Best Hausa Novels

Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: LAYLERH MALEEK.txt

Chapter 64 of 65

*Chapter 81*

Wani irin numfashi me sanyi ya fesar,musamman alokacin da yaji yanda sugar lips d’in Laylerh’n ke tsotsan tongue d’insa.

Yayinda daga gefe guda kuwa tsikar jikinsa ne ke wani irin tashi, lokaci d’aya komai ya soma k’ok’arin k’wace mai.
Tabbas yasan idan aka k’ara wasu y’an minutes, zaikai wani stage da ba lallaine ya iya jurewa ba.

Ahankali yad’an tallafo hab’arta tare da zare bakinsa daga cikin nata, ya k’urawa kyakkyawar fuskarta ido, hakan da yayi d’inne kuma yasa Laylerh’n lumshe Idanunta, tare da d’an fito da harshenta, tana lashe sauran saliva d’insa dake kwance akan lips d’inta.

Ahankali ya jawo wata leda dake gefensa, tare da bud’eta ya ciro magungunan dake ciki, b’are iya adadin magungunan da yasan Laylerh’n zata sha yayi, daga jikin kowani sachet, kafun shima ya b’are nasa ya watsa acikin bakinsa, ba tare kuma da yasha ruwa ba haka ya had’iyesu.

Pills d’in da Laylerh’n zata sha kuwa acikin tafin hannunsa ya zuba su, tare da d’ago kansa ya kalleta, cikin murya mai tafiya da sigar lallab’awa yace.

“Zakisha magungunanki yanzu sai na k’ara miki chocolates ko�

Jin abunda ya fad’a d’inne kuma yasa ta k’wab’e fuska, tare da d’ago kanta ta kalleshi.
“No Yah M.Jay ni banason shan magani, saboda akwai d’aci sosai.� Tayi maganan cikin muryarta da yafi kama da zallan shagwab’a.

Kansa yad’an girgiza mata ahankali kuma, cikin nuna tsananin kulawarsa agareta yace.

“I know Ayshnoor amma please kisha kinji, banason kinajin pain, kuma I promise you idan kikasha zan baki duka ledan chocolates d’innan.�

Idanunta tad’an zaro waje, saboda jin ya ambaci bata duka ledan chocolates yasa ta d’anji sanyi acikin ranta, murmushin daya bayyana white teeth d’inta tayi, cikin gamsuwa da maganar tasa kuma tace.

“To zansha.�

Shid’inma murmushi yayi mata, tare da d’aukan bootle water ya mik’a mata, bayan yasa ta bud’e bakinta ya zuba mata pills d’in.
Duk da cewar kuma magungunan akwai d’aci sosai amma haka ta daure ta had’iyesu.

Tana gama had’iyewa kuwa ya mik’o mata duka ledan da chocolates d’in ke ciki, wanda ciki kuwa harda babban kwalban Nutella, bud’e ledan tayi tana k’arewa chocolates d’in nata kallo, saidai kuma wani Leda na daban da tagani acikin chocolates d’inne yasata d’agowa ta kalleshi, kaman zatace masa wani abu kuma sai ta fasa, kaitsaye ya ciro ledan tare da bud’e wa.

Abunda ta gani acikin ledanne kuma yasa ta sake kallonsa da sauri, had’e da ciro abun ta mik’a masa.

Kansa yad’an girgiza mata, tare da nuna ta da hannunsa, cikin sanyi yace.

“Naki ne ba nawa ba Ayshnoor.�

Idanunta tad’an zaro waje,tare kuma dasa hannu ta dafe chest d’inta, cikin d’an yanayin mamaki tace.

“iPhone 12promax wow!�
Lokaci d’aya kuma ta saki
Murmushi mai kama da dariya, tare da kamo hannunsa ahankali tace.

“Thanks so much Boo.�

Kansa ya d’an jinjina mata tare dasa hannunsa, ahankali ya shafi gefen fuskarta.
Asanyaye cikin kuma muryar dake bayyana kasalan dake tattare dashi yace.
“Ayshnoor please help me ki barni nad’anyi bacci ajikinki kinji, I’m tired duk jikina ciwo.�

Murmushi tayi tare da jinjina masa kai alaman. “To.� saboda duk hankalinta naga sabuwar wayarta, da ayanzun take k’ok’arin b’areta daga kwali, sosai taji dad’i musamman da colourn wayan ta kasance milk.

Maleek kuwa da gaba d’aya maganin da yasha, ya sauk’ar masa da kasala hannun Laylerh’n ya kama tare da mik’ar da ita tsaye, kana shima ya mik’e bayan ya matsar da kayan da sukayi breakfast d’in gefe.

Still kuma yana rik’e da hannunta haka suka nufi d’aki.

Suna shiga cikin d’akin kuwa ya rage duk wani haske dake ciki, tare kuma da k’ara gudun AC anutse ya jata zuwa kan gado.

Rigar dake jikinta ya zare, tare da hayewa saman gadon ya jawota jikinsa.

Atare suka sauk’e wani irin ajiyar zuciya mai k’arfi, saboda yanda d’umin jikin junansu ya ratsa su, musamman Maleek da d’umi da kuma taushin jikin Laylerh’n ya sashi jan dogon numfashi, tare da lumshe Idanunsa ya sake matseta k’am ajikinsa, Tabbas komai na Laylerh’n yayi masa hundred percent, kuma dama abune daya sani tuntuni cewa, Ayshnoor d’in nasa komai nata na dabanne.

Tafukan hannayensa ya kifa akan naked skin d’in bayanta, tare da soma shafa jikin nata ahankali.

Yanayin daya keyi mata d’inne kuma yasa ta lumshe Idanunta, had’e da sake shigewa cikin jikinsa, saidai kuma yanayin yanda breast d’inta ke gogan chest da kuma nipples d’insa ne yasa duk suka jisu acikin wani sabon yanayi na daban.

Almost 17minutes suka kwance ahaka, batare da d’ayansu yaji yanayin ya ishesa ba, saidai ma k’ara samun kansu acikin shauk’in juna da sukayi.
Yayinda daga b’angare guda kuwa tuni magungunan da Maleek d’in yasha sun soma aiki, ta hanyar sashi jin wani irin bacci, duk da cewar kuma magungunan daya shad’in pain relievers ne kawai amma suna saka bacci, shiyasa duk yaji jikinsa yayi weak sosai ga kuma idanunsa dake ta faman lumshewa.

Yana acikin wannan yanayin ne kuma wani bacci mai k’arfi ya d’aukesa.

D’umin numfashinsa da kuma sautin numfashin dake fita ahankali ne yasa Laylerh’n d’an d’ago kanta ta kalleshi, kyakkyawar fuskarsa dake cike da yalwataccen saje ta zubawa ido, bata ko k’yaftawa.

Tabbas zata iya rantsuwa akan cewar bata tab’a ganin wani wanda yakai Yah M.Jay d’in nata kyau ba, komai nasa dabanne, musamman zara zaran eye lashes da kuma eyebrow d’insa dake ashirye tsab tsab, ga kuma shining red lips d’insa da yake k’arawa fuskar tasa kyau.

Hannunta tasa ahankali ta shafi soft beard d’insa, da akullum shi yake d’auke mata hankali akan fuskarsa.

“Yah M.Jay mai kyau ne!!!�
Tafad’i hakan cikin yin k’asa da murya, tare kuma da sake mak’alewa acikin jikinsa.
Difference feeling takeji sosai akansa, saboda feeling d’insa da takeji ayanzun, ba shine takeji da ba, wannan feeling d’in na musamman ne, ba kuma akan kowa ake jin irinsa ba, sai dai akan mutum na musamman, Kamar dai shi da ayanzu ya zamo Mijinta.

K’warai takan ga kasantuwarta da Maleek d’in kamar amafarki, haka kuma zamantowanta mata agaresa tamkar al’amara, saidai kuma abune da yake abayyane cewa k’arfi da kuma ikon Ubangiji ya wuce komai, Allah Ne kad’ai keyin komai alokacin da yaso, ya hanaka alokacin da kake buk’ata, ya kuma baka alokacin da kafi tsananin buk’ata.

Idanunta da suka ciko da hawaye ta d’an lumshe, tare da sake hugging d’in Maleek d’in sosai, ahankali kuma ta dawo da kanta dake kan k’irjinsa, daidai saitin inda zuciyarsa take, yanayin yanda taji zuciyar tasa na bugawa anutse ne kuma yasa akasalance ta saki murmushi, kasancewar itama maganin da tasha d’in ya somayi mata aiki, dan tuni ta farajin yanayin bacci na satarta, da yake kuma dama akwai gajiya ajikin ta, shiyasa ko mintuna 10 ba arufa ba itama bacci ya d’auketa.

***

Aunty Aina’u dake zaune zugum akan sofa ne, tayi saurin d’ago da kanta ta kalli Momy wacce ita d’inma take zaune duk yanayinta babu dad’i.

Gyara zama Aunty Aina’u tayi tare kuma da sake kallon Momy’n, cikin kuma nuna sak’ewar guiwanta akan abun tace.

“Nikam gaskiya nagaji da way’annan abubuwan da suketa faruwa, yanzu fa almost 2years kenan da mukeson ganin bayan Captain Maleek da wannan shegiyar Laylerh’n amma abun ya kasa yiwuwa, duk wani plant d’in da muka tsara saiya warware, first kin tsara cewar Maleek zainemi Laylerh’n da aurenta amma bamu cimmawa hakan ba, har Najeeb ya saketa, fine naji plant dinki daya yayi aiki, wanda kikasa Najeeb yaje d’aya daga cikin gidajen Maleek ya ga sirrukan soyayyar Laylerh da yake ta b’oyewa tsawon shekaru, saboda haka nema yasa ya sauwak’e mata, bayan nan kuma kince zakisa Maleek ya maida Laylerh’n karuwarsa, amadadin hakan sai gashi ya maida ita matarsa ta sunnah, why duk way’annan abubuwan suke faruwa? hakan na nufin cewa kenan mu bamu da sa’a kwata kwata arayuwa, ga dukiya munaji muna gani amma mallakarta na nema ya zame mana bala’i, koda yake dama anfad’amin cewa har abada bazamu tab’a yin nasara akan LAYLERHMALEEK ba, amma nak’iji, To yanzu kam na tabbatar, kuma Insha Allah Zan cire hannuna akan wannan lamarin saboda yanzu duniya abun tsoroce, baka bi wani da sharri bama yaka k’are....�

Harara Mom da ta cika tayi fam ta watsa mata tare da cije labb’anta, Tabbas ayanzu ita kad’ai tasan tafasar da zuciyarta keyi akan al’amarin, saboda kwata kwata ma yanzu Abbou Jaheed ya daina sata acikin duk wani al’amura nasa, ya daina fad’a mata komai daya shafesa, domin hatta auren Laylerh da Maleek d’in sai ana Gobe za’a d’aura ta sani, k’warai taji babu dad’i akan hakan, saidai yanzu babban abundake damun zuciyarta shine burinta da har yau yak’i cika, abu mafi tashin hankali kuma da take tsoron faruwarsa, itace ranar da Abbou Jaheed zai san gaskiyar abunda taji ma tana k’ullawa y’ay’ansa.
Lallai tasan awannan ranar komai nata yazo k’arshe, saboda Abbou Jaheed bazae tab’a yarda yaci gaba da zama da ita ba, sannan kuma ba haihuwa tayi dashi ba balle tasa ka ran samun wani kaso daga cikin tarin dukiyarsa.

Tabbas ayanzu mafita d’ayane ke gareta, kodai tayi regreting abunda ta aikata ko kuma ta sanja taku, saidai abu mafi sauk’i agareta shine yin regreting, Domin da hakan zuciyarta tafi aminta, abune kuma da tasani cewa Allah Yana jin k’an bayinsa masu tuba, matuk’ar kuma ta nemi yafiyan Maleek da Laylerh to tasan Allah Ma zai yafe mata, lallai wannan shine abu mafi sauk’i agareta, saboda tamkar ceton kanta tayi, matuk’ar ta share duk wani mummunan tunani da kuma k’udirin dake cikin zuciyarta, sannan ta kuma gamsu da duk abunda Aunty Aina’u ta fad’a, gaba d’aya duniya ba komai bace saidai idan kaine ka d’auketa wata abar girmamawa, nan kuma gaba d’aya rayuwarka zata k’are awahala da yawan buruka wanda har abada bazasu tab’a cika ba.

Jikinta amatuk’ar sanyaye ta kalli Aunty Ayna’u, tare dasa hannu ta d’an matse hawayen dake cikin idanunta, saboda ayanzu ta sakejin gamsuwar cewar idan har ta cutar da Laylerh Maleek har abada Allah bazae tab’a barinta ba.

Hannun y’ar uwarta Aina’u ta kamo, cikin muryarta da tayi sanyi sosai tace.

“Insha Allah Aina’u bazan sake cutar da rayuwar Laylerh da Maleek ba, kamar yanda bazan sakeyi musu mummunan fata ba, zan kuma nemi yafiyarsu, amma kafunnan dole saina gyara tsakanina da Ubangijina da kuma Mijina, duk da cewar ya watsar dani ayanzu, amma bazan gajiya ba Insha Allah zanyi k’ok’ari wajen ganin na gyara kura kuran da nayi masa, tun ada bansan Meyasa na zamanto Mace mai tsananin son zuciya ba, idanuna sun rufe harta kai ga ina abu kaman ba Musulma ba, na manta cewar Allah Ne keyin yadda yaso, kana na manta cewar idan bai tsara abuba, har abada baya tab’a yiwuwa, lallai Tabbas zan gyara kuskurena, zanyi kokarin zama ta kwarai ko badan kowa ba, kodan saboda kaina da kuma karshena.�

Rungume Mom d’in Aunty Aina’u tayi saboda, ita dama tuntuni zuciyarta ta jima da karyewa, saboda wani wa’azi da taji, kuma Insha Allah zata nemo wa’azin ta sakawa y’ar uwarta, wanda tayi imani hakan zai sake sawa zuciyar Momyn tayi sanyi, kuma dama tuncan sunsani cewar, duk wani abu da zakayi wanda zai cutar da d’an uwanka ba abu bane maikyau, kuma sannan Allah baya yafe laifin dake tsakanin bawa da bawa, saidai har idan har wanda ka zalunta d’in ne ya yafe maka, To Allah Ma zai yafe maka, duk sun san hakan amma son zuciya da dukiya suka rufe musu ido, sam suka kasa nazartar abunda zai amfanesu.

*3:00pm*
Daidai ya soma bud’e idanunsa da suka d’an k’ank’ance saboda baccin daya share sama da awanni yanayi.

Jikinsa dake had’e dana Laylerh ya zare, tare da zuro k’afafunsa ya sauk’o daga kan gadon, agogon dake sak’ale ajikin bango ya kalla, ganin da yayi kuma lokaci ya d’anja har 3:2 pm ne yasashi mik’ewa tsaye, tare da d’an dafe kansa dake sarawa, sam baisan haka magungunan da suka sha d’in keda k’arfi sosai ba, saboda tun kwanciyarsu da k’yar ya iya tashi yayi sallah’n azahar, koda ya tashi Laylerh’n ma kukan shagwab’a ta saka masa, tare da cewa ita bacci bai isheta ba, haka dai ya lallab’ata tayi sallah’n, bayan ta idar da sallah’nne kuma suka sake komawa wani bacci’n, ba shi ne ya farka ba kuma sai yanzu da la’asar ta kusa.

Still kuma ya tashi ne bawai dan baccin ya ishesa ba, saidan yunwan dake damun cikinsa, wanda ya kuma san cewar bashi kad’ai ne yakejin yunwan ba harda Laylerh’nsa.

Hannunsa ya daura akan handle din kofar toilet d’in, tare kuma da tura k’ofar kana ya kutsa kansa ciki, kaitsaye gaban babban jakuzzie’n dake cikin toilet d’in ya nufa.

Adaddafe ya had’a musu duk wani abu dayasan zasu buk’ata, tare kuma da juye wani turaren wanka mai dadin kamshi acikin ruwan jakuzzie’n.

Bayan ya kammala komae ne kuma ya dawo cikin d’akin, tare da zare long jeans d’in dake jikinsa.

Direct gaban gadon ya nufa, tare da bud’e hannayensa duka biyu ya d’auki Laylerh’n da har yanzu ke bacci, kaitsaye toilet d’in ya nufa da ita.

Still kuma tana jikinsa, ya shiga cikin jakuzzie d’in, kwantar da ita yayi akan chest d’insa tare da lumshe idanunsa, yana mejin yanda ruwan ke ratsa duk jikinsu.

Haka kuma d’umin ruwan daya ratsa cikin jikinsu d’inne yasa ta bud’e idanunta akasalance, ta sauk’e ganinta akansa.

“Boo!!�
Tak’ira sunansa ashagwab’e tare da sake manna kanta da jikinsa.

“Ummm Shugarnoor!!!�
Ya amsa mata, da wata irin muryar da dadinta yasata d’an lumshe Idanunta, tare da d’an lasan lips d’in bakinta, cikin yanayin dake nuna jin dad’in mood d’innasu ne kuma ta juyo ta fuskancesa.

Idanunsa dake alumshe yad’an bud’e tare da yi mata wani irin kallo’n dayasa duk taji tsikar jikinta ya zuba, Daga cikin ruwan kuwa hannayensa yasa ahankali ya had’e waist d’insa da nata.
Atare suka fitar da wani sexual eraction sound.
Saboda wani irin abu da sukaji ya ratsa duk ilahirin jikinsu.

Harshensa yad’an zaro waje tare da bud’e bakinsa, ahankali yace.

*”I LOVE YOU Shugarnoor!!� *

harshenta ta d’aura akan Lips d’insa daya d’an bud’e su tare, da lumshe idanunta, saboda yanda kalmar tasa ta shigeta sosai, cikin kuma muryarta dake shaking tace.

*� I LOVE YOU too Boo!!!�*

*(Love you all guys)*

*10:20 pm*
4/12/21, 7:52 AM - Ummi Tandama: *82*

Lumsassun idanunsa ya bud’e saboda yanda yaji amo da kuma sautin muryar nata, ya sake hautsuna tunaninsa tare dajin wani irin kasala na musamman.

Tabbas yanayin maidad’ine agaresu, irin kuma dad’in da misalta shi keda wahala, saidai ga duk wanda ya kallesu, zai gane hakanne kawai ta yanda suke sake shigewa jikin juna.

Sake rungumeta yayi sosai tare da d’aukan soap ya soma goga musu ajikinsu.
Sannu ahankali cikin yanayi’n nutsuwa kuma, yayi musu wankan atare.
Tare da d’aura towel akan waist d’insa ita kuma ya saka mata bathrobe a jikinta, kama hannunta yayi har zuwa gaban sink suka d’auro alwala.
Still kuma yana rik’e da hannunta haka suka fito daga cikin toilet d’in.

Yanzun ma shi da kansa ya shafa mata body lotion a jikinta, kamar dai yanda yayi mata da safe.
Bayan ya gama shafa mata mai d’inne kuma da kansa ya bud’e wardrobe d’inta ya ciro mata wata net tight pencil gown marar nauyi, mik’a mata rigar yayi tare da yi mata alama akan tasa, kana ya juya shima ya soma kimtsa kansa.

Laylerh kuwa ganin ya juya mata bayane yasa ta shirya kanta atsanake tare da zura rigar daya bata d’in a jikinta, saidai kuma kasancewar rigar ya kamata sosai ne yasa duk wani shape d’in jikinta bayyana.

Dogon gashinta daya kwanta agadon bayanta ta d’aure, tare da neman waje ta zauna, Idanunta ta tsayar akan Maleek d’in daya gama shirya kansa cikin wasu had’add’un riga da wando.
Kamar yanda kuma komai yasa ajikinsa yana yi masa kyau, haka wannan kayan d’in ma sun amshi jikinsa sosai.

Juyowan da taga Yayine kuma yasata yin k’asa da kanta tare da kama y’an yatsun hannunta ta shiga murzawa.

“Zo muyi sallah.� Ya fad’a adaidai lokacin daya gama daidaita tsayuwarsa akan darduma carpet d’in dake shimfud’e agefen gadonsu.

Jin abunda ya fad’a d’inne kuma yasa ta mik’ewa tsaye, tare da k’arasawa gaban drawer ta d’auko hijab ta saka a jikinta.

K’arasowa wajen da Maleek d’in ke zaune tayi, tare da d’an tsayawa abayansa, daidai lokacin kuwa ya tada sallah.
Cikin nutsuwa ta bisa sukayi sallah’n, bayan sun idar da sallah’nne kuma ya kama hannunta suka fita falo.

Ganin kuma yanda take ta hamma ne yasashi gane cewar ita d’inma yunwa takeji sosai.
Akan d’aya daga cikin kujerun falon ya zaunar da ita, tare da k’arasawa gaban fridge ya d’auko musu, babban goran fresh yoghurt da kuma cups.

Bayan ya zuba musu yoghurt d’in acikin cup ne kuma, ya zauna akusa da ita, tare da soma bata yoghurt d’in abaki tana sha ahankali.
Saida kuma tasha fiye da rabin cup d’in kafun ta janye kanta ahankali, tare da karb’an cup d’in daga hannunsa, ahankali takai bakinsa kamar yanda yayi mata.

Duk da cewar kuma baiso shan yoghurt d’inba, amma ganin da yayi cewar Laylerh’nne zata basa yoghurt d’in da kanta, ya sashi bud’e bakinsa anutse ya soma sha.
Bai kuma janye kansa ba har saida duka yoghurt d’in dake cikin cup d’in ya k’are.

“Ka k’oshi?.�
Ta tayi masa tambayar alokacin da ta ke saka tissue ta goge masa bakinsa, da duk ya b’aci da yoghurt d’in.

“Eh, kefa?.� Ya dawo mata da tambayar.

“Nima.� Tafad’a asanyaye tare da ajiye cup d’in dake hannun nata, ta kwantar da kanta akan chest d’insa.

Idanunta da har yanzu ke cike da bacci ta d’an lumshe, saboda kwata kwata sam baccin da tayi d’in bai isheta ba, Dan ji yake kamar ma yanzune maganin da tasha zai soma aiki.

Shikuwa Maleek ganin yanda Laylerh’n ta lafe acikin jikinsa ne, yasashi soma shafa bayanta ahankali, saboda tun d’azu ya fahimci cewar bawai baccin da tayin ya isheta bane.

Aikuwa shafata daya soma yid’inne yasa ta sake narkewa ajikinsa, cikin k’ank’anin lokaci kuwa ta sake maida baccinta.

Shid’inma idanunsa ya d’an lumshe adaidai lokacin da yaji d’umin numfashinta na sauk’a acikin jikinsa.
Wanda kuma hakan alamace dake nuna masa cewar Laylerh’n tayi bacci.

“Ayshnoor!� Ya k’ira sunanta akasalance, jin bata amsa shi bane kuma yasa shi sake gyara mata kwanciyarta, tare da zaro waya da kuma earpiece d’insa dake cikin aljihun wandonsa, sak’ala earpiece d’in yayi acikin kunnensa, tare da kunna wak’ar Aligatie (Running on my mind) yana saurara.
Yanayin yanda yayi da idanun nasa ne kuma, yasa duk wanda ya gansa zaiyi tunanin cewar bacci shid’in ma yakeyi kamar dai yanda Laylerh’n keyi.

Ahankali Oum Ayush dake tsaye abakin k’ofar da zai sada ta da falon saman ta juyo ta kalli su Abbou Jaheed dake bayanta, wanda ayanzu sun share sama da 10minute suna tsaye abakin k’ofar suna ta doka sallama da knocking amma ba’a amsa musu ba.

“Anya suna nan kuwa?.�
Abbou Khareem ya tambaya, saboda yanda suka share tsawon mintuna suna knocking k’ofar batare da an bud’e musu ba.

“Sunanan Oum Ayush bud’e mana k’ofar falon mushiga.�

Abbou Jaheed ya fad’a atak’aice saboda ya gaji da tsayuwa awajen.

Hannu Oum Ayush tasa ta murd’a handle d’in k’ofar ahankali, tare da tura kanta cikin falon kana su Abbou Jaheed dake tsaye suka rufa mata baya.

Turus haka suka tsaya gaba d’ayansu, saboda tozali da idanuwansu sukayi musu da Maleek wanda ke zaune akan sofa ya lumshe idanunsa, Yayinda Laylerh’n ke jikinsa, da dukkan alama kuma dukansu bacci sukeyi.

Wani irin murmushi mai d’auke da tsananin farinciki ne ya bayyana akan fuskar kowannensu, musamman ma Abbou Jaheed daya kasa d’auke idanu akansu, saboda yanda yaga sunyi matuk’ar dacewa da juna, wanda ayanzu ya sake tabbatarwa kansa cewar Lallaine Maleek da Laylerh ya dace, haka itama Laylerh’n da Maleek ta dace.

Saidai kuma tuna irin tarin k’addarorin da suka fuskanta ne yasa shi jin idanunsa sun ciko da k’walla, Domin har yau ya kasa iya cire damuwar mummunan k’addarar da ta auku acikin rayuwar Maleek d’in, saidai kuma ya sani cewar Allah Baya tab’a d’aurawa bawansa abunda bazae iya ba, saboda haka yayi imani cewa komai yayi farko zaiyi k’arshe, idan kuwa k’addara ta dindince, to Allah Yakan sawa zuciyar bawa salama, tare kuma da k’arfin jure k’addarar da ta sameshi.

Oum Ayush da fuskarta ke cike da yalwataccen murmushi ne, ta k’arasa shigowa cikin falon, tare kuma dasa hannunta ahankali tad’an tab’a kafad’ar Maleek d’in, saboda duk atunaninsu bacci yakeyi.

Sab’anin gaskiyar lamarin daya kasance, idanunsa kawai ya lumshe amma bawai baccin gaske ya keyi ba, bai kuma ji knocking d’innasu bane saboda ya saka earpiece akunnensa, sannan ya kuma k’ure volume d’in wak’ar da yakeji.

Jin da yayi antab’a kafad’ansa ne kuma yasashi ware idanunsa ahankali, tare da sauk’esu akan Oum Ayush dake tsaye tana sakar musu murmushi.

Idanun nasa yad’an zaro waje tare da d’an saurin gyara zamansa.

“Oum Ayush.�
Yak’ira sunanta cikin yanayin dake bayyana mamakin ganinta.

Oum Ayush kuwa hararan wasa ta watsa masa, tare dasa hannu ta d’an buge kanshi, cikin kuma nuna masa tsananin kulawa tace.

“Wato dama ba bacci kakeyi ba, shine kanajin mu muna knocking nida su Abbou Jaheed amma kaki bud’ewa ko, to gamu mun shigo.�

Murmushin daya d’an bayyana hak’waransa yayi, tare da juyawa ya kalli su Abbou Khareem da suka k’araso cikin falon suka zauna.

Ahankali ya sakarwa Abboun nasa murmushi, tare da dawo da kallonsa ga Laylerh dake kwance ajikinsa tana bacci.

Batare kuma da yaji kunyan su Abbou Jaheed dake cikin falon ba, ya d’aura bakinsa adaidai saitin kunnenta, cikin muryarsa dake fita slowly yak’ira sunanta, tare kuma da hura mata sassanyar iskan dake bakinsa.

Ashagwab’e tad’an motsa tare da sanya hannayenta ta mak’alesa, Domin duk da kasancewar bacci takeyi amma hakan bai hanata jin sautin muryarsa acikin kunnuwanta ba.

“Ayshnoor!� Ya sake k’iran sunanta akaro na biyu, tare dasa hannunsa ya tallafo hab’arta cikin muryar dake bayyana shauk’inta akansa yace.

“Wakeup Ayshnoor nah Oum Ayush da Abbou Jaheed nefa suka zo.�

Tamkar wacce aka zabura haka ta bud’e idanunta, tare da d’an d’agowa ta kalleshi.
Da idanu yayi mata alama akan ta juya ta kalli su Abbou’n.

Da atunaninta wasa Yah M.Jay d’in keyi mata, amma kuma ganin da gaske yakeyi ne yasa tayi saurin juyowa, ai kuwa atake ta sauk’e Idanunta akan su Oum Ayush d’in, da sauri ta diro daga jikinsa, tare da fad’awa jikin Oum Ayush d’in ta rungumeta k’am, cikin muryar dake bayyana zallar shagwab’a tace.

“Nayi kewarku Oum Ayush nah.�

Murmushi Oum Ayush tayi tare dasa hannunta tashafa kan Laylerh’n, murya d’auke da farinciki tace.

“Nima nayi kewarki sosai Laylerh, amma kwana d’aya ne fa kawai tak, gashi kuma naga aure yayi dad’i har kinsaba da mijin naki.�

Saurin sanya tafukan hannayenta tayi ta rufe fuskarta, tare da zame jikinta daga na Oum Ayush d’in ta zauna akusa dasu Abbou Jaheed, tare kuma da gaishesu akunyace, saboda sosai maganan da Oum d’in ta fad’a yasata jin kunya.

Su Abbou Jaheed kuwa fuska asake duk suka amsa mata gaisuwan nata, tare da tambayarta jikinta, saboda kafun suzo Oum Ayush ta fad’a musu cewar batajin dadi.

Akunyace duk ta amsa musu gaisuwar tasu, tare da mik’ewa ta kawo musu drinks da ruwa.

Still dawowa tayi ta zauna akusa da Abbou’n, wanda suke d’an tab’a hira sama sama da Abbou Khareem.

Bayan kuma sun d’ansha drinks din da takawo musu d’inne, Abbou Khareem ya d’anyi musu Nasiha, irin wanda iyaye keyiwa yayansu idan sunyi aure.
tare da bawa Laylerh’n atm card d’in bank d’in daya sa mata sadakinta na aure aciki.

Kasancewar kuma yammaci ya danyi ne yasa basu wani jima ba sukayi musu sallama, har waje kuwa Laylerh da Maleek d’in suka rakosu, gefe Oum Ayush ta jawo Laylerh’n tare da tambayarta batun ciwon mararta, da sauki ta bata amsa, saboda tun adaren jiya ta nemi ciwon marar nata ta rasa.
wani abu me kaman chocolates Oum Ayush d’in ta bata, tare da tabbatar mata cewar kullum tasha guda d’aya, zai taimaka mata sosai.

Godiya tayiwa Oum Ayush d’in, bayan kuma sun tafi ne Maleek ya kama hannunta suka koma cikin gida.

Suna shiga cikin falon nasu kuwa wayar Maleek din ta soma ringing, ganin sunan Fou’ad akan screen din wayarne kuma yasashi saurin picking call din tare da kara wayar akan kunnensa.

Daga b’angaren Fou’ad kuwa jin Maleek ya daga wayarne yasashi d’an gyara zamansa tare da shafa sumar kansa, cikin yanayin dake bayyana tsananin farincikinsa yace.

“Kagama yangan angwancinka nima soon zan angwance malam, saboda na samu mata ajiya kawai har mun daidaita tsakaninmu Insha Allah zamuyi aure nan bada jimawa ba.�

Murmushi Maleek d’in yayi, tare da d’an lumshe idanunsa ahankali yace.

“Naji To Wacece matar?�

“Aleeyah frnd din Laylerh mana, gaskiya babe din ta hadu, yanzu ma maganan da nake maka fa harna fadawa Abbana, yace nanda 3daya zaije gidansu, kai intak’aice maka dai Insha Allah nanda 2weeks Ina da mata, nima nagaji da zama haka�

Murmushi Maleek d’in yayi, batare kuma da yace komai ba ya katse kiran, saboda yasan halin Fou’ad matuk’ar ya biye masa to zai ta damunsa da surutu ne, shikuwa ayanzun akwai abunda yakeson aiwatarwa.

Kallon Laylerh dake gefensa yayi, tare da manna mata kiss a forehead dinta, asanyaye yace.

“Bari naje wani waje Ina dawowa yanzu.�

Kai ta jinjina masa alaman to, shikuwa Cikin hanzari ya juya ya fita, ganin kuma da tayi cewar zama waje Dayan zai takurata ne yasa ta jawo sabuwar wayarta tare da soma setting d’in abubuwa Domin ayau takeson fara amfani da ita.

Ab’angaren Maleek kuwa yana fita daga cikin gidan, kai tsaye hotel ya nufa, saboda acanne yake da yakinin samun mutumin da yake nema.

*(Yau nayi yping mai yawa amma ya goge😭 yanzu kuma wallahi bacci nakeji)*

*10:06 pm*
4/13/21, 11:27 AM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting by*
fatymasardauna

*Note editing*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.