Best Hausa Novels

Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: LAYLERH MALEEK.txt

Chapter 44 of 65

*Chapter 62*

Idanu Oum Ayush ta rumtse tare kuma da cigaba da ambatan kalmar “Innalillahi wa inna Ilaihirraju’un!!�
Domin kuwa ba kad’anba abunda idanuwanta suka gane mata ajikin farar takardar da Najeeb d’in ya bata suka d’aga mata hankali.
Sake k’urawa rubutun dake cikin takardar idanu tayi, aranta tana mejin wani irin k’unci da ciwo.
Cikin muryarta kuma dake d’an carkewa kana kuma yake bayyana alaman tsananin damuwar da ta samu kanta aciki tace.

“Yah Subahanallah Najeeb ka saki Laylerh? meyasa zaka aikata haka batare da neman shawara ba? Meyasa Najeeb, shin bakasan cewa Allah Bayason saki ba, duk da kasancewarsa halak, Why Najeeb why kayi gaban kanka? Menene fa ida da kuma ribar aikata hakan? sannan da wacce irin hujja ka aikata hakan? shin ma kasan ya ciwo da kuma d’acin maida y’a mace bazawara yake? Musamman ga Laylerh yarinya k’arama?�

Idanunsa wanda suke zubar da k’walla ya bud’e, tare da d’ago kansa ya kalli Oum Ayush d’in, cikin wata irin sassanyar murya yace.
“Ko kad’an banyi niyar tozarta Laylerh ba Oum Ayush, saboda Ina sonta, inasonta sosae, amma ya zanyi da soyayyar da takewa Maleek? yaya zanyi? soyayyar Maleek dake zuciyarta ya wuce duk wani gaban kwatance Oum Ayush kuma kema kinsan hakan, a iya soyayyarta kad’ae ya kamata na saudakar, balle kuma idan akaje ga zuciyar Maleek, wallahi nayi rantsuwa Oum Ayush bazan kumayi kaffaraba akan soyayyar da Maleek da Laylerh keyiwa juna, Bawae soyayyace da kowa yasani ba, wata irin halittace dake sake ginuwa akowacce rana, k’arfinta da kuma zafinta ya wuce duk yanda kowa ke zato, tayaya zan zama silar katse fara da burinsu? tayaya zan zamo maison kae haka? Tayaya? Bazan iyaba Oum Ayush domin Maleek ne kwance acikin zuciyar Laylerh bani ba, nayarda zan jure rashinta domin kuwa haka Allah Ya tsaramin, sannan inason dan Allah Ki fahimci cewar ban aikata hakan dan banasonta ba, Inason Laylerh wallahi Inasonta sosae!!!�
Kasa k’arasa maganan nasa yayi asakamakon wani irin yanayin da yaji ya samu kansa aciki, hakanan yaji kamar ya fashe da kuka, saidai kuma amma yasan yin hakan tamkar maida kansa rago ne.
Kansa ya d’an shiga girgizawa ahankali batare kuma daya sake cewa komae ba ya juya ya nufi hanyar fita daga falon gaba d’aya.
Tsura masa idanu Oum Ayush tayi har ya gama ficewa daga cikin falon.
Still wasu irin hawaye masu zafine suka silalo daga cikin idanunta, yayinda acikin zuciyarta takejin wani irin matsanancin tausayin Laylerh’n na k’ara shiga jiki da jininta, Tabbas bazatace Najeeb baiyi Namijin k’ok’ari ba, domin ba kowane zaiyi irin abunda yayi ba, saidai kuma har acikin zuciyarta bataso ya gano matsananciyar soyayyar dake tsakanin Laylerh da Maleek d’in ba.

Jikinta amatuk’ar sanyaye ta maida paper’n cikin envelope d’in tare dasa hannayenta duka biyu ta tallafi hab’arta, Allah Yasani har acikin zuciyarta bataji dad’in sakin da Najeeb d’in yayiwa Laylerh’n ba, domin saki ko yaya yake bashi da dad’i, duk dama tasan cewar hakan mafarin k’arshen wata matsalace, amma koba komae ayanzun Laylerh’n ta zama wata k’aramar bazawara, tunda auren nasu ko wata d’aya bai wuce ba, tasan kuma zuwa yanzu baza’ace wani abu na auratayya bai tab’a shiga tsakanin Laylerh da Najeeb d’inba.

Acan b’angaren Najeeb kuwa lokacin daya fito daga falon Oum Ayush d’in direct sashinsu ya nufa, yayinda gaba d’aya jikinsa ke asanyaye, Sam bayajin dad’in zuciyarsa, abubuwa tare da damuwa duk sun masa yawa.

Ahankali ya murd’a handle d’in k’ofar d’akin, cikin kuma muryarsa wanda bata fita da kyau yayi sallama, tare da kutsa kansa ciki.
Yana sa kansa acikin d’akin kuwa idanunsa suka sauk’a akanta, har yanzun dae kwance take kamar yanda ya tafi ya barta.
Idanunsa masu d’auke da rauni ya lumshe, tare kuma da jingina bayansa ajikin k’ofar shigowa d’akin.
Wani irin sabon sonta da k’aunarta yakeji na ratsa zuciyarsa, hak’ik’a baesan cewa yanason Laylerh’n ba saida ya rabu da ita.
Inama da ace k’addara zata barshi ya rayu da ita rayuwa tahar abada, Inama da ace babu Maleek acikin rayuwar ta, lallai tabbas da yasan watarana zata soshi, domin zaiyi iya k’ok’ari wajen ganin ya koya mata sonsa, saidai amma kuma Ina, k’addara ta riga fata.

Ahankali ta d’an soma bud’e idanunta, wanda suka d’an k’ank’ance saboda kukan da tayi, bud’e idanun nata da tayi kuwa, yayi daidai da soma sarawa’n kanta, wani irin sassanyar ajiyar zuciya ta sauk’e, tare dakai hannunta ahankali ta rik’e kannata, cikin kuma son samawa kanta kuzari ta tashi zaune.
D’an soma k’arewa d’akin nasu kallo tayi, batare kuma da tayi zato ko tsammaniba ta sauk’e idanunta akansa, saboda har yanzu tsaye yake ajikin k’ofar still kuma idanunsa alumshe suke, wanda kuma hakan alamane dake nuna cewar yayi nisa acikin duniyar tunaninsa.

Cikin yanayin mamaki take kallonsa domin bata tab’a ganinsa acikin irin wannan yanayin ba, saidai kuma yanayin yanda taga yayi tsayuwar nasane ya d’auki hankalinta, domin yayi kyau sosai, sai yanzunne kuma ta lura da shigar maroon jumper’n dake jikinsa, da kalanta ya bayyana kyau da kuma hasken fatarsa,
Ji kuma da tayi ajikinta cewar yana cikin damuwa ne, yasa taji zuciyarta ta karye.

“Yah Najeeb!!�
Ta k’ira sunansa murya amatuk’ar sanyaye.

Jin amo da kuma sautin muryarta da yaji acikin kunnuwansane ya sashi dawowa daga duniyar tunanin daya fad’a, ahankali kuma ya bud’e idanunsa ya sauk’esu akanta.
Sanadiyar hakan kuwa yasa idanunsu suka fad’a cikin na juna.

Wani irin murmushin daya bayyana asalin kyawun fuskarta tayi, cikin kuma murya mai d’auke da sakalci tace.
“Tunanin mekakeyi? yanda zaka d’auko Dr yamin injection ko?�

Idanunsa da suka ciko da k’walla ya sunkuyar k’asa tare da d’an jinjina mata kai, cikin son b’oye matsanancin damuwarsa akanta yace.

“Eh saboda naji har yanzu jikinki da zafi, bansan sai yaushe ne zakiyi lafiya ba Laylerh!�
Ya k’are maganan yana me kokarin maida k’wallan dake cikin idanunsa.

D’an k’aramin bakinta ta turo gaba, tare da sake shagwab’e fuska, asanyaye tace.
“Yanzu ma fa kaena ciwo yakeyi Yah Najeeb, please kabani ruwa nasha.�

Jin abunda ta fad’ane ya sashi sake d’ago kae ya kalleta, ganin ita d’inma kallonsa takeyi ne yasashi sakar mata wani murmushi mai kama dana k’arfin hali, anutse ya k’arasa gaban maidaidaicin fridge d’in dake cikin d’akin, bud’e murfin fridge d’in yayi tare da dauko bottle water marar sanyi ya nufo gareta.
Koda ya iso jikin gadon kuwa mik’a mata goran ruwan yayi, tare da matsawa can gefe ya tsaya.
Itakuwa kafa goran ruwan tayi abakinta har saida tasha fiye da rabin ruwan kafun ta janye bottle d’in daga bakinta.
K’afafunta ta zuro k’asa tare da mik’ewa tsaye.
Najeeb kuwa ta gefen idanunsa yake kallonta, harta gama zura bedroom slippers ak’afanta.
Kaitsaye ta nufi hanyar toilet, hakanne kuma ya bashi daman d’ago kansa ya bita da kallo, har saida ta shige cikin toilet d’in kuma kafun ya d’auke idanunsa daga kanta.
Wani irin sassanyar murmushi mai d’auke da ma’anoni daban daban yayi, saboda har acikin ransa yana buri da kuma fatan da cewa da auren wata macen kamarta.

Laylerh kuwa tana shiga toilet d’in fuskarta kawae ta wanke, tare da juyowa ta fito, wanda tayi hakanne kuma saboda yanda takejin idanunta da sukayi nauyi, da kuma ganinta dake d’an disashewa.
Jin bakinta ba dad’ine kuma yasa direct ta k’arasa wajen da take ajiye hand bags d’inta, d’aya daga cikin handbags d’in ta d’auka tare kuma da zuge zips d’insa ta ciro wani babban chocolate.
Akan madaidaicin stull din dake gaban dressing mirror ta zauna, tare da b’are ledan chocolate d’in ta soma gutsura da kad’an kad’an.

Ganin hakan da yayine kuma yasashi d’an soma matsowa inda take ahankali, duk da cewar kuwa k’irji da zuciyarsa bugawa suke sosae amma haka ya cije, tare da soma yunk’urin bawa kansa k’arfin guiwa.

“Laylerh!�
Ya k’ira sunanta cikin wata irin muryarsa da yayi sanyi sosae.

Yanayin yanda amo da kuma sautin muryartasa suka fitane kuma yasa Laylerh tayi saurin d’ago kai ta kalleshi.
Saidai kuma wani bak’in abu da ta hango acikin idanunsa yasata saurin sadda kanta k’asa.

Ahankali ya d’an rank’wafo gareta tare da d’aura hannayensa akan shoulders d’inta ya mik’ar da ita tsaye.

Wani irin kallo ya shiga yi mata da idanunsa wanda sukayi jajur, kana awahalce yace.

“I’m very sorry Laylerh!!.�

Yanayin yanda yayi maganar da muryarsa wacce ke bayyana abunda ke kwance acikin zuciyarsa ne, ya tilasta mata d’ago kae ta kalleshi, cikin mamaki, da kuma wani bak’on yanayin da ta samu kanta aciki tace.

“Yah Najeeb Sorry for what?�

Idanunsa ya d’an lumshe, tare da sake matse shoulders d’inta dake cikin hannayensa, asanyaye yace.

“Saboda nayi wani abu da bansan ya zaki d’aukesa ba, bansan tayaya zaki fuskanci hakan ba Laylerh, amma nayi imani cewa hakan shine mafita, sannan banyi komae dan na cutar dake ba Laylerh, please forgive me!!!�

Ya kai k’arshen maganan nasa yana me had’e tafukan hannayensa waje d’aya, alaman rok’o.

Idanunta wanda suka d’an soma sanja kala ta zuba masa, domin sam ta kasa sanin inda kalaman nasa suka dosa.

“Inasonki Laylerh, inasonki sosae, amma sonda yake miki ya zarce nawa, buri da kuma fatansa akanki ko kad’an ba yankakke bane, yana miki son da daga shi, babu wani wanda yake miki irinsa, ni a iya zuciyata kawae nakejinki Laylerh amma shi ked’ince gaba d’aya rayuwarsa, I don’t mean to hurt you Laylerh, just kawae na yarda komae yazone amatsayin k’addara, amma bazan tab’a mantawa dake ba Laylerh har abada....�

Kasa k’arasa maganan nasa yayi saboda yanda zuciyarsa ke wani irin tsalle da kuma harbawa.

Laylerh kuwa idanu kawae ta tsura masa sam ma bata fahimtar ma’anar abu ko d’ayane daga Cikin kalamansa, babban abunda ya jefata acikin rud’ani da mamaki kuma shine hawayen da idanunta ke gane mata kwance acikin idanun Najeeb d’in, abunda ko sau d’aya bata tab’a gani ba.
Hakanan taji yanayin yazo mata wani na daban, yayinda jikinta ke bata cewar Lallai tabbas akwae abunda yake faruwa.

“Yah Najeeb meyasa.....�

“Shiii!! Karkice komae please, sannan kije Oum Ayush na k’iranki.�
Ya katseta daga maganar da takeyi d’in ta hanyar fad’an haka.

Idanunta dake kansa ta d’an lumshe tare da dafe daidai saitin zuciyarta da takejin tana bugawa akai akai. Yayinda wani abu maikama da tsoro da kuma fargaba suka lullub’e ta, wanda duk batasan dalilin faruwar hakan ba.

Ahankali ta rab’a tagefensa tare da soma tafiya ahankali dan zuwa amsa k’iran da yace Oum Ayush nayi mata.

Idanu ya tsura mata tare dasa hakw’aransa
Ya cije labb’ansa da k’arfi.
Ganin kuma ya isa bakin k’ofar fita daga cikin d’akinne yasashi d’an d’aga murya.

Sunanta ya k’ira, da wani irin tone din da bata tab’a jinsa atattare dashi ba.

Duk da cewar kuwa harta kai jikin k’ofar amma hakan bai hanata tsayawa ba tare da juyowa ta fuskancesa.

Murmushin da yafi kuka ciwo da kuma kallo mai d’auke da tsananin shauk’i yayi mata, hannayensa ya hard’e akan k’irjinsa, cikin silently mood yace.

“Please ki kula da kanki, kada kiyi kuka mai yawa, sannan kuma karkiyi fushi mai yawa!�

Duk da batasan cikakken ma’anan kalaman nasa ba amma haka tasamu kanta da jinjina masa kai, kana asanyaye ta murd’a handle d’in k’ofar ta fice.

Haka ta nufi sashin Oum Ayush zuciyarta cike da fargaba, duk yanda kuma taso daidaita nutsuwarta, ta yanda k’wak’walwarta zata bata ma’anonin kalaman Najeeb d’in abun yaci tura.

Isowarta sashin Oum Ayush d’inne kuma yasa ta tsaida tunaninta waje d’aya tare da murd’a handle d’in k’ofar ta shiga.

Najeeb kuwa ganin fitan Laylerh’nne yasa shi d’aukan wani big trolly ya zuba kayansa dama duk wani abu dayasan zae buk’ata aciki, passport d’insa ya d’auka sai kuma car key da wayoyinsa.
Kaitsaye ya fice daga cikin d’akin.

Koda ya fito compound d’in gidan kuwa babu kowa sai y’an tsirarun soldiers d’in Maleek dake shawagi suna kewaye gidan.

Cikin motarsa k’irar Mercedes benz C300 2018 ya saka trollyn nasa, batare da tunanin komae ba kuwa ya shiga cikin motar tare dayi mata key, bayan kuma mai gadi ya wangale masa gate d’in gidanne ya cilla hancin motar tasa waje.
Daga gidan kuwa kaitsaye office d’in Abbou Jaheed ya nufa, domin kuwa da bakinsa yakeson sanar masa abunda ya aikata batare da tambaya ko neman shawaran kowa ba, yana kuma da hujja akan hakan koda kuwa duk mutanen duniya zasu k’alubalance sa.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.