Best Hausa Novels

Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: LAYLERH MALEEK.txt

Chapter 3 of 65

*Chapter 7*

Sauƙe idanunsa da yayi akanta ne yasa duk tsikar jikinsa mimmiƙewa, take yaji wani sabon yanayi ya ziyarcesa, numfashi ya fesar tare da soma yawo da idanunsa akanta baya ko ƙiftawa.
Ɗago ɗara ɗaran kyawawan Idanunta tayi, wanda hakanne ya bawa eye balls ɗinta daman sauƙa acikin nasa idanun.
Wani irin faɗuwar gaba ne ya ziyarceta, cikin sauri ta janye idanunta tare dayin ƙasa da kanta, hakanan taji duk tazama wata iri. Ahankali tasake yin ƙasa da idanunta, tare da kawar da kanta gefe. Cikin yanayin sanyi ta ƙarasa shigowa cikin falon, tare daɗan durƙusawa cikin sassanyar muryarta tace.
"Abbu barka da yamma." Murmushi Abbu yayi tare da cewa. "Yauwa Laylerh ya school É—in?." É—an murmushi tayi ahankali ta ce. "Alhamdulillah."
Idanunta ta ɗaga tare da ɗan kallon Alhaji Ahmad Rufa'e wanda tun shigowanta fari'ar dake kwance akan fuskarsa ta ƙaru. Cikin yanayin ta na nutsuwa tace.
"Ina yini."
Sake faɗaɗa fari'ar dake kwance akan fuskarsa yayi, murya asake yace. "Lafiya ƙalau Laylerh ya karatu, ana nan anata fama ko?."
Kai ta jinjina masa alaman "Eh." still har yanzu fuskarta É—auke yake da murmushi.
Kallon Abbu Alhaji Ahmad Rufa'e yayi cikin yanayin jin daɗi yace. "Masha Allah Alhaji Jaheed Laylerh ta girma, wancan zuwan nawa fa tana ƴar ƙarama da ita, dan in ban manta ba lokacin shekarunta 11 ko."

Murmushi Abbu yayi, tare da jinjina masa kai, cikin dattako yace.
"Ae kasan girman Æ´a mace babu wuya."
ShiÉ—in ma Alhaji Ahmad Rufa'e'n murmushi yayi, dan tabbas ko maganan da Abbun ya faÉ—a haka ne.

Laylerh da duk taji ta kura ɗan muskutawa kaɗan tayi, tare da sakeyin ƙasa da idanunta, hakanan takejin wani iri ajikinta, gashi jikinta na bata cewar ana kallonta.

Najeeb ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ɗan lumshe idanunsa, wanda tun shigowarta suke aikin kallonta basa ko lumshewa, hakanan yaji wani diffrent feeling akan yarinyar, duk da kasancewar tana da ƙananun shekaru, amma ya lura tana da abubuwan burgewa da yawa ajikinta, sosai kuma ya karanci yanayinta, cikin zuciyarsa yake maimaita sunan da yaji Abbu ya ƙirata dashi wato "LAYLERH".
"Nice name." Ya faɗa batare daya bari sautin muryarsa ta fito fili ba, saidai laɓɓansa da suka ɗan motsa, baisan meya saba har yanzu ya kasa ɗauke idanunsa akanta.

Bazata iya jure zaman wajen ba, musamman yanda taji tsikar jikinta na zubawa, miƙewa tsaye tayi domin ayanzu ba abun da takeso kaman ganinta aɗakinta, dan ko tantama batayi, kasancewar taji ajikinta cewa ana kallonta.
Ganin Laylerh'n ta miƙe tsaye ne yasa Abbu cewa.
"Laylerh baki ga Yayanki Najeeb bane? kigaishe sa mana."

Jin Maganan da Abbu ya faɗa ne yasa akaro na biyu ta ɗago kyawawan idanunta ta kalleshi, kasancewar tun ɗazu idanunsa akanta yake, shiyasa idanunsu suka faɗa cikin na juna, saurin sadda kanta ƙasa tayi tare da kama ƴan yatsun hannunta ta shiga murzawa, cikin muryarta dake cracking tace.
"Ina yini."
Akaron farko kenan daya janye idanunsa daga gareta, cikin son samawa kansa nutsuwa yace. "Lafiya."
Jin sauƙar muryarsa acikin kunnuwanta ne yasanya ta sake ɗago kai ta kalleshi, wani abu da ta tuna ne yasa ta ɗauke idanunta daga kansa, tare da miƙewa tsaye cikin yanayin nutsuwarta ta nufi ɗakinta, kasancewar ta ɗebo gajiya amakaranta shiyasa takejin kanta nayi mata ciwo kaɗan kaɗan.

Ta gefen idanunsa yabita da kallo,har ta shige wani É—an corridor dake cikin falon, wanda anan cikin corridor É—in É—akinta yake, ganin ya daina ganinta ne yasa shi É—auke kansa daga kallon hanyar da tabi.

Alhaji Ahmad Rufa'e ne ya kalli Abbu cikin sakin fuska yace. "Tabbas Alhaji Jaheed nakusa samun suruka, masha Allah fatan dai baka manta da alƙwarin dake tsakanin mu ba."
Cikin son ƙarfafawa aminin nasa guiwa Abbu Jaheed yace. "Tayaya zan manta da alƙwari me girma irin wannan, hakan ma bazata faru ba, kuma Insha Allah ina meyi maka albishir da cewa kafun ka koma Polland zan cika maka wannan alƙawarin naka dana ɗauka, dan ni kaina nafiso ayi komai agabanka."
Murmushin jin daÉ—i Alhaji Ahmad yayi tare da cewa.
"Alhamdulillah lallai zanji daÉ—in hakan kuwa."
Murmushi Abbu Jaheed yayi, sannan suka ci gaba da hirarsu.

Laylerh kuwa kaitsaye ɗakinta ta wuce, tana shiga ta turo ƙofar ɗakin nata tare da murza handle ɗin, school bag ɗin dake rataye akan kafaɗanta ta ajiye, tare da cire hijab ɗin dake jikinta.
Anan kan É—an madaidaicin gadonta ta zauna, tare da sakin ajiyar zuciya, ahankali ta É—an lumshe idanunta, wanda suka É—anyi ja saboda gajiya da kuma stress.
Kallon da Najeeb keyi mata me ɗauke da ma'anoni kala kala ne ya dawo cikin mind ɗinta, da sauri ta buɗe idanunta tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, ashagwaɓe tace. "Ko waye shi ma oho, har da zaiyita wani kallona?." Ƙwafa tayi tare da soma ƙoƙarin watsar da tunaninsa acikin kanta, tashi tayi cikin nutsuwa ta soma ƙoƙarin cire uniform ɗin jikinta.
Koda ta kammala cire uniform É—in wani baby pink towel ta É—aura ajikinta wanda ko cinyoyinta basu kai ga rufewa ba, kaitsaye ta wuce toilet dan sosai takejin kanta na sarawa, tun safe kuwa takejin mararta aÉ—an É—aure, ruwan zafi ta haÉ—a dashi tayi wanka sannan ta É—auro alwala.
Koda ta fito daga cikin toilet ɗin, tsane jikinta tayi, tare da shafa wani body lotion ajikin ta, haka take bata dason yawan kwalliya, shi yasa ko powder bata shafa akan fuskarta ba, ƙarasawa gaban sif ɗin kayanta tayi tare da buɗewa, kayan cikin drawer'n ta zubawa ido kamar wacce ke na zartan wani abu, ɓangaren dogin rigunanta ta kalla, wanda kusan ma sune sukafi yawa acikin kayan nata, kasancewar tafison abayas, and kimono fiye da kowani kaya, wata blue ɗin abaya me adon manyan duwatsu wanda ke haɗe da ɗan gyalensa ta ciro, rigace me kyaun gaske dan ƙirar turkish abaya ce.
Anutse ta zura rigar ajikinta, baƙaramin kyau kuwa rigar tayi mata ba, dan ta bayyana ɗan madaidaicin shape ɗin jikinta wanda kullum ƙara fitowa yake, bama kamar hips ɗinta wanda suke ta ƙara faɗi da kuma buɗewa, wanda kuma hakan na da nasaba da girma da take ƙarawa ako wacce rana, dogon gashinta daya nannaɗe ta tubke waje ɗaya, tare da ɗaura vail ɗin abayan akanta, jin yanda mararta ke ƙara murɗawa ne yasa ta zauna akan bedside drawer, ahankali taɗan rumtse idanunta tare da ɗaura hannunta akan mararta, wanda asannu sannu ciwon ke ƙaruwa, abubuwa da yawa take saƙawa azuciyarta, daga gefe guda kuwa zuciyarta na neman gangarawa wani sashi ne na daban, wanda hakan ne ke ƙara jefa tunaninta cikin rauni, batason ko menene ke shirin faruwa da ita ba, saidai wani lokaci tunaninta yakan tafiya ne da kowani ƙwayan bugun zuciyarta.
Jin ciwon marar na sake nuƙurƙusanta ne yasa ta sake rumtse idanunta, tare da cije jajayen laɓɓanta, jin bazata iya jure zaman bane yasa ta tashi daga kan bedside ɗin, nan kan saman gadonta ta kwanta, tare da jawo blanket ta rufa ajikinta.

6:40 pm dai-dai.
Baƙar motarsa ƙiran Toyota Avalon, bugun 2020 ta danno kai cikin farfajiyar gidan, awannan karon baya tare da soldiers ɗinsa, hasalima shi da kansa yake driving motar.

Ganin motarsa ta kutso kai cikin gidan ne yasa soldiers din dake compound ɗin gidan shiga taitayinsu, inda duk suka ƙame awaje ɗaya.

Daga yanayin yanda yake tuƙin motar kaɗai zaka gane irin yanda yake cike da isa, kuma komai nasa yana yinsa ne acikin nutsuwa, kasancewarsa bashi da yawan hayani ya.
Atsakiyar compound É—in gidan yayi parking motar, wanda ya É—auki sama da 7 minute bai fito daga cikin motar ba.
Sanin yagama daidaita parking ɗin motar ne ya sashi ɗauke hannunsa akan steering motar, ɗan jingina bayansa da jikin kujeran motar yayi, tare da fesar da iska ta bakinsa, cute cat ɗinsa me kalan milk dake kwance akan kujeran ɓangaren me zaman banza ne tayi saurin hayewa jikinsa, ɗagota yayi tare da ɗan soma shafa gashin bayanta, yanason cutie ɗin nasa, wanda sanadin haka ne tayi matuƙar sabo dashi.
Madaranta ya ɗauko anutse ya soma bata abaki har sai da ta ƙoshi, gane ta ƙoshi ne yasa shi ɗaurata akan shoulder ɗinsa, anutse ya buɗe murfin motar ya fito.
Ganin fitowarsa daga cikin motar ne yasa soldiers É—insa soma sara masa, kasancewar haka suka sabayi masa ako da yaushe.
Abdul ne ya taho da sauri cikin takunsu na isassun maza wanda idan sunayi sai ƙasa ta amsa, da dukkan alama sun samu horo me tsanani awajen ogan nasu, dan duk wani soja dake cikin gidan daka kallesa, zaka san ba ragon namiji bane, da alama duka sojojin nasa horarru kuma ƙwararru ne, dan dukansu tsayayyu ne, kana kuma matasa masu jini ajika.
"Well come back Sir."
Abdul da ƙarasowarsa kenan yafaɗa cikin yanayin girmamawa.
Kansa ya jinjina alaman "Yauwa." Tare da É—an juyowa yayiwa Abbul É—in kallo me alamar magana, shiÉ—in ma Abdul kallonsa yayi, gane abun da kallon Ogan nasa ke nufi yasa cikin sauri yace.
"Yess Sir nayi mana takeaway É—in lunch harma dana dinner."

Jin haka yasa batare daya sake cewa komai ba, ya nufi babban ginin benen dake tsakiyar compound ɗin gidan, wanda kuma nanne zai sadashi da babban falon gidan har izuwa sashinsa da ƙofar shigansa ke cikin falon.
Ahankali ya murɗa handle ɗin ƙofar falon ya shiga, zuwa lokacin babu kowa acikin falon dansu Abbu sun tafi masallaci yin sallah'n Magriba da ta Isha, Larai ce kaɗai ke tsaye akan dining area tana shirya dinner, yayinda ta kusan cike saman babban table ɗin cin abincin, dan girke girken da akayi yau ɗin na musamman ne, an girka abinci kala daban daban sunkai 7 banda drinks ɗin sha da aka haɗa kala daban daban, wanda kuma hakan duk aikin Larai da sauran kukus ɗin gidan ne, dan aƙalla suna da kukus sunkai 5 agidan, amma duk da hakan baya hana Laylerh aikatuwa, dan watarana Momy hana kukus din komai take, tace Laylerh ce zatayi, to yaudai Allah Ya samawa Laylerh lafiya daga yin aikin gidan.

Kaitsaye ƙofar part ɗinsa ya nufa. Ƴan yatsun hannunsa yakai jikin wata na'ura dake jikin ƙofar tasa, na'urar na ɗaukan hoton ƴan yatsunsa ƙofar ta buɗe, tura ƙofar yayi ya shiga ciki, yana shiga kuwa ƙofar da kanta ta kulle. Ƙarasawa tsakiyar falon yayi, tare da ɗaura hannunsa akan schoulder ɗinsa, kamo cutie ɗin nasa wanda ta fara bacci yayi, anan kan lallausan carpet ɗin dake malale atsakiyar falon ya ajiyeta, sannan ya nufi bedroom ɗinsa.
Yana shiga cikin ɗakin kuwa ya soma ƙoƙarin rage kayan jikinsa, rigar t-shirt na Calvin Clain Jeans ɗin dake jikinsa ya cire, aɗan ƙagauce ya cire takalmin sopport ɗin dake ƙafansa.
Zama yayi akan wata haÉ—aÉ—É—iyar cushion dake cikin É—akin.
Dan lumshe idanunsa yayi, yayinda ahankali yakejin kasala na sauƙar masa, jingina bayansa da jikin kujeran yayi, tare da sakin ajiyar zuciya, hakanan yau ɗin yakejin yanayinsa duk ba daɗi, hannunsa yasa ya dafe daidai saitin zuciyarsa dake beating, wanda cikinta ke cike da fata haɗi da muradi da kuma burin samun abun da takeso, tabbas zuciyarsa cike take da muradi, wanda yayi imani cewa ƙaddara na kewaye da wannan muradin nasa, mafarkin da yayi adaren jiya ne yasoma dawowa cikin kansa filla filla, hakan kuwa shiya sanyashi buɗe idanunsa, tare da tashi tsaye kaitsaye ya nufi toilet, sam bayason maimaita tunanin mafarkin nasa because mafarkin kaman abune marar tushe awajensa. Ruwan shower me sanyi ya sakarwa kansa, ba tare da ya bari ruwan ya jima yana dukansa ba yayi wanka haɗe da ɗauro alwalan sallan Isha.
Koda ya fito daga wankan da wani farin towel ya tsane jikinsa, sama sama ya shafa men body lotion ajikinsa, wasu riga da wandon crazy jeans masu kyau yasaka, wanda suka sake bayyana hasken fatarsa, kasancewarsa mai son ƙamshi sosai, wannan yasa ako da yaushe baya barin jikinsa ba ƙamshi, hakan ne kuwa yasa koda bai shafa turare ba jikinsa ƙamshi yake.
Wata haɗaɗɗiyar lallausan darduma ya ɗauka haɗi da wayarsa wanda keta faman ringing ganin ƙiran bawani me mahimmanci bane yasashi ƙin ɗagawa, darduman na riƙe ahannunsa haka ya fito daga part ɗinsa ya nufi masallaci.

Ɓangaren Laylerh kuwa jin ciwon marar nata ya ɗan lafa ne yasa ta tashi tayi sallan magriba, koda ta sallame sallan bata tashi ba saida tayi sallan Isha, ɗan muskutawa gefe tayi tare da kwantar da kanta ajikin gado, azkar take amma gaba ɗaya tunani da hankalinta sun tafi zuwa wani waje daban, daga jiya zuwa yau wani irin fitinannen baƙon yanayi takesamun kanta aciki, babu wani minti da zai wuce batare da tayi tunaninsa ba, haka zalika ko wani bugun zuciyarta ɗaya da tunaninsa yake tafiya, haka takeji kaman ana zana mata tunaninsa acikin jininta, wani abu na musamman takeji akansa, wanda kuma hakanne kesawa taji zuciyarta na ƙoƙarin bayyanar da rauninta, batasani ba, bata kuma san meyasa tunaninsa ke sawa taji kaman tayi kuka ba, haka takeji ajikinta tanason kasancewa dashi, ayanzu ba abun da takeson shaƙa kaman ƙamshin sa, wani irin fitinannen feeling takeji akansa.
Samun kanta da tayi cikin shauƙin tunaninsa ne yasa ta sake matse jikinta waje ɗaya, tare da lumshe kyawawan idanunta.

Kusan atare suka shigo cikin gidan su dukansu, Najeeb wanda shiya fara ganin Maleek ɗin, murmushi ne ya faɗaɗa akan fuskarsa, cikin sakewa ya miƙawa Maleek hannu alaman su gaisa, akaron farko kenan tun wayewar gari zuwa yanzu da ya ɗan saki murmushi akan fuskarsa, wanda shima iya kansa kan laɓɓan bakinsa, hannu ya miƙawa Najeeb ɗin suka gaisa.
Alhaji Ahmad Rufa'e ne ya fafaÉ—a fari'arsa tare da É—an bubbuga kafaÉ—an Maleek É—in cikin kulawa yace. "Wellcome back son, i hope kadawo nan Nigeria da zama?."
ÆŠan murmushi yayi wanda ya bayyana tsantsar kyaunsa, cikin husky voice É—insa yace.
"Haka nake tunani."
Murmushi dukansu sukayi, cikin jin dadi Abbu da Alhaji Ahmad Rufa'e sukace.
"Allah yasa."
Abbu ne ya dubi Maleek É—in cikin kulawa yace.
"M.J ga Najeeb ina fatan zamanka a America baisa kamantashi ba."

ÆŠan kallon Najeeb É—in yayi, wanda shima kallonsa yake, batare da ya ce komai ba ya jinjina kai, alaman bai mantashi ba. ÆŠauke kansa yayi gefe tare daÉ—an lumshe idanunsa, wanda hakan ya zame masa sabo kuma É—abi'a.
Najeeb kuwa ƙurawa M.J ɗin idanu yayi, hakanan yaji wani abu aransa game da Maleek ɗin, saidai atake yakau da tunanin dake ransa.

Kusan atare duk suka shiga cikin falon, Momy dake zaune tana ganinsu ta saki murmushi, cikin kulawa da son karrama baƙin nasu tace. "Sannunku da dawowa, kusan mintuna 15 kenan da dinner ke jiranku a dinning."
Murmushi Abbu yayi, tare da kai dubansa ga Maleek wanda ke ƙoƙarin nufar sashinsa.
"Maleek."
Abbu yaƙira sunansa.
Tsayawa da tafiyan yayi tare da É—an juyowa ya kalli Abbu'n nashi. Shima Abbun kallonsa yayi.
Tabbas shi mutum ne me saurin fahimta, sometimes ma yafi fahimtar magana ta ido, fiye da yanda mutum zai furta, wannan yasa ko awajen horar da É—alibai yakan sa su koyan yanda zasuyi magana da idanunsu, haka kuma idan aka musu magana da ido zasu fahimta, yakan gane abun dake zuciyar mutum daga yanayin kallon da mutum É—in keyi masa, gane abun da Abbu ke nufi ne ya sashi fasa shiga side din nasa.
Ƙarasawa dining area din sukayi, wanda tuni anriga da an ƙara yawan kujerun waje, sabanin da da kujeru 4 ne awajen.
Zama sukayi dukansu, yayinda Momy ta shiga ƙoƙarin seving ɗinsu. Abbu ne ya ɗago kai tare da duban Momy cikin kulawa yace.
"Kisa aƙiramin Laylerh?."

Wani baƙin cikine ya tokare maƙoshin ta, sam batason kulawan da Abbu ke bawa Laylerh,Batare da ranta yaso ba ta ƙira ɗaya daga cikin masu aikin gidan, tace da ita taje ta ƙira Laylerh.
Cikin sauri kuwa haka me aikin nasu ta tafi dan cika umarnin Momy'n.

Laylerh da har yanzu ke zaune akan sallaya ta lumshe idanunta tare da dafe saman mararta dake murɗawa, jin ana knocking ƙofar ɗakin nata ne yasa ta bude idanunta, tare da juyawa ta zubawa ƙofar idanu, still knocking ƙofar da aka cigaba da yine, yasa ta miƙewa tsaye, duk da cewar tanajin ciwo amararta amma haka ta cije. Ƙarasawa jikin ƙofar ɗakin tayi tare da buɗewa.
"Kizo in ji Hajiya." Me aikin tafaÉ—a tana me kafe Laylerh'n da idanu.
Kai Laylerh ta jinjina alaman. "To." sanin halin Momy yasa batare da ta koma cikin ɗakin nata ba ta fito, yayinda ta ware ɗan kwalin dake kanta taɗan yafa zuwa wuyanta, duk dama dai vail ɗin dashi gwamma babu dan yana showing sosae. Tana ƙarasowa cikin falon, takai dubanta kan dining area'n, take kuwa idanunta suka sauƙa akan faffaɗan bayansa, kasancewar zaman da yayi ya bawa cikin falon baya ne, wani irin fitinannen sanyi ne taji na shiga jikinta, tare da ratsa tafin ƙafanta, yayinda hancinta ya shiga zuƙo mata daddaɗan ƙamshin turarensa.
Ƙasa tayi da kanta tare da ƙarasowa dining area ɗin.
Najeeb da tun shigowanta cikin falon ya zuba mata idanunsa, har zuwa yanzu kuwa bai É—auke kallonsa daga gareta ba, baisan me yasa ba hakanan yake samun kansa dason kallonta, wani abu na musamman yakeji adangane da ita.
Cikin sanyi taja kujera ta zauna, ɗan ɗago da kanta tayi, bisa tsautsayi idanunta suka faɗa cikin na Najeeb dake jifanta da kallo me ɗauke da ma'anoni daban daban, sauƙe idanunta ƙasa tayi, tare da sauƙesu akan yatsun hannun Maleek dake ɗaure bisa saman table ɗin cin abincin.
Ƙurawa kyawawan fararen yatsun nasa idanu tayi wanda suke ɗauke da shining nails, yatsarsa ta tsakiya ta ƙurawa ido wanda ke sanye da wani haɗaɗɗen shining ring, ajikin ring ɗin an rubuta A.M da manyan baƙi.
Kallon ring ɗin dake hannunta tayi da kyau, sam basu da maraba da wanda ke hannunsa saidai ita harufan da aka rubuta akan nata L.M ne nashi kuma A.M, ɗan jim tayi tare da murza zoben nata, duk da ita kanta batasan da ya akayi zoben ya shiga hannunta ba amma tanason zoben sosai, dan bata taɓa mantawa watarana tun tana ƙarama, ta kwanta bacci koda ta tashi sai gani tayi an sanya mata zobe aɗaya daga cikin yatsun hannunta, tun daga wannan lokacin kuwa bata taɓa cire zoben daga hannunta ba.
So take taÉ—an saci kallonsa amma nauyin hakan takeji.
Ganin duk sun fara cin abincinne yasa ta É—auki plate tayi seving kanta.

Duk yanda taso cin abincin nata ta kasa, domin hakanan takejin kallon da Najeeb keyi mata duk ya takurata, gefe guda kuma ga ciwon marar ta da ya tsananta, rumtse idanunta tayi tare da É—an karyar da wuyanta gefe, ciwo mararta keyi sosae.

Najeeb ne ya tsaida cin abincin da yakeyi tare da zuba mata ido, dan ya karanci cewa akwai abun dake damunta.
"Laylerh!." Yaƙira sunanta cikin wata silent voice.

Laylerh da ayanzu ciwon nata yakaita maƙura har ta kai ga idanunta sun kaɗa sunyi ja, ahankali ta ɗago da kanta ta kallesa.
Idanunsa yaÉ—an zaro waje ganin yanda idanunta suka sauya launi ne yasa cikin kulawa yace.
"Are you okay?."
Samun kanta tayi da kasa tanka masa, lokaci É—aya wasu hawaye suka kwaranyo daga cikin idanunta.

Wanda Sauƙan hawayen nata yayi daidai da ɗago kai da Maleek yayi, wanda tun zuwanta bai ɗago kansa daga abun da yakeyi ba.
Ganin hawaye a idanunta ne ya sashi janye idanunsa daga kanta, asanyaye ya É—an lumshe idanunsa.

*( Menene fata da burin dake cikin zuciyar Laylerh da Maleek? Idan ƙundin Ƙaddaransu ahaɗe take dana juna, me kuke tunanin zai faru anan gaba idan Najeeb ya shigo cikin rayuwar Laylerh? Tabbas akwai wata soyayya me tsananin zafi da taɓa zuciya agaba, kada ku manta tun afarko na faɗa muku cewa wannan salon na dabanne, haka zalika LAYLERH MALEEK daban yake da sauran labarai da kuka sani, kar ku manta yanzu akafara wasan. sannan kuyi haƙuri jia kunjini shiru nayi typing ne ya goge shiyasa, kuma typing akwai wahala sosai😪)*

*Vote nd Comment*

*fatymasardauna*
1/19/21, 8:10 PM - Ummi Tandama: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

       *LAYLERH MALEEK*

     *Writting By*
Phatymasardauna

                    *Wattpad*
             @fatymasardauna

#hausanovels

                   *Chapter 8*

Idanu Najeeb ya zuba mata ganin yanda take ta mutsu mutsu, ga kuma hawaye still na sauƙa akan fuskarta, ganin yanda take taune lips ɗinta ne yasa shi jin wani iri ajikinsa, asanyaye ya sake ƙiran sunanta, akaro na biyuk enan.                   
Kasa amsa masa tayi saima rumtse idanunta da tayi, tare da cizan laɓɓanta, asanyaye ta sa hannu ta share hawayen dake kwance akan fuskarta, jin bazata iya jurewa bane yasa ta ɗaura kanta akan table ɗin cin abincin, sosai marar nata ke ci gaba da  murɗawa, ahankali ta soma sakin sheshsheƙan kuka, tare da dafe saman marar nata da hannunta.         
Tashin sautin sheshsheƙan kukanta ne yasa hankalin su Abbu Jaheed dawowa kanta, cikin kulawa haɗe da nuna tsantsar damuwa Abbu Jaheed yace. 
"Subahanallah Laylerh lafiya meke damunki?."
Yayi maganar cikin yanayi na ɗan ruɗewa.                  
Jin muryar Abbu ne yasa kukan nata ƙaruwa, cikin  sheshsheƙan kuka tace.  "Abbu mara na zai faɗo ƙasa, ciwo nakeji sosai."          
Cikin tausayawa, Abbu da  Alhaji Ahmad suka haɗa baki wajen faɗin.  "Subahanallah!."      
Ɗan jim Abbu Jaheed yayi, take kuma tunanin ƙiran Doctor ya zo masa, waya ya zaro daga cikin aljihunsa, cikin yanayin damuwa yace.
"Bari naƙira Dr.Yazo ya dubaki."         
Baisaurari komae ba yayi dialing number'n Dr.Ishaq.
Bugu biyu kacal Dr. Ishaq  ɗin ya ɗaga, bayan sun gaisane Abbu  yayi masa bayanin abun dake faruwa,  kasancewar sa family doctor ɗinsu, yasa take yace gashinan zuwa.                 Jin hakanne yasa Abbu ya aje wayar, kallon Laylerh'n ya kuma yi wanda har yanzu ke aikin kuka, yayinda ta duƙunƙune jikinta waje ɗaya da dukkan alama ciwon marar ne ke wahalar da ita.       
Cikin tausayinta Abbun yace.    "Sannu ko Laylerh, yanzu Dr. zai zo ya dubaki, am sorry jeki ɗaki ki kwanta kafun Dr. Ishaq ɗin yazo."                 
Jin abun da Abbun ya faɗa ne yasa ta ɗan jan kujeran da take kai baya, cike da son daure ciwon da takeji ta miƙe tsaye,  tashin ta tsaye kuwa yayi daidai da wani irin murɗawa da mararta yayi, wanda hakan yasa ta rumtse idanunta da ƙarfi, tare da sakin wata ƴar ƙara, take jiri ya kwasheta, hakan yasa tatafi luuu zata faɗi, cikin azama Najeeb yasa hannu ya tarota ta faɗa jikinsa. 
Daidai lokacin  kuwa Maleek ya ɗago kansa, wanda tun fara kukan nata ya sadda kansa ƙasa  baisake ɗagowa ba sai yanzun,  ɗago idanunsa da yayi yayi daidai da faɗawarta jikin Najeeb.     Wani irin abune yaji ya caki ƙahon zuciyarsa, wanda zafi da raɗaɗin sa ya ratsa cikin ƙwaƙwalwa da sassan jikinsa, rumtse idanunsa da suka kaɗa sukayi jajur yayi tare da buɗe bakinsa ya fesar da wani zazzafan numfashi.               

Najeeb kuwa taro Laylerh'n da yayi ta faɗa jikinsa ne, ya sashi jin wani irin shock, take yaji gaba ɗaya tsikar jikinsa sun mimmiƙe, lokaci ɗaya wani irin yanayi ya soma ratsa ƙashi da bargonsa, hannayensa dake rawa yakai kan kyakkyawar fuskarta, cikin wata irin murya me sanyi yace.  "Laylerh! please wake up,  ki buɗe idanunki please."  Yafaɗi maganan aɗan ruɗe, dan yanda yaga idanunta na lumshewa, ya sanyashi jin faɗuwar gaba.          
Duk da cewar tana jinsa amma bazata iya amsa masa ba, saboda hakanan takejin kamar tunani da hankalinta na ƙoƙarin barin jikinta, idanunta ne suka cigaba da  lumshewa, yayinda jikinta ya sake.         
Ganin haka ne yasa Abbu tasowa hankalinsa amatuƙar tashe ya taho kan Laylerh'n, ɗago ta yayi daga jikin  Najeeb, ahankali Abbu ya shiga girgizata tare da soma ƙiran sunanta. Ganin kamar bata cikin hayyacinta ne yasa Abbu ɗago kai ya dubi Maleek wanda ya lumshe kyawawan  idanunsa, yayinda  yayi kamar baisan abun da ke faruwa ba.   
Hankalin Abbu aɗan tashe yace.   "Please M.J sake ƙiran Dr.Ishaq, Laylerh ta fara fita hayyacinta banason wani abu ya sameta.."     
Abbu bai ida maganar tasa ba Dr.Ishaq ya shigo cikin falon.
Ganinsa ne yasa Abbu sauƙe ajiyar zuciya, da kansa ya ɗaga Laylerh'n inda ya kwantar da ita akan wata luntsumemiyar kujera dake nan side din dining area'n.      
Ƙarasowa cikin falon Dr. Ishaq yayi, hannunsa riƙe da ƴar jakarsa wacce ya zuba kayan aikinsa da yasan zai ɓuƙata aciki.          
Cikin kulawa Abbu da duk ciwon Laylerh'n yasa shi cikin damuwa yace.      "Please Dr. kayi checking ɗinta, naga kaman bata motsi."           
Kai Dr.Ishaq ya jinjina alaman duk yanda Abbun keso haka za'ayi. 
Ɗan ranƙwafawa yayi tare da buɗe ƴar jakarsa ya ciro abubuwan dayasan zai buƙata.   
Cikin wasu ƴan sakanni ya gama yi mata duk wasu gwaje gwajen da zaiyi mata. 
Acikin ƴan sakannin nan kuwa idan ka kalli fuskar Abbu da kuma Alhaji Ahmad, damuwa  kawai zaka hango akwance, yayinda Najeeb kuwa ya bada duk wani attention ɗinsa akan Laylerh'n, fararen kyawawan legs ɗinta wanda suka ɗan bayyana, sakamakon doguwar rigarta da ta ɗan ɗage ya zubawa ido baya ko ƙiftawa,daga cikin zuciyarsa kuwa abubuwa da yawa yake saƙawa.               

Maleek.           
Harzuwa yanzu idanunsa alumshe suke, ga wanda baisan meke faruwa ba, idan yazo zai iyi tunanin cewa  bacci yake, saidai kuma azahirance ba hakan bane,  shi kaɗai yasan abun da yakeji acikin zuciyarsa, ahankali yake fitar da numfashi, yayinda yakejin jikinsa duk ba daɗi, lokaci ɗaya yaji kansa nayi masa ciwo,  jingina bayansa da jikin kujeran da yake kai yayi, ajiyar zuciya yake saki akai akai, daga cikin ƙirjinsa kuwa zuciyarsa ce ke beating da sauri sauri.
                      
Daga ɓangaren Dr. Ishaq ma ajiyar zuciyan ya sauƙe, dan gane abun dake damun Laylerh'n yasa komai yazo masa cikin sauƙi, kuma ciwon nata ma ba sosai irin yanda zai tsoratar ɗinnan bane.             
Wasu ruwan Injection guda biyu ya ciro acikin jakarsa tare kuma da Injection din, take yasoma haɗawa dan yasan idan yayiwa Laylerh'n su zata ɗan samu relief.           
Ahankali taÉ—an soma ware shanyayyun idanunta wanda sukayi luhu luhu, da dukkan alama tanajin ciwon ajikinta sosai.
Akan Dr. Ishaq ɗin ta sauƙe idanunta wanda ke tsaye yana haɗa ruwan alluran da zaiyi mata.         
Ganin allura ahannunsa ne yasa ta ƙarasa ware idanunta, take jikinta ya soma ɓari saboda tsoro.   
Ganin ta buɗe idanunta ne yasa Abbu ya ƙaraso kusa da ita, cikin kulawa yace. 
"Laylerh sannu ko, ya jikin naki?."      Ashagwaɓe taɗan soma girgiza kanta, cikin muryarta da ta sanja amo tace.     "Please Abbu kafaɗa masa banason allura."        
Murmushi Abbu yayi tare da shafa kanta, cikin matsanancin tausayinta yace. 
"Sorry bazai miki da zafi ba, kuma ae alluran ita zata kashe miki pain din da kikeji, kiyi haƙuri amiki alluran kinji."  Abbu yafaɗi maganar cikin lallashi.
Kai ta cigaba da girgizawa take hawaye suka cika idanunta, Allah Yasani arayuwarta tana matuƙar tsoron allura, saboda hakane ma ko ganinta batason yi.               
Ganin da gaske alluran Dr.Ishaq ke ƙoƙarin yi mata ne yasa ta fashewa da kuka, amatuƙar tsorace ta soma jijjiga kanta tare da ɗan yarfa hanna yenta, cikin sheshsheƙan kuka tace. 
"Please Ya M.Jay kace kada amin allura am scared,  pleaseeeeee .....!!" Taja maganan cikin wani irin yanayi dake nuna cewar bada iyaka bakinta takeyin maganna ba, har da zuciyarta.        

Sauƙan maganganunta acikin kunnuwansa ne ya sashi rumtse Idanunsa da ƙarfi, lokaci ɗaya wasu abubuwa suka shiga yawo acikin tunani da ƙwaƙwalwarsa, tabbas irin hakan ya taɓa faruwa, wani lokaci da take buƙatar taimakonsa kamar yanda takeyi yanzu'n, kansa ya shiga girgizawa yayinda memories din baya ke ƙokarin dawo masa, lokaci ɗaya tunaninsa ya soma juyewa, abubuwa da yawa ne suka shiga bijiro masa. lokaci ɗaya jikinsa ya soma ɓari, take jijiyoyin jikinsa suka mimmiƙe, wanda hakan yasa gargasan jikinsa ma miƙewa, bazai iya jure yanayin da yake ciki ba, kukan Laylerh ne ke ƙoƙarin haukata masa tunani, ji yake kaman ana buga masa guduma acikin kansa, idanunsa ne suka soma yi masa gizon, abun da ya faru da Laylerh'n shekarun baya da suka wuce, kansa ya soma girgizawa take gaba ɗaya mood ɗinsa ya sauya, cikin wani irin matsanancin huci haɗi da nuna zallar yanayin da yake ciki da ƙarfi ya buga table din dake gabansa, wanda hakan yajawo plates da kuma glass cup's ɗin dake kan table din suka watse, tare da tarwatsewa aƙasa.  
Ƙaaran buga table din da kuma fashewan cups ɗin da yacika falon ne yasa su Abbu atsorace suka maida hankalinsu garesa, hatta Dr. Ishaq da ke shirin yiwa Laylerh allura  tsaida komai yayi, ya zubawa M.Jay ɗin idanu.          
Har yanzu jikinsa rawa yake, yayinda ya dunƙule hannayensa waje ɗaya, yana sakin wani irin zazzafan huci.
Ganin yanda jikinsa keta faman ɓari ne yasa abun cikin yanayin sanyi yaƙira sunansa.         
Jin muryar Abbu acikin kunnuwansa ne ya sa duk wani tunaninsa tsayawa, zuciyarsa tafasa take, yayinda yakejin zuciyarsa kamar zata faso ƙirjinsa ta fito waje, kansa ya girgiza dan bayajin zai iya jurewa yanayin da yake ciki, miƙewa tsaye yayi, cikin wani irin taku dake bayyana zallan izza da kuma ikonsa haɗi da nuna cewa shiɗin tsayayyen namiji ne ya nufi ƙofar da zata sadashi da falonsa, ko gani sosai bayayi saboda yanda idanunsa suka kaɗa sukayi ja. 

Idanu su Abbu suka zuba masa har saida ya ɓacewa ganinsu, ajiyar zuciya Abbu ya sauƙe, tare da zama akan kujera yayi shiru, da yawan lokuta wani abu na haukata tunanin ɗan nasa wanda baisan ko menene ba, ba tun yauba ya fahimci cewa, Maleek ɗin nada wata damuwa acikin zuciyarsa, wanda ya kasa bayyanata ga kowa.
Lumshe idanunsa yayi lokaci ɗaya yaji zuciyarsa ta karye, haƙiƙa rashin Oum Abdiyya shiya ruguza rayuwarsu, tabbas ya sani da tana nan duk wata matsala na Maleek zata sani amatsayinta na uwa.      
Laylerh da ganin yanda Maleek ɗin ya rikide alokaci ɗaya ne yasa taji zuciyarta ta sake raunana, taso ayau din koda sau ɗaya ne ta kalli kyakkyawar fuskarsa, saidai hakan baiyi wuba, danko ayanzu bayansa kawai ta iya gani.             
Kallonta Dr.Ishaq yayi cikin son lallaɓata yace.  
"Kitsaya na miki alluran bazan miki da zafi ba."         
Kanta ta girgiza take kuma ta sake sakin sabon kuka, cikin muryarta dake rawa tace. 
"Tsoro nakeji, please Ya M.Jay tsoro nakeji."      

"Ya M.Jay." Najeeb da ya zuba mata mayun idanunsa, ya maimaita sunan da take faɗi acikin zuciyarsa. Hakanan baisan me yasa ba yakejin wani iri idan ta ƙira sunan M.J ɗin. Ahankali ya taso daga inda yake tare da ɗan matsowa kusa da ita, anan kan hannun kujeran da take kwance ya zauna, cikin wani irin yanayin dake fusgarsa akanta yace.  
"Oh sorry Laylerh, please stop crying."  
Yafaɗi maganar tare da ɗaura hannunsa akan nata hannun, wanda hakan da yayi kuwa ba ƙaramin tayar masa da tsikar jikinsa yayi ba, taushi da kuma laushin hannunta ne suka soma ratsa shi, hakan ya sashi ɗan lumshe idanunsa.            
Cikin shagwaɓar da ita kanta batasan ta iya taba tace. 
"Da zafi sosai."    Idanunsa ya kuma zuba mata, ahankali ya jawota jikinsa, tare da sanya tafin hannunsa ya rufe idanunta.       
Akaron farko kenan na rayuwarta da ta fara shiga jikin wani namiji wanda yake ba muharraminta ba, kuma har yayi hugging ɗinta haka, hakanan taji komai na duniyar ya daina yi mata daɗi, tunanin M.Jay ɗinta ne ya soma dawowa cikin brain ɗinta, asanyaye ta saki kuka, cikin shagwaɓa ta soma motsa laɓɓan bakinta, magana takeson yi amma takasa, wani abune acikin zuciyarta da takeson bayyana shi, amma harshenta yayi nauyi, dole haka ta rumtse idanunta.     
Ganin haka ne yasa Dr. Ishaq soka mata alluran dake hannunsa.    Idanunta ta zazzaro tare da fasa ihu, take ta soma yunƙurin guduwa, riƙeta Najeeb yayi ƙam dan yasan idan yabarta alluran zai iya karyewa ajikinta. 
Haka tanaji tana gani akayi mata alluran guda biyu, babu yanda ta iya.  Ana gamawa kuwa ta fashe da kuka, ahankali ta zame jikinta daga na Najeeb ɗin ta kwanta aƙasan carpet,  tsakani da Allah ta ke kukanta, wanda ita kanta batasan kukan meye takeyi ba, dan har acikin zuciyarta ba wai kukan alluran takeyi ba.
            
Ganin haka yasa Abbu yin murmushi, kasancewar yasan tun ada can ma Laylerh nada shagwaɓa sosai da kuma yawan koke koke musamman idan bata da lafiya.          
Magunguna Dr.Ishaq ya rubuta wanda za'a sayo abata. 
Kallon Abbu yayi cikin son kwantar masa da hankali yace.
"Bawata matsala bace babba, insha Allah zata warke, wannan injection ɗin su zasu kashe mata pain ɗin, kuma za su sata bacci, idan ta tashi kuma insha Allah zata jita normal, sometimes dama ana samun irin haka,amma no problem zataji sauƙi Insha Allah."
Cikin gamsuwa Abbu yace "Alhamdulillah." Hannu ya bawa Dr. Ishaq din sukayi musabaha, sannan ya amshi takardan    maganin da za a sayowa Laylerh'n.
         
Najeeb wanda gaba ɗaya ya zama very weak saboda riƙon da ya yiwa Laylerh'n, shiya karɓi takardan maganin daga wajen Abbu, inda yace zaije ya sayo.             
Ganin haka yasa Abbu yace wa Momy ta kai Laylerh ɗaki, dan har tafara bacci anan kan carpet ɗin.   
Babu yanda Momy ta iya dole haka takai Laylerh'n ɗaki, domin koda wasa batason nuna tsanar Laylerh agaban idanun Abbu, kasancewar ta jima da gane cewa Abbu na matuƙar son Laylerh'n sosai.

Kusan atare Najeeb da Dr. Ishaq suka fita daga cikin falon, inda Dr.Ishaq ya wuce office É—insa, shi kuma Najeeb kaitsaye ya nufi pharmacy dan siyawa Laylerh magani.
Duk da cewa tuƙi yake amma kwata kwata tunani da hankalinsa basa tare dashi, ba abun dake yawo acikin tunani da kuma brain ɗinsa, sai haɗuwar jikinsa da na Laylerh, idanunsa ya lumshe domin moment ɗin ya masifar ratsa shi, lallai yana da buri akan Laylerh wanda dole kuma saiya cikashi.

Ɓangaren Maleek kuwa, koda ya ƙarasa bedroom ɗinsa, kaitsaye toilet ya wuce, har yanzu zuciyarsa zafi take masa, rigar dake jikinsa ya cire, tare da ƙarasawa gaban shower ya sakarwa kansa ruwa, kasancewar hakanne kaɗai zaisa shi yaji zuciyarsa tayi sanyi.
Hannunsa yakai inda ya shafi tattoo ɗin dake kwance agefen cikinsa, wanda aka rubuta AYSHNOOR da manya baƙi tare kuma da juya harufan, ta yanda bakowane zai fahimci abun da aka rubuta awajen ba.
Lumshe idanunsa yayi, ahankali yakejin wani irin sanyi na shiga jikinsa, duk yanda zuciyarsa takai ga tafasa sai yaji ta soma yin sanyi. Kansa ya kifa ajikin bango, yayinda ya zamana ruwan shower'n na dukan naked skin É—in bayansa.
Laɓɓan bakinsa dake ɗauke da danshin ruwa yaɗan motsa, asanyaye cikin wani irin yanayin da ke bayyana zallan abun dake cikin zuciyarsa yace.
"I can't live without you!".

*Please comment and vote.*

18/ November/2020

*fatymasardauna*
1/19/21, 8:10 PM - Ummi Tandama: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
Phatymasardauna

*Wattpad*
@fatymasardauna

#future

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.