Best Hausa Novels

Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: LAYLERH MALEEK.txt

Chapter 45 of 65

Ci gaba da kutsowa cikin falon tayi saidai kuma abunda idanunta suka gane matane yasa ta tsayawa, tare da kafe Oum Ayush d’in da idanu.

Wanda tun da Najeeb ya tafi yabarta take ahaka, ta zuba tagumi da duka hannayenta biyu, kallo d’aya zaka mata kafahimci kuma cewar tana cikin damuwa.

“Oum Ayush!�
Laylerh’n ta k’ira sunanta adaidai lokacin da ta k’araso tsakiyar falon.

Amon sautin muryar Laylerh’nne kuma yasa Oum Ayush dawowa hayyacinta, wanda hakan yasa ta sauk’e idanunta akan Laylerh’n, take kuwa cikin sauri ta b’oye envelope d’in dake hannunta, tare da k’ok’arin samawa fuskarta fake smile wanda zata yak’i duk wata tambaya da Laylerh’n zata zo mata dashi.
Cikin kuma son kauda tantama acikin zuciyar Laylerh’n tace.

“Na’am Laylerh yaushe kika shigo?�

“Yanzu na shigo, amma Oum Ayush meyake faruwa naganki ahaka? Kodai jikin Yah Maleek ne ya sake tashi!!�

Ambatan sunansa kad’ae da tayi acikin maganar nata shiya raunata duk wani gab’a dake jikinta, saboda dama shid’inne acikin mine d’inta.

Baga ita ba kuma harga Oum Ayush d’in jin da tayi Laylerh’n ta ambaci sunan Maleek shi ya k’ara sanyaya mata jiki, har takai ga damuwar ta ta bayyana k’arara.
Tabbas sai ayanzunne tasake hango abunda Najeeb ya hango, shin ma tayaya zai iya jurewa yanda Laylerh’n ke mu’amalantuwa da sha’anin Maleek d’in? kowani magananta d’aya fa da zatayi akansa ne, komae shine, shine acikin zuciyarta, tunaninta dama jinin jikinta.

Itakuwa Laylerh zuciyartace ta sake karyewa musamman da taga yanda Oum Ayush d’in ke kallonta bata ko d’auke ido.

“Please Oum Ayush meyake faruwa? Yah Najeeb yace kina k’irana, Dan Allah idan wani abune yasake samun Yah M.jay ki fad’amin please!!!�

Ta k’are maganar cikin yanayin magiya, lokaci d’aya kuma hawaye suka cika idanunta.

“Ba abunda ya sake samun Maleek, hasalima yana nan lapia.�

Ta fad’i hakan dan son samawa zuciyar Laylerh’n nutsuwa.

Amma kuma sam Laylerh bataji zuciyarta ta gamsuba, saidai babu yanda ta iya, asanyaye tace.

“Yah Najeeb yace kina k’irana.�

Kai Oum Ayush d’in ta jinjina alaman “Eh.� Duk da kuwa tasan bata fad’i hakan ba, amma saitaji wani irin tausayin Laylerh’n ya lullub’e zuciyar ta.
Wanda Hakan yasa taja wani irin dogon numfashi, tare da d’an matsawa ta kamo hannun Laylerh’n ta zaunar da ita akan kujeran dake kusa da nata.

K’warai so take Laylerh’n ta fahimci abunda zata fad’a mata, duk da cewa kalaman dake bakinta suna da nauyi sosae amma ya zama dolene tasan hakan, Dan awannan lokacin ba amfanin b’oye saki ga wanda aka saka.

hannunta tasa ahankali ta shafi fuskar Laylerh’n, cikin so da kuma bata k’warin guiwa tace.

“Tabbas wata k’addarar takan zuwa da sauyi, sannan kyakkyawar k’addara takan zo ta kori mummuna, kamar yanda yake komae da zae faru da bawa rubutaccen al’amarine, wanda Allah Ya tsara masa tunkafun zuwansa duniya, ba kuma Lallai ne fahimtarka da kuma abunda ya sameka su zamo abu d’aya ba.
Lallai littafin k’addara guda d’ayane amma yana da shafuka mabanbanta, yau idan mai dad’i ya bud’e, gobe watak’ila akasinsa ne zai bud’e.�

D’an tsagaitawa da maganan nata tayi tare da sake damk’e hannun Laylerh’n dake cikin nata.

“Kada zuciyarki ta tab’a karaya Laylerh, domin babu abunda yake dawwamemme, watarana abunda kakeso karasa, watarana kuma abunda kakeso ka samu sannan wanda bakaso ya nisanta dakai, idan kuma kasamu abunda bakaso yau, to hakan Bawae yana nufin cewa har abada bazaka tab’a samun wanda kakeso bane, ba akanki ba kad’ai dayawan matan duniya suna fuskantar wannan k’alubalen, hakan kuwa yakansa suji babu dad’i koda kuwa ba wanda suke so bane ya aikata musu hakan, Tabbas matuk’ar sunsan ciwon kansu dole zasuji babu dad’i, domin hakan kamar ragewar wata k’ima ne na y’a mace, banason kiyi kuka bakuma naso ki zargi kanki, kawae ki d’au k’addararki domin kuwa hakan ma wata damace.�

Takai k’arshen zancennata adaedae lokacin da take sawa Laylerh’n envelope d’in Najeeb ya bata ahannunta.

Tabbas k’wak’walwa da zuciyarta sun d’au charge, wanda hakan yasa ta kasa tantance ma’anar wasu maganganun.
Envelope d’in dake saman hannunta ta tsurawa ido, yayinda takejin wani sashi na zuciyarta na bugawa.

Ahankali ta bud’e envelope d’in tare da zaro takardar dake cikinsa ta warware.

Take kuwa idanunta suka sauk’a akan d’an tak’aitaccen rubutun dake cikinsa.
Tsurawa rubutun idanu tayi yayinda kuma take ware kowacce kalma d’aya bayan d’aya, ahaka har tazo kan kalmomin dake k’arshe wanda suke d’auke da harafin Divorce.

Adaidai kan kalmar ta tsaida idanunta bata ko k’yaftawa, yayinda kuma duk wani tunanin da Brain d’inta keyi ya tsaya cak.

Adaedae lokacinne kuma wayar M.Jay dake kan kunnensa ta zame ta fad’i k’asa, saboda jin maganan da Abbou Jaheed ke fad’a masa cewar yayi maza yaje sashin Oum Ayush yasanar da ita cewar kada ta sanar da Laylerh duk wani abu dake faruwa, sannan kuma kada ta bata takardar sakin da Najeeb ya rubuta mata.

*5/March/2021*
*1:15 pm*

*(🙏🏻Kaena ya dau charge ne nashiga test sai yanzu na nutsu, amma dai kam yau nasha da k’yar🤢.)*
3/9/21, 4:41 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*NOTE: Please and Please masu karantamin novels d’in LaylerhMaleek a YouTube kudaina tunda bada izinina kukeyi ba, sannan baku tambayeni ba kawae kuna ta karantamin book, bayan kuma kunsan book d’in ba free bane, abunda kukeyi ba abubane me kyau saboda a k’a ida duk abunda ba mallakinka bane kafun kayi amfani dashi yana da kyau kafara neman izinin mamallakin abun, kudaina please hakan bashida kyau tunda bawae izinina kuka nema ba, gaban kanku kukayi, banason abunda zaisa na samu matsala da mutane, so kuma kada kubari ku samu matsala dani🙏🏻*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.