Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: LAYLERH MALEEK.txt
Chapter 5 of 65
*Chapter 12*
Idanunsa ya rumtse lokaci É—aya yaji duniyar na neman juya masa, bugun zuciya da numfashinsa ne suka nemi tsayawa sakamakon jin kalaman Abbu'n, yayinda shock É—in daya shiga yasa shi kasa motsa koda Æ´ar yatsar sa.
Wanda hakan yasa yanayinsa da nata suka kasance alokaci ɗaya, tamkar diran aradu haka taji sauƙan kalaman Abbu'n acikin kunnuwanta, manya manyan idanunta wanda alokaci ɗaya suka sauya launi ta zazzaro waje, jin maganganun Abbu Jaheed ɗin yasa zuciyarta yin nauyi, take wasu irin abubuwa suka shiga haukata mata tunani da nutsuwarta, ahankali ta soma girgiza kanta, yayinda sabin zafafan hawayen da suka cika idanunta suka samu daman gangarowa kan fuskarta, gaba ɗaya jikinta ya ɗauki rawa, cikin wata irin sarƙaƙƙiyar murya wanda take dauke da cracking tace. "A...b..b.u..." Katseta daga maganan da take ƙoƙarin yi ɗin Abbou yayi cikin tsananin tausayinta da kuma tausayin maraicinta da yakeyi yace.
"Ki yarda dani Laylerh bazan taɓa zaɓa miki mijin da zai cutar dake ba, haka kuma amatsayina na Uba dole ne na zaɓa miki Mijin da zai zamo *GARKUWA* agareki, wanda zai share miki dukkan kukanki, ya kuma hanaki tuna cewar ke marainiya ce, Farincikin ki akullum shi nake burin gani Laylerh, burina ki samu miji nagari ki kumayi zaman aure nagartacce, domin burin kowani Uba aduniya shine ya aurar da ƴarsa ga Namiji mafi nagarta da halin ƙwarai, wanda ko bayan ransa zai kula masa da ɗiyarsa!." Ɗan numfasawa Abbun yayi tare da sauƙe ajiyar zuciya. Cikin sanyi ya cigaba da cewa. "Alƙawari na ɗauka Laylerh, alkawarin bawa Najeeb aurenki tun kina da shekaru 11 aduniya, ayanzu kin kawo girma saboda haka nake fatan cika wannan alƙawarin dana ɗauka." Damƙe hannunta yayi ƙam cikin kulawa yace. "Kada kicemin a'a Laylerh, kada ki watsamin ƙasa ta hanyar ƙin karɓan zaɓin da nayi miki, duk da cewar bana fatan yi miki dole arayuwa, saboda haka kina da zaɓi, idan har baki aminta da Najeeb ba, kada ki ɓoyemin ki faɗa agabana kuma agaban kowa da kowa, ina me tabbatar miki da ashirye nake na bawa Aminina Alhaji Ahmad da kuma ɗansa Najeeb haƙuri, domin alƙawari ne dana ɗaukawa kaina cewar bazan taɓa miki dole ba, koda kuwa umarni nabaki kika shallake, kada ki ɓoye abun dake cikin rai da zuciyarki Laylerh, lallai kema kina da zaɓi!." Abbu Jaheed ya faɗi maganar cikin bayyana zallan abun dake cikin zuciyarsa.
Hawayen dake gudu akan fuskarta kaman an kunna famfo ne suka kasa tsayawa, lokaci ɗaya duk wani tunani da nutsuwarta suka kau, yayinda bugun zuciyarta ya tsananta, har takai ga ƙirjinta gaba ɗaya na amsawa, wani irin shuuuu haka takeji acikin kunnenta kaman wanda aka watsa mata ruwa, laɓɓa da harshenta ne sukayi nauyin da har takai ga ta kasa motsa su.
Najeeb da tunda aka fara maganan ya shiga shock zuba mata idanunsa yayi, lokaci ɗaya yaji komai na kansa na warwarewa, ko da wasa bai taɓa tunanin samun auren Laylerh'n zaizo masa asauƙi har haka ba, shi kaɗai yasan abun da yakeji akan Laylerh, wanda bai gama tabbatar da cewar zuciyarsa ta kamu da son Laylerh'n ba saida Abbu yayi wannan maganan, wanda shima a iyaka tsawon rayuwarsa baisan da ita ba. *"LAYLERH"* Abbou Jaheed yaƙira sunanta, domin gaba ɗaya ya lura da yanayin yanda jikinta ke rawa, ga kuma ruwan hawayen da yake ta sauƙa akan kyakkyawar fuskarta, hakanne yasa lokaci ɗaya yaji zuciyarsa ta karye, yayinda yanayin damuwa ta maye gurbin fuskarsa, zallan fargaba ya bayyana acikin idanunsa. Ɗaga idanunnata dake cike da ƙwalla tayi ta kalli Abbou'n, wanda hakan ke nuna cewar batajin zata iya furta wata kalma daga bakinta. Maleek Tamkar yanda bugun zuciyarsa da numfashinsa ke ƙoƙarin tsayawa haka ma tunaninsa, akaron farko kenan daya samu kansa cikin irin wannan condition ɗin, the first time kenan dayaji zuciyarsa na barazanar tarwatsewa, yayinda kuma ƙirjinsa yayi masa nauyi, akaron farko kenan dayaji yana son jin wani abu daga bakinta, wanda yayi imani cewa jin hakan daidai yake da ruguza gaba ɗaya shafin rayuwarsa, wanda ananne kuma littafin sabuwar ƙaddararsa zai buɗe, wanda baya tunanin acikinsa akwai wani sassauci, idanunsa wanda sukayi jajur kaman jan garwashi ya buɗe, akaron farko kenan da tun zamansa awajen ya ɗago idanunsa ya kalleta, haƙiƙa da ace wani daga cikinsu zai kallesa, to da yagano haƙiƙanin abun dake cikin rai da zuciyarsa. wanda ya jima yana ɓoyewa, tabbas yaji ajikinsa cewa ayau wani babi nadaga cikin littafin Ƙaddaran rayuwarsa ƙoƙarin buɗewa, wanda ya tabbatar cewa babine na Ƙaddara mafi girma me matuƙar wahalarwa da kuma tsuma zuciya. Kamar yanda ya zuba mata ido kuwa haka dukanninsu suka zuba mata nasu idanun, harda Momy kuwa wacce gaba ɗaya akalan tunaninta ƙoƙarin soma sanjawa. Ajiyar zuciya Abbou Jaheed ya sauƙe, tabbas ya karanci wani yanayi daga kan fuskar Laylerh'n, wanda kusan shi kaɗai ma ya isa nusar dashi abun dake cikin zuciyarta, gaba ɗaya jikinsa ne yayi sanyi, hakanne kuwa ya sashi ɗan lumshe idanunsa. Cikin sanyi haɗi da raunin daya samu nadaga ƙwarin guiwarsa ya ɗan shafa kan Laylerh'n, atausashe yace "Kinsan banason kukanki ko kaɗan, saboda haka ki share hawayenki, domin ni bazan taɓa yi miki dole akan abun da ba kya so ba, saidai kuma inason kisani, bazan taɓa miki zaɓin danasan zai cutar da rayuwarki ba, nafahimci dukkan yanayinki Laylerh saboda haka kibar kuka!." Asanyaye ya ƙarasa maganar, haɗe da ɗan jan kujeran dayake kai baya, ya miƙe tsaye, lokaci ɗaya yasoma ƙoƙarin barin dining area'n. Ganin hakane yasa ta sadda kanta ƙasa, sosai zuciyarta ke bugawa, yayinda gaba ɗaya duk wani kafar sadarwa na jikinta yayi sanyi, abubuwa da yawa ne ke yawo acikin zuciya da tunaninta wanda tayi imani cewa nan gaba kaɗan suna iya jikkata mata zuciya. Amatuƙar sanyaye ta juyo ta kalli Abbou wanda yake gab da barin dining area'n, bazata iya jurewa ba, domin gaba ɗaya rauni ya cika zuciyarta, cikin wani irin matsanancin kuka daya ciwota, ta miƙe tsaye da wani irin gudu taje ta faɗa jikin Abbun, tare da rungumesa ta baya, wani irin fitinannen kuka ta saki me ratsa zuciya, cikin kukan haɗi da muryarta da bata fita da kyau tace. "NA AMINCE Abbou, Na amince, bana fatan na kasance me butulci agareka ba, da nayi hakan kuwa Abbou gwara na rasa raina, Na amince da duk wani zaɓinka agareni zan rayu aduk yanda kaso......" Kukane ya sarƙe mata numfashi hakan yasa ta sake rungume Abbou Jaheed ɗin ƙaƙam. Tabbas maganganunta daidai suke da zuban wuta ajikinsa, haka kuma daidai suke da soyewa haɗi da ƙuntatar zuciyarsa, idanunsa ya rumtse da ƙarfi, take kuma jikinsa ya soma wani irin ɓari, wani irin mahaukacin yanayi ya samu kansa aciki me wuyar fassaruwa, wanda da ace yasan zai samu kansa acikin irin yanayin, to da koda wasa bazai sake ƙafarsa tatako cikin Nigeria ba, wanda hakan gashi ya zamanto silar rugujewar ƘUNDIN RAYUWARSA. Hawayen dake cikin idanun Abbou Jaheed ne suka samu daman zubowa kan fuskarsa wanda shi kansa bai ankara da hakan ba saida suka samu daman zubowa, da sauri yasa hannunsa ya goge hawayen, tare da ɗan juyowa ya shiga shafa kan Laylerh'n, yayinda yakejin wani irin farinciki na ratsa zuciyarsa, cikin son bayyana zallan farincikin da yake ciki yace. "Masha Allah! Allah Yayiwa rayuwarki albarka, yasaki acikin farinciki kamar yanda kika sani ayanzu, ina me miki fatan nasara da kuma cigaban rayuwa, insha Allah Bazakiyi danasanin zaɓin dana miki ba, domin Najeeb ma ɗan uwa kuma Yaya yake awajenki, Nagode Laylerh Allah ya miki albarka!." Ya faɗi maganar yana me shafa bayanta, dan har yanzu kuka take me tsuma zuciya. kukan da duk wanda ya jisa saiya tausaya mata, kukan da ya zamanto tamkar sauƙan yayyafin ruwan zafi acikin kunnuwan Maleek, kukan dake motsa masa zuciyarsa wanda ke cike da zogi haɗi da zallar ƙuna, kukan da raɗaɗi da kuma zafinsa ke ƙona zuciyar Maleek, kukan da yake neman zautar dashi haɗi da fitar dashi hayyacinsa, kukan dayafi komai hautsuna tunaninsa, bayajin zai iya jurewa domin hawayenta azabtar dashi suke, wanda hakanne yasa take wani zazzafan ciwon kai ya rufesa, hakanne ya sashi miƙewa tsaye batare da yana iya kallon gabansa ba ya nufi hanyar barin dining, gaba ɗaya jikinsa ya sake, yayinda zallan damuwa ya bayyana atattare da duk wani yanayinsa, idanunsa ne suka kaɗa sukai jajur kaman wuta, duk da kuwa cewar dishi dishi yake gani haka ya nufi side ɗinsa. Najeeb kuwa da kwata kwata yakasa ɗauke idanunsa akan Laylerh dake kuka, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da lumshe idanunsa, wani haɗaɗɗen yanayi yakejin kansa aciki wanda hakan yasa murmushi bayyana akan fuskarsa, take yasoma hasashen wata duniya ta daban, wanda yake da tabbacin zai samu kansa aciki matuƙar yakasance tare da Laylerh, tabbas ya jima da sanin cewa Laylerh'n tana da wani irin sirrin kyau nata na musamman, musamman yanayin tsarin halittar jikinta wanda babu wani ɗa namiji da zai iya kallo ya kau da kansa, Laylerh tayi daidai da choice of mind ɗinsa, komai nata is natural, still murmushi ya sake tare da soma ɗan jujjuya kujeran daya ke kai, hakanan yakejin wani irin fitinannen ƙaunarta na ratsa duk jikinsa, haƙiƙa shi kansa bai gamsar da kansa cewar Laylerh zaɓinsa bane sai yau, da yakejin ƙaunarta na huda dukkan sassan jikinsa yana shiga jininsa. Jin taƙi daina kukan nata ne yasa Abbou Jaheed ɗan ɗagota daga jikinsa, cikin lallashi haɗi da ƙaunarta yace. "Kukan namiye ne haka Laylerh? badai kin aminta da zaɓin dana miki ba?." Cikin sheshsheƙan kukan ta jinjina masa kai alaman "Eh." Murmushi Abboun yayi mata, tare da sanya hannu ya shiga goge mata hawayen da gaba ɗaya ya ɓata fuskarta, again cikin son ƙarfafa mata guiwa yace. "Kuka bai kamaci fuskarki ba Laylerh, farinciki ya kamata kiyi domin dayawan Ƴaƴa mata burin ganin aurensu suke, to ke kinsamu zakiyi aure meye kuma na kuka, ko kinason kisani hawaye ne?." Saurin girgizawa Abboun kai tayi alaman "A'a." Kanta yaɗan shafa tare da cewa. "Yauwa Laylatuna, to muje kici abincinki kinji!." Hannunta ya kamo ya nufo da ita kan dining ɗin, kujera yaja tare da zaunar da ita, plate ɗin abinci ya turo mata gabanta tare da spoon yace "Taci." Kasa koda kyakkyawan motsi tayi, domin har yanzu jikinta rawa yake, hawayen dake fita a idanunta kuwa ta kasa yi musu controll domin haka nan suke ta zuba sha kaman ankunna famfo, kafun kuwa ta gama goge wasu, wasu sun kwaranyo. hannunta na rawa ta ɗauki spoon ɗin tare da soma juya abincin, kwata kwata batajin zata iya sanya wani abu acikinta, bakinta ma bata tunanin iya buɗesa. *Ya M.Jay.* shine kawai keta yawo acikin mind ɗinta, ahankali taɗan saci kallon gefen da tasan yana zaune, ganin kujeransa wayam ba kowane yasa taji zuciyarta tayi wani irin dokawa, yayinda wani sabon kuka me sauti marar controll ya kuma ƙwace mata, hakan yasa ta kifa kanta akan table ta shiga rera kuka.
*Note Editing*
*(am sorry na muku late update wallahi bani da charge ne, kuyi manage da wannan insha Allah Gobe da safe zan muku sabon update yanzu wayana saura 10 percent😪.)*
1/19/21, 8:11 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Writting By*
Fatymasardauna
*(This book is mainly for those that pay, if you know you did'nt pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay-0002214625 Abubakar Muhammad Sardauna Jaiz bank, Whatsapp number 07017879464.)*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.