Best Hausa Novels

Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: LAYLERH MALEEK.txt

Chapter 41 of 65

*Chapter 58*

Gaba d’ayansu zaune suke acikin falon daga Buzuwa har Munnira wacce ke zaune akan sofa tana ta shirye shiryen event d’in da zasu yi yau ita da k’awayenta na Bride To Be.

Ganin yanda Alhaji Farouk d’in ya shigo cikin falon duk gaba d’aya jikinsa asanyaye ne yasa Buzuwa k’ura masa ido cikin yanayin mamaki kuma tace.
“Alhaji lafiya kuwa naganka duk jikinka asanyaye, meke faruwa?.�

Sauk’akk’ar ajiyar zuciya ya sauk’e tare da neman waje anan kusa da ita ya zauna.
Kallon Munnira dake ta faman izurin gabanta yayi, kana cikin sanyi ya k’ira sunanta wanda hakanne kuma yasa bisa dole ta tsaida abunda takeyi d’in tare da d’agowa ta kalli mahaifinnata.

Buzuwa kuwa idanu ta zuba masa cike da mamakin ganin sabon yanayinsa domin kuwa tasan kafun fitansa ya sanar da ita cewar gidan Alhaji Jaheed zaije, fuskarsa kuma dauke da fari’a ya fita sab’anin yanzu da damuwa ta maye gurbin fari’ar.

“Wai meke faruwane Alhaji kodae wani abune na daban ya samu Maleek d’in?.�
Tayi masa duka tambayoyin ta hanyar cigaba da tsura masa ido.

Asanyaye cikin kuma taraddadin yanda zasu d’auki abun ya d’an jinjina masu kai, kana cikin nutsuwa yace.
“Tabbas wata matsala ta kunno kai wacce bamusan tayayane zamu maganceta ba, ban kuma san wani ba hagon fahimta zakuyi wa maganar ba.�
Shiru yayi tare da kallonsu duka biyu, wanda kuma sud’inma kallonsa sukeyi basa ko k’yafta ido.
Shi kuwa gyara zama yayi kana asanyaye yace.
“Asanadiyar hatsarin motar da Maleek ya samu likita ya tabbatar da cewar bazae tab’a iya haihuwa ba, bi ma’ana k’waya k’wayan haihuwarsa sun samu matsala, duk macen da zata zauna dashi saidai ta zauna da hak’uri amma bazae tab’a haihuwa ba!!�

Darammm dammm haka zuciyoyi da k’irjin Buzuwa da kuma Munnira suka buga, saboda tsananin mamaki da kuma al’ajin jin maganan daya fito daga bakin Alhaji Farouk d’in.
Amatuk’ar razane Buzuwa ta zazzaro idanunta waje, kana cikin yanayin tashin hankali tace.
“Subahanallah, Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un, Maleek bazai tab’a haihuwa ba? Ya samu matsala amararsa? Ya ilahi yanzu ya zamuyi kenan wannan wani irin sabon tashin hankaline da ba’a samasa rana ya tunkaro mu.�
Ta k’are maganar tana me sharce gumin dake tsatstsafo mata.

Munnira kuwa gaba d’aya cikin wani irin shock ta samu kanta, lokaci d’aya kuma taji har wani ciwon kai da jiri na neman kwasheta, domin kuwa sosae maganan Abban nata ya bata tsoro, idan dagaske Maleek ya samu matsala ita meye makomarta kenan?
Tayiwa kanta tambayar da bata da amsarta.

Alhaji Farouk kuwa matartasa ya kalla kana cikin sanyin murya yace.
“Lallai tabbas Maleek ya had’u da k’addara, ayanzu kuwa zab’i ya rage garemu, nidai kam idan asonane bazan hanashi auren Munnira ba, duk da kuwa ita kad’aice y’a d’aya tilo da Allah Yabamu, dole za musu muga jika ta wajenta, amma kuma to ya zamuyi k’addara ta riga fata, saidai kawai mujira Allah yayi ikonsa.�

Kallo mai d’auke da ma’anoni Buzuwa ta watsawa mijinnata, lallai kuwa Tabbas sunga samu sunkuma ga rashi nan take, hakika ita macece maison dukiya da kuma jin dad’in rayuwa, kasancewar kuma munnira itace y’a d’aya tilo da Allah Yabata wannan yasa ta d’iga duk wani burinta akan Munniran, tana matuk’ar son y’artata ta auri mai dukiya, wannan dalili yasa koda Alhaji Farouk d’in ya kawo maganar Maleek sanin irin tarin dukiyar da Alhaji Jaheed da kuma shi kanshi Maleek d’in ke dashi yasa tayi saurin amincewa, Tabbas tasan cewa ayanzu idan Munnira ta auri Captain M.Jay d’in bak’aramin dukiya da arziki zasu tara ba, kasancewarsa wanda bazai tab’a haihuwa ba hakan zaisa ya sakewa Munniran kud’i, saidai kuma amma bazata tab’a iya jurewa tanaji tanagani y’arta lafiyarta k’alau amma ace bazata haihu ba, Tabbas tana da burin ganin jinin Munniran.
“Lallai wannan shine tsaka me wuya, ga arziki b’aro b’aro ga kuma tawaya.�
Tafad’i hakan cikin yin k’asa da murya tare kuma dasa hannu ta dafe kanta da lokaci guda ya d’au charge.

Alhaji Farouk kuwa Munnira wanda idanunta suka ciko da k’walla ya kalla, cikin tausasa murya yace.
“Duk da inason aurenki da d’an Aminina Maleek, amma hakan bazai tab’a sawa na tauyeki ba, lallai dole kina da zab’i, shin kinaga zaki iya rayuwar aure da Maleek duk da wannan lalurar da ta sameshi? zaki iya zama dashi batare da haihuwa ba har abada?.�

Shiru gaba d’aya falon ya d’auka duk da kuwa taji tambayar da Abban nata yayi mata.
Kanta ta sunkuyar k’asa tare da lumshe idanunta tana me tuno tsananin had’uwa da kyawun Maleek d’in, wanda ayanzu ke tayi mata gizo acikin idanunta.
K’warae shid’in Miji ne na nunawa sa’a, sannan kuma atattare dashi akwae abubuwan burgewa, ya had’u tako ta ina, yayinda kuma komai nasa ya kasance anutse, tayaya wata mace da ta samu dama zata bari cikakken gwarzon Namiji kamarsa ya sub’uce mata? Tabbas rasashi asarace babba, domin tayi imani auren Namiji kamarsa ba k’aramin d’aga mata darajarta zaiyi ba, aurensa sa’ane kuma samun hakan sai mace mai sa’a, Ina batajin zata barsa waidan kawae saboda baya haihuwa, itakam wallahi tana kwad’ayin zama dashi ahaka, Kodan fitinannen kyaun dayake dashi kuwa, duk da kuwa cewar zata so ace ta haifa masa kyawawan yara masu kama dashi.
D’ago kanta tayi kana cikin sauri tace.

“K’warai nikam na amincewa aurensa ahaka Abba, zan zauna dashi.�

Idanu Buzuwa ta zazzaro cike da mamaki had’i da tsoron abunda y’arta ta ta fad’a, hatta Alhaji Farouk d’in kuwa idanu ya zubawa y’ar tasa, sakamakon jin abunda ta fad’a.

Buzuwa kuwa kai ta d’an soma girgizawa, domin kuwa ta riga da ta gama yanke hukunci, duk da cewar tasan zasuyi asara sosae amma kuma gwara wannan asarar da wata asarar, fuskarta babu alaman wasa tace.

“Lallai yau Munnira nasake tabbatarwa da kaina cewar baki da hankali, ke shashasha ce, kina tunanin cewar wae kyau da kud’i sunfi haihuwane? hmmm to idan ma haukane yasa kika amincewa auren Maleek ahaka to ki dawo hayyacinki ki jini, bazaki tab’a aurensa ba, matuk’ar yana tare da wannan lalurar, maganar kud’i da kyau kuwa duniyarnan da fad’i take, domin kuwa bashi kad’ai bane kyakkyawa, akwai kyawawa da yawa ciki da wajen k’asarnan, saboda haka Allah yasa shid’inma ba mijinki bane, duk da cewar kuwa yanzu aurennan saura kwana uku amma hakan bashi zaisa afasa soke shiba, naji nayarda zan fuskanci jama’ar dana gayyata na fad’a musu cewa an fasa auren, yaje Allah Ya had’asa da mai aurensa amma bawai keba.�

Tsaida maganar nata tayi tare da juyowa ta kalli Alhaji Farouk cikin nuna babu sauyi akan maganarta tace.
“Batare da wani dogon nazari ba kak’irasu kasanar dasu cewa anfasa maganar auren, har abada babu aure tsakanin Y’armu munnira da kuma d’ansu wanda baya haihuwa.�

Idanu Alhaji Farouk ya d’an zazzaro waje cikin yanayin damuwa kuma asanyaye yace.
“Kada kiyi haka dan Allah ko kinmanta cewa Alhaji Jaheed Gwani abokinane, tayaya zan k’i basa auren y’ata akan wannan dalilin, koba komai kuma Maleek matsayin d’a yake awajena, kuma ya kamata mu tausaya masa kodan lalurar da ta samesa.�

Saurin girgiza kanta tayi kana cikin kafiya tace.
“Wallahi awannan zancen babu wani batun tausayawa, shin atunaninka yau idan da ace Munnira ce ta samu wannan matsalan Maleek d’in zai iya yarda ya aureta ne? musamman yasan cewa yana tashen kyau da dukiya mai zaiyyi da macen da bata haihuwa? to haka muma y’armu bazata auri Namijin da baya haihuwa ba, dama can ahalinsu bayawane dashi ba, basu da wani dangi shiyasa sukeso muma su yankemu ya zama bamuyi gaba ba, nidai na gama magana kakira danka sanar dasu ma ehe.�
Tana gama fad’in haka ta mik’e tsaye tare da kamo hannun Munnira ta wuce da ita d’akinta.
Alhaji Farouk kuwa haka ya zauna shiru acikin falon shi kad’ai, zuciyarsa cike da nauyin yanda zai fuskanci mutum mai kamala da mutumci kamar Abbou Jaheed yace, suyi hakuri da alk’awarin auren da yayiwa d’ansu, yanzu bazai iya basu yarsa ba, lallai abun da matuk’ar kunya sosae, amma kuma to ya zaiyi? Allah ma yasani yana matuk’ar bin maganan matarsa, duk abunda ta fad’a koba mai kyau bane babu yanda ya iya bisa dole haka zaibi.
Jikinsa duk amace haka ya mik’e ya nufi bedroom d’insa.

Acan cikin d’akin Buzuwa kuwa munnira ta kalla, wanda duk tayi jugum zuciyarta cike da alhinin matsalar da ta samu Maleke d’in, Allah yasani itakam tana jin wani feelings d’insa, duk da cewar ayanzu tasan ta rasasa kenan amma zata so ace koda sau d’ayane ta rab’i jikinsa, bi ma’ana tasamu shiga jikinsa ta yadda zata mallaka masa kanta koda kuwa babu aure atsakaninsu, domin kuwa tun da ta sakashi acikin idanunta kullum da feelings d’insa take kwana take tashi, jarababben sha’awarsa takeji, saboda tasan cewa maza irinsa sam basu da wasa, duk macen da ta shiga hannunsu to ba makawa sai sun zautar da ita da salonsu.

Buzuwa kuwa kafad’an y’ar tata ta dafa, cikin son bata nutsuwa tace.
“Ko kad’an kada kiji wani abu akan barin Maleek, saboda akwae maza kyawawa da zasu soki har kuma ki mori dukiyarsu, Tabbas kam nasan munyi rashin abunda muke so, amma ae akwae gaba, rashin haihuwa ba abubane da za’a iya shanyewa, balle ma matsalar badaga gareki take ba, can daga wajensane kuma har abada ake kira Bawae na k’alilan d’in lokaci bane, ninasani zaki samu wani wanda ya fisa.�

Saurin girgiza kae Munnira tayi kana cikin sanyin murya tace.
“Har abada Momy har abada bazan tab’a samun wanda ya kaisa ba, saboda ko tantama banayi cewar irinsa shi kad’aine, tayaya ma kike tunanin zan samu wani Namiji irin Maleek? mutumin daya had’a komae da komae na rayuwa, mutumin da ganinsa ma sai mai sa’a arayuwa, mutumin da ko kusa ban tab’a tunanin taka inda ya taka ba, kin kuwa sam wayeshi Momy? Wallahi irinsa ko babu dukiya kuka still ba haihuwa mata rububinsa za sukeyi, saboda shid’in na dabanne komai nasa na musammanne, kuma Momy keda kanki ma kinsan hakan.�
Ta k’are maganar tana me lumshe idanunta had’e da rungume hannayenta, saboda wani irin shauk’in da takeji akansa, duk da cewar kuwa baya kusa da ita amma haka takejin feelings d’insa.

Ganin hakanne kuma yasa Buzuwa tab’e baki, tare da soma tattare kayayyakin dake baje akan gadonta, Dan itakam Allah Yasani ta gama magana ba kuma zata tab’a bari y’arta ta auri wanda likitoti suka tabbatar da cewa bazae tab’a haehuwa ba.

*Maleek*
Ahankali ya d’ago kansa wanda ya kwashe sama da 20min kan cinyar Oum Ayush,
Kallon Oum Ayush d’in yayi tare da d’an gyara zamansa, ahankali kuma cikin sanyi kamar wani k’aramin yaro yace.
“Please Oum Ayush zanci abinci.�

Kallonsa Oum Ayush d’in tayi cike da kulawa, tare kuma dajin sanyi aranta, sakamakon jin cewar da kansa yau d’in ya buk’aci abinci, sab’anin sauran kwanakin da saidai ayita binsa da abincin amma yana sharewa.
Cikin yanayin dake bayyana samun nutsuwarta tace.
“To Maleek mekakeson ci sae na dafa ma.�
Idanunsa ya d’an lumshe kana akasalance yace.
“Southern baked BBQ chicken and fruit salad kawae!�
Yanayin yanda ya k’are maganar yana d’an taune jajayen lips d’insane yasa cikin sauk’i zagane cewar mararsa ce ke ciwo, musamman saboda yanda ya dafe kan marar da tafin hannunsa.

Take kuwa tausayinsa ya kama Oum Ayush wanda hakan yasa cikin kulawa tace.
“Sannu ko bari naje yanzu na had’a maka, amma akwae chicken biryani dana dafa d’azunnan kona kawoma kafaraci?�

Kansa ya d’an girgiza alaman “A’a.�
hakanne kuwa yasa ta juya cikin sauri ta fice daga falon don sama masa abunda ya buk’ata d’in.

Shikuwa sake lumshe tsumammun idanunsa masu kyau yayi, kana ahankali cikin daure ciwon da yakeji amarar tasa yace, da Fou’ad wanda ke zaune acan gefe kad’an yaje d’akinsa akwae laptop d’insa ya d’auko mae.
Hakan kuwa akayi babu musu Fou’ad ya mik’e tsaye tare da ficewa daga falon kaitsaye yanufi sashin Maleek d’in.
Shikuwa Maleek sake jingina bayansa yayi da jikin kujera, tare da sauk’e wata irin sassanyar ajiyar zuciya, sannu ahankali yakejin wani irin sanyi na ratsa duk ilahirin jikinsa yayinda wata irin sassanyar iska ke shiga kowani sashi na jikinsa.
Lallai tabbas koda ace bai bud’e idanunsa ya sauk’e ganinsa akanta ba babu makawa yasan cewa itace tazo, domin yayi imani cewa akanta kad’ae yakejin irin wannan difference mood d’in, matuk’ar kuwa tana kusa dashi to koda bai bud’e idanunsa ba yasan itace.

*25/February/2021*

*7:40 pm*
2/28/21, 10:13 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*Not editing*

*59*

Sanyayyun idanunta wanda suke d’auke da danshin hawaye ta lumshe, tare dasa hannu ahankali ta dafe daidai saitin zuciyarta.
Duk da cewar ta fita ta barshi afalon sam batayi tunanin sake da wowa ta sameshi ba, musabbabin dawowarta falon kuma shine manta wayarta da tayi.
Saurin mannewa ajikin kofar falon tayi tayanda tasan koda ya bud’e idanunsa bazai ganta ba.

Shikuwa ahankali ya bud’e kyawawan idanunsa tare da sauk’e ganinsa adaidai saitin k’ofar shigowa cikin falon, saidai kuma rashin ganin kowa awajen yasa shi sauk’e wani irin gauron numfashi, tare kuma da tsaida idanunsa adaidai k’ofar shigowa cikin falon, domin kuwa Tabbas zuciya da gangar jikinsa sun shaida masa cewar lallaine tana kusa dashi, because akanta kad’ai yakejin irin wannan yanayin.

Ita kuwa Laylerh ba koma one ya hanata k’arasa shigowa cikin falon ba kamar yanda taji zuciyarta na bugawa da sauri sauri, musamman ma ganinsa da tayi ayanzun, ahankali tasa hannunta ta dafe kirjinta dake tsalle kaman zai fad’o waje, tare kuma da sake lumshe idanunta.
Asanyaye ta fitar da wani numfashi mai sauti, yayinda kuma lokaci d’aya duk taji jikinta yayi relax.

“Laylerh!!.�
Fou’ad ya kira sunanta, wanda yanzu dawowansa daga sashin Maleek d’in, ganin Laylerh’n da yayi atsayene kuma yasashi jin mamaki k’warai.

Ita kuwa Laylerh jin muryar Fou’ad dinne yasa tayi saurin bud’e idanunta, wani irin kunyansa da tajine kuma yasa tayi k’asa da kanta tare da soma wasa da y’an yatsun hannunta.

Fou’ad kuwa kallon tsab ya mata tare da d’an gyara tsayuwarsa anutse yace.
“Halan Oum Ayush kike nema ko?.�

Kanta ta d’an girgiza kana asanyaye tace.
“Aa phone d’ina nazo d’auka.�

Jin yanda tayi maganan asanyaye cikin fusgan numfashine kuma yasashi saurin jinjina kai alaman ya fahimta, batare kuma daya sake ce mata komae ba yasakai ya shige cikin falon, aransa yana me tabbatarwa da kansa cewar koda ga salon maganarta kad’ai dole ta jawo hankalin d’a Namiji, ballantana kuma idan aka tafi ga tsarin halittarta, tana da wani irin body structure mai kyau da d’aukar hankali, wanda ba iya Namiji d’aya ba, maza da yawa idan suka ganta to fa lallai zasu haukace akanta, duk da kuwa cewar bata da yawan shekaru sosae amma kuma ayanzu duk wani cikar halittar y’a mace ya bayyana ajikinta, tabbas Laylerh’n ta cika macen da dole soyayyarta bazatayiwa zuciyar da ta kama da sauk’i ba.

Saurin kauda tunanin dake zuciyarsa yayi tare da fad’in. “Astaghfirullah!� domin yasan ita d’in matar wanice, haka kuma fasalta yanayin tsarin halittarta sam ba daidai bane.

K’arasowa gaban Maleek d’in da har yanzu idanunsa ke kan k’ofar falon yayi, mik’a masa laptop d’in yayi tare da neman waje ya zauna.

Daidai lokacin kuwa ta sako k’afarta cikin falon, cikin kuma yanayin sanyin da ayanzu yake neman zame mata jiki ta ke tafiya ahankali, yayinda kanta ke k’asa tana me aikin mummurza y’an yatsun hannunta.

Hakika shigowanta cikin falon shiya sanya zuciyarsa tsananta bugawa, yayinda yasakejin komai nasa ya zama very weak, ahankali ya sauk’e idanunsa akan kyakkyawar fuskarta, wanda kuma hakanne ya tilasta masa d’an lumshe idanunsa, saboda yanda yaji wani irin sanyi na ratsa cikin jiki da b’argonsa.

Ita kuwa Laylerh duk da cewar bata d’aga kanta ta kallesa ba, amma hakanan taji ajikinta cewar idanunsa na yawo akanta, hakanne kuwa yasa takejin kamar k’afafunta zasu hard’eta ta fad’i.
Ta bayan wasu had’add’un Royal Gothic Chairs dake cikin falon tab’i tare da k’arasawa inda ta zauna d’azun, cikin sa’a kuwa tana isa wajen taga wayartata aje akan sofa, d’aukan wayar tayi tare da juyawa cikin yanayi na d’an sauri ta soma tafiya don barin cikin falon, wanda tun shigowarta cikinsa heart d’inta ke abnormal beating, duk yanda idanunta ke so da mararin ganinsa kuwa ta kasa iya d’aga kai ta kallesa, Sam batasan meyasa yau d’in takejin hakan akansa ba, duk da cewar sometimes takanji hot feelings akansa, amma feeling dinta na yau akansa da banne, wannan dalilinne ma yasa take sauri wajen ganin tabar cikin falon.
Agarin saurinnata ne kuma batare da ta lura ba adon dake jikin d’aya daga cikin Gothic chairs din ya kama k’asan skirt d’inta, wanda bisa dole hakan ya tilasta mata tsayawa.
Asanyaye ta b’ata fuska ganin da tayi cewar dole saita tsugunna kafun ta iya cire k’asan skirt dinnata daga jikin abun.

Kyawawan fararen k’afafunta da suka bayyana saboda d’an d’agewa da skirt dinnata yayi ya zubawa idanu, tare da maida hankalinsa ga kallon kyakkyawan red anklet chain d’in dake sak’ale a k’afarta na dama, sosai anklet d’in ya karb’i fatar nata kasancewar sa red colour mai adon white stones.
Kallon k’afafunnata yake da kyau baya ko k’yaftawa yayinda kuma sannu ahankali yakejin zuciyarsa nayi masa sanyi.

B’angarenta kuwa hardai yanzun tanajin idanunsa na yawo akanta, wanda kuma hakanne yasa ahanzarce ta janye skirt d’inta, cikin sauri sauri ta fice daga cikin falon, domin tayi imani cewa matuk’ar ta k’ara mintuna 4 masu kyau acikin falon to fa lallai bazata iya controling kai da kuma abunda ke cikin zuciyarta ba.
Da rikitattun idanunsa ya bita harta fice daga cikin d’akin kuwa bai d’auke idanunsa daga kallon hanyar da tabi ta fita d’inba.

Fou’ad da tun shigowar Laylerh’n ya zubawa Maleek d’in idanu, gyara zamansa yayi tare da d’an kawar dakansa gefe cikin d’an d’aga murya ta yanda yasan Maleek d’in zai iya jiyosa yace.
“Mutum dai yaci gaba da d’ibawa kansa zunubi ta hanyar yiwa abunda ba mallakinsa ba kallon k’urulla kallon haram.�
Jin abunda Fou’ad d’in ya fad’ane yasashi juyo da kansa, ya fuskanci Fou’ad d’in wanda yayi kamar ba daga bakinsa maganar da yayi yanzun ta fito ba.
Sam shikam Allah Ma yasani ayanzu bayida lokacin biyewa Fou’ad, saboda ya fuskanci cewar sai mutum nada lafiyane ma yake wani abun.

Shigowar Oum Ayush cikin falon ne kuma hannunta d’auke da d’an madaidaicin tray, yasa shi maida kallonsa gareta, saboda tsabar yunwan da yakeji har wani irin jiri ne ke damunsa, yana kuma kyautata zaton cewa cikin magungunan da Dr.Mouhammad ya basa akwai wanda yakesa cin abinci sosae.

A gabansa Oum Ayush ta ajiye madaidaicin tray d’in wanda samansa ke d’auke da plate d’in southern baked BBQ chicken da kuma d’an k’aramin glass bowl wanda ta zuba yankakken fruit salad mai sanyi aciki.

“Bismillah!.�
Tafad’a adaidai lokacin da take tura masa plate d’in gabansa.
Kasancewar kuma dama yunwa yakeji sosai hakan yasa baijirayi komae ba, cike da nutsuwa ya fara cin abincin, yayinda kuma time
to time yake d’an lumshe kyawawan idanunsa masu d’auke da gajiya da kuma yanayin bacci.
Oum Ayush kuwa hira suke d’anyi kad’an kad’an da Fou’ad wanda yace shi bazaici abincin ba.

B’angaren Laylerh kuwa tana fitowa daga falon kai tsaye part dinsu ta nufa, koda ta k’arasa sashin nasu bata samu Najeeb ba, wanda kuma da ‘alama baya gidanne ma baki d’aya.
Anan kan d’aya daga cikin kujerun falon ta kwanta, tare da d’aukan trow pillow ta rungume ak’irjinta, ahankali haka takejin bugun zuciyarta na lafawa, yayinda kuma nutsuwarta ke dawowa jikinta.
Saidai kuma har zuwa yanzun brain d’inta ta kasa daina maimaita mata kalmar da Abbou Jaheed ya fad’a cewar. “Doctors sunce Maleek bazae tab’a haihuwa ba!�
K’warai sosai maganar ta daki zuciyarta, tare kuma da wujijjiga tunaninta.
Ita da kanta take tambayar kanta dalilin shigowar wannan mummunar k’addarar cikin rayuwarsu.
“Shikenan Maleek bazai samu mai sakashi farinciki ba? bazae tab’a haihuwa ba hakan kuma na nufin har abada kenan? Shin tayaya zai iya jurewa wannan k’unci da kuma ciwon?�
“Lallaine kowani bawa da irin salon k’addararsa arayuwa, amma kuma ta Yah M.Jay ta kasance mai muni da kuma cutarwa, yah Allah Kabashi iko da kuma k’arfin jure duk way’annan damuwowin!!�
Tafad’i hakan abayyane cikin wata raunanniyar murya, wanda kuma hakanne ya bayyana zuban hawaye akan kyakkyawar fuskarta.
Tabbas tasan cewa ayanzu idan tace zatayi wani tunani ko kuka zuciyarta na iya bugawa, Hutu kawai takeson saboda har yanzu tana d’anjin ciwon kai kad’an kad’an.
Wayarta dake hannunta ta kunna tare da soma duba sak’onnin da aka turo mata, wanda cikinsu kuma harda sak’on komawarta makaranta da kuma na WAEC examination d’in da zasuyi nan da 2week.
Haka dae ta d’an duba sak’on da akayi mata d’in sama sama nanma saboda gudun kada tayi tunani mai zurfine shiyasa, tana cikin shafa wayar nata kuwa bacci b’arawo ya d’auketa.

Acan falon Abbou Jaheed kuwa a sosae Maleek yaci abincin da a Oum Ayush d’in ta kawo masa, duk da cewar kuwa bai cinye abinci da kuma fruit salad d’in duka ba amma yaci sosae.
Yana kammala cin abincin kuwa ya mik’e tsaye, da yake kuma y’an miskilancinnasa na kusa baice da su Oum Ayush d’in komae ba yasa kai ya fice daga cikin falon.
Kaitsaye sashinsa ya nufa, daga cikin tangamemen falonnasa kuwa direct bedroom d’insa ya shige.
Kayan dake jikinsa ya d’an rage tare da kutsawa cikin bathroom d’insa yayi wanka.
Bayan ya fito awankanne kuma yasaka wasu sauk’ak’akk’un riga da wando, wanda yasan cewa bazasu ta kurasaba.
Magungunansa yasha tare da hayewa saman makeken gadonsa ya kwanta.
Lokaci d’aya kuwa wasu irin tunani suka shiga yawo acikin k’wak’walwarsa, wanda asanadinsu ne kuma yaji zuciyarsa tayi matuk’ar karyewa, saidai kuma a irin yanayin da yakejin kansa ayanzu yasan matuk’ar ya biyewa damuwar dake sukar zuciyarsa, to bai wuce wata sabuwar matsala ta sameshi.
Sanin hakan da yayine kuma yasa lokaci d’aya yasoma k’ok’arin zeroying mind d’insa.
Kyawawan idanunsa masu d’auke da abubuwa kala kala ya lumshe, tare kuma da soma fitar da wani irin breath mai sanyi.
Cikin abunda bai wuce 20minutes ba kuwa wani irin nannauyan bacci ya d’aukesa, wanda kuma dama hakan shine burinsa.
Tunda ya fara baccin nasa kuwa bashine ya farkaba sai kusan magriba, haka yakejin jikinnasa gaba d’aya ba k’wari, toilet ya shiga ya d’auro alwala bayan ya fito daga toilet d’inne kuma kai tsaye ya wuce masallaci.
Anan cikin masallacin dake jikin gidansu yayi sallan Magrib, yana kuma zaune acikin masallacin har aka k’ira sallan Isha, bayan ansallame sallan Isha d’inne kuma ya dawo gida, again kuma wani baccin yakeji sosai, haka dolensa yasake komawa ya kwanta.

Awani k’arin abun mamakin kuwa shine daga shi har Laylerh yau d’in haka suka kasance kamar wasu bugaggu, domin ita d’inma bacci tayi sosai sallah ne kawae ke ta da ita, yanzun ma koda Najeeb ya dawo akan gado ya sameta, tana ta faman aikin bacci, saidai kuma kasancewar shid’in baya cikin mood maidad’i hakan yasa bai ta she ta ba, koda ya gama abunda zaiyi rab’awa yayi ya kwanta agefenta, yayinda yakejin k’irji da kuma zuciyarsa nayi masa wani irin k’una da kuma tarin rad’ad’i, aduk lokacin kuwa da zuciyarsa ta hasko masa abunda idanuwansa suka gane masa yau d’in sai yaji wani irin haushi, takaici, da kuma tsanar kanshi ya rufesa.
Haka dai zuciyarsa cike da tunani kala kala bacci ya d’aukesa.

*Washegari*
8:30 am

Wani irin juyi mai d’auke da alaman gajiya da kwanciyar nata tayi, kana ahankali ta soma ware kyawawan idanunta wanda suka d’auki kusan awa uku akulle, domin kuwa tunda tayi sallan asuba ta sake komawa sabon baccin da sai yanzu ta farka.

Tashi zaune tayi tare kuma da soma k’arewa cikin d’akin kallo, daidai lokacin kuwa wayarta dake aje akan bedside drawer ta soma fidda sassanyar wak’an Ali Gatie na (Running On My Mind) wacce ita ta kasance ringintone d’inta, saboda tana matuk’ar son wak’ar sosae.
Akasalance ta kai dubanta ga wayar, ganin kuma cewa sunan Oum Ayush ne ke yawo akan screen d’in wayar, yasa cikin sauri tasa hannu ta d’auki wayartata tare kuma da picking call d’in.
Oum Ayush dake kan layi kuwa jin Laylerh ta d’auki wayarne yasa batare da ta tsaya jin ta bakin Laylerh’n ba tace.
“Baccin ya isa haka, yanzu yanzu kizo dining area muyi breakfast.�

“To.� Kawae tace asanyaye, Oum Ayush kuwa take ta kashe wayar.

Ahankali ta zuro da kyawawan k’affunta k’asa, had’i da mik’ewa tsaye, y’ar ficikar rigar baccin dake jikinta ta kalla, wanda ita kanta ma batasan ya akayi ta saka ta ba, saboda tsabar baccin dake damunta jiyan.

Kaitsaye toilet ta wuce danyin wanka, sanin da tayi kuma cewa su Oum Ayush na jiranta ne yasa bata wani b’ata lokaci awajen wankan nata ba.

Bayan ta fito daga wankanne kuma ta tsane jikinta, tare da zama agaban dressing mirror ta shafawa jikinta mai, kamar kullum kuma iya powder,mascara da kuma kwalli kawae ta shafa, sai wani brown lips gloss da ta shafawa jajayen labb’anta, hakanne kuwa yasa lips d’innata ya fito da kala maikyau.

Turaren oud ta shafa had’e da d’aukan wata doguwar rigar English wears mai kalan brown ta sanya ajikinta, kasancewar kuma rigar irin pencil gown d’innanne maibin jiki, hakan yasa ta d’aura wani light brown denim jacket akan shigartata, sosai kuwa hakan ya k’ara bayyana yalwataccen kyawun da tayi.

K’aton agogon dake cikin d’akin ta kalla, take kuwa idanunta suka gane mata lokaci 8:55 am daidai.

Agurguje ta nannad’e dogon gashinta, tare kuma dasaka wani hulan turban mai kalan brown akanta.
Light brown shoes masu gashin kuliya tasaka ak’afanta, kana tasa hannu ta d’auki wayarta dake aje akan mirror.
Cikin sauri haka ta fice daga cikin d’akin.
Koda ta fito compound d’in gidan kaitsaye part d’in Momy ta nufa domin kuwa acan sukeyin breakfast.

Gaba d’ayansu zaune suke akan babban dining table d’in ciki kuwa harda Najeeb wanda sama da mintuna 15 kenan da zuwansa wajen amma yakasa kai koda loman abincine bakinsa.

Kamar kuma yanda suka hallara awajen cin abincin haka shima ya hallara, yayinda yayi wani irin kyau cikin shigar armany jeans da kuma crazy shirt d’in dake jikinsa.
Tabbas kallo d’aya zaka mishi ka fahimci cewar akwai sanjin yanayi atare dashi, saidai kuma amma yakasa bari idanunsa su nuna hakan.

Sab’anin mahaifinsa wanda tun zamansa awajen ya fahimci cewar Abboun nasa na d’auke da damuwa acikin zuciyarsa domin ya lura lokuta zuwa lokuta Abbou Jaheed d’in ke satan kallonsa, duk da kuwa baisan meyene azuciyar Abboun nasa ba, amma zuciyarsa ta fad’a masa cewa bawai abubane mai dad’i.

Ahankali yake d’an jujjuya tea spoon d’in dake hannunsa, daga gefe guda kuwa baked mozzarella stick d’in dake gabansa ya zubawa ido, duk da cewar kuma ya d’anyi nisa atunaninsa amma hakan baihanashi ji ajikinsa cewar Laylerh’n ta shigo cikin falon ba.
Wani sassanyar k’amshin daya daki hancinsane kuma ya sake tabbatarwa da kansa cewar Lallai ita d’ince, domin awajenta kad’ai yakejin irin k’amshin.

Ita kuwa Laylerh ganinsu duka akan dining area d’inne yasa anutse ta k’araso wajen. Bayan ta gaishe dasu Abbou Jaheed ne kuma anutse taja kujeran dake kusa da Najeeb ta zauna.
Wanda kuma hakan yasa ya zamana ita dashi suna facing juna.

K’asa k’asa batare kuma da ta bari idanunta sun sauk’a akansa ba, cikin shaking voice d’inta tace.

“Good morning Yah M.Jay....�

Shiru yayi kamar baijita ba, sannan bai kuma d’ago kansa ya kalleta ba, still tea spoon d’in dake hannunsa yake ta faman juyawa.

Laylerh kuwa jin bai amsa mata bane yasa ta lumshe idanunta wanda lokaci d’aya suka ciko da hawaye, Sam batasan meyasa wani lokaci idan ta gaishesa baya amsawa ba, bayan kuma yasan tasan cewar yanajinta.

“Why?�
Ta tambayi kanta.

“Saboda yasan ke mairaunice akansa.�
Wani b’angare na zuciyarta ya bata amsar hakan.

Fuskarta ta d’an shagwab’e, saboda sam bataji ta gamsu da hakan ba.

“Good morning!�
Najeeb dake gefenta ya fad’a k’asa k’asa, adaidai lokacin da yake turo mata plate d’in dake gabansa, wanda samansa ke d’auke da chips and ketchup, sai kuma wani d’an bowl wanda aka zuba perfect vanilla soufflé aciki.

Wani irin kunyansane ya kamata dan sai alokacinne ma take tunawa cewar sam basu gaisaba lokacin da ta tashi sallan asuba bayanan yana masallaci.

D’an sunkuyar da kanta k’asa tayi, kana asanyaye tace.

“I’m sorry morning Yah Najeeb.�

Murmushin daya bayyana kyawun fuskarsa yayi batare kuma daya ce mata komae ba ya kawar da kansa gefe.

Ganin hakanne kuma yasa jiki amace ta soma cin abincin daya turo mata d’in.

Almost 20minutes kenan yanzu da kowa yake ta hidimansa akan dining table d’in.

Ahankali Abbou Jaheed ya d’ago ya kallesu bayan kuma ya kammala goge bakinsa da tissue paper ne, yayi gyaran muryar dayasa dukanninsu d’agowa suka kalleshi, saidai banda M.Jay wanda tun d’azu yake ta abu d’aya kaman statue.

Abbou Jaheed kuwa d’an satan kallon gefen da Maleek d’in ke zaune yayi, kana cikin tausasa murya yace.

“Kuyi hak’uri da abunda za kuji daga bakina, domin kamar yanda na had’aku jiya na sanar daku matsalan da tasamu Maleek, haka yau ma nake mai bak’in cikin sake sanardaku wata magana wanda nasan bazata tab’a yi muku dad’i ba.�

Tsagaitawa da maganan nasa yayi tare da kallon Maleek wanda har yanzu kansa ke k’asa.

Anutse cikin kuma yanayin tausayawa yace.

“Bazan tab’a gajiyawa da baka hak’uri ba Maleek, nasan cewa kanajin ciwo da kuna acikin zuciyarka, amatsayina na mahaifinka kuwa ba zanso duk wani abu dazai cutar dakai ba, amma kasani bani da wani zab’i ayanzu wanda ya wuce fad’a maka gaskiya, domin kuwa Tabbas abune da yake abayyane, cewar ba kowacce mace ko iyaye bane ke barin y’ay’ansu su auri wani Namji ko Mace wanda bazasu tab’a haihuwa ba, hak’ik’a kowa yana da irin k’addararsa amma kasani wannan k’addarar k’addarace mai ciwo, domin kuwa asanadin ta jiya da dare Alhaji Farouk ya k’ira ya sanar dani cewa, Matarsa ta shaida cewar maganar aure tsakaninka da y’arsu Munnira babu ita, Tabbas Nikam na fahimcesa domin da ace asonshine zai iya baka auren y’arsa, saidai kuma amma ita kanta uwar yarinyar tana da nata hakk’in, shin ayanzu a kuma irin zamaninnan wace y’a mace ko kuma iyayene kake ganin zasu baka y’arsu ka aura bayan kana tare da wannan lalurar? k’addarama ace zaka samu hakan to bai zama lallai ya zamana son gaskiya ake maka ba, watak’ila zata aurekane Dan dukiyarka, wata k’ila kuma zata aurekane Dan kyau da matsayinka, wata k’ila kuma zata aurekane Dan kawai tayi suna, wanda ni kuma Ina matuk’ar jin tsoron hakan Maleek inajin tsoron wani abu dazai sake samun rayuwarka, duk da cewar inaji ajikina cewar wannan k’addarar zata sama maka farinciki watarana!!!�

*(Team Maleek inakuke🗣🗣🗣🗣🗣🗣 gobe zanyi Chapter 60, kuma kusani ga duk wani masoyin Maleek gobe ranarsace)*

*28/February/2021*

*1:45 pm*
3/1/21, 8:56 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*Not editing*

#divorce💔

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.