Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: LAYLERH MALEEK.txt
Chapter 33 of 65
*Chapter 49*
Ahankali ta bud’e idanunta wanda suka share kusan one hour a kulle, cikin sauri tasanya hannunta ta dafe daidai saitin zuciyarta dake wani irin mummunan bugawa, yayinda kuma lokaci d’aya taji wani irin tsinkewar zuciya had’i da fad’uwar gaba me k’arfi ya ziyarceta.
“Subahanallah!!�
Tafad’a cikin wata irin muryarta da tayi sanyi sosae, Jin da tayi kaman ana buga mata guduma a tsakiyar kanta ne yasata tashi zaune, tare da zuro da k’afafunta k’asa.
Idanunta tad’an lumshe tare da sake dafe daidai saitin zuciyarta, da har yanzu ke cigaba da bugawa, tabbas batasan da yaushe ne bacci ya d’auketa ba, ita dai tasan cewa kafun yanzun ta rik’e wayartace a hannunta tana kallo.
Ahankali ta d’aga kanta ta kalli babban agogon bangon dake sak’ale acikin d’akin, ganin da tayi lokaci ya d’an ja ne yasa ta yunk’ura ta sauk’o daga kan gadon gaba d’aya.
Ahankali cikin rashin k’arfi da kuma kuzarin da ta samu kanta aciki ta wuce toilet.
Yanayin yanda k’aran fad’uwar motoci biyun suka cika gaba d’aya wajenne yayi sanadiyar dawowan hankalin mutane garesu, ganin irin mummunan accident d’in da akayi ne kuma yasa, hankalin jama’an dake wajen yayi mummunan tashi, domin tuni har d’aya daga cikin motocin tafara hayak’i.
Hakan yasa cikin gaggawa da kuma son ceto rayuka, Jama’a suka nufi wajen da motocin suke da gudu.
Lokaci d’aya wasu daga cikin mutanen suka soma k’ok’arin ciro Maleek da kuma d’ayan mitumin daya kasance shine matuk’in d’aya motar, yayinda wasu kuwa suka shiga k’iran emergency dan basu taimakon gaggawa.
Kasancewar motocin duk sun kwanta ne yasa da k’yar mutanen suka iya ciro ko wannensu daga cikin motarsa, saidai kuma abunda ya k’ara d’agawa jama’ar dake wajen hankali shine, babu mutum d’aya acikinsu dake numfashi, sannan gaba d’ayansu duk jini ya wanke musu fuska.
Salati da sallallami kawae jama’ar wajen keyi, domin ganin da sukayi ya nuna musu cewa, dukansu basa numfashi, da alaman ma cewa babu rai ajikinsu.
Nanfa wasu daga cikin mutanen dake tsaye awajen suka shiga duba motocin acewarsu ko zasu samu wayoyinsu da kuma ID card dan sanin ko sud’in su waye, ta yanda za’a samu asauk’ak’e asanar da y’an uwansu.
Cikin sa’a kuwa suka tsinci wayar Maleek da kuma ID card d’insa, abun mamakin kuwa wayarsa ko fashewa d’aya batayi ba, tana nan normal, hakama na d’ayan me motar saidai nashi screen d’in wayar ta d’an fashe kad’an.
Isowan Emergency wajen cikin gaggawa ne yasa mutanen suka taimaka musu wajen saka su Maleek d’in acikin mota, duka wayoyi da kuma ID card d’in da suka samu suka mik’awa ma’aikatan lafiyan.
Nanfa cikin gaggawa motar Emergency d’in ta kama hanya zuwa babban asibitin nan me suna Nizamiyye Hospital.
Yanayin yanda motar Emergency’n ke matsanancin gudu ne kuma yasa cikin y’an k’alilan d’in mintuna suka samu isowa cikin harabar babban asibitin.
Da wani irin sauri Doctor’s suka zo da irin gadon nan da ake d’aukan marassa lafiya acikinsa.
Anan kan gadon aka d’auki kowannensu cike dason basu taimakon gaggawa kaitsaye aka wuce dasu Intensive Care Unit wato (ICU) dan basu taimakon gaggawa kasancewar duk acikinsu babu wanda yake numfashi.
Likitotine wanda ak’alla zasu kai guda 6 suka duk’ufa akan Maleek wanda kansa keta faman zubda jini, tabbas babu numfashi ajikinsa, amma kuma wani babban abun mamakin shine zuciyarsa na bugawa, al’amarin daya d’aure musu kai kenan, sanin kuma da sukayi cewar Idan har basu dage wajen yin k’ok’arin dawo da numfashinsa ba to tabbas bugun zuciyartasa ma zai iya tsayawa, hakan kuma zai iya jawo sanadiyar rasa rayuwarsa gaba d’aya, nan fa cikin azama suka shiga k’ok’arin tsaida jinin dake zuba akansa, kasancewar ya bugu sosae akannasa shiyasa yake ta zubarda jini ba k’akk’autawa, Uwa uba kuma duk glasses d’in motar ya caccake masa jiki.
Sab’anin abokin accident d’in nasa da buguwa kawae ya samu, akai da kuma k’afarsa, saidai kuma buguwar k’afartasa yafi na ko ina muni, dan k’afartasa taji ciwo sosae, saidai shi bashi da wata matsala bayan wannan, Inda kuma cikin sauk’i likitotin dake kansa suka samu daman ceto numfashinsa, ganin kuma da sukayi cewar akoda yaushe zai iya dawowa cikin hayyacinsa ne, yasa suka kaishi wani d’aki na daban.
Yayinda doctors d’in dake aiki akan Maleek kuwa suka ci gaba da gudanar da aikinsu, domin har yanzu sun kasa samo numfashin Maleek d’in.
Laylerh
Ahankali ta bud’e murfin k’ofar bathroom d’in ta fito, yayinda fuskarta da kuma hannaye da k’afafunta ke d’auke da danshin ruwa, wanda hakan nuna cewar alwala ta d’auro acikin toilet d’in.
Cikin yanayin sanyin jikin da takejin kanta aciki ta k’arasa gaban drawer’nta, ta ciro wani d’an madaidaicin Hijab d’inta ta saka, juyawa tayi tare da jingina bayanta da jikin drawer’n ahankali ta lumshe idanunta, wanda tun d’azu takejin k’walla nason taruwa acikinsu wanda kuma sam batasan dalilin hakan ba, gaba d’aya tun tashinta abacci takejin mood d’inta ya sauya batare kuma da tasan dalilin hakan ba, fad’uwar gaba take taji, da wani irin tsoro wanda batasan daga inane yake b’ullowa ba, babban abunda ke k’ara da gula mata lissafi kuwa shine tunanin Maleek dake fad’o mata akai akai, wanda kuma hakanne ke haifar mata da k’arin bugun zuciya.
“Yah Allah Kasa komai yazomin cikin sauk’i, Allah Kaga zuciyata ayanzu gab take da bugawa, ina rok’oka kada ka tabbatar da mummunan mafarkin da nayi akan Yah M.Jay, Ya Allah Kaduba maraicin mu!!!�
Tafad’i hakan cikin muryarta da tayi rauni sosai, tare dasa d’an yatsanta ta share hawayen dake k’ok’arin sauk’a daga cikin idanunta.
Hak’ik’a ayanzu nutsuwar zuciya da kuma farinciki takeso, domin su kad’aice zasu kore mata tsanancin tsoron da takeji.
Asanyaye cikin bawa kanta k’warin guiwa ta k’arasa gaban d’an madaidaicin carpet d’in dake shumfud’e a gefen gadonta, wanda kuma an shumfud’a carpet d’inne musamman dan akeyin Sallah akansa.
Daidaita tsayuwarta akan carpet d’in tayi, tare fuskantar gabas ta tada sallah’n azahar wanda tuni masallacin dake gefen gidannasu har sun shiga salla’n.
Kasancewar ayanzun kusan k’arfe 1 da wasu y’an mintuna ake nema.
Koda ta idar da sallan kuwa anan kan sallayan ta kwanta, duk da cewar tanajin yunwa na k’wak’ulan cikinta amma batajin zata iya saka ko wani irin abinci acikinta.
After 1hour.
Kusan atare gaba d’aya likitotin da har yanzu ke tsaye akan Maleek d’in suka d’ago kansu suka kalli juna, yayinda kowannensu yanayin fuskarsa ke d’auke da matsanancin damuwa, tabbas sunsha wahala matuk’a wajen ganin Maleek d’in ya tsira da numfashi, sunkuma yi sa’a domin Allah Ya dafa musu wajen ganin sun dawo masa da numfashinsa, duk da cewar bai farfad’o ya dawo hayyacinsa ba, amma tabbas suna saka ran farfad’owarsa akoda yaushe, ganin da sukayi kuma ya bugu sosai akansa da kuma sauran sassan jikinsa ne yasa suka d’anyi masa gwaje gwaje dan tabbatar da lafiyar jiki da kuma na kansa, sunji dad’i k’warai da sukaga cewar buguwan da yayi akannasa bai tab’a masa kansa ba, saidai wani babban matsala da suka gani daga wani waje na dabanne yasa su shiga alhini tare dajin matsanancin tausayin Maleek d’in ya cika musu zuciya.
D’aya daga cikin doctors d’inne yayi masa duk wasu alluran da suka dace, sannan sukayi treating duk wani ciwo dake jikinsa, duk dama ciwukan nasa y’an k’ananan yankane daya samu ta sanadin glasses d’in da suka d’an cakesa.
Nanfa biyu daga cikin doctors d’in suka tura gadon da yake cikin wani special room, inda babu yawan hayaniya sosai.
After 2hours
Acan gida kuwa Abbou Jaheed ne zaune acikin katafaren falonsa wanda yaji komai da komai na more rayuwa, domin kuwa falo ne wanda ya amsa sunan falo, irin na manya manyan masu kud’i da kuma matsayi.
Zaune yake akan d’aya daga cikin luntsuma luntsuman kujerun dake cikin falon, agabansa kuwa wani babban stool ne wanda samansa ke d’auke da wasu invitations card’s masu yawan gaske, d’aya bayan d’aya kuwa haka yake d’aukan cards d’in yana dubawa, da dukkan alamu kuma katunan dake gabannasa na d’aurin auren Maleek ne.
Turo k’ofar falon da kuma sallaman da yaji anyi ne yasashi d’ago kansa, abakinsa kuwa yana me amsa sallaman, da Abbou Khareem da kuma Fou’ad ne sukayi ta.
Ganinsu da yayine yasashi d’an sakin murmushi, tare da cewa. “Kuyi hak’uri na d’ago ku akan uzururrukan da kukeyi.�
Murmushi dukansu sukayi tare da k’arasowa cikin falon, wato inda Abbou Jaheed d’in ke zaune.
“Babu komae Yayah Allah Dai yasa muji alkhairi.�
Cewar Abbou Kareem fuskarsa d’auke da yalwatacciyar murmushi.
“Insha Allah Ma alkhairi ne.� Abbou Jaheed ya fad’a yana me d’an gyara zama.
Fou’ad kuwa dake k’ok’arin zama akan had’adden sofan dake malale atsakiyar falon, cikin girmamawa yace.
“Abbou barka da gida.�
“Yauwa barka dae Malam Fou’ad ya aiki, da kuma fama da Jama’a?.�
“Lafiya Alhamdulillah.�
Fou’ad ya amsa yana me d’an shafa kansa.
“To Masha Allah dama haka akeso.�
Abbou Jaheed ya fad’a yana me k’ok’arin har had’a cards d’in dake zube agabansa.
Shiru sukayi na d’an wani lokaci kafun Abbou Jaheed d’in ya zaro wasu daga cikin invitations cards d’in dake gabansa ya mik’awa kowannensu, fuskarsa d’auke da damuwar da sam ya kasa b’oyeta afili da kuma bad’ininsa yace.
“Ga katin auren Maleek nan, d’azu way’anda na bawa kwangilan bugawa suka kawomin, abunda yasa na k’iraku kuma kenan, domin nasan kuma kunada naku jama’an da zaku gayyata, gasunan sai ku d’ebi wanda zai isheku.� Ya k’are maganar yana me tura musu katunan gabansu.
Jin abunda Abbou Jaheed d’in ya fad’ane kuma yasa, Fou’ad d’ago kai ahankali ya maida dubansa ga Abbou Jaheed d’in, wanda take ya karanci zallan damuwa akan fuskarsa, tabbas yasan abunda Abbou Jaheed d’in keyi k’arfin haline kawae, saboda kallo d’aya zakayi masa kafahimci cewa yana cikin damuwar rashin ganin d’ansa.
Ajiyar zuciya ya sauk’e kana jikinsa amatuk’ar sanyaye, cikin ladabi da kuma sanyin murya ta yanda ya tabbatar cewa Abbou Jaheed d’in zai fahimcesa yace.
“Kayi hak’uri da abunda zan fad’a Abbou domin nasan ba lallaine yayi maka dad’i ba, saidai kuma ya zama
dole na fad’a maka cewar kwata kwata Maleek bayason auren nan, domin saboda hakanne ma yaje ya b’oye kansa awani waje, wajen da babu wanda yasani acikin mu, hak’ik’a inajin tsoron abunda zaije ya dawo bayan an d’aura aurennan, saboda akullum Maleek yana ikirarin cewa shi bazai tab’a zama da wata mace ba, burinshi akoda yaushe shine yayi rayuwarsa shi kad’ai, please Abbou Dan Allah Ajanye maganar auren nan.�
Murmushi me d’auke da dattako Abbou Jaheed yayi, tare da d’ago kansa ya kalli Fou’ad d’in.
Tabbas shi kansa ya jima da fara irin wannan tunanin, amma kuma saidai yasan ko kad’an babu alfano acikin tunanin nasa, barin cikakken Namiji me lafiya kamar Maleek babu aure sam ba daidai bane, saboda arayuwar ko wani d’a Namiji me lafiya yana buk’atar Mace, domin Mace itace duk wani ginshik’in jin dad’i, saida Mace arayuwar ko wani Namiji zai kasance acikin farinciki, tabbas Mace itace komai na rayuwar d’a Namiji, domin saida mace ne kowani Namiji zaisan wanene shi.
Ajiyar zuciya Abbou Jaheed d’in ya sauk’e, tare dayin gyaran murya, cikin tausasa kalamansa yanda yake da yak’inin cewa Fou’ad d’in zai gamsu yace.
“Bawai ina son tursasawa Maleek koyi masa auren dole bane, ina duba abunda ya dace ne, hak’ik’a burin kowani uba shine yaga ya aurar da y’ay’ansa bawai y’ay’ansa mata ba kawae harda maza, domin barin cikakken Namiji baligi agida wanda ya haura shekaru 30 ba daidai bane, matuk’ar yana da lafiya kuma yana da halin yin aure to yayi kawai, saidai kuma idan yana da hujjar cewa bazae tab’a kusantar zina ba, wannan zai iya zama yayi rayuwarsa shi kad’ai, tabbas ada bandamu akan Maleek yayi aure ko a’a ba, domin duk da cewa zuciya bata da k’ashi, amma Ina da yak’ini akansa, tabbas Ina da yak’inin cewa ban haifi fasik’i ba, hak’ik’a najima da bawa Maleek zab’i akan ya nemo matar da yakeson aura, amma yayi watsi da magana ta, haka na hak’ura na k’yalesa, nabarsa ne kuma saboda inaso naga iyaka gudun ruwansa, saboda tabbaci da nake dashi akansa, saidai kuma lokaci d’aya ya ruguza duk wata yarda ta da nake dashi akansa, nagansa da idanuna ya dawo gida acikin maye, cikin k’azamammen yanayin da duk wani Uba na duniya bazai so yaga d’ansa aciki ba, tabbas nasan Ilan maye, yakansa mutum ya aikata komai, ciki kuma harda zina, to Fou’ad ka gayamin tayaya zanbar tilon d’ana Maleek ya kasance acikin irin wannan halin? wannan dalilin shiyasa na yanke hukuncin d’aura masa aure ko da yana so ko bayaso, bankuma yi hakan don banason sa ba, saidan Ina guje masa fad’awa halaka da kuma tsinuwar Allah..�
Sosae jikin Fou’ad yayi sanyi asakamakon jin kalamai da kuma hujjar Abbou Jaheed nason yiwa Maleek aure, hak’ik’a ada yana ganin kamar cewa Abbou Jaheed d’in nason tauye Maleek ne, amma ayanzu tabbas ya fahimci komai, domin shi kansa yana da yak’inin cewa matuk’ar Maleek d’in ya fara shaye shaye to watarana maye zata iya sawa ya aikata ba daidaiba, domin sarai yasan abokinnasa yana da k’arfin sha’awa.
Baki ya bud’e da niyar cewa wani abu amma kuma saidai k’iran da ya shigo wayar Abbou Jaheed ne yasashi tsuke bakinsa.
Abbou Jaheed kuwa akaron farko kenan da yaji k’iran waya ya tsinkar masa da zuciya.
Asanyaye ya kai hannu ya d’aga wayar, duk da cewar bakuwar number ya gani amma hakan bai hanashi d’agawa ba tare da kara wayar akan kunnensa, sallaman da akayi masa ya amsa, saidai kuma jin abunda wanda ke kan wayar ke fad’ane yasashi jin wani irin matsanancin fad’uwar gaba da kuma tashin hankali me tsanani wanda har saida ya kaisa ga mik’ewa tsaye, cikin kid’ima da kuma rud’ewa ya ambaci kalmar “Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un!!!�
Batare kuma daya daidaita nutsuwarsa ba yasaki wayar tasa ta fad’i k’asa.
Hakan da yayin kuwa shiya saka hankalin su Abbou Khareem da kuma Fou’ad yayi wani irin masifaffen tashi, cikin yanayin mamaki da kuma rud’ewa suka shiga tambayarsa ko lafiya.
Kasa amsa musu yayi sai sa hannu da yayi ya dafe daedae saitin zuciyarsa, da kuma k’irjinsa dake bugawa sosae, ganin hakane yasa Fou’ad nufar wajen fridge ya d’auko goran ruwa me sanyi, mik’awa Abbou Jaheed d’in goran ruwan yayi, cikin yanayin damuwa yace.
“Abbou lafiya meyake faruwa ne?.�
Wani irin numfashi Abbou Jaheed da gaba d’aya hankalinsa baya jikinsa yayi, cikin muryarsa da ta sark’e yace.
“Maleek ne yayi accident, Khareem Maleek d’ana yayi accident, baisan inda kansa yake ba, Innalillahi Wa’inna Ilaihirraju’un, Ya Allah Kasa kada na zamo silar rasa rayuwar.......�
Cikin tashin hankali Abbou Khareem yasa hannunsa ya toshewa Yayan nasa baki, kansa ya d’an girgiza cike dason samarwa d’an uwannasa nutsuwa yace.
“Kada kace haka Yayah Allah Yana tare damu, yafi kowa sanin niya da kuma nufin dake cikin zuciyarka, awani asibiti Maleek d’in yake, mu hanzarta zuwa dansanin halin da yake ciki.�
“Nizamiyye hospital!� Abbou Jaheed d’in ya fad’a da muryarsa wanda take fitar da zallan tashin hankalin da yake ciki.
Yayinda Fou’ad kuwa tsabar shocking d’in da ya samu kansa aciki, kasa furta komai yayi, sai jikinsa dake ta faman karkarwa.
Hannun Abbou Jaheed d’in Abbou Khareem ya kamo cikin dauriya yace.
“Muje muje lokaci na k’urewa.�
Haka suka fice daga cikin falon dukansu babu wanda yake da gamsashshiyar nutsuwa atattare dashi, ko awajen tuk’in mota ma Fou’ad ne ya iya dauriyan tuk’asu, saidai kuma irin gudun da yake tsulawa yasa duk wanda ya ga motar tasu saidai ya kauce ya basu hanya.
Yanayin yanda Fou’ad d’in ke gudu kaman zai tashi sama ne yasa cikin mintuna kad’an suka iso farfajiyar asibitin.
Ko tsayawa gama daidai ta parking baiyi haka suka fito cikin tashin hankali sukayi cikin asibitin, murafen motar ma a bud’e suka barsu.
Abbou Khareem ne ya d’auki wayar Abbou Jaheed d’in ya k’ira numbern da aka k’irasu dashi d’azun dan sanin inda aka ajiye Maleek d’in.
Da yake kuma numbern na d’aya daga cikin doctors d’in asibitin da suka karb’i Maleek d’inne, yasa cikin sauk’i Doctorn ya musu kwatancen office d’insa, suna zuwa kuwa suka samu duka doctors d’in atare awaje d’aya.
Ganin irin tashin hankali da kuma damuwan dake d’auke akan fuskokinsu ne yasa Doctors d’in soma k’ok’arin kwantar musu da hankali.
Ta hanyar ce musu Maleek d’in yana nan lafiya.
“Kufad’amin idan wani abu ya samu d’ana, yana Ina ku kaini naga Maleek, shi kad’aine d’an dana Haifa aduniya Dan Allah ku fad’amin cewa Maleek yana darai bai mutu ba!!!� Abbou Jaheed ya fad’i hakan cikin tashin hankalin da yakejin kansa aciki.
Murmushi Dr.Mouhammad yayi, wanda shine babban likitan dake kan case d’in Maleek d’in, cikin son kwantarwa da Abbou Jaheed d’in hankali yace.
“Alhaji Jaheed Gwani ka kwantar da hankalinka domin d’anka bai mutu ba, domin tabbatar da hakan kuwa kana iya Bina muje kaga d’anka.�
Ae ma kafun Dr Mouhammad ya rufe bakinsa, tuni Abbou Jaheed yace.
“Muje Doctor muje nagansa.�
Shigewa gaba Dr Mouhammad yayi, yayinda su Abbou Jaheed suka rufa masa baya.
Kaitsaye d’akin da Maleek d’in ke kwance suka nufa, bud’e musu k’ofar d’akin Dr. Mouhammad yayi tare dayi musu alama akan su shiga, riga rigen shiga kuwa sukayi, yayinda kuma suna shiga suka sauk’e idanunsu akan Maleek d’in dake kwance flat akan gado, kansa nad’e da bandage.
Cikin sauri Abbou Jaheed ya k’arasa kusa da gadon, tare dasa hannayensa duka biyu ya rungume Maleek d’in, lokaci guda yaji wasu irin hawaye sun cika idanunsa, matsanancin tausayin d’annasa ne ya kamasa, hakan yasa ya d’aura kansa akirjin Maleek d’in daidai inda zuciyarsa take, wani irin ajiar zuciya me k’arfi ya sauk’e alokacin da kunnuwansa suka jiye masa sautin bugun zuciyar Maleek d’in, cikin zuciyarsa yace.
“Alhamdulillah!�
K’arasowa wajen Maleek d’in su Abbou Khareem da Fou’ad sukayi, cike da tausayin Maleek d’in suka shafa kansa dake lik’e da bandage.
Gaba d’ayansu tausayi suka bawa Dr.Mouhammad hakan yasa shi d’anyin gyaran murya cikin kulawa yace.
“Ayanzu Maleek hutu yake da buk’ata, bazan hanaku zama awajensa ba, amma saidai ku kiyaye yin surutu, sannan zai iya bud’e idanunsa any time, zuwa anjima kad’an akwai alluran da zanzo na sake yi masa, so dan Allah Ku kula sosae.�
“Insha Allah Zamu kula doctor.�
Cewar Fou’ad dake k’ok’arin maida k’wallan dake cikin idanunsa.
Kai Dr.Mouhammad ya jinjina, anutse yasa kai ya fice daga cikin d’akin, zuciyarsa cike da alhinin ta yanda zai fara fad’awa Alhaji Jaheed abunda ya samu d’ansa sanadiyar accident d’in da yayi.
Fitan Dr. Mouhammad ne yasa su Abbou Jaheed d’in neman waje suka zauna, nan fa Abbou Khareem ya zaro wayarsa dake cikin aljihunsa, ya turawa Oum Ayush sak’on cewa Maleek d’in yayi accident, bayan ya tura mata sak’onne kuma ya turawa Momy da kuma Najeeb suma, daga haka baisake turawa kowa ba ya ajiye wayartasa.
Acan gida kuwa Oum Ayush dake zaune tana kallo, Jin alamar shigowan sak’o cikin wayarta ne yasa ta d’aukan wayar ta duba, saidai kuma ganin abunda ke rubuce ajikin sak’on ba k’aramin d’aga mata hankali yayi ba, take cikin matsanancin damuwan da ta samu kanta aciki tayi dialing numbern Abbou Khareem d’in, cikin sa’a kuwa tana k’ira ya d’aga, Jin yanda hankalinta ya tashi sosae ne kuma yasashi soma k’ok’arin kwantar mata da hankali, ta hanyar fad’a mata cewar Maleek d’in bai wani ji ciwo sosai ba.
Nantake kuwa tace masa gatanan zuwa.
“Kitaho da Laylerh.� Abunda ya fad’a kenan ak’arshe ya kashe wayar.
Cikin gaggawa kuwa Oum Ayush ta d’auko mayafinta, tare da makullin motar ta, koda ta fito daga sashin nasu kai tsaye sashin su Laylerh’n ta nufa.
Kusan sau biyu tayi knocking k’ofar falon amma shiru ba’a amsa mata ba, kasancewar damuwa ne kwance aranta, hakan yasa batare da wani tunani ba ta tura k’ofar falon ta shiga, ganin da tayi kuma babu kowa acikin falonne yasa ta shiga k’walawa Laylerh’n k’ira.
Laylerh kuwa da har yanzun ke kwance anan kan carpet d’in da tayi sallah, kamar daga sama taji muryan Oum Ayush na kwad’a mata k’ira, hakan yasa cikin sauri ta mik’e tsaye, tare da bud’e k’ofar d’akin ta fice.
Ganinta sanye da Hijab ne yasa Oum Ayush kamo hannunta, cikin muryarta da tayi sanyi sosae tace.
“Zo muje ki rakani wani waje Laylerh.�
Batare kuma da ta jira me Laylerh’n zata ceba ta kamo hannunta suka nufi hanyar fita daga falon.
Fuskar Laylerh’n d’auke da mamaki had’i da rud’u tace.
“Oum Ayush Ina zamuje?, bani da takalmi kibari na d’auko takalmi na.�
Jin abunda tace ne yasa Oum Ayush tsayawa, tare da cewa.
“Kiyi sauri ki d’auko takalmin naki.�
Ganin damuwa kwance akan fuskar Oum Ayush d’inne yasa Laylerh juyawa cikin sabon faduwar gaban da ta samu kanta aciki ta koma cikin d’aki, wani black half cover shoe me tsananin kyau tasa ak’afanta, cikin sauri ta fito.
Sake kamo hannunta Oum Ayush tayi suka fice daga cikin falon.
Ita dai kam kamar rak’umi da akala haka take bin bayan Oum Ayush d’in.
Har saida suka iso jikin mota kafun Oum Ayus d’in ta sake mata hannu.
Nanfa Oum Ayush ta shiga wajen driver itakuwa ta shiga gefen me zaman banza.
Da wani irin speed Oum Ayush ta ja motar yayinda maigadi ya wangale musu gate suka hau saman shumfud’add’en titin dake malale a k’ofar gidan.
Tunda suka shiga motar Laylerh ke kallon Oum Ayush da gaba d’aya yanayinta ya nuna cewa tana cikin damuwa.
Asanyaye kana cikin voice d’inta dake cracking tace.
“Oum tun safe k’irjina bugawa yake, gaba na yana ta fad’uwa, tsoro nakeji matsananci, Dan Allah Oum kifad’amin meke faruwa? Kuma Ina zamuje haka?.�
Shiru Oum Ayush tayi ta kasa amsawa Laylerh’n tambayoyinta, daidai lokacin kuwa suka kawo cikin asibitin.
Ganinsu acikin asibiti ne kuma yasa Laylerh zaro manya manyan idanunta, cikin matsanancin tsoro tace.
“Wayene bashi da lafiya Oum, Dan Allah Karki cemin Yah M.Jay ne, karki cemin mafarkina na jiya ne yakeson zama gaskiya, pleaseee.....�
da katawa da tafiyan Oum Ayush tayi tare da juyowa ta fuskanci Laylerh’n, cikin muryarta da yayi sanyi sosae tace.
“Shi ne Laylerh Maleek ne yayi accident!�
Wani irin bugawa zuciyar Laylerh tayi wanda yayi sanadiyar durk’ushe wanta awajen, tare da zub’e guiwowinta ak’asa.
8February/2021
*7:30 pm*
2/13/21, 7:53 AM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Writting By*
fatymasardauna
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.