Best Hausa Novels

Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: LAYLERH MALEEK.txt

Chapter 32 of 65

*Chapter 48*

Ajiyar zuciya Abbou Khareem ya sauk’e, cikin yanayin fahimtar k’unan da d’an uwannasa yakeji acikin zuciyarsa yace.
“Tabbas nasan kanajin babu dad’i acikin zuciyarka, amma ni sai nake ganin cewa Maleek yabar gida ne saboda bayason wannan auren da za’ayi masa, saboda ayanzu yasan cewa shi ba k’aramin yaro bane, cikakken Namiji ne shi da yake da y’anci kamar kowa, yana da choice d’in da zai nemo mace aduk inda yake ya aura, gaskia gaba d’aya tunanina ya tsaya akan cewar Maleek bayason wannan auren ne, meyasa ba za’a fasa maganan auren ba, asake bashi lokaci ya nemo matar aure da kansa inaga hakan zae fi yiwa kowa dad’i, amma fa ban fad’i hakan amatsayin umarni ba shawara ce kawae atak’aice.�
Ahankali Abbou Jaheed d’in ya d’ago kai ya kalli k’aninnasa wato Abbou Kareem.
Maida kansa yayi batare da yace komai ba, sai wani irin murmushi me d’auke da ma’anoni daban daban da yayi, tabbas tuntuni dama yasan cewa watarana sae hakan ya faru, shikuwa ba wae kawae yanayin abunda yaso akan y’ay’annasa bane, duk wani abu da yakeyi yana yine saboda nesanta faruwar abun kunya.
Mug d’in coffee d’in dake hannunsa ya ajiye tare da d’an gyara zamansa, ahankali cikin muryarsa da tayi sanyi sosae yace.
“Bawae ina tauyewa Maleek hakk’insa bane na neman mata da kansa, na basa dama almost 3 times amma ya share abun, ya yi watsi da duk wata magana na, duk dacewar bana nuna masa bayyananniyar soyayya amatsayinsa na tilon d’ana hakan bawae yana nufin cewa bana sonsa bane, ayanzu muna cikin wani rayuwa da bayyana matsanancin soyayya ga d’a kan jawo masa tab’arewar rayuwa, tabbas bazan iya jure ganin Maleek acikin wani hali ba, ko ya yake kuwa, saidai inason kowa yasan cewa na bawa Maleek dama amma yayi watsi da ita, na basa zab’i amma ya kawar, k’warai shiba yaro bane da zan tursasa sa dole akan sae ya auri wacce na kawo masa amatsayin zab’in a, hak’ik’a ni kaena ban tab’a tunanin tursasa Maleek akan auran wacce baya soba, saidai kuma ayanayin yanda naga ya fara karkata akalar rayuwarsa izuwa wani waje na daban yazame min tilas na d’au mataki na kuma dage wajen dawo dashi hanya, bansan me yake damun Maleek ba, bansan meyasa yake son maida rayuwarsa wata abar banza ba, da idanuna nagansa ya dawomin gida acikin maye, cikin talatainin dare, Kareem bazan iya jure hakan ba, wannan dalilin shiyasa na yanke shawarar cewa dole saiyayi aure, saboda komae wani lokaci aure yakan zamo silar gyara rayuwar d’an Adam, tabbas nasan akwae damuwa me tarin yawa acikin zuciyar Maleek, saidai kuma bani da wata hanya da zan iya magance masa ita sai ta hanyar sama masa abokiyar zama, wacce zata d’ebe masa kewa, tun yana k’arami ya taso da maraicin rashin mahaifiya, yayi gaba d’aya rayuwarsa cikin kad’aici da kewa, shin yanzu bai cancanci zama da mace ba? ko idan harshi bazai ne ma ba ni saina zauna bannema masa ba? lokacin da zan zubawa Maleek idanu ya wuce, yanzu lokaci ne da ya kamata ace yasan waye shi, wani irin dukiya ne baitara ba? yana da kud’i dukiyar da har ya mutu bazasu tab’a k’arewa ba, idan har mutum yana da hankali yana kuma da jini ajikinsa sannan yana da sana’ar yi aure shine abunda ya kama ce sa, koba komae idan Allah Ya azurtasa da zuri’a zasu zamar masa garkuwa anan gaba.�
Gama fad’in hakan da yayi yaja kujerarsa baya, batare daya tsaya jin wani abu daga bakin kowannensu ba ya mik’e tsaye anutse ya nufi hanyar babban d’akinsa dake nan cikin falon.

Ajiyar zuciya me k’arfi Oum Ayush da kuma Abbou Kareem suka sauk’e, tabbas sun gamsu da kalaman Abbou Jaheed d’in domin kuwa duk wani abu yana da iko akan y’ay’ansa, sannan hakk’in kowani ubane ya zab’awa y’ay’ansa rayuwar da ta dace wanda agaba zasuyi alfahari da ita.
Hak’ik’a ada suna ganin kamar wani abu da Abbou Jaheed d’in keyi baya dacewa, amma ayanzu sun fahimci gaba d’aya dalilin da yasa yake hakan.
Jiki asanyaye Abbou Kareem ya mik’e tsaye yabar dining area din domin dama ya kammala cin abincin sa.
Hakan yasa dining table d’in ya rage daga Oum Ayush Momy sai kuma Laylerh da tunda Abbou Jaheed ya fad’i maganarsa ta farko ta sunkuyar da kanta k’asa har zuwa yanzu kuwa bata d’ago da kannata ba, yayinda ayanzun kuma babu abunda ya tsaya mata arai kaman jin da tayi cewar yau kwana 4 kenan da M.Jay d’in baya gidan, abunda yafi girgizata kuwa shine jin da tayi Abbou Jaheed yace da idanunsa yaga Maleek d’in acikin yanayin maye.
Tabbas way’annan abubuwa guda biyun sun matuk’ar d’aga hankalinta, wanda har hakan yasa ta kasa kai koda loma d’aya na abinci bakinta.
Sosae jikinta yayi sanyi, yayinda a gefe guda kuwa idanunta tab suka cika da k’walla, awannan karon kam sanadin k’wallan nata ya banbanta dana kullum, saboda wani irin matsanancin tausayin d’an uwan nata ne ya shiga jikinta, wanda har hakan ya haifar da bayyanar rauninta.
Ahankali ta lumshe idanunta dake cike da k’walla, hakanne kuwa ya bawa hawayen dake cikin idanunnata daman gangarowa kan fuskarta.
Cikin wata irin sassanyar muryar da babu wani me iya jin amo ko sautin sa tace.
“Kana ina Yah M.Jay!!!�
Zuciyata da tunanina kullum a kanka suke, lallai nayarda cewa SONKA NE k’addarata, haka zalika an rubutamin soyayyarka acikin jini da tsokana, tabbas ayau kawae kuma ayanzu naji ajikina cewa da gaske kaene k’addarata, k’addara mafi girma.
“INASONKA Yah MALEEK INA MATUK’AR SONKA! hak’ik’a kuma koda ace bansame ka ba zan cigaba da sonka har mutuwata...�

Idanu Oum Ayush ta zuba mata da kyau, sakamakon yanda taga tun d’azu bakinta na motsi amma kuma batajin amon sautin maganar nata acikin kunnuwanta.
“Laylerh.�
Ta k’ira sunanta cikin d’an d’aga murya.
Hakanne kuwa ya zaburar da ita had’e da dawo da ita cikin hayyacinta, cikin sauri tasanya hannu ta shiga share hawayen dake kan fuskarta.
Cike kuma da son daedae ta nutsuwarta ta d’ago kae ta kalli Oum Ayush d’in.
Oum Ayush ko kasa d’auke idanunta daga kan Laylerh’n tayi, domin taga duk wani sigar damuwa ya bayyana k’arara akan fuskarta.
Gama karantar yanayin Laylerh’n kuma da tayi ne yasa ta d’an numfasawa, ahankali tace.
“Kibar duk wani tunani kici abincinki, tun d’azu ko loma d’aya bakiyi ba gashi sae hucewa yake, ko baki da lafiya ne?�
Kai ta d’an girgiza cikin kuma muryarta da ta zama very slowly tace.
“Kaina ne yake ciwo.�
“Sannu kinsha magani ne?.� Cewar Oum Ayush tana me d’an daga kafad’anta.
“A’a bansha ba.�
“Okay kici abincin saikisha magani ko.�
Jin ance Tasha maganine yasa ta kwab’e fuska, akasalance tace.
“Ni nak’oshi da abincin zanje nasha magani kawai.�
Batare kuma da tajira me Oum Ayush d’in zata ceba, tayi saurin mik’ewa tsaye, koda ta fara tafiya kuwa har k’afafunta suna hard’ewa saikace wata marar gaskiya.
Da kallo kawae Oum Ayush ta bita harta fice daga cikin falon kafun ta d’auke kanta.
Itama tashi daga kan dinning d’in tayi, domin dama duk sun kammala cin abincin, harta Momy Abbou Kareem na barin wajen itama ta tashi ta tafi.

Jikinta amatuk’ar sanyaye haka ta koma sashinsu, koda ta shiga falonnasu kuwa bata samu Najeeb ba, saidai k’amshin turarensa wanda ya cika falon da tajine, ya tabbatar mata da cewar ya gama abunda zaiyi har ya shirya ya fita.
Bata wani damu da zama acikin falon ba, direct d’aki ta wuce tayi kwanciyar ta akan gado, tare dajan blanket ta rufe jikinta dashi.
Wayarta dake aje akan bedside drawer ta d’auka, tare da kunna data’nta ta shiga Tiktok dan son d’ebewa kanta kewa da kuma rage tunani.

Munnira
Da fuskarta wanda tasha uban meckup ta d’ago kae ta kalli mahaifiyarta ta dake tsaye agefe, itama tasha meckup da ado, kallo d’aya kuma zakayi musu dukansu kasan cewa suna cike da k’asaita, da kuma arrogance, babuma kamar Buzuwa wanda ita gaba d’aya jitake tafi kowa saboda y’arta zata shiga gidan k’asaita kud’i da kuma wayewa, kasancewar kuma yau zasu fara gudanar da events d’in da suka tsara na bikin shiyasa duk suka sha ado, mutanen da suka gayyata kuwa sae wane da wane, saboda ayanzu sunce sunfi k’arfin mutane masu d’an matsakaicin k’arfi, Dan nan da y’an kwanaki suna saran zamowarsu millionaires.
“Mom.�
Munnira ta k’ira sunan maman nata murya d’auke da damuwa.
Jin yanayin yanda amon muryan Munniran yasanja ne kuma yasa Buzuwa juyowa batare da ta amsa ba ta fuskanci y’artata.
Marairaice fuska Munniran tayi tare da kamo hannun Maman nata, murya k’asa k’asa tace.
“Mama nifa agaskiya kwana biyunnan inacikin damuwa, tunfa lokacin da Captain Maleek yazo ya tafi bai kuma sake zuwa ba har yau, kuma ko d’an irin k’irana awaya d’innan ma bayyiba Anya ma kuwa yana sona kamar yanda nake sonsa?.�
Jin abunda Munniran ta fad’ane yasa Buzuwa ta saki Murmushi tare da neman waje ta zauna,
kamo hannun Munniran tayi cikin son kwantarwa da y’ar nata hankali tace.
“Wannan sam bae kamata ya dameki ba Munnira, kuma da ace baya sonki ae kwata kwata bazae amincewa aurenki ba, kinsan irin mijin da zaki aura yawan ci kullum a busy suke, saboda haka karki damu kanki wae dan ayanzu baya nemanki, da zaran kinshiga gidansa to fa mungama dashi, Insha Allah shi da kansa zaina bibiyanki ke kuma kina ja masa aji, wannan alk’awarine na miki.�
Wani irin murmushin jin dad’i Munnira tayi tare dayin fari da idanunta, cike dajin dad’in kalaman Mahaifiyar nata tace.
“Shiyasa nake alfahari dake Mom, saboda nasan zaki tsayamin akan komae.�
“K’warai kuwa kedae tashi muje Jama’a sunata jiranmu.� Cewar Buzuwa dake yunk’urin tashi tsaye.
Mik’ewa Munniran tayi cikin jin dad’i da farinciki tabi bayan mahaifiyar tata suka fice.

Ahankali yake taka steps d’in da zae bashi daman k’arasa shigowa cikin falon, sanye yake da dogon wandon uniform d’insa na soldiers da kuma wata white rubber crazy shirt, sosae kayan sukayi masa kyau, saidai kuma gaba d’aya yanayinsa ya sanja, kallo d’aya zaka masa kafahimci cewa baya cikin yanayi me dad’i, saboda duk wani alaman rashin lafiya ya bayyana ajikinsa, yayinda yabar yalwataccen beard akan fuskarsa, wanda hakanne kuma ya k’ara k’awata fuskar tasa.
Kasalalliyar ajiyar zuciya ya sauk’e adaedae lokacin da ya gama sauk’owa daga kan steps d’in, wanda kuma hakanne ya bashi daman samun kansa acikin k’awataccen falon.
Sauk’e idanunsa da yayi kuma akan hoton Laylerh ne yasa shi d’an lumshe idanunsa tare dasa hannu ya dafe daedae saitin zuciyarsa dake beating da sauri, sam baisan meyasa ba hakanan yau tun tashinsa yake jin fad’uwar gaba da kuma wani irin tsinkewar zuciya mai tsanani, hakanne ma yasashi rik’e addu’a k’am abakinsa, amma kuma wani abun mamakin har yanzu baiji bugun zuciyar tasa ta lafa ba, yayinda ajikinsa yakejin kamar wani abu ne zai samesa yau d’in, jin kuma da yayi gaba d’aya zaman gidan ya dameshi ne yasashi shiryawa tsab dan zuwa zaga gari ko hakan zae rage masa kewa da kuma kad’aicin dake damunsa.
Domin tunda yazo gidan gaba d’aya tunanin Laylerh ya hanasa sukuni, ko idanunsa ya rufe ita kawae yake gani.
Car key d’insa dake aje akan d’an madaidaicin table d’in dake cikin falon ya d’auka, sannan kai tsaye ya nufi hanyar fita daga cikin falon.
Batare kuma da ya tsaya locking k’ofar falon ba kaitsaye ya nufi wajen da motarsa k’irar Mercedes benz ke fake, akasalance ya bud’e murfin motar ya shiga, duk da kuwa cewar baya wani jin k’arfi sosai ajikinsa, haka ya daure ya tada motar.
Kasancewar kuma yasa Abdoul ya ne momasa maigadi ne yasa kafun ya iso bakin gate d’in ma tuni maigadin ya wangale masa k’ofa, hakan yasa kaitsaye ya cilla hancin motar tasa kan shumfud’adden titin da ya mamaye gaba d’aya unguwar.
Tafiya kawae yake akan shumfud’add’en titin batare da yasan inda ya dosa ba, daga gefe guda kuwa mood d’insa ne keci gaba da sauyawa daga yanayin farinciki zuwa akasin hakan.
Fad’uwar gaban da yakeji ne ya tsananta, wanda hakan yasa shi cigaba da ambaton sunan Allah Abakinsa.
Daidai ya sha wata kwana, d’aya daga cikin wayoyinsa k’iran Samsung Galaxy fold 2 ta soma k’ara, kasancewar kuma yau ya kunna wayoyin nasa ne yasashi maida kallonsa ga wayar dan ganin wake k’iransa.
*Hak’ik’a wannan lokacin,da kuma way’annan y’an sakannin sune mafarin k’addaransa ta biyu, sannan kuma mafarin tsautsayi, tsautsayi me matuk’ar girgiza rayuwa, lallai wannan itace k’addaran da zata sauya masa rayuwa, K’addara mafi girma agaresa.
Tabbas kamar yanda Babu wanda ya isa gujewa mutuwa, haka ma babu wanda ya isa gujewa K’addaransa.
Lallai dole abu biyu zasu kasance Arayuwar Maleek farinciki ko akasin haka, tabbas sae da wata k’addaran wani MURADI da kuma BURI ke samun daman cika.*
Maida idanunsa ga wayar tasa da yayine, yasa batare da sani ko ankara ba motarsa da kuma wata motar da ta shawo kwanan sukayi wani irin mummunan karo, wanda hakan yasa duka motoci biyun sukayi wani irin k’ara da kuma mummunan buguwa har saida yakai ga kowaccensu ta fad’i rigingine.

*(Dan Allah Banason yawan k’orafin da kukemin kan cewar wae na takurawa Maleek da yawa, Wallahi haka labarin LaylerhMaleek yake, ba kuma naso na sanja ko kuma na cire wani abu daga ciki, Dan Allah Kudaena nunamin cewa kamar bansan me nake rubutawa ba, nasani kuma Idan kukayi hak’uri komae zai tafi Normal rashin hakuri shi zaisa kuga kaman anayin ba daidaiba🙏🏻🙏🏻🙏🏻 kuyi hakuri mun koma school wallahi shiyasa duk bana samun zaman yin editing.)*

*5February/2021*

3:45 pm
2/8/21, 9:26 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*Note edit*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.