryan Abbou Jaheed din asanyaye, da kuma yanda yaƙira asalin sunanta ne yasata ɗago kai ta kalleshi, saidai tunkan yakai ga cewa komai taji zuciyarta ta tsananta bugawa, domin kuwa Abbou Jaheed ɗin bai taɓa ƙiranta da sunanta na asali ba.
Abbou Jaheed kuwa hannunsa yasa acikin aljihunsa tare da soma ciro wasu bandir bandir ɗin kudi wanda aƙalla yawansu yasa zasu kai dubu ɗari biyar, anan kan saman table ɗin dake gabansu ya ɗaura kuɗaɗɗen tare da kamo hannunta ya ɗaura akan kuɗaɗen, idanunta ta zubawa Abbou Jaheed ɗin sakamakon rashin sanin abun da hakan da yayi ke nufi.

Ajiyar zuciya ya sauƙe, ganin irin kallon da Laylerh'n keyi masane ya sashi gyara zama, ahankali cikin kulawa haɗe da tausayinta da yakeji yace.
"Haƙƙin kowani ubane ya damƙawa ƴarsa sadakinta atafin hannunta, saboda haka ganaki sadakin, haƙƙin ƙine kina kuma da damar da zakiyi duk abun da kikeso dashi matuƙar abun bai kaucewa ƙa'idan addini ba."

Wani irin ruftawa taji zuciya da ƙirjinta sunyi, yayinda kalman "SADAKI" da taji Abbou Jaheed din yafaɗa, ya sanya lokaci ɗaya taji duk wani tunaninta ya tsaya cak, lokaci ɗaya kuma zuciyarta ta tsananta bugawa, take taji wani abu na sukan tsoka da kuma jinin jikinta, samun kanta tayi da kasa ɗauke idanunta akan Abbou'n nata, sanadin haka kuwa yasa hawaye suka cika idanunta, jikinta ne ya ɗauki rawa, wanda hakan ya bawa hawayen dake cikin idanunta daman gangarowa kan kyakkyawar fuskarta.

Wani irin shu'umin murmushi Momy ta sake, tare da ɗan cije laɓɓanta, cikin zuciyarta tace.
"Kin fara kuka kenan Laylerh daga yanzu har ƙarshen rayuwarki, tabbas daga kan wannan daren mummunan ƙaddaranki zata fara bibiyanki, ayau akuma cikin wannan daren zaki rasa duk wani farinciki, tabbas zakiyi kuka Laylerh kuka irin na fitar hayyaci, kukan kuwa da babu me rarrashinki."
Still wani shu'umin murmushin tayi, domin kuwa ta hangowa kanta zallan nasara, wannan dama ce da ta jima tana fata da burin samu, daman kisan duk wani farinciki dake cikin zuciyar su, daman kawar wa da Laylerh budurcinta, haka kuma daman nesanta ƙauna me tsananin ƙarfi.

*(Kuyi haƙuri two days bana baku update kullum kuma akan kari, wallahi bani da lapia seriously, dan Allah kuyi haƙuri dani zanna baku update duk bayan kwana ɗaya please! Kumin wannan uzurin dan Allah🙏🏻)*
1/19/21, 8:12 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*(This book is mainly for those that pay, if you know you did'nt pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay-0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz bank, whatsapp number 07017879464.)*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.