Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: LAYLERH MALEEK.txt
Chapter 24 of 65
*Chapter 39*
Tamkar sauk’an rugugin aradu haka su biyun sukaji sauk’an kalaman Abbou Jaheed d’in acikin kunnuwansu, wanda kuma ba iya su bama harta su Oum Ayush saida sukaji maganar Abbou Jaheed d’in tazo musu abazata.
“What!!!�
Ya fad’a cikin wata irin murya dake bayyana zallan tashin hankalinsa, tare da juyowa cikin sauri ya fuskanci Abbou Jaheed d’in, wanda jin kalaman da ya fad’a d’inne kuma yasa shi saurin juyowa tare da zazzaro idanunsa waje, cike kuma da rashin fahimtar inda kalaman Abbou Jaheed d’in suka dosa, cikin mauryarsa da tasanja amo lokaci guda ya maimaita kalmar ta. “Aure!!� abakinsa dan hakanan yajita wata iri, duba da irin yanda shigar Kalman cikin kunnuwansa ta haifar masa da matsanancin bugun zuciya, da kuma fad’uwar gaba.
Abbou Jaheed kuwa ganin yanayin tashin hankalin da Maleek d’in ya shiga ne yasashi d’aure fuskarsa tamau, batare kuma da alaman wasa ko wargi ba akan fuskartasa yace.
“Eh Aure zakayi kamar yanda kaji na fad’a, saboda bazan zuba maka idanu ka zauna haka ba, inaso kuma kasan cewa hakan umarnine ba wai shawara ba, na riga dana gama yanke hukunci, ba kuma zan tab’a sanjawa ba, saboda haka koda Yaushe yazamana kana cikin shiri, saboda ba neman amincewa ko yardarka nake da buk’ata ba, domin na baka dama amma kayi wasa dashi, atunaninka haka zanzuba maka ido, ina kallo kanayimin duk abunda kaga dama acikin gida? bayan kuma kasan cewar bazan tab’a lamuntar hakanba, sannan zab’i ya rage naka ko kaso ko karka so aurenka babu fashi, domin kai ba k’aramin yaro bane da za’a tsaya tambayar amincewarka ko akasin haka.�
Idanunsa da sukayi jajur lokaci d’aya ya rumtse da k’arfi, domin hakanan yaji k’afafunsa na neman gaza d’aukar nauyinsa, yayinda kuma take guiwowinsa suka yi sanyi, shikam idan ba yaudarar kansa yakeyi ba saiyakejin kamar kunnuwansa basu jiye masa maganganun Abbou Jaheed d’in adaidai ba, kansa ya d’an soma girgizawa ahankali, cikin cijewa da kuma k’ok’arin daure zuciyarsa ya had’e labb’an bakinsa ya ciza, wani irin tafasa da yaji zuciyarsa nayi ne kuma yasashi juyawa cikin sauri ya soma sauk’a daga kan y’an k’ananan steps d’in da zai nesanta ka da dining area’n.
Laylerh kuwa dake zaune wanda tuni kalaman Abbou Jaheed d’in sun sa tazama kaman statue, bayan Maleek d’in tabi da idanunta wanda suka cika da ruwan hawaye batare da ta sani ba, yayinda kuma taji wani irin abu mekaman dutse ya tokare k’irjinta.
“Mekenan me hakan yake nufi, M.Jay aure zaiyi kaman yanda itama tayi aure? Wannan wace iriyar k’addarace me matsanancin girma?�
Tayiwa kanta tambayar da har acikin zuciyarta bata da gamsuwa akan hakan, meyake shirin faruwa da’ita ita kanta batasani ba, raunannun idanunta wanda suke shirin zubo da k’wallan dake cikinsu ta lumshe, cikin karyewar zuciyar daya risketa ta kifa kanta anan saman table d’in dake gabansu, tare kuma dasa hannu ta dafe daedae saitin zucuyarta dake bugawa da sauri, tabbas wani abu me kama da matsanancin fad’uwar gaba da kuma tsoro takeji, wanda hakanne kuma yasa ta keji ajikinta kaman tarasa wani babban kaso na babin nutsuwarta.
Saidai kuma jin da tayi Abbou Jaheed d’in na fad’awa su Abbou Kareem cewar y’ar gidan abokin aikinsa ne ya zab’awa Maleek d’in, wato Alhaji Faruk yasa tayi saurin d’ago kanta, domin kuwa tasan cewa Alhaji Farouk d’in baida wata y’a sai Munnira, matashiyar budurwar dake matsanancin jin kai, da kuma isa had’i da d’agawa wacce akoda yaushe take ganin tafi kowa, duk da kuwa cewar baza’a k’irata da sunan mummuna ba amma bata da wani kyau irin na fitar hankali.
Lips d’inta ta ciza tare da d’anyin kasa da kanta, domin sam bataso wani daga cikinsu yakaranci yanayin da take ciki.
Saidai kuma duk yanda taso ga b’oye yanayin nata hakan baisa Najeeb kasa fahimtar sanjawar da mood d’inta yayi lokaci d’aya ba.
Saidai kuma sanin abunda ya shirya acikin zuciyarsa yasa shi kasa ce mata komae, saima maida hankalinsa da yayi akan plate d’in abincin dake gabansa.
Ab’angaren Maleek kuwa zuciyarsa cike da k’una haka ya k’arasa part d’insa, kaitsaye bedroom d’insa ya wuce, ahankali ya maida k’ofar bedroom d’in nasa ya rife, cikin yanayin daya samu kansa ya jingina bayansa ajikin k’ofar tare da rumtse idanunsa da k’arfi, yayinda kalaman Abbou Jaheed kedawowa cikin kansa filla filla.
Abayyane ya tambayi kansa cewar.
“Meyasa k’addara zata zab’a masa irin wannan rayuwa me cike da k’uncin?
Shin tayaya nema zuciyarsa zata iya jure d’aukan way’annan manya manyan k’addarorin da suke tunkarosa?
Meyasa Abbou Jaheed zaiyi masa haka? Meyasa!!!�
Yafad’a cikin k’araji tare dasa hannunsa ya naushi k’ofar d’akin, tabbas da ace zai iya bud’e baki ya furta rashin amincewarsa ga kalaman Abbou Jaheed d’in ayau da yayi hakan, ko da zaiji sanyi da nutsuwa acikin zuciyarsa, saidai kuma amma bashi da wani zab’i domin kasantuwar Abbou Jaheed amatsayin mahaifinsa yasa ya zame masa dole yin biyayya agaresa.
Asanyaye ya tako zuwa tsakiyar d’akin nasa, hakanan yakejin duk zuciyarsa ba dad’i.
Abakin gadonsa ya zauna tare da sa tafukan hannayensa ya rufe fuskarsa, magana ta gaskiya shine baya ji ajikinsa cewar zai iya zama da wata mace amatsayin mata, saboda fata da kuma buri d’aya kawae yake dashi, wanda kuma ya riga da yayi losing d’insu tuntuni, hakan yasa sam bayajin wata mace amatsayin abokiyar zamansa, tabbas ya yarda cewa soyayyar Laylerh tana d’aya daga cikin manyan k’addarorinsa haka ma kuma rasata, shima k’addara ne me d’auke da k’alubale na musamman, hak’ik’a yasan cewa akoda yaushe Allah Ne ke tsarawa bawa fad’uwa da kuma nasararsa, shi ne kuma ya tsara masa komae, amma bayajin acikin tarin k’addarorinsa akwae wata bayan Laylerh, saboda yayi Imani cewa Laylerh ita kad’aice mace da aka rubuta masa acikin k’addaransa, kuma itace rauninsa, samunta nasara ne rashinta kuma nak’asu ne acikin rayuwarsa, ya yarda cewa zae rayu da dafin sonta acikin zuciyarsa, zafi k’una da kuma radad’in da yakeji na soyayyarta akoda yaushe k’onasa suke, k’una me tsananin zafi, duk da hakan kuwa akullum salon soyayyarta sanjawa yake acikin zuciyarsa, wanda ayanzu shi kansa baisan wani irin soyayya bane yakeyiwa Laylerh’n, abu d’aya kawai yasani shine, da gaba d’aya zuciya da rayuwarsa yake sonta, zai kuma ci gaba da sonta har k’arshen rayuwarsa, saboda soyayyarta agaresa babban garkuwa ne dake k’arawa zuciyarsa k’wari.
Wani irin numfashi me tafiya da ajiyar zuciya ya sauk’e, ahankali ya sulale jikinsa ya kwanta akan gadon tare da lumshe kyawawan idanunsa, wanda suka sanja launi daga farare zuwa ja.
Sama da mintuna 10 ta d’auka tana aikin jujjuya spoon d’in abincin dake hannunta, duk kuwa ga yanda taso samawa kanta nutsuwa ta kasa, yayinda kuma ta kasa sa koda lomar abinci d’aya ne abakinta.
Tana nan ahaka kuwa harsu Abbou Jaheed suka kammala cin abincinsu suka tashi, hakan yasa daga ita sai Najeeb ne suka rage akan dining table d’in.
Wanda kuma gaba d’aya a ankare yake da yanayin Laylerh’n, duk da baisan asalin dalilin dayasa tasamu kanta ahakan ba, amma yaji ba dad’i saboda ko kad’an bayason ganin damuwa akan fuskarta.
Ahankali ya d’ago kansa tare da sauk’e idanunsa akanta.
Ganin yanda ta sadda kanta k’asa ne yasashi k’iran sunanta asanyaye, batare kuma daya d’auke idanunsa akanta ba.
Jin amo da kuma sautin muryarsa ne yasa ahankali ta d’ago kanta cikin muryarta da tayi sanyi sosae ta amsa masa, saidai kuma sam bata yarda ta sauk’e k’wayoyin idanunta acikin nasa ba, tayi hakanne kuma dan gudun kada ya karanci yanayinta.
“Tunanin me kike?�
Ya jefo mata tambayar da bata shirya amsa masa ba, saidai kuma gudun kada ya zurfafa har yakai ga gano asalin abunda ke damunnata ne yasa asanyaye tace. “Ba komai!�
“Kin tabbata?� Yafad’a yana me yawo da idanunsa akanta.
Kai ta jinjina masa alaman “Eh.�
“To kici abincinki idan kuma kin k’oshi kitashi kije ki kwanta dare yayi.� Ya fad’i maganar yana me kai dubansa ga agogon dake d’aure atsintsiyar hannunsa, wanda yake nuna k’arfe 8:45 pm.
Jin abunda yace dinne kuma yasata mik’ewa tsaye da sauri, domin dama neman hakan take, duk da cewar kuwa acikinta tanajin yunwa saidai bata da dama ko nutsuwar cin abinci, Jan kujeran da ta zauna baya tayi, cikin yanayin sanyin daya rusketa ta soma k’ok’arin barin wajen cin abincin.
Da wani irin kallo ya bita har ta fice daga cikin falon, ajiyar zuciya me k’arfi ya sauk’e tare da d’aukan bottle water ya soma sha.
Laylerh kuwa cikin yanayin sanyi ta k’arasa part d’innasu, ahankali ta tura k’ofar bedroom d’in ta shiga, direct gaban had’add’en dressing mirror ta nufa, hakanan tasamu kanta tana me k’urawa kyakkyawar innocent face d’inta idanu ta cikin madubin, take kuwa abubuwa da yawa suka shiga yawo akwanyarta, hannu tasa ta dafe k’irjinta dake dukan uku uku, hakanan takejin wani irin yanayin tsoro na sauk’ar mata, yayinda maganar auren Maleek d’in yayi mata tsaye acikin ranta, wanda yasa duk takejin komai ba dad’i.
“Mezai faru idan Yah M.Jay yayi aure? Then me auren nasa yake nufi? Rayuwa zaiyi da wata mace na har abada? kyakkyawar fuskarsa, da kuma murmushinsa, had’i da komae da komae nasa wata dabance zata ke gani, hakan na nufin kusancina dashi yazo k’arshe?� Abayyane tayiwa kanta duka tambayoyin, wanda kuma hakan yasa wasu irin hawaye masu zafi suka biyo kan k’uncinta, hak’ik’a tana da fata da kuma buri akan Mah Boo d’inta, dukkuwa da cewar akwae auren Najeeb akanta, amma koda da sau d’ayane bata tab’ajin d’igo d’aya na zazzafar soyayyarsa ya ragu acikin zuciyarta ba, akullum kuma tanajin cewa lallai watarana zasu kasance atare kamar yanda take gani amafarkinta yawancin lokuta, wani irin so takeyiwa Maleek tarasa, saidai tayi imani cewa zata iya sadaukar da komae na rayuwarta akansa.
Najeeb.
Ahankali ya turo k’ofar d’akin ya shigo, saidai kuma ganinta atsaye da yayi ne yasashi maida k’ofar ya rufe ahankali, jingina bayansa da jikin k’ofar d’akin yayi had’e da sauk’e idanunsa akan tsararriyar surar jikinta, duk da cewar kuwa tabawa k’ofar shigowa d’akin baya amma hakan baihanashi gane cewar kuka takeyi ba, gajiyayyun idanunsa masu d’auke da kasala ya lumshe, saboda yanda yakejin wani irin feelings na musamman akanta.
Anutse yasoma takawa zuwa gareta, saidai kuma yanayin yanda gaba d’aya tunaninta ya tafi zuwa wani waje na daban yasa sam bata ji motsin takunsa ba.
Isowarsa gareta da kuma yanda sassanyan k’amshin turarenta ya bugesa ne yasashi lumshe ido, tare da fesar da wani irin numfashi.
Ahankali cikin wani sabon yanayin daya samu kansa aciki, yasa hannayensa ya rik’o kafad’arta tare da juyo da ita hakan yasa jikinsu had’ewa waje d’aya.
Da sauri ta d’aga d’ara d’aran idanunta ta kalleshi domin kwata kwata bata kawo aranta cewar zai shigo d’akin yanzu ba.
Jefa idanunta acikin nasa da tayi ne kuma yasa tsikar jikinsa motsawa, yayinda kuma yaji wani irin abu na yawo ajikinsa.
Da idanunsa wanda suka d’an soma lumshewa, ya kalli y’an siraran hawayen dake kwance akan fuskarta, sake matso da jikinsa gab da nata yayi, wanda sanadin hakan kuma yasa numfashinsu gauraya waje d’aya.
Yanayin yanda take iya jiyo sautin bugun zuciyarsa ne kuma yasa ta lumshe idanunta.
Shi d’inma Najeeb da yakai k’ololuwa kasa jurewa yayi, har saida ya lumshe idanunsa, tare da kamo tafukan hannayenta, cikin wani irin sanyin yanayi ya d’aura bakinsa akan nata.
*19/1/2021*
*Note edit*
1/20/21, 8:26 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Writting By*
fatymasardauna
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.