Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: LAYLERH MALEEK.txt
Chapter 55 of 65
*Chapter 72*
*â€ÂNAJEEBâ€?*
Ta k’ira sunan dake yawo akan screen d’in wayar, cikin zallan yanayi na mamaki, domin ko kusa bata tab’a kawowa aranta cewar k’iran Najeeb d’in zai shigo wayarta adaidai lokacin ba.
Tsurawa screen d’in wayar nata idanu tayi, had’e kuma da tsayawa ta kasa picking call d’in, tamkar kuma yanda numfashinta ke fita da sauri sauri haka ma bugun zuciyarta, idanunta ta d’an lumshe ahankali, tare da kai hannunta ta d’auki wayar nata k’irar iPhone11, saidai kuma cikin rashin sa’a tana d’aukar wayar, k’iran Najeeb d’in na katsewa.
Ai kuwa katsewar k’iran nasa ne ya bata daman sauk’e wani irin k’akk’arfan ajiyar zuciya, lumsassun idanunta ta bud’e tare dajan jikinta ta zauna akan wani Gothic chair dake kusa da gadon dake cikin d’akin.
Kunna hasken screen d’in wayar nata tayi, still kuma sunan Najeeb d’in take kallo, Yayinda a zuciyarta take tunanin sake bin k’iran nasa, saidai kuma idan ta bi k’iran nasa ya d’aga tace masa me?
Samma ita batayi tunanin k’iransa ba, tun bayan abunda ya faru atsakaninsu, sai kuma gashi shid’in akaron farko ya k’irata.
D’an sake lumshe idanunta tayi alokacin da hoton fuskarsa ya fad’o mata, murmushin daya sabayi akullum ne ya shiga yawo acikin tunaninta, wanda hakan yasa itama batare da tasani ba tad’an saki murmushi, Tabbas batajin soyayyarsa acikin zuciyarta, haka kuma batajin k’iyayyarsa, cause ma bashi da wani aibu ko tawaya da zaisa mace ta k’isa, kawai dai ta tsaida zuciyarta awaje d’aya ne, sannan kuma zuciyartata akan abu d’aya kawai ta ginu, wanda kuma har abada batajin zuciyartata zata tab’a sauyawa daga kan abunda ke rayuwa acikinta.
Turo k’ofar d’akin da akayine kuma yasa tayi saurin bud’e idanunta, ganin kuma cewar Oum Ayush ne ta shigo cikin d’akin yasa tayi saurin kawar da tunanin da takeyi.
Oum Ayush kuwa cikin kulawa ta dubi Laylerh’n tare da tambayarta ko tayi sallah.
Kai Laylerh’n ta jinjina mata alaman “Eh.�
“Yauwa to taso muje a fara miki wankan Amarya, saboda na kula idan ba mufara yanzu ba, to anan gaba bamu da wani isashshen lokaci.�
Ta kai k’arshen maganan nata, tana me kamo hannun Laylerh’n.
Laylerh kuwa jin abunda Oum Ayush ta fad’ane yasa ta d’an shiga mamaki, cikin kuma son samun gamsuwa tace.
“Wankan Amarya kuma Oum Ayush? Meyasa? Ni yanzu ai ba amarya bace.�
Murmushi Oum Ayush tayi, Kamar kuma zata ce wani abu, sai ta fasa, saboda ba yanzune take son Laylerh’n ta sani ba.
Ahaka suka fice daga cikin d’akin, tana me rik’e da hannun Laylerh’n batare kuma da taba ta amsar tambayarta ba.
Direct wani keb’abb’en waje dake cikin sashin Oum Ayush d’in suka nufa, inda suka taradda wasu mata biyu na zaune, wanda ga dukkan alama kuma Oum Ayush d’in ce ta gayyatosu.
Ita dai Laylerh ido ta zuba musu alokacin da suka sa ta cire kayanta, wani d’an k’aramin towel suka bata ta d’aura, Kamar kuwa yanda suka umarceta akan ta shiga cikin wani abu mai kaman bathtub, haka ta shiga ciki ta kwanta babu musu.
Wani irin abu mai
Tsananin k’amshi matannan suka shiga shafa mata ajikinta, tare da zuba wani irin ruwa mai kaman madara acikin bathtub d’in, wanda ya zamana yana ratsa ko ina d’inta.
Oum Ayush dake tsaye agefe kuwa, murmushi tayi musamman ganin yanda matan biyu ke aikinsu yanda ya dace, ta tabbata cewa awannan karon Maleek zai samu farinciki marar yankewa, domin tayi imani cewar da jikin Laylerh’n kad’ai aka barsa, zai samu gamsuwa hundred percent.
Agogon dake daure atsintsiyar hannunta ta kalla, ganin time da tayi ya d’anja ne, yasa ta juyawa ta koma cikin falonta, inda tabar manya mata biyu kuma k’wararrun masu gyaran Amarya’n da ta d’auko, d’aya daga Maiduguri d’aya kuma daga Niger 🇳🇪 na k’ara Murje jikin Laylerh’n, had’e kuma da tsuma mata jikinta da daddad’an k’amshi marar gushewa.
*MALEEK*
Ahankali ya d’an lumshe idanunsa, wanda suka b’ata tsawon mintuna,ya suna kallon kyawawan taurarin da suka k’awata sararin samaniya, daga gefe guda kuwa wani irin ni’imtaccen iska da sanyi ne ke ratsa kowani silin b’ulin gashin dake jikinsa.
Hak’ik’a kewarta yakeji sosai, wanda har hakan yasashi kasa zama acikin falon sa, ya fito wajenne kuma wai ko zai samu nutsuwar zuciya, saidai kuma amma Ina, babu abunda ya sauya, domin kowani bayan second ji yake zuciyarsa na sake azalzala dason ganinta.
Wani irin sassanyan numfashi ya fitar, tare dasa hannunsa
ahankali ya shafi tattausan sajen dake kwance akan fuskarsa.
Tabbas shikam yayarda cewa matsanancin kewarta da yakeyi ne, ke sawa yaji wani irin hot feeling na yawo acikin jikinsa.
Pink tongue d’insa ya ciro tare da kama jajayen labb’an bakinsa ya lasa,
hakan da yayi d’inne kuma ya tuno masa da moment d’insu time d’in da aka d’aura mata Aure da Najeeb.
Wani irin abune yaji ya tokari k’irjinsa, take kuma d’aci ya ziyarci mak’oshinsa sam baisan meyasa ba, akullum idan ya tuna cewar wani ya tab’a mallakan Laylerh’n, ya kanji kamar yayi hauka, domin k’unci da tsananin k’unane ke mamaye zuciyarsa, sosai yakejin ciwo da kuma rad’ad’in abun, wanda har hakan yasa sam sam baya mason tunawa.
Idanunsa da suka d’an sanja kala lokaci d’aya ya bud’e, tare kuma da kawar da kansa gefe, haka yakejin tamkar yanzu ne abun ke faruwa, tamkar yau ne aka d’aura auren Laylerh’n da wani daban.
K’arfen daya rik’e ya sake tare da d’an soma jan jikinsa dake b’ari baya, wanda tuni gargasan jikinnasa duk sun mimmik’e, abu kamar wasa kuma sai gashi mood d’insa ya sanja lokaci d’aya.
Juyawa yayi cikin kunci da tafasar zuciya ya koma cikin falon.
Fou’ad dake zaune acikin falon kuwa, ganin Maleek d’in ya shigo afusace ne yasashi saurin maida hankalinsa garesa, bakinsa ya bud’e da niyar yiwa Maleek d’in magana, amma kuma saidai abunda yaga Maleek d’in ya d’auko ne yasa shi jan bakinsa yayi shiru, saima idanu daya tsura masa.
Maleek kuwa k’arasowa cikin falon yayi, tare da jawo wani babban table dake tsakiyar falon.
Takardar cocaine d’in dake hannunsa ya fasa akan saman table d’in, batare daya jira komai ba kuwa ya kafa kansa akan table d’in ya soma shak’an fowder’n.
Sauri sauri haka yake shak’an cocaine d’in, tamkar wani zautacce ko kuma mayunwacin zaki.
Fou’ad kuwa dake zaune idanu ya tsurawa Maleek d’in baya ko k’yaftawa, Allah Yasani yana matuk’ar mamakin hali irin na Maleek d’in, wanda kuma har yau ya kasa sanjawa.
Kansa ya d’an girgiza cike kuma da takaicin halin da Maleek d’in yasa kansa aciki yace.
“Ko yaushe kasani abunda kakeyi bamai kyau bane, tayaya zaka maida cocaine tamkar wani abinci ko abun shanka? Koda yaushe idan ranka ya b’aci sai kata shak’awa kanka masifa, masifar da kasan illanta da kuma cutarwarta, har sai yaushe ne zaka girma Maleek? Sai yaushe zaka daina aikata kuskure akan kuskure? Bakajin maganan kowa, duk abunda zuciya ta fad’a maka shi kawai kake aikatawa, Why Maleek? Why? Ni nasan cewa idan Laylerh tasan kana irin wannan rayuwar bazata tab’a jin dad’i ba, dole ne kuma zatayi kuka, yanzu kafison abunda zai cutar dakai kuma ya cutar da Laylerh kenan? ahaka kuma kullum kake ganin dacewar ku da ita, hmmmm nasani da ace kowa zaisan hakan to da duniya ta gamsu cewar Laylerh da Najeeb ta dace bawai dakai me shan hodar ibilis ba!!!�
Akaron farko ya d’ago kansa, tun bayan kifa kansa da yayi akan table d’in, idanunsa wanda suka rune sukayi jajur ya zubawa Fou’ad, wani irin kallo yake masa mai alaman magana, da kuma nuna matsanancin b’acin rai, saidai kuma acikin irin yanayin da yake sam bayajin zai iya magana, hakan yasa shi jingina da sofa, tare kuma da maida fitinannun idanunsa ya kulle.
Fou’ad kuwa harara ya watsa masa, batare kuma daya sake cewa komai ba, ya tashi gaba d’aya yabar cikin falon.
Fitansa daga cikin falonne kuma yasa Maleek d’an zame jikinsa ya kwanta, haka yake jin duniyar na juya masa, sama ya koma k’asa haka k’asa ta koma sama, saidai kuma idan da sabo ya sabawa hakan, domin dama ance sakai yafi bauta ciwo.
Yana acikin badmood dinnasa ne kuma nannauyan bacci ya d’aukesa.
Acan gidansu Laylerh kuwa Kusan awa guda matannan suka b’ata suna yi mata gyaran jiki, har dai saida tayi laushi kafun suka barta ta sarara, bayan ta koma dakinta ne kuma ta sakeyin sabon wanka tare da d’auro alwala tazo ta gabatar da salla’n Isha.
Saboda tsananin gajiyan da yake damunta ne kuma yasa tana kwanciya bacci ya d’auketa, daga gefe guda kuwa kowani kusurwa na jikinta, dadda’an k’amshi yake fitarwa.
Washegari
Tun k’arfe 7 tatashi, Kamar kuma safiyan jiya yauma da madarar shanu ta karya, bayan kuma ta keb’e Kanta ad’akine ta d’auki sauran ragowan maganin da Oum Ayush ta bata jiya ta shanye, sam tama manta wani k’a’idar shansa da Oum Ayush d’in ta fad’a mata.
Bayan tagama shanye maganinne kuma Oum Ayush tazo ta kama hannunta suka wuce wajen masu yi mata gyaran jiki.
Yau ma d’indai sosai jikinta yasha gurza, saidai kuma ita kanta idan ta shak’i k’amshin dake fita ajikinta, sai taji wani irin hot feeling ya ratsa ta.
Almost 1hour da shan maganin nata ne kuma, taji wani irin ciwon Mara na d’an taso mata, saidai kuma sanin da tayi cewa bawai period d’inta ne zaizo ba, yasa bata wani damu sosai ba.
Koda aka gama yi mata gyaran jikin ma d’aki ta koma ta kwanta, saboda ta lura tun safe bak’i ke zuwa cikin gidannasu, gashi sai hidiman canja furnitures da kuma gyare gyara ake tayi agidan,wanda duk ita batasan na meye ne hakan ba.
Tana kwanciya kuwa ba jimawa bacci ya d’auketa.
Only 20mn kuwa acikin baccin nata taji wani irin azababben ciwo na tashi daga cikin mararta, wanda yayi sanadiyar bud’e idanunta.
Ahankali ta tashi zaune tare dasa hannu ta dafe marar nata dake yi mata wani irin ciwon da bata tab’a jin irinsa ba.
Santala santalan legs dinta ta zuro k’asa daga kan gadon, tare da yunk’urin mik’ewa tsaye, saidai kuma bata kai ga k’arasa mik’ewa tsayen ba, ta saki wani irin azababben k’ara tare da saurin komawa ta zube akan guiwowinta.
Daidai lokacin ne kuma Oum Ayush da Aunty Zee harma da Aleeya suka shigo cikin d’akin.
Jin ihunta da sukayi ne kuma yasasu k’arasa shigowa cikin d’akin da sauri.
Oum Ayush ne tayi hanzarin rik’ota, hankalinta atashe tace.
“Lafiyanki k’alau kuwa Laylerh, me yake damunki?�
Kanta ta d’an shiga girgizawa, tare kuma da soma yarfa y’an yatsun hannunta, kasancewar zuwa yanzu sosai marar nata ta tsananta ciwo, ko tsayuwa mai kyauma ta kasa yi.
“Marana Oum Ayush, marana ciwo yake inajin kaman zai fashe!!�
Tayi maganan cikin muryar kukan daya k’wace mata, tare kuma da sake ci gaba da yayyarfa yatsunta.
“Subahanallah!�
Dukansu suka had’a baki wajen fad’a, cikin yanayin tausayawa kuma Oum Ayush dake rik’e da ita ta zaunar da ita akan gado, hannunta d’aya tasa ta d’an danna saman marar Laylerh’n, Jin kamar marar ta kunbura ne kuma yasa Oum Ayush saurin d’agowa ta kalli Laylerh’n, fuskarta d’auke da tarin damuwa tace.
“Ya ilahi Laylerh me kika sha haka, kodai period time d’inki ne yayi?�
K’ara volume d’in kukanta tayi, tare kuma da d’an girgiza kanta alaman “A’a ba period d’inta bane.�
Kwantar da ita Oum Ayush tayi, tare da d’anyin Jim tana me son nazartar yanayin Laylerh’n, aikuwa take wannan maganin ya fad’o mata arai, Da sauri ta kamo hannun Laylerh’n tare da fad’in.
“Ina maganin dana baki jiya da safe, wanda nace kina shan kad’an kad’an?.�
Duk da azababben ciwon dake cinta kuwa, saida taji k’irjinta ya buga alokacin da Oum Ayush ta tambayeta maganin, ad’an tsorace kana kuma da muryar sheshhek’an kuka tace.
“Nashanye!.�
Idanu Oum Ayush ta zazzaro waje cike da tsananin mamaki, da kuma tsoron abunda zai biyo baya.
Hankalinta amatuk’ar tashe tace.
“Why Laylerh? Why? Meyasa zaki shanye shi duka? Koda na kawo miki saida na fad’a miki yanda zaki na sha, amma saboda shegen son zak’i irin naki, kin shanyesa lokaci d’aya, kin san k’arfinsa kuwa? Meyasa kikayi haka Laylerh? Wallahi ko tantama banayi shiya saka miki wannan azababben ciwon maran da bashi da magani anan kusa.�
Idanunta dake tsiyayar da hawaye ta rumtse da k’arfi, had’e da sakin wani azababben nishin wahala.
Sam kwata kwata ma ita bataji fad’an da Oum Ayush d’in keyi ba, saboda zuwa yanzu ciwon nata k’aruwa yake bayan kowani second.
Ganin yanda take ta mik’ewa ne kuma yasa Oum Ayush tashi tsaye, zuciyarta cike da danasanin bawa Laylerh maganin, ta fice daga cikin d’akin.
Kaitsaye d’aki ta wuce tare da d’auko wayarta, tayi dialing number’n family Dr d’insu.
Bayanin ciwon Laylerh’n ta masa, take kuwa yace gashinan zuwa.
Duk da tasan cewar maganin hospital bazaisa Laylerh’n ta daina jin radad’in ciwon ba, koda ma ace ta samu maganin ciwon maran, To fa feeling din da zatakeji bazai tab’a barinta ba dole sai Namiji yayi sex da ita kafun ta samu cikakken relief, Thank God Ma yanzu aurenta da Maleek d’in saura 3days.
Ruwa maisanyi Oum Ayush d’in ta kai mata tasha, still har yanzu kuma kukan ciwon marar take.
Mintuna 15 kacal tsakani Dr ya k’araso, checking d’inta yayi da kyau, gane kuma da yayi cewar akwai feeling mai k’arfi ajikinta ne yasashi yi mata alluran relief da kuma wanda zai sata bacci, domin yasan yawan feeling ma na d’aya daga cikin best abunda ke jawo ciwon mara.
Aikuwa yana yi mata injections bacci ya d’auketa, wasu pain relievers ya bata sannan ya tafi.
Ganin ta samu bacci ne kuma yasa su Oum Ayush fita waje suka jawo mata k’ofar.
Aranar yau d’in gaba d’aya hidima sosai sukayi, domin ayau ne ma’aikatan OJC Concept suka zo suka sanja musu gaba d’aya furnitures d’in falukan gidan, furnitures masu kyau da tsada aka zuba musu.
Acan b’angaren Laylerh kuwa tunda Dr yayi mata injections, bacci take bata farka ba, har saida aka yi sallan Isha.
Koda ta tashi haka taji duk jikinta babu k’wari, hatta awajen yin wanka saida Oum Ayush ta taimaka mata, bayan kuma ta biya sallolin dake kanta ne, Oum Ayush ta kawo mata kayan fruits tasha, ko mintuna 30 ba ayiba kuwa still ta sake komawa wani baccin.
Wani babban abun mamaki kuwa shine kamar yanda Laylerh’n ta wuni tana bacci, haka ma Maleek dake can gidansa, shima yau d’in wuni yayi yana abu d’aya, saboda tun cocaine d’in daya sha daren jiya har yanzu bata gama sakeshi ba, kasancewar cocaine d’in nada k’arfi sosai.
The following day
Thursday.
Tabbas komai aka sawa lokaci sai yazo, Kamar dai yanda yakasance yau auren saura kwana biyu.
Gaba d’aya yanzu gidan nasu acike yake da jama’ar Oum Ayush wanda yawancinsu k’awaye da kuma y’an uwanta ne, saidai kuma awannan karon harda mutanen Egyft suma sunzo, wanda suke matsayin y’an uwansu Abbou Jaheed.
Sosai aketa hidiman biki, duk da cewar ba za’ayi program ko daya ba, amma hakan bai hana jama’a cika acikin gidan ba.
Saidai kuma rashin lafiyar Laylerh’n gaba d’aya yasa jikin su Oum Ayush yayi sanyi, saboda har yanzu marar nata bai daina ciwo ba, tana dai samun relief ne kawai idan tasha maganin baccin da Dr ya bata, daga zangar ta tashi abaccin kuwa amfanin maganin na k’arewa ciwon zai dawo, ga wani matsanancin feeling d’in da yake neman haukata mata lissafi, wanda akoda yaushe hakan ke sawa taji kaman tayi kuka, wannan dalilin yasa bata ko fitowa yanzu gyaran jikin ma an d’an lafa mata dashi.
Acan b’angaren su Abbou Jaheed ma sam basu zauna ba, Dan tuni sun gama raba invitations cards wa jama’arsu.
Ciki kuwa harda Fou’ad wanda shine ya tsaya akan komai da komai na bikin, hatta kayan da Ango zai sa yariga daya tsara komai.
Yayinda ya tura invitations card ga kowa, kama daga kan friends d’insu harma da abokan aikinsu.
Ab’angaren Maleek kuwa ya lura da yawan zirga zirgan da Fou’ad d’in keyi, saidai kasancewarsa ba mutum ne me yawan shisshigi ba, shiasa bai tambaya ba, hasalima gaba d’aya wunin yau a office d’insa yayi, saboda ayyuka sun d’anyi masa yawa, shi yasama bai dawo gidan ba sai 11pm, koda ya dawo kuwa bai kula da abunda yaga Fou’ad din nayi ba, kaitsaye bedroom d’insa ya wuce ya kwanta.
*Friday*
Alhamdulillah yau Koda ta tashi bata ji ciwon marar nata ya tsananta kamar yanda ya sabayi mata akwana biyun da suka wuce ba.
Samun k’arfi ajikinta da tayi ne kuma yasa ta fito zuwa falo.
Sosai kuwa su Oum Ayush sukaji dad’in ganin jikin nata, hakan nema yasa Oum Ayush ta k’ira meyin zanen Henna ta zana mata, wani irin kyau’n da Laylerh’n tayi kuwa har d’auke idanun jama’a yake, musamman da zanen red henna d’in ya kwanta akan skin d’inta.
Ita dai kam har yanzu ta kasa fahimtar komai, dake faruwa acikin gidan.
Saidai ayau d’in tasa aranta cewar zata tambayi Oum Ayush dan sanin hak’ik’anin abunda ke faruwa.
Hakanne kuwa ya kasance domin tana idar da sallah’n Isha ta mik’e tsaye, direct bedroom d’in Oum Ayush ta nufa.
Oum Ayush dake zaune akan gado tana Ware wasu Sabin clothes din da aka kawo mata d’inki, ganin Laylerh’n da tayi ne kuma ya sata sakin murmushi.
Tare da cewa.
“Laylerh bakiyi bacci ba?.�
Kanta tad’an jinjina alaman “Eh.�
Asanyaye kuma ta zauna agefen Oum Ayush d’in, cikin muryarta dake tafiya very slowly tace.
“Oum Ayush wai waye zaiyi aure? naga gaba d’aya anata hidima.�
D’an dakatawa daga duba clothes d’in Oum Ayush tayi, tare da juyowa ta kalli Laylerh’n, fuskarta d’auke da murmushi tace.
“Auren wa kike tunanin za’ayi agidannan Laylerh idan ba naki ba? Kodai baki shiryawa yin auren bane?�
Kanta ta d’ago da sauri, tare da zaro idanunta waje, murya na rawa tace.
“Aure na kuma Oum Ayush?�
Jinjina mata kai Oum Ayush tayi, tare da kamo hannayenta ta rik’e Cike kuma dason bata k’warin guiwa tace.
“Abunda zuciya keso ne zata samu Laylerh, sannan kuma muradin dake yawo acikin zuk’ata biyu ne ke son cika, Insha Allah Ayanzu babu wani abu dazai dakatar da farincikin ku, saboda haka kwanta kiyi bacci, domin gobe da sassafe za’a shiryaki..�
Baki idanu harma da hanci ta bud’e tana kallon Oum Ayush, da kalamanta suka sa taji ta tamkar ta zama wata statue, domin gaba d’aya tunaninta tsayawa yayi, abu d’aya ne kawai ke kai kawo acikin Brain d’inta shine AURE’n da Oum Ayush tace za’a mata.
Saidai tunanin nata baije ko ina ba, haka bisa dole ta katse shi, alokacin da taji Oum Ayush d’in na cewa.
“Ta kwanta anan d’akin, ita zata je wajen Abbou Khareem.�
Har Oum Ayush d’in kuwa ta fice Laylerh bata d’auke idanu akanta ba.
Gaba d’aya ma tarasa tunanin me zatayi.
Hakan yasa ahankali ta sulale ta kwanta akan gadon, tare da lumshe idanunta, ga mamakinta kuwa ji tayi wasu irin k’walla masu sanyin gaske na bin gefen fuskarta.
K’wallan da ita kanta batasan na menene ba.
Lokaci guda kuma taji wani irin sanyi na ratsa cikin tafin k’afanta dama zuciyarta.
Hakan kuwa shi yasa ta dunk’ule jikinta waje d’aya, tare da soma sauk’e wani irin ajiyar zuciya.
*M.Jay*
*12:30 am*
Sassanyar iska da kuma sanyin dake hura jikinsa ne yasashi bud’e idanunsa wanda suka b’ata tsawon lokaci a kulle, duk da cewar kuwa ba bacci yake yi ba, domin yanzu ak’alla 1 hour ya b’ata da kwanciyarsa amma sam bacci yak’i zuwarwa idanunsa.
Wani irin bak’on yanayi yakejin kansa aciki, yanayin daya kasa fassarasa, domin zai iya cewa tunda yake aduniya bai tab’a jin zuciyarsa tayi sanyi irin na yau d’in ba.
Ajikinsa yakejin cewa Lallai da gaske wani abu babba zai faru dashi, domin hatta bugawar zuciya da numfashinsa ayau d’in sun sanja.
Sake gyara kwanciyarsa yayi akaro na barkatai, tare da d’aga idanunsa ya kalli agogo, hakanan yake ganin daren yau d’in yayi masa tsayi, tamkar ma gari bazae waye ba yake ji.
Kansa ya d’an girgiza tare da tashi zaune, ahakikanin gaskiya so yake ya gano asali da kuma gaskiyar abunda yakeji, saboda yanda yakejin kamar yana zumudin wani abune wanda baisan menene ba.
Ganin kuma da yayi, tunani na shirin haukata masa Brain d’insa ne, Yasashi Saukowa daga kan gadon, tare da wucewa toilet ya d’auro alwala.
Koda ya fito daga toilet d’in sallaya ya shumfud’a tare da soma gabatar da nafilfilu.
Haka ya d’auki lokaci mai tsawo yana sallah, har sai k’arfe 3 kafun ya sake komawa ya kwanta.
Cikin ikon Allah kuwa yana kwanciya bacci mai d’auke da mafarkai kala kala ya d’aukesa.
Ana soma kiraye kirayen sallah’n Asuba kuwa ya farka.
Tare da Fou’ad sukaje masallaci, suna dawowa kuma ya sake komawa bacci.
Fou’ad kuwa ganin Maleek d’in ya sake komawa bacci ne yasashi sakin murmushi, tare da daukan waya ya kira Abbou Jaheed.
Basu wani jima suna wayan ba kuwa sukayi sallama.
Fou’ad na ajiye wayan ya shiga kimtsa musu abubuwan da zasu buk’ata, shikansa ayau jin zuciyarsa yake babu ko digo na damuwa, akaron farko dai yau Captain Maleek Jaheed Gwani zai angwance.
Tabbas arana irin ta yau din babu wani wanda zai iya misalta farinciki da kuma annushuwar dake cikin zuciyar duk wani wanda yasan Laylerh Maleek.
Ranace ta musamman wanda bazasu tab’a manta taba har abada.
Ranace da zuk’atan dake d’auke da dakon juna zasu zama abu d’aya, buri d’aya, fata d’aya, kana kuma muradi d’aya.
K’warai wannan SATURDAY d’in tazo da mahimmanci sosai acikin a halin.
10:00am
Daidai
Hayaniya da kuma surutan dake tashi acikin falonne yasashi d’an soma bud’e idanunsa.
Addu’an tashi daga bacci yayi tare da d’an yunk’ura ya tashi zaune.
Tabbas hayaniya yakeji acikin falonnasa bawai kunnuwansa ne keyi masa gizo kamar yanda ya dauka ba.
Yar karamar tsaki yayi domin yasan cewa, idan ba Fou’ad ba babu wanda zai tara masa jama’a acikin gida.
Saukowa daga kan gadon yayi, tare da wucewa toilet kaitsaye.
Wanka yayi sannan yayi brush, duk da cewar kuma yanajin yunwa sosai amma bayajin zai iyacin wani abinci.
Ahankali ya murd’a handle d’in k’ofar toilet d’in ya fito, jikinsa sanye da white bathrobe.
Turus haka ya tsaya yana me kallon Fou’ad da SOORAJ wanda suke zaune akan gadonsa, gaba d’aya dukansu sunyi wani irin kyau, cikin shigar babbar rigar dake jikinsu.
Murmushi SOORAJ yayi masa, tare da tasowa ya k’araso kusa da shi.
Hannunsa yasa yad’an bugi shoulder’n Maleek d’in.
Cikin yanayinsa na wanda bai saba magana ba yace.
“Congratulations!!�
Murmushi shima Maleek d’in yayi, duk da baigane akan me SOORAJ d’in keyi masa congrats ba.
Fou’ad kuwa tasowa yayi, cikin hanzari ya jawo Maleek d’in.
“Kayi sauri ka shirya bamu da lokaci 11 daidai bama african time.�
Fou’ad ya fad’a adaidai lokacin da yake kai Maleek d’in gaban mirror.
Still batare daya fahimci inda kalaman Fou’ad din suka dosa ba, ya d’auki. Men body lotion d’insa ya shiga shafawa.
Bayan ya kammala ne kuma ya gyara beautiful beard d’insa da kuma tarin sumar kansa.
Had’add’en spray d’insa ya shafa, ganin kuma yana k’ok’arin bud’e closet d’insa zai d’auki kaya ne yasa Fou’ad yayi saurin mik’o masa set d’in wata had’addiyar white getzner da aka killacesa cikin wani had’add’en kwali.
“What?�
Ya fad’a yana me kallon kwalin da Fou’ad d’in ke mik’o masa, wanda aka k’yale jikinsa da ado.
“Kasa.�
Fou’ad ya basa amsa atak’aice, tare kuma da ajiye masa kwalin agabansa.
Kallon Fou’ad d’in yayi, Kamar kuma zaice wani abu saiya fasa, tare da d’aukan kwalin ya bud’e.
Idanunsa ya d’an lumshe saboda ganin had’add’iyar getzner’n da aka k’awata ta da d’inki, riga da wando da kuma babbar riga, wanda akayiwa wani fitinannen aiki da blue colour d’in zare.
“What babbar riga? Nasaka saboda meye?�
Yayi maganan cikin wata had’add’iyar muryarsa da ba’a saba jinta ba.
Matsowa kusa dashi SOORAJ yayi, cikin yanayin son bashi k’warin guiwa yace.
“Kasa please kada kayi musu, zamuce daurin aure, kayi sauri munajiranka afalo.�
Ko jiran abunda Maleek d’in zaice bayyiba ya ja hannun Fou’ad suka fita daga cikin d’akin.
Maleek kuwa kayan yabi da kallo, azuciyarsa yana me mamakin kyau da kuma tsadan getzner d’in, musamman aikin da akayi wa babban rigar yasan yaja kud’i.
“Bikin waye To kenan?.�
Yayiwa kansa tambayar da babu mai basa amsarta.
Ganin kuma idan ya tsaya zai b’atawa kansa lokaci ne, yasashi d’aukan riga da wandon ya saka, kafun daga bisani ya d’aura babbar rigar akai.
Yah Allah Bak’armin kyau kayan sukayi masa ba, wanda shi kansa saida yaji hakan ajikinsa.
Aikuwa kyawun nasa bai sake bayyana ba, saida ya d’aura wata had’add’iyar hulan dake had’e da kayan, me ratsin blue colour asaman akansa.
Black socks ya sakawa fararen k’afansa, tare kuma da zura wasu had’add’un classicshoe masu kalan blue, wanda suka k’ara bayyana had’uwa da kuma kyaun kwalliyarsa.
Still wannan kwalin ya bud’e ya ciro agogon Rolex mai kalan bluesy ya daura akan tsintsiyar hannunsa.
Sassanyan turaren Dolce&Gabbana ya fesa ajikinsa, tare da d’an juyawa ya kalli mirror.
Kyawawan idanunsa ya d’an lumshe, domin ya gamsu da irin baiwar kyau da Allah Yayi masa.
Ahankali ya shiga tafiya da takunsa mai matuk’ar d’aukar hankali.
Hannunsa ya daura akan handle d’in kofar tare da murdata Ahankali.
Wani irin fitinannen kamshinsa daya daki hancinsu Fou’ad ne kuma yasa duk suka maida kallonsu ga kofar bedroom d’insa.
“Wow!!!�
Shine abunda gaba d’ayansu suka fad’a alokacin da sukayi ido biyu dashi.
Lallai Tabbas ayau ko makiyinsa zai shaida irin kyaun da yayi, Tabbas sun sake yarda cewa Maleek kyakkyawa ne ajin farko, ko su da suke maza ma ya burgesu inaga mata.
Hannunsa Sooraj d’in Zeeyaderh ya kamo, tare da yiwa su Fou’ad alama akan su tashi su tafi.
Ahaka suka fito gaba dayansu kowannensu kallo d’aya zaka masa, kasan cewa kud’i, Hutu da kuma kyau na kai musu.
Cikin wata had’add’iyar 2020 Mercedes Benz G63 suka shiga, shida SOORAJ ne abaya, sai Fou’ad dake gaba wanda shi zaiyi driving d’insu.
Sauran friends din nasu kuwa wanda basu wuce su 4 ba, kowannensu motansa ya shiga.
Haka motocin suka jero akan shumfud’add’en titi’n, dagani kasan wasu masu matsayinne acikin motan.
11:40 am gaba d’aya k’ofar gidan Acike yake da dubbannin jama’a, kama daga kan manyan y’an kasuwa zuwa masu siyasa, ciki kuwa harda govenors na wasu states mabanbanta, wayanda duka bakin su
Abbou Khareem da kuma Abbou Jaheed ne.
Kowa ka gani acikin bakin kuwa fuskarsa dauke take da murmushi, banda su Abbou Jaheed da suka rasa inda zasu kai farincikin su.
Ahankali ya d’ago kansa daga danna wayarsa da yakeyi, ganin hanyar da suka kamane kuma yasashi saurin kallon Fou’ad, cikin yanayi nadan mamaki yace.
“Fou’ad Ina zamuje ne?�
“D’aurin aurenka.�
Fou’ad ya bashi amsa kaitsaye.
Daidai lokacin kuwa suka iso bakin harabar gidannasu dake cike da jama’a.
Idanunsa ya d’an zaro waje, tare kuma da sa hannunsa yad’an dafe zuciyarsa, wanda tun tashinsa yakejin tana tsananta bugawa.
Mutanen dake cike awajen ya kurawa idanu, zuciyarsa cike da wasi wasi.
Saidai kafun ma yayi wani tunani kamo hannunsa da SOORAJ yayi ya katse masa duk wani hanzarinsa.
Abdoul ne ya karaso da sauri ya bud’e musu murfin motar, aikuwa yana sako k’afarsa waje yaji bugun zuciyarsa ya tsananta.
Bai kuma tsinke da al’amarin ba saida yaji marok’a na shelan cewa Ango ya iso, wanda hakan yasa masu Algaita suka soma busawa.
Abbou Khareem ne ya k’araso inda suke tare da kamo Maleek d’in suka k’arasa cikin wajen da aka k’awatasa dan d’aura auren.
Koda suka shiga cikin wajen kuwa kallone ya dawo kansu, zaunar dashi Abbou Khareem yayi kana shima ya zauna.
Tare kuma da sanarwa limaman dake wajen cewa Ango yazo za’a iya d’aura auren.
Kamar yadda yazo a shari’ar musulunci Abbou Jaheed ne ya dubi Abbou Khareem, tare dayin gyaran murya cikin nutsuwa da kuma bayyana farincikinsa, yace.
*Ni Alhaji Jaheed Ina nemawa d’ana ABDOUL MALEEK JAHEED auren AYSHA MAHMOUD NA’EB bisa sadaki Naira Million Biyu.�*
Murmushi Abbou Khareem yayi tare da gyara zamansa cikin girmama yayannasa yace.
*â€ÂNi Alhaji Abdoul Khareem na bawa ABDOUL MALEEK JAHEED GWANI auren AYSHA MAHMOUD NAEB a bisa sadaki 2million Naira.â€?*
*Alhamdulillah Aure ya d’auru*.
*(This page is dedicated to all LAYLERHMALEEK fans)*
*25/March/2021*
*10:23 pm*
3/27/21, 7:16 AM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Not editing*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.