Best Hausa Novels

Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: LAYLERH MALEEK.txt

Chapter 48 of 65

*Chapter 65*

Mik’ewa Oum Ayush tayi domin zuwa k’iran Laylerh’n kamar yanda Abbou Jaheed ya buk’ata, acikin zuciyarta kuwa tana mejin dad’in yarda da shawararsu da Abbou Jaheed d’in yayi, domin kuwa ko ba komai tafiyan Laylerh’n gidan Aunty Zee zai d’an rage mata kad’aici da kewa, kasancewar akwae y’ar k’anin Mijin Aunty Zee d’in Aliya agidan kuma bata wuce sa’ar Laylerh’n ba.

Ahankali ta tank’washe kyawawan k’afafunta dake aje bisa kan sallayan da take zaune akae, maida gajiyayyun idanunta tayi ta lumshe, tare kuma da fesar da wani sassanyar numfashi, Tabbas sallah’n da tayi yanzu da kuma addu’o’in da tayi sune suka sanyaya mata zuciya, duk da cewar kuwa bata wani jima da tashi abaccin daya d’auke ta ba, yanzu tashinta kenan tayi wanka tare kuma da gabatar da sallan la’asar wanda lokacin da akayisa tana bacci.
Jingina bayanta tayi da bango, tare kuma da ware idanunta ahankali ta sauk’esu akan kyawawan y’an yatsunta, akan k’aramar yatsar hannunta na dama wanda ke d’auke da had’add’en gold ring ta sauk’e ganinta, hakanan taji wani irin abu mai sanyi na yawo acikin zuciyarta, lokaci d’aya kuma taji duk wani k’warin guiwar dake jikinta ya somayin k’asa, yayinda tunani kala kala suka soma bijirowa cikin k’wak’walwarta, Hak’ik’a ta yarda cewa ita mai matsanancin raunine akansa, saidai batasan meyasa ba akowani lokaci idan tunaninsa ya motsawa mind d’inta sai taji kamar tayi kuka, haka kuma zata ke jin kanta amatsayin wata na daban wacce tarasa duk wani abunda takeso.
Still sake lumshe idanunta wanda suka ciko da k’walla tayi, daidai lokacin kuwa aka turo k’ofar d’akin aka shigo.
Duk da kuwa cewar taji alaman wani ya shigo cikin d’akin amma hakan baisa ta ta bud’e idanunta ba, saboda tasan cewa tana bud’esu tofa hawayen dake cikinsu ne zasu sauk’a akan fuskarta, ita kuwa ayanzu sam bata son wani yaga gazawarta.

Ahankali Oum Ayush ta maida k’ofar ta rufe, hango kuma Laylerh’n da tayi akan sallayane yasa duk taji jikinta yayi sanyi, saboda kallo d’aya kawae zaka mata kafa himci cewa tana d’auke da damuwa mai tarin yawa acikin zuciyarta.
D’an girgiza kae Oum Ayush d’in tayi, cike kuma da tausayin Laylerh’n ta k’arasa shigowa cikin d’akin.

“Laylerh!!�
Oum Ayush ta k’ira sunanta da wata irin sassanyar murya.

Jin muryar Oum Ayush acikin kunnuwanta ne kuma yasa tasoma kokarin shanye hawayen dake idanunta, saidai Ina duk yanda tasoyin hakan ta kasa, kasancewar hawayen dake cikin idanun nata sunzo wani gab’a da shanye su abune me wahala, musamman ma idan za’ayi duba da abunda ke cikin zuciyarta.

“Laylerh!!� Oum Ayush ta sake kiran sunanta akaro na biyu, bayan ta k’araso gab da inda ta ke zaune.
Hannunta tasa ahankali ta dafa kafad’an Laylerh’n, kana anutse tace.

“Yauwa kin tashi daga baccin ko? dama babu kyau bacci bayan la’asar naso na tasheki amma kuma tuna irin yanayin da kike ciki yasa na k’yaleki, kinyi sallah ne?�

Ahankali ta d’an jinjina kanta alaman “Eh.� Saidai kuma har yanzu bata bud’e idanunta ba.

D’an Jim Oum Ayush tayi tare da zuba mata idanu, saboda hakanan azuciyarta taji ta k’ara tausayin Laylerh’n, musamman ma yanzu da ta tab’a ta, dan ta d’anji d’umin zazzab’i kad’an ajikinta.
Uwa uba kuma shirun da taga tayi, lallaine tasan abun yana damunta azuciya, domin kasancewar babu soyayya atsakaninta da Najeeb, shine zaesa ta kasajin wani iri adangane da rabuwa dashi ba.

D’an rank’wafowa Oum Ayush d’in tayi tare da kamo hannayen Laylerh’n duka biyu, cikin yanayin kulawa irin wacce Uwa zata bawa duk y’ay’anta idan ta gansu acikin damuwa tace.

“Kiyi hak’uri ko Laylerh, Tabbas dukkan tsanani yana tare da sauk’i, watarana kuma Insha Allah komae zae wuce kaman bai faru ba, tashi kije Abbou Jaheed na jiranki afalon sa�
Ta kai k’arshen maganan nata tana me tada Laylerh’n tsaye.
Wanda kuma sai asannanne ta bud’e lumsassun idanunta, wanda suka taho da wasu irin siraran hawaye.

Ganin kuma hawaye akan fuskarta ne yasa Oum Ayush girgiza mata kai, alaman kada tayi kuka, had’e dasa hannunta ahankali ta share mata hawayen da suka zubo mata.
Again Murmushi tayi mata tare da cewa.
“Kiyi sauri su Abbou Jaheed suna jiranki.�

Still kanta kawae ta jinjina, batare kuma da ta motsa labb’an bakinta ba, ta juya asanyaye ta fice daga cikin d’akin.

Oum Ayush kuwa da kallo ta bita har ta fice, wani irin sanyi taji jikinta yayi, musamman da tafahimci cewa ayanzu Laylerh’n tana da buk’atar wanda zae bata ingantacciyar kulawa, wanda zai hanata kuka, ya kuma iya jure shagwab’anta, Tabbas wani take buk’ata mai zuciya irin nata, wanda tunani da komansa yakasance yana da alak’a da tata zuciyar, wanda zai fahimci hak’ik’anin damuwarta koda kuwa bata furta masa da bakinta ba.
Ajiyar zuciya mai k’arfi ta sauk’e tare kuma dajan wani dogon numfashi, Tabbas komae abayyane yake, amma saidai kusancin Laylerh’n ga abunda zuciyarta keso ayanzu babu abunda zae haifar sai wata sabuwar matsala, Sam bakuma zata so hakan ya faru akaro na biyu ba.
Wannan dalilin yasa tayi saurin kawar da duk wani tunanin dake cikin ranta, direct itama ta juya ta fice daga cikin d’akin, koda ta fito compound d’in gidan kuwa kaitsaye part d’in su Laylerh’n ta nufa, musamman dan had’a mata abubuwan da tasan zata buk’ata.

Acan b’angaren Laylerh kuwa tun fitowarta daga sashin Oum Ayush d’in falon Abbou Jaheed ta nufa.
Koda ta k’arasa ahankali ta tura k’ofar falon ta shiga, bakinta d’auke da sassanyar sallamar, da sai mutum yayi dagaske zai iya jiyo amonta.
Amma kuma kasancewar mutanen dake cikin falon kowannensu acikin alhini yake, hakan yasa sukaji sallaman nata rad’au acikin kunnuwansu.

Abbou Jaheed ne ya d’ago da kansa ya kalleta adaidai lokacin da ta gama k’arasa shigowa cikin falon, tare da neman waje ta zauna acan gefe.

“AYSHA taso kizo nan!�
Ya fad’i hakan cikin matsanancin tausayinta da yakeji na dukan k’irjinsa.

Ai kuwa babu musu ahankali ta mik’e tsaye, cikin yanayin sanyin da tasamu kanta ta k’araso inda Abbou Jaheed d’in ke zaune, yayinda acikin ranta take me mamakin yanda yau Abbou Jaheed d’in ya k’ira realname d’inta.

Adaidai kusa da k’afafunsa ta zauna, wanda sai alokacinne kuma ta lura da Aunty Zee dake zaune acan gefe, yanayin fuskarta ne tad’an sanja daga damuwa zuwa murmushi, gaishe da Aunty Zee d’in tayi, da kuma Abbou Khareem dake zaune.

Dukansu cike da kulawa suka amsa mata, yayinda Aunty zee kuwa muryarta ta kasa b’oye tausayin Laylerh’n da takeji.

“Abbou gani.�
Tafad’a tana me gyara tank’washewar da tayiwa k’afafunta.

Abbou Jaheed kuwa da zuciyarsa ta gama yin rauni, kamo hannayenta yayi ya rik’e, akaron farko kenan da yaji kuma yaga yanayin fuskarta ya juye masa izuwa na mahaifanta, take kuma lokacin daya d’auketa amatsayin amana ya shiga dawo masa, lokacin da tarasa Uwa mahaifiya agareta, rik’onta ya dawo wajensu, still k’addara ta sake rabata da Mahaifinta, hakan yasa ta zama bata da kowa sai su, meyasa alokacin baiyi abunda ya dace ba? Meyasa ya d’auki alk’awarin da nauyinsa ya zo ya zame musu damuwa gaba d’ayansu? Hak’ik’a arana irin ta yau yanajin kamar baiyiwa amanarsa rik’o mai kyau ba, gaba d’aya rayuwar Laylerh’n da tayi abayane ya shiga dawowa cikin kansa, ci da sha, dama duk wani farincikinta yana samuwa ne daga wajen mutum d’aya, wanda yakasance alokacin shine mutum na farko daya fi kowa kusanci da ita, shine wanda yasan abunda ke fili da kuma wanda ke b’oye acikin zuciyarta.
Tabbas idan akwai k’addara to shima akwai wani hakk’i daya tauye, wanda ya tabbata da ace iyayen Laylerh’n suna raye, to da yau sai sunfi kowa jin ciwo da kuma k’uncin abunda ya faru, tayaya zai iya warware wannan al’amarin?
Tambayar da yayiwa kansa kenan wacce kuma bashi da amsarta.

Lokaci guda kuwa idanunsa suka cicciko da k’walla, saboda raunin da yake cikine kuma yasa hawayen dake cikin idanun nasa suka soma k’ok’arin gangarowa zuwa kan fuskarsa.

Laylerh da tun rik’e hannunta da yayi take kallonsa, ganin hawaye a idanunsa ne yasa, taji gaba d’aya hankalinta ya tashi, hannunsa daya rik’e nata dashi ta kama gam, cikin nuna tsananin kulawa da kuma damuwa ta k’ira sunansa, bakinta ta bud’e daniyar yin magana, amma sai hakan ya gagareta saboda wani irin abu da taji ya soki kirjinta.
Idanunta ta rumtse da k’arfi saboda Allah Yasani cewar bazata iya jurewa ganin hawayen Abbou Jaheed d’inta ba.
Asanyaye ta sake matsowa kusa dashi tare da d’aura kanta akan guiwowinsa.

Hakan da tayi d’inne kuma yasa Abbou Jaheed controlling hawayensa, ahankali ya soma shafa kanta, murya atausashe kana kuma cikin yanayin dake bayyana k’aunarsa agareta yace.
“Hak’ik’a da ana iya sauya k’addara go goge zanen abunda ya wuce da nayi hakan Laylerh, da na nesantaki da duk wasu munanan k’addarorin dake bibiyar ki, da kuma ace nasan wannan ranan zata zo, to da har abada ban bari an d’aura aurenki da Najeeb ba, duk da kuwa nasan cewar Najeeb baiyi hakan dan ya cutar da rayuwarki ba, kamar yanda nasani cewa har abada bazae tab’a iya cutar dake ba, Tabbas na zab’a miki Najeeb ne amatsayin miji, saboda ya cancanta, na kuma yi musu alk’awarin bashi aurenki tun lokacin kina k’ank’anuwa, sam ko kusa banyi hakan dan na cutar da rayuwarki ba Laylerh, domin duk da kasancewar bani na haifeki ba, amma ina miki son da nakeyiwa d’an cikina, kuma koda banine mahaifinki ba, jinin dake gudana acikin jikinki na d’an uwanane, ke d’in wata kyautace guda d’aya da Allah Ya bamu, saboda haka bazan tab’a son abunda zai cutar dake ba Laylerh...�

D’an tsagaitawa da maganganun nasa yayi, tare dasa hannunsa ya d’ago kanta, cikin son bata k’arfin guiwa da kuma nuna mata cewar tana da gobe mai kyau yace.

“Kada kiyi bak’inciki ko k’unci Laylerh domin k’addararki ce tazo ahaka, sannan kuma kada ki yiwa Najeeb mummunan zato akan abunda ya aikata, domin ko kad’an Najeeb baiyi haka dan ya cutar da rayuwarki ba, yamin bayanin komai kuma nafahimta, sannan nasan kema watarana In sha Allah Zaki fahimta, domin ni Abbou Jaheed har abada bazan tab’a yi miki zab’in da zai cutar da rayuwarki ba, sannan kuma akullum inaso kina tuna cewar komae daya faru da kuma wanda zai faru duk k’addararren al’amarine, Allah Baya tab’a d’aurawa bawansa abunda bazae iyaba, aduk kuma lokacin da kikaji k’unci ki ambacesa zae sauk’ak’amiki kinji!!�

Kanta tajinjinawa Abbou Jaheed d’in alaman gamsuwa, tare kuma da k’ok’arin b’oye duk wani abunda ke damun zuciyarta.

Ganin k’warin guiwa akan fuskarta ne kuma yasa Abbou Jaheed yaji zuciyarsa tayi wani irin sanyi.

Kanta ya sake shafawa, domin har acikin ransa yana me alfahari da ita.
Cikin kuma son jin ta bakinta yace.

“Mun yanke shawara nida Abbou Khareem da kuma Oum Ayush cewar zakije gidan Aunty Zainab kiyi iddah’n ki acan, saboda acan din zakifi samun nutsuwa, idan yaso bayan kin gama iddah’n saiki dawo, idan kuma kinaga zaki zauna anan d’in shikenan.�

K’asa tayi da kanta tare da d’an soma wasa da y’an yatsun hannunta, cikin kuma yanayin sanyi mai kaman shagwab’a daya zame mata sabo tace.
“Abbou Jaheed duk hukuncin da kuka yanke akaina daedae ne.�

Jin abunda tace d’inne kuma yasa Abbou Jaheed da kuma Abbou Khareem jinjina kai.

Daidai lokacin kuwa Oum Ayush ta shigo cikin falon, jaye da wani babban trolleybag da ta zubawa Laylerh kayan ta aciki.

Ajiye trolleybag d’in tayi, tare da kallon Aunty Zee cikin kulawa tace.

“Ya kamata kutafi domin naga magriba na k’ara shigowa.�

Hakan da tace d’inne kuma yasa Aunty Zee mik’ewa tsaye, tare da jan trolleybag d’in Laylerh’n ta nufi hanyar waje dashi.
Ganin hakanne kuma yasa Oum Ayush ta rufa mata baya.

Laylerh kuwa asanyaye ta mik’e tsaye, Abbou Khareem ne ya rik’o hannunta ya samata bandir d’in kud’i na 50/50k, had’e kuma da damk’a mata ATM CARD d’inta, wanda tun lokacin da akayi bikinta atm card din ke hannunsa, wanda ayanzu ya k’ara zuba mata kud’ad’e masu yawa aciki.

Bakinta na shagwab’a ta bud’e, saidai kuma saurin girgiza mata kai dayayi yasa dole tayi shiru.
Haka suka fito daga falon Abbou Jaheed d’in tana tsakiyarsu, har wajen da motar Aunty Zee ke fake suka rakata, bayan ta shiga motar ta zaunane kuma Oum Ayush ta mik’o mata wayarta.
Karb’an wayar tayi tare da ajiyewa akan cinyarta, kana ta jingina bayanta da jikin kujeran motar.
Idanunta da sukayi raurau ta tsayar akan had’add’en part d’insa da take hangowa, haka takejin zuciyarta na wani irin bugawa, shi kawae taji tanason gani ayanzun, domin tasan ba k’aramin kewa da kuma wahalar da ita soyayyarsa za suyi ba.
Idanunta da suka d’an ciko da k’walla ta lumshe.
Adaidai lokacin kuwa da motar Aunty Zee zata fita daga gidan, motarsa ta kunno kai.
Jin k’ara da kuma horn d’in motar tasane yasa tayi saurin bud’e idanunta, cikin sa’a kuwa ta sauk’esu akansa, inda yake zaune ab’angaren driver.
Idanunta ta tsura masa bata ko k’yaftawa, shikuwa samma bai kula dasu ba domin sauri yake sosae.
Ganin hakanne kuma yasa Aunty Zee ta matsa gefe saida ya shige cikin gidan kafun sukuma suka fita.

Fitansu daga cikin gidan kuwa yayi daidai da zubowar hawayen dake cikin idanunta.

Shikuwa Maleek da sauri ya fito ko gama daidaita parking d’in motar tasa ma baiyi ba.
Hakan yasa hankalinsu Abbou Jaheed
dawowa kansa, cikin yanayin mamakin irin saurin da yakeyi Abbou Khareem yace.

“Captain lafiya kake kuwa?�

Kansa ya jinjina, cikin kuma yanayinsa na wanda bai cika yin magana ba yace.

“Zanbar Nigeria yau, wani aikin gaggawa ya tasomin, 7:00 pm daidai flight d’inmu zai tashi.�

Cike da mamaki dukansu suka bud’e baki suna me binsa da kallo, kasancewar yayi musu maganar ne yana tafiya batare dako tsayawa yayi ba.

*5:30 pm*
3/13/21, 10:08 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*Not editing*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.