Best Hausa Novels

Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: LAYLERH MALEEK.txt

Chapter 8 of 65

*Chapter 15*

Gaba ɗaya hankalinta akan M.Jay ɗin yake, wanda hakanne kuma yasa ko kaɗan bataji motsin buɗe ƙofar ɗakin nasa da akayi ba.
Kyawawan idanunta dake cike da ruwan hawaye ta zuba masa, hakanan taji duk gaba É—aya jikinta yayi sanyi, yayinda lokaci É—aya taji wani irin matsanancin tausayinsa ya rufe mata zucia.
Idanunta taÉ—an lumshe, cikin wata irin sassanyar murya me É—auke da sanyin amo tace.
"Please Yah M.Jay katashi, ka buɗe idanunka kaga yanda jini ya ɓata maka bedsheet, please dan Allah ka bude idanunka kaji!."

Kamar amafarki, kana kuma cikin nannauyan yanayin daya samu kansa aciki, yaji sauti da kuma amon muryarta na ratsa kunnuwansa, hakan yasa duk da bai gama sanin awace duniya yake ba, ahankali ya É—an soma motsa kyawawan sexy eyes É—insa wanda suka masa nauyi, cikin dauriya haÉ—e da wani fitinannen baccin da bai gama sake shi ba, yaÉ—an soma buÉ—e kyawawan idanun nasa kaÉ—an kaÉ—an, anan kan kyakkyawar fuskarta ya tsaida idanun nasa, yayinda ahankali yake É—an buÉ—ewa da kuma lumshe su, duk kuwa da cewar baya iya ganin fuskar nata da kyau, amma hakan bai hanasa shaida cewar itace agabansa ba.

Mayun idanunta masu ɗauke da ruwan hawaye ta zuba mai bata ko ƙyaftawa, ganin da tayi ya ɗan buɗe idanunsa ne, ya sata waro nata idanun.
Take taji wani irin sanyi na ratsa duk ilahirin jikinta, wanda hakanne ya tilasta mata ƙiran sunansa.
"Yah M.Jay!."
Ta faÉ—a cikin wata irin unique voice É—inta me daÉ—in sauraro.
Wanda sanadin zaƙi da kuma daɗinta yasa idanunsa dake amarairaice ƙara buɗewa, sanadin hakanne kuma yasa shi soma ganin fuskarta da kyau.

Da idanunsa masu É—auke da zallan yanayin bacci, wato really sexy eyes yake kallonta, yayinda yake mata wani kallo, irin kallon nan mai kama dana mayen sha'awa, tare kuma da kashe jiki.
Akaron farko kenan itama da ta kasa ɗauke idanunta akansa, duk da kuwa da irin kallon da yake mata, wanda yasa takejin kaman an jona mata shocking ajikinta, lokaci ɗaya tsikar jikinta suka mimmiƙe, wani irin yaaaarr yaarrr haka takeji ajikinta, yayinda takejin wani abu na musamman na ratsa cikin ƙashi da ɓargonta.
Bata taɓa ba, haka kuma bata saba ba, bakuma tajin zata iya jurewa kallon da yake mata, saboda hakan baƙon yanayi ne awajenta, wanda kuma sanadinsa ya sa takejin kaman zata shiɗe, kyawawan idanunta dake cike da ƙwalla ta lumshe.
hakanne kuma ya bawa hawayen dake cikin idanunta daman sauƙawo kan fuskarta, batare kuma da ta shiryawa hakan ba.

Ganin hawaye na sauƙa akan fuskarta ne yasa akasalance ya lumshe idanunsa, ahankali yakejin wani sassanyan yanayi na shiga jikinsa.
akaron farko kenan kusan sama da 7 years da zuciyarsa ta fara kwaɗaita masa riƙe hannunta, wanda kuma tunanin nasa yayi daidai da abun da ke cikin zuciyarsa.
Ahankali cikin yanayin sanyi ya É—aura hannunsa akan nata hannun da ta É—aura bisa saman kyakkyawar fuskarsa.
HaÉ—ewar hannun nasu waje É—aya kuwa, shi ya sanya shi lumshe idanunsa tare da jan wani dogon numfashi.
Itama Laylerh jin sauƙan hannunsa akan nata ne yasa ta lumshe idanunta, wanda eye lashes ɗin samansu ke ɗauke da danshin hawaye.
Take kuwa lokaci É—aya wani irin zazzafan yanayi ya soma fusgarta, tabbas shi É—in kawai takeji yana yawo acikin jikinta.

Haƙiƙa hakan ya zame musu yanayi na musamman, kuma yanayin farko da ya fi komai daɗi acikin yanayin rayuwarsu.
Kamar kuma yanda sassanyar iska me dadi ke hura duk wani ƙofar gashi na jikinsa, haka itama ya kasance takeji acikin jikinta, sanadin hakan yasa yanayinta yaso fin nasa yanayin ƙarfi, dan wani irin diffrent feeling takeji akansa, wanda cikin mintuna kaɗan yake neman fitar da ita daga duniyar tunaninta.

*LAYLERH!!.*

Abbou Jaheed da kusan mintunansa 10 da shigowarsa cikin ɗakin ya ƙira sunanta da wata irin kakkausar murya, kasancewar tun shigowarsa ya zubawa gaba ɗayansu idanu yana kallonsu.

Tamkar sauƙan guduma atsakar kanta, haka taji sautin muryar Abbou Acikin kunnenta, lokaci ɗaya gabanta yayi wani irin faɗuwa, yayinda ƙirjinta ya soma dukan uku uku, cikin hanzari haɗi da zallan tsoro ta ture kan M.jay ɗin wanda ta ɗaura bisa kan cinyarta, ahankali taɗan soma ja da baya, tare da zubawa Abbou Jaheed dake tsaye abakin ƙofar shigowa ɗakin idanunta wanda suka firfito waje saboda tsoro.

ShiÉ—inma Abbou Jaheed É—in kallonta yake, saidai wani abun mamaki babu alaman wasa ko murmushi akan fuskarsa.
Ganin hakan kuwa shiya ƙara tsorata zuciyarta, cikin hanzari ta diro daga kan gadon tare dayin ƙasa da kanta, dan batasan me zata cewa Abbou Jaheed ɗin ba.
Lura da hakan da Abbou Jaheed din yayi ne, yasa shi sake haÉ—e fuska cikin muryarsa da bata É—auke da alaman wasa yace.
"Da nace ki ƙirashi, hakan na nufin kizo ki zauna ne?."

Cikin tsoro ta soma girgiza kanta, take duk jikinta ya É—au rawa, cikin sanyin murya tace.
" Kayi haƙuri Abbou ƙin tashi yayi shine na tashe shi, kuma ma jini na gani ajikinsa shi yasa na hau, amma bazan sake ba......."

"Ya isa!." Abbou ya faÉ—i haka ta hanyar katseta daga maganan nata, fuskarsa kwata kwata babu alaman walwala.
"Zoki wuce!." Ya faɗi hakan cikin kaurara murya tare dayi mata nuni da ƙofar fita daga cikin ɗakin.

Ganin yanda Abbou ya tsume ne yasa taji gabanta ya faÉ—i, saboda akaron farko kenan da taga Abbou Jaheed É—in yayi mata magana cikin tsawa, domin kuwa tasan hakan ba al'adarsa bace, ji tayi gaba É—aya jikinta yayi sanyi, hakanne yasa hawaye taruwa acikin idanunta, kasancewar dama ita gwanace wajen saurin kuka.

Cikin hanzari tazo ta raɓa ta gefen Abbou Jaheed din ta wuce, duk kuwa da yanda zuciyarta ke ƙara kwaɗaita mata son sake kallon M.jay ɗin, amma tsoro da fargaba sun hanata haka ta fice daga ɗakin.

Jin alaman fitanta daga cikin É—akinne yasa Maleek dake kwance maida idanunsa ya lumshe.

*"Maleek"*
Abbou Jaheed dake tsaye ya ƙira sunansa.
Batare da ya buÉ—e idanu ko motsa jikinsa ba yace. "Na'am!!."

Idanu Abbou Jaheed ya zuba masa, tare da ƙarasowa cikin ɗakin, kallon tattoo ɗin dake jikin Maleek ɗin yayi, tare da girgiza kansa, kana ya maida dubansa zuwa ga bedsheet ɗin da Maleek ɗin ke kwance akai, wanda ke ɗauke da ɗan ɗigo ɗigon jini, cikin yanayin dake ɗauke da ɗan mamaki yace.
"Jinin meye wannan ajikin bedsheet É—inka?"
Jin tambayan da Abbou Jaheed ɗin yayi masane ya sashi ɗan buɗe idanunsa, tare da kallon gefensa inda ɗigo ɗigon jini ya ɓata, hannunsa yakai kan cikinsa tare da ɗan shafa saman ciwonsa, wanda yakejin yana ɗanyi masa zafi kaɗan kaɗan, koda ya ɗago hannun nasa jini ya gani anan jikin tafin hannunsa, wanda hakan ke nuna masa cewa jinin daga ciwonsa yake fitowa, ahankali ya maida idanunsa ya rufe, saboda baisan dame zai amsa tambayar da Abbou'n yayi masa ba.
Ganin yayi shiru ne yasa Abbou Jaheed zuba masa ido, aransa yana me mamakin hali irin nasa, sam baidamu da kansa ba bare kuma lafiyar jikinsa, wata irin rayuwa yake ta ko oho, banda taurin zuciya da miskilancin tsiya ba abun da ya iya, kullum sai yayi ta abu kaman Jarumi, bayan kuma azahirance ba hakan yake ba.
Sake dubansa Abbou Jaheed ɗin yayi da kyau, domin hakanan jikinsa ya basa cewa kamar Maleek ɗin ba adaidai yake ba, kasancewar bai taɓa ganinsa acikin irin wannan yanayin ba.
Take wani sabon tunani yaso É—arsuwa acikin ran Abbou Jaheed É—in, amma sanin da yayi cewa É—an nasa baya shaye shaye yasa shi kawar da wannan tunanin acikin ransa, domin ayanzu sam bayason abun da zai kawowa zuciyarsa, da tunaninsa kokwanto.
ÆŠan gÆ´ara tsayuwarsa yayi, cikin kulawa ya dubi Maleek din agajarce yace.
"Kasameni a falo by 8:00 am."

Kansa kawai ya iya jinjinawa Abbou'n, saboda har zuwa yanzu bai fara jin kansa adaidai ba, duk da cewar baya cikin maye, amma haka yakejin kansa yayi masa nauyi.

Juyawa Abbou Jaheed yayi ya fice daga cikin É—akin batare da ya sake cewa Maleek din komae ba.

Jin motsin fitan Abbou Jaheed daga ɗakin ne ya sashi buɗe idanunsa, ahankali ya ɗan ɗago da kansa tare da tashi zaune ya jingina bayansa da jikin saman gadon da yake kai, amatuƙar kasalance yakai dubansa ga haɗaɗɗen agogon dake saƙale jikin bangon ɗakin.
7:40 am daidai da ya gani ne yasashi sanya hannu ya ɗan murza idanunsa, dan yana ganin kaman gizo ne idanunsa keyi masa, sake duban agogon yayi inda yaga 7:41 am, wato har minti ɗaya ya ƙaru akan ganinsa na ɗazu.
Cikin hanzari ya tashi daga kwancen da yake, duk da cewar ba shi da wani kuzari ajikinsa kaitsaye haka ya nufi toilet, zuciyarsa cike da takaici, domin kuwa ko sallan asuba baiyi ba, abun da tunda yake a iyaka tsawon rayuwarsa bai taɓa bari yayi missing ba, matuƙar kuwa da lafiyansa. amma wani abun takaici sanadin cocaine ɗin daya shaƙa sai gashi yau har 7:41 am bai yi sallan asuba ba, treating ɗin ciwonsa yayi tare da ɗauro alwala, yazo ya gabatar da sallah.

Aɓangaren Laylerh kuwa tana fita daga part ɗin M.jay ɗin kaitsaye compound ɗin gidan ta nufa, ba kaɗan ba kuwa tsawan da Abbou Jaheed ɗin ya yi mata ya tsorata ta, kasancewar tunda take da Abboun bai taɓa yi mata magana cikin irin wannan sigar ba, ako yaushe yana yi mata magana ne cikin yanayin lallaɓawa da kuma tausayi.
Da tunani kala kala acikin ranta haka ta ƙarasa wajen da driver ke tsaye yana jiranta, koda drivern ya ganta buɗe mata murfin motar yayi ta shiga, cikin sauri shima yashiga tare dayiwa motar key, maigadi ne ya wangale musu makeken gate ɗin gidan, wanda hakan yabawa drivern daman cilla motar kan titi.
Jin motar tasu ta hau titi ne yasata kwantar da bayanta ajikin kujeran da take kai tare da lumshe idanunta, har zuwa yanzu zuciyarta bata daina bugawa ba, kyakkyawar fuskarsa da kuma haɗaɗɗun idanunsa ne suka soma yi mata yawo acikin idanunta, wanda hakan yasa lokaci ɗaya tsikar jikinta suka mimmiƙe.
Tabbas ganinsa da tayi yau ɗin yasa ta samu kanta cikin wani irin sabon yanayi me wuyar fassaruwa, yanayin daya zamar mata me daɗi kuma na musamman, tunawa da yanda sexy eyes ɗinsa keyi mata wani irin kallo ne yasa ta rungume hannayenta akan ƙirjinta, tare da sakin wani lallausan murmushi, sosai yanayin ya mata daɗi, dan taji moment ɗin har acikin jikinta, lallai ta sake yardarwa kanta cewa Yah M.Jay ɗin na musamman ne, haka kuma komai nasa me kyau ne, tuna yanayin yanda ya ɗaura hannunsa akan nata ne yasa ta saurin ware idanunta, saboda wani irin sabon shock da taji ya shigeta.
Daidai lokacin kuwa suka kawo ƙofar shiga makarantar tasu.
Anutse ta buÉ—e murfin motar ta fito, kaitsaye da É—an sassarfa ta nufi hanyar shiga makarantar, dan kuwa baifi saura 5 minute ba ne ya rage arufe gate É—in shiga makarantar nasu gaba É—aya.
Koda ta shiga cikin makarantar kai tsaye class dinsu ta nufa.
Tana ƙarasawa cikin ajin Teemah da tun ɗazu take jiran zuwanta, tana hangota ta saki murmushi tare da ƙarasowa da gudu ta faɗa jikinta.

Idanunta taɗan lumshe tare da ɗan jan jikinta baya, cikin salo da kuma yanayinta na shagwaɓan da ya zame mata jiki tace.
"Auchh Teemah zaki karyani."

Murmushi Teemah tayi, tare da É—anyin fari da idanunta, cikin son bayyana abun dake cikin ranta tace.
"Dole ae tunda anyimin Surprise!."

Da É—an mamaki Laylerh ta kalleta, cikin rashin fahimta tace
"Surprise kuma?."
"Yeah." Teemah tafaɗa tana me kamo hannun Laylerh'n suka ƙaraso kan parmanent sit ɗinsu.
Bayan sun zauna ne cike da zumuɗi Teemah ta zuge zip ɗin jakarta tare da sa hannu ta ciro wata waya ƙiran iphone 8+ ta miƙawa Laylerh.
Idanu Laylerh taÉ—an zaro cikin mamaki tace.
"What?."
Murmushi Teemah tayi, cike da murna tace. "Ya Mu'azamz ne ya sayamin, jiya kusan kwana nayi banyi bacci ba saboda murna." Murmushi Laylerh tayi tare da É—an rungume Teemah'n, cikin son tayata farinciki tace.
"Congrat my headache saura kuma ki bari ya hanaki karatu."
Kai Teemah ta girgiza tare da cewa.
"Bazan taɓa bari hakan ya kasance ba kuwa Insha Allah." Murmushi sukayi su dukansu.
Shigowan malami cikin ajin nasu ne kuma yayi sanadiyar katsewar hiran nasu, inda suka maida gaba É—aya hankalinsu kan darasin da ake koya musu.

M.Jay
koda ya idar da sallah ganin bashi da wadataccen lokaci ne yasa anan cikin ɗaki ya gudanar da gym ɗinsa, wanda yin hakan kuma ya ɗaukesa kusan sama da 1hour, lokaci ɗaya duk gaba ɗaya jikinsa ya jiƙe da gumi, duk da kasancewar sanyin A/C' na busawa acikin ɗakin kuwa, hakan bai hanasa fitar da gumi ba, kasancewar ya motsa jikinsa sosai, lokaci ɗaya yaji duk wani kasala da kuma bad mood ɗin da yakejin kansa aciki sun kau.

Track suit É—in dake jikinsa ya cire tare da É—aura towel akan waist dinsa, kaitsaye ya wuce toilet dan yanaso yayi wanka. Bai wani jim acikin toilet É—in ba ya fito, bayan ya sake treating ciwonsa inda ya naÉ—e wajen da sabon bandage.
koda ya fito kuwa bai wani ɓata lokaci wajen kimtsa kansa ba, hakanan yau ɗin yaji yana buƙatar saka kayan da suka kasance na al'adar hausawa wato riga da wandon jumper, domin kuwa yana dasu saidai bai fiye sawa bane kawae.
Kasancewar zaman da yayi a USA gaba É—aya kullum cikin uniform yake, hakan yasa bai fiye saka wasu tarkacen kayayyaki ba.
Ƙarasawa gaban drawer'n sa yayi tare da buɗe ɓangaren da yake ajiye manyan kayansa, wani haɗaɗɗen yadin getzner ya ciro wanda aka masa ɗinkin half jumper da kuma wandon pencil.
koda yasa kayan kuwa sosai suka zauna ajikinsa, yayinda suka sake bayyana zallan kyau da kuma kwarjininsa.
wasu black toms ya saka aƙafansa, tare da feshe jikinsa da wani fitinannen turaren Dolce & Gabbana me daɗin ƙamshi,
Koda ya kalli madubi, kallo ɗaya yayiwa kansa ya ɗauke kai, domin ya riga daya sani tunda daɗewa cewa shi kyakkyawane, haka zalika komai nasa me kyau ne, don haka baya buƙatar duba madubi.
Sanin cewa Abbou Jaheed na jiransa a falo ne yasa bai wani tsaya bata lokaci ba kaitsaye ya nufi falon. Koda ya ƙarasa cikin falon kuwa zaune suke dukansu ciki kuwa harda Alhaji Ahmad Rufae da kuma Najeeb, sai Momy dake zaune agefensu. Ganinsu a zazzaune ne yasashi ƙarasowa cikin falon, cikin girmamawa ya gaishe da Alhaji Ahmad Rufae, fuska asake Alhaji Ahmad din ya amsa masa. Ɗan haɗe fuskarsa yayi, tare da maida asalin mood dinsa na Soldier ya miƙawa Najeeb dake zaune hannu sukayi musabaha, yayinda zuciyar ko wannensu da abun da take saƙawa.

kan kujeran dake facing na Abbou Jaheed ya zauna, batare daya kalli Momy ba yace mata.
"Good Morning!."

Momy da tasan cewa da ita yake ne yasa ta washe baki, fuska asake ta amsa masa gaisuwar tasa, dan har acikin ranta so take tasamu karɓuwa awajensa, domin ta hakanne kaɗai zata iya cimma buri da kuma ƙudurin dake ranta, wanda alƙawari ne ta ɗaukar wa kanta, cewar dashi zata yi amfani wajen ruguza rayuwar Laylerh.

Abbou Jaheed wanda dama tuntuni zuwan Maleek É—in yake jira ne ya É—ago kansa, tare da É—anyin gyaran murya, cikin yanayin dattako irin nasa yace.
"Alhamdulillah ban taraku anan dan na sanar daku wani abu na daban ba, saidan sanin cewa dukanku kuna da haƙƙi akan maganar da zanyi." Ɗan numfasawa Abbou Jaheed ɗin yayi tare dayin gyaran murya, kana yace.
"Na tsaida lokacin auren Laylerh da Najeeb nan da makonni uku masu zuwa. ina fatan kuma dukanku zakuyi farinciki da hakan."

Tamkar Sukan kifiya akan ƙahon zuciyarsa haka yaji sauƙan kalaman Abbou Jaheed ɗin acikin kunnuwansa.
Idanunsa ya rumtse domin ko kaÉ—an bayason sake jin wani batu daya danganci auren Laylerh'n, wanda yayi imani hakan zai iya fasa masa zuciya.

(Wayyo Bacci😪😓😭😴)

*3/December/2020. time 9:50 pm*
1/19/21, 8:12 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*(This book is mainly for those that pay, if you know you did'nt pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay-0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank. Whatsapp Number 07017879464)*

                   *Chapter 16*

Zaune suke ita da Teemah aƙasan wata bishiyar flower, wanda kuma da yawan lokuta sukan zauna awajen ne,  idan suka fito break.
Sassanyar iskan bishiyan dake hura duk ilahirin jikinta ne yasa ta lumshe idanunta,  tare da sakin ajiyar zuciya me ƙarfi, wani irin daddaɗan yanayi ta samun kanta aciki, wanda kuma hakanne ya taimaka wajen gusar mata da kaso 40 acikin 100 na damuwar dake kwance acikin ranta.  
kallonta ta mayar ga Teemah dake ta  aikin latsa wayarta, time to time take sakin murmushi, wanda hakan ke bayyana cewar tana jin dadin abun da takeyi acikin wayar tata, zubawa Teemah'n idanu tayi, yayinda lokaci ɗaya kuma maganar auren ta da Najeeb ya dawo cikin tunaninta, wanda hakan yasa ta lumshe kyawawan idanunta, take kuwa wani irin faɗuwar gaba da tsoro suka sauƙar mata, in one second duk wani yanayin nishaɗin da takejin kanta aciki ya kau,  wanda hakan yasa  damuwa ta maye gurbin farincikin dake kan fuskarta.       
Teemah kuwa da take buga game din zombie high way awayanta  ba tare da ta ɗago kai ta kalli Laylerh'n  ba tace.   "Babe  kinsan yanda game ɗinnan keda daɗi kuwa?."        
Laylerh da tun ɗazu idanunta ke alumshe, yayinda ta faɗa wata duniya ta daban, hakan yasa sam bata ji abun da Teemah'n ta faɗa ba, hasalima gaba ɗaya hankali da nutsuwarta ba'ajikinta suke ba.   
Jin shiru Laylerh'n bata amsa  bane yasa  Teemah ta cire kai daga kallon  wayarta ta, tare da ɗagowa ta kai dubanta  zuwa ga inda Laylerh'n ke zaune.         
Ganin Laylerh'n tayi shiru ne yasa ta ƙira sunanta, cikin yanayin mamakin sauyawan mood ɗinta lokaci ɗaya.      

Laylerh kuwa kasancewar har  zuwa yanzu bata cikin nutsuwarta, hakan yasa still bataji ƙiran sunan ta da Teemah'n tayi ba.         
Idanu Teemah ta zuba mata, domin bata taɓa ganin Laylerh'n acikin matsananciyar damuwa irin wannan ba, gane cewa da gaske Laylerh'n ta tafi duniyar tunani ne yasa Teemah ɗan buga kafaɗarta, cikin kulawa tace.  "Wai meye haka Laylerh?.". 

Jin Teemah ta taɓata ne yasa ta buɗe idanunta wanda sukayi jajur dasu.               

"Tunanin me kikeyi?."
Teemah ta tambaya tana me tsareta da idanu.         
Ƙasa tayi da kanta haɗe da fesar da wani irin numfashi me zafi, tabbas tasan cewa agaba ɗaya rayuwarta bata da wata ƙawa ko ƴar uwa sama da Teemah, duk da kasancewar tasan ƙwaƙwalwa da kaifin hankalinsu iri ɗaya ne da na Teemah'n, amma tanaji ajikinta cewa Teemah zata iya warware mata wani  abu daga cikin matsalarta, hakanne kuwa yasa taji zuciyarta ta aminta da ta faɗawa Teemah'n damuwarta.         
Ganin yanda idanun Laylerh'n suka ciko da ƙwalla ne yasa Teemah cewa. 
"Ganin hawaye a idanunki, da kuma shirun da kikayi, hakan alamace dake nuna cewar lallai akwai damuwa atattare dake,  meyake damunki Laylerh,  ko Abbou Jaheed ne zai koma Polland?."         

Idanunta ta lumshe tare da girgida kai alaman "Aa."     

Ajiyar zuciya Teemah ta sauƙe, cikin halin nuna kulawa tace. 
"Okay tell me whats wrong? ba kuma naso ki ɓoyemin komai dan Allah!."     
Jin abun da Teemah'n  ta faɗane yasa idanunta sake cikowa da ƙwalla, kanta dake ƙasa ta ɗago tare da duban Teemah wanda ta tsura mata ido.    Ganin ruwan hawayen dake cikin  idanun Laylerh'n sun ƙaru ne, yasa Teemah zaro idanu, cikin yanayin mamaki tace.
"Laylerh kuka kuma? Please  ki faɗamin meke damunki da har ya saki kuka!."           
Ayanda takejin zuciyarta, yasa  batajin zata iya ɓoyewa Teemah komai,  kuma ya zama dole ta faɗawa Teemah'n  koda hakan zaisa taji sanyi acikin ranta, ƙoƙarin shanye hawayen nata tayi, cikin sanyi da kuma muryar dake bayyana rauninta tace. 
"Teemah Aure Abbou Jaheed zai yimin, zai aurar dani ga wani daban, wanda bansan cewa yana sona ko baya sona ba, tsoro nakeji Teemah bansan ya ake zaman aure ba, bansan ta ina zan fara ba, zuciya ta da ƙirjina bugawa suke, inajin gaba ɗaya duniyar bata min daɗi, haka nakejin tamkar zan rasa wani abu ne da yafi komai mahimmanci arayuwata!." 
Ta faɗi maganar hawayen dake cikin idanunta suna me sauƙa akan fuskarta.  
Idanu Teemah ta ɗan zaro cikin yanayin mamaki tace.  
"Aure kuma Laylerh? wai kina nufin Abbou Jaheed da kansa yace zai aurar dake? waye zai aura miki to?."    Teemah tayi mata duka waƴannan tambayoyin alokaci ɗaya, domin ba kaɗan ba maganar auren Laylerh'n  ya shigeta.         
Guntun hawayen da suka ɗan gangaro daga cikin idanunta ta share, araunane tace. 
"Ki taɓa saitin zuciyata kiji Teemah, gaba ɗaya fargaba ne ya cika cikinta,  sannan inajin wani abu me zafi na sukana."     
Tsagaitawa da maganan tayi tare da kamo hannun Teemah ta ɗaura adaidai saitin zuciyarta, cikin wani irin yanayi tace. 
"Tabbas inada buƙatar sanin haƙiƙanin abun da nakeji acikin zuciyata Teemah, ki taɓa zuciyata da kyau kiji, sam bata da nutsuwa, haka zalika tunani da komai na akansa ne, yanzu na, anjima na, da ma ko yaushe na,  inajinsa yana gudana ajikina tamkar yanda  jini ke gudana, haƙiƙa nayi imani cewa matuƙar na cigaba da rayuwa ahaka wannan yanayin zai illatamin zuciya da kuma gangar jiki, please Teemah ki faɗamin  me yasa nakejinsa ako yaushe? ko acikin baccina shi nake gani, ko wani bugun zuciyata da tunani haɗe da komai nasa yake tafiya, shin me hakan yake nufi ki faɗamin dan Allah tun kafun narasa hankali na!."         
Idanu Teemah ta zuba mata akaron farko kenan da taji ajikinta cewa, ƙawartata  ta samu zaucewar ƙwaƙwalwa. 
Riƙo hannun Laylerh'n tayi da kyau cikin rashin fahimtar inda kalaman Laylerh'n suka dosa tace.   "Ki dawo cikin hayyacinki Laylerh, kada ki bari ki zautar da kanki akan abun da gaskiyarsa yake abayyane, bansan akan wa kike magana ba, ki faiyyace min komai ta yanda zan fahimta, sannan kidaina waƴannan kalaman masu wuyar fahimta please!."             
Jin abun da Teemah'n ta faɗa yasa ta lumshe idanunta, tare da ɗan soma girgiza kai, akaron farko kenan da ta riga ta fahimci cewa Teemah, bazata iya warware mata tsalarta ba, haka zalika kuma ba zata taɓa fahimtar abun dake cikin rai da zuciyarta ba, "Why ƙaddara zata zo mata da nauyi me girma irin haka?, nauyin da har takai ga tanajinsa kaman zai fasa mata ƙwaƙwalwa."
Lallai bata da mafita wanda kuma hakan yasa taji duk gaba ɗaya zaman makarantar ya isheta,  miƙewa tsaye tayi, tare da sa hannu ta dafe kanta da lokaci ɗaya taji yana sara mata. 
Kallonta Teemah tayi tare da cewa.  "Ina kuma zakije?."   
"Class!." ta bata amsa asanyaye batare kuma da ta jirayi komai ba ta fara tafiya.  
ÆŠan jim Teemah tayi na wasu lokuta tare da binta da idanu, itakam sam bata fahimci komai akan lamarin Laylerh'n ba, hasali ma gani tayi kaman Aljanu ne ke damunta.
Ganin cewar da gaske tafiya class Laylerh'n zatayi ta barta yasa cikin hanzari ta rufa mata baya.                    

MALEEK.  
Duk yanda yaso daidaita nutsuwarsa ya kasa, baisan meyasa  jin duk wata magana da ta shafi auren Laylerh'n ke matuƙar haukata masa tunani ba,   idanunsa da sukayi ja ya lumshe tare da sa tafukan hannunsa ya rufe kyakkyawar fuskarsa,  lokaci ɗaya duk wasu maganganun da Abbou Jaheed  da kuma Alhaji Ahmad ɗin keyi, suka daina shiga cikin kunnuwansa, domin gaba ɗaya zuciyarsa tatafi izuwa wani waje na daban.             
Abbou Jaheed wanda suka gama tattaunawa da Alhaji Ahmad Rufae, akan maganar auren Laylerh'n ne ya ɗago da kansa, tare da dawo da kallonsa ga Maleek wanda har yanzu bai buɗe fuskarsa dake arufe da tafukan hannunsa ba.          
"Maleek!." Abbou Jaheed ya ƙira sunansa cikin nutsuwa.              
Jin sautin muryar Abbou Jaheed ɗin acikin kunnensa ne ya sashi ɗan janye tafin hannunsa daga kan fuskarsa, idanunsa da suka kaɗa sukayi jajur ya buɗe haɗi da yin ƙasa dasu, kasancewar sam bayaso ayanzun kowa ya fahimci irin situation ɗin da yake ciki, cikin wata irin murya dake son ɓoye damuwarsa yace. 
"Na'am."    
Ɗan zuba masa idanu Abbou Jaheed ɗin yayi, ahankali ya sauƙe ajiyar zuciya tare da cewa. "Sama da shekara 2 kenan yanzu dana zuba maka ido inason naga gudun ruwanka, saidai kuma na lura da cewa kwata kwata babu tunanin aure acikin ƙwaƙwalwarka, saboda haka kasa aranka cewar, kamar yanda na zaɓawa Laylerh Miji, na kuma sa aurenta lokacin ɗaya,  haka kaima zanyi maka, saboda haka ya rage naka a iya lokacin daya ragema ka nemo matar aure, idan kuma ba haka ba dakaina zan nemo maka wacce zata dace dakai."           
Jin abun da Abboun ya faɗane yasashi ɗago kansa, hakanan yaji kalaman Abbou Jaheed ɗin kaman tatsuniya, duk da kuwa yasan cewa duk abun da Abbou Jaheed ɗin yafaɗa tabbas zai iya aikatawa, amma kwata kwata bayaji ajikinsa cewar zai rayu da wata mace.        
Idanunsa ya ɗan lumshe tare kuma da sakin wani murmushi, wanda iya kansa laɓɓan bakinsa, tabbas ya yarda da cewar, muradi da kuma fata ɗaya ne acikin zuciyarsa, wanda kuma rashin samun cikar burinsa daidai yake da ƙin yin aurensa har abada.
Sama da 10 years kenan daya ɗauka yana dakon abubuwa da yawa acikin rai da zuciyarsa,  tun baisan me yakeyi ba, tun kuma baigane me yake ji ba, har hakan ya cakuɗa da numfashinsa, ya zamanto bugun zuciyarsa, duk wani zafi da yakeji ya jure, ako yaushe akuma ko wacce rana buri ɗaya ne ke yawo acikin zuciyarsa, wanda kuma ayanzu wannan fata da burin suka cika da tarin ƙaddarori masu wuyar ɗauka.   
Ahankali ya miƙe tsaye dan bayajin zai iya cigaba da zama acikin falon.     Batare daya cewa kowannensu ƙala ba, kansa tsaye ya nufi hanyar ƙofar fita daga cikin falon.
Hakanne kuwa yasa duk suka bisa da kallo.     
Saidai kuma banda Najeeb wanda ayanzu yake ƙoƙarin gaskata zargin dake cikin zuciyarsa, saidai kuma koma meye bayajin zai iya barin abun da ayanzu ya gamsu cewar lallai yanaso.             

Koda ya fita daga cikin falon kaitsaye compound É—in gidan ya nufa, inda ma aikata kota ina keta hidimomi, masu bawa flowers ruwa, da masu wanke cars duk suna aikinsu.
Direct babban parking space É—in gidan ya nufa, wanda kuma ananne tarin motocinsa ke fake.
Abdoul dake zaune ganin Ogan nasa ya fito, yasa cikin sauri ya taso tare da ƙarasowa inda yake, cikin girmamawa yace.  "Good Morning Sir."  
Kansa kawai ya iya jinjina wa Abdoul ɗin, wanda hakan ke nuna cewa ya amsa.  ƙarasawa jikin wata haɗaɗɗiyar sabuwar motarsa ƙiran Mercedesbenz CLA 35 yayi, ganin hakanne yasa Abdoul gane cewa yau ogan nasa mercedes ɗin yake son hawa.
Cikin hanzari kuwa ya ciro key ɗin motar, tare da buɗewa M.Jay ɗin murfin motar ya shiga,  shikuwa Abdoul kamar yanda ya saba, nan wajen zamansa na driver ya shiga tare da murzawa motar key, cikin ƙwarewa ya fitar da ita daga parking space ɗin, maigadi dake tsaye kuwa  yana ganinsu ya wangale masu gaba ɗaya gate ɗin gidan,  cikin ƙwarewa Abdoul ya cilla hancin motar waje, sanin inda ogan nasa yafi zuwa idan yana cikin garin na Abuja ne,  yasa batare daya tsaya wani ɓata lokoci ba ya miƙi hanyar da zata kaisu Maitama Estate.   

Ɓangaren Laylerh kuwa tun komawarsu class ta samu kanta da kasa iya aiwatar da komai, hakanan ta zama wata so silently, yayinda gaba ɗaya tunani da nutsuwarta suka ƙaura izuwa wani waje na daban, sanadin hakan kuwa yasa duk wani malamin da zai shigo yi musu lecture bata taɓa fahimtar komai akan hakan, saboda hakanan takeji kaman anshafe mata ƙwaƙwalwa.        
Yayinda acikin ranta kuwa fata da kuma burin son sanin haƙiƙanin abun dake cikin zuciyarta ne, duk ya hanata sukuni, haka kuma duk yanda Teemah taso Laylerhn ta saki jikinta kasawa tayi, duk kuwa yanda taso ta ɓoye damuwarta ta kasa.
Ahaka har aka tashe su daga makarantar, kamar kullum kuma kamar koda yaushe tare suka jero suna tafiya, ahaka har suka fito daga cikin makarantar, suna fitowa kuwa kowaccensu tasamu driver na jiranta. 
Laylerh da tatafi zata shiga mota ne, Teemah ta riƙo hannunta, wanda hakan yasa tafasa shiga motar ta juyo ta fuskanci Teemah'n.  
Idanu Teemah ta ɗan lumshe cikin sanyin muryar dake bayyana tausayin ƙawarta ta tace.  
"Please Laylerh ki daina damuwa kinji, kisa aranki cewa auren da Abbou Jaheed zai miki shine mafi alkhairi agareki, kuma nasan Abbou Jaheed bazai taɓa zaɓa miki mijin daya san zai cutar dake ba, dan Allah ki daina sa damuwa aranki kinji please!!."  
Teemah'n ta ƙare maganan tana me haɗe hannuwanta biyu waje ɗaya, wanda hakan ke nuna alaman roƙo.     Ayanayin da take ciki yasa batajin zata iya cewa Teemah'n komai, domin yanzu babu abun da takeson gani da ji, kamar M.Jay. ɗan lumshe idanunta tayi tare da jinjinawa Teemah'n kai alaman  "To."  Murmushi Teemah tayi mata, sannan ta juya ta nufi wajen da motar gidansu ke fake.   
Asanyaye ta shige motar tare da É—an kwantar da kanta asaman kujera tana maida numfashi, ahaka drivern yaja suka bar harabar makarantar.

Maitama Estate.

Tsaye yake agaban wani  haɗaɗɗen glass frizer, yayinda hannunsa ke riƙe da zungureriyar kwalban wine, sai kuma wani ɗan ƙaramin glass cup da ya riƙe a hannun damansa, ahankali yake ɗan jujjuya cup ɗin, wanda ya riga daya zuba wine ɗin aciki, yayinda gaba ɗaya tunaninsa ya tafi izuwa wani waje daban.    
Idanu wani haɗaɗɗɗen gayen dake zaune akan ɗaya daga cikin kujerun falon ya zuba masa, *Fou'ad* kenan tabbas yana mamakin hali irin na abokin nasa, ajiyar zuciya ya sauƙe akaro na barkatai, ɗan gyara zamansa yayi cike kuma da ƙaunar abokin nasa yace.   "Meyasa kake ɓoye sirrin dake cikin zuciyarka Maleek? batun yauba nasan kana ɗauke da damuwa, wanda ko da ace baka faɗa ba, gaba ɗaya yanayinka ya nuna hakan, meyasa kake ɓoye abunda ke cikin zuciya da ƙirjinka?, meyasa kake ƙoƙarin haramtawa kanka abun da Allah Ya halatta ma? ya kamata ka farka daga wannan nannauyan baccin da kake, because yanzu rayuwa ta sanja, then zurfin ciki baya kawo komai sai dana sani, meyasa ako da yaushe kake tauyewa zuciyarka haƙƙinta bayan kuma kasan ta kamu da SO matsananci?."          
Idanunsa ya ɗan lumshe  tare kuma da buɗesu alokaci guda, Ajiye kwalban wine ɗin dake hannunsa yayi, ahankali cikin nuna halin ko in kula ya ƙaraso cikin falon, kan wata kujera dake facing na Fou'ad din ya zauna, ba tare kuma da ya kalli Fou'ad ɗinba, cikin husky voice ɗinsa  yace.  "So? menene kuma SO?... its in possible, because i dont have any feeling in my mind."                

Murmushi Fou'ad yayi domin shi yariga daya san waye Maleek, ya kuma san komai agame dashi, taurin rai dana zuciya tamkar aminai suke awajensa, kwata kwata baya taɓa ɗaukan kuskurensa, always gani yake shi akan daidai yake.     
Miƙewa tsaye Fou'ad ɗin yayi tare da ƙarasawa wajen da Maleek ɗin ke zaune, hannunsa ya ɗaura akan shoulder ɗinsa, cikin kulawa yace.  "SO ne Maleek, ni nayi imani cewa akwai so acikin zuciyarka, meyasa kake ɓoyewa? meyasa bazaka iya faɗa ba? Meyasa....."        
"Enough Fou'ad, Enough is Enough please!!."  Maleek din  yafaɗi haka ta hanyar katse Fou'ad daga maganan da yakeyi.  Bayajin zai iya jurewa jin kalaman da yawancin lokuta Fou'ad ɗin ke faɗa masa, wannan dalili yasa sometimes bayason zuwa wajen Aboki kuma Aminin nasa, saboda ako yaushe so yake saiya ƙuresa.   Wayayoyinsa dake aje kan table ya ɗauka, batare da ya kalli Fou'ad ɗin ba ya juya ya nufi hanyar fita daga falon.   
Da kallo Fou'ad ya bisa har ya fice daga cikin falon. Murmushi yayi tare da komawa kan kujera ya zauna, daman ya sani ako da yaushe Maleek ɗin baya karɓan gaskiya aduk yanda tazo masa.              
Abdoul dage zaune aharabar gidan Fou'ad ɗin kuwa, ganin yanda Ogan nasa ya fito kaman afusace ne yasashi saurin tashi tsaye, cikin hanzari ya ƙarasa jikin mota, tare da buɗewa Maleek ɗi murfin motar yashiga. 
Shiɗin ma shiga yayi, yayinda tun kafun yaja motar yayiwa gateman alaman ya buɗe Musu gate ɗin zasu fita, ba ɓata lokaci kuwa gateman ɗin ya wangale musu gate ɗin gidan suka fice.     
Koda suka fara tafiya lumshe idanunsa yayi, yanamejin yanda sanyin A/C ke ratsa dum jikinsa.
kalmar "SO" da Fou'ad ya faɗa ita keta yi masa yawo acikin ƙwaƙwalwarsa,  hakanan yaji ya tsani kalmar domin yayi imani cewa abun da yakeji acikin zuciyarsa ya fi karfin aƙirasa da sunan SO, tabbas kalmar SO tayi kaɗan ta ɗauki nauyin abun daya jima yana sukar zuciyarsa.

Ɓangaren Laylerh kuwa tunda suka ɗauki hanyar dawowa gida bata buɗe idanunta da suke alumshe ba, ahankali kala kalan tunani ke cika zuciyarta, yayinda wani irin maganaɗisun son ganinsa ke yawo ajikinta. Jin tsayuwar motar tasu ne yasa ta gane cewar sun iso gida.
Ahankali ta buɗe idanunta tare da ɗaukan school bag ɗinta dake gefenta, anutse ta buɗe murfin motar ta fito, batare da ta tsaya sauraran komai ba kuwa ta nufi haɗaɗɗiyar ƙofar da zata sada ta da babban falon gidan, koda ta ƙarasa jikin ƙofar ahankali ta murɗa handle din ƙofar ta shiga falon bakinta ɗauke da sallama, babu kowa acikin falon sai tv plasma dake ta faman ɓaɓatu shi kaɗai.
Kasancewar agajiye take jin kanta yasa kaitsaye ta nufi hanyar da zai sadata da É—akinta.
Yanayin yanda ta sadda kanta ƙasa ne yasa sam bata ma lura dashi ba. Najeeb dake tsaye idanunsa yaɗan lumshe tare da sakin ajiyar zuciya, tsawon 10 minute kenan daya ɗauka atsaye yana jiran dawowarta.
Ganin zata wuce batare da ta ganshi bane yasashi kamo hannunta. Wanda hakan yasa ta juyo amatuƙar razane, tare kuma da ƙoƙarin fasa ihu saboda ta tsorata sosai, cikin sauri yasa hannunsa ya toshe mata baki, tare da ɗan soma girgiza mata kai, alaman kada tayi ihu.
Faɗawar idanunta cikin nasa ne yasata sauƙe wata ƙatuwar ajiyar zuciya tare da lumshe idanunta, murmushin daya bayyana asalin kyawun fuskarsa yayi, cikin silently voice yace. "Matsoraciya kawai!." Jin yace mata matsoraciya ne yasata buɗe idanunta, tare kuma da daidaita nutsuwarta, cikin yanayin shagwaɓan daya zame mata jiki tace.
"To meyasa zaka tsoratani?."
"Saboda inason sanin wace irin mata zan aura!." YafaÉ—a yana me bin duk jikinta da idanu.
Jin da tayi ya ambaci aure ne yasa ta É—ago manya manyan idanunta ta kallesa.
Wani irin yaaarrr yaji ajikinsa sakamakon kallon da tayi masa, hakanne kuma yasashi kamo hannunta duka biyu ya riƙe ƙam acikin nasa, ahankali ya matso gab da ita wanda har hakan yasa numfashinsu gauraya dana juna. ahankali idanunsa suka ɗan fara lullumshewa, cikin muryarsa da ta sanja amo yace.
"INASONKI Laylerh, Inasonki sosai da sosai!!." Yanayin yanda ya ƙare maganar cikin wani irin tone ne yasata lumshe idanunta, wanda sanadin hakan yabasu daman sake kusanci da juna sosai, still kuma har yanzu hannayenta na cikin nasa.
Daga waje kuwa ahankali Maleek ya ɗaura hannunsa akan handle din ƙofar shigowa falon, kasancewar ƙofar ba akulle take bane yasa take ta buɗe, sako kansa cikin falon da yayi ne, ya sashi sauƙe idanunsa akansu.

*5/December/2020*
1/19/21, 8:12 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*(This book is mainly for those that pay, if you know you did'nt pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay-0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank. Whatsapp number 07017879464.)*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.