Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: LAYLERH MALEEK.txt
Chapter 4 of 65
*Chapter 9*
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fesar da sassanyar iska ta bakinsa, jin yanda sanyin ruwan shower ɗin ke ratsa duk jikinsa ne ya sashi kashe shower'n, tare da jawo wani fari ƙal ɗin towel ya ɗaura akan waist ɗinsa, ƙarasawa gaban sink ɗin dake cikin toilet ɗin yayi tare da ɗauro alwala, hannunsa ya ɗaura akansa, cikin nutsuwa ya soma ɗan kaɗe gashinsa dake ajiƙe da ruwa, hannunsa yakai jikin wani hangers wanda anan jikin hangers ɗin yake rataye duk towels ɗinsa, ɗaya daga cikin towels ɗin ya ciro tare da soma goge jiƙaƙƙen gashin kansa, koda ya gama goge kannasa kuwa, nan cikin wani durstbin ya jefa towel ɗin, sannan kaitsaye ya fice daga cikin bathroom ɗin.
Koda ya fito kuwa nan kan wata chair dake aje agaban mirror ɗinsa ya zauna, yayinda gaba ɗaya jikinsa ke ɗauke da danshin ruwa, yayinda gargasan jikinsa suka kwanta lub, daga gefe guda kuwa farar fatarsa har wani shining take, wani ɗan ƙaramin towel dake aje akan dressing mirror ɗin nasa ya ɗauka, wanda dashi yayi amfani wajen goge naked skin ɗinsa, wani lallausan body lotion ya shafa, haɗe kuma da shafa wani body spray me daɗin ƙamshi ajikinsa, wanda gaba ɗaya ƙamshin spray ɗin ya cika ɗakin.
Cikin nutsuwa ya miƙe tsaye tare da ƙarasawa gaban sif glass ɗinsa, wanda ke cike da kayan sawansa, wani simple 3 quater jeans ya ciro tare da sawa ajikinsa.
Haka Batare daya saka riga ba ya ƙarasa gaban bedside drawer ɗinsa, ɗan jan murfin drawer'n yayi tare da ciro wani ɗan ƙaramin box me kaman akwati.
Ƙarasawa gaban wata lallausar kujeran dake gefen gadon yayi ya zauna.
Ahankali ya kai hannunsa kan cikinsa daidai inda ya ɗaure da bandage, cikin nutsuwa ya soma warware bandage ɗin dake nannaɗe akan ciwon dake gefen cikin sa, ahankali yake ɗan cije jajayen laɓɓansa, tare da ɗan rumtse idanunsa, wanda da dukkan alama ciwon dake wajen na ɗan yi masa zafi.
Koda ya gama cire bandage É—in maida kansa yayi ya ajiye, tare da jingina bayansa da jikin kujera, ahankali yake É—an sakin numfashi.
Still lumshe idanunsa yayi yana mejin yanda ciwon nasa keyi masa zafi, duk da cewa kuwa yanzu kusan 3 weeks kenan dajin ciwon nasa, kasancewar sunje wani aiki ne cikin rashin sa'a bullet ya samesa agefen cikinsa.
Akasalance ya buɗe ɗan ƙaramin farin box ɗin da ya ajiye agabansa, inda ya ɗauko wani sabon bandage da kuma wani magani.
Sanin zafin maganin ya sashi rumtse idanunsa, ahankali yaɗan soma shafa maganin wani irin zafi da raɗaɗi ne suka shiga ratsa ƙwaƙwalwarsa, cije lips ɗinsa yayi, cikin ƙarfin hali haka ya naɗa sabon bandage akan ciwon, duk da kuwa cewar yanajin zugi da zafi ajikinsa amma dole haka ya daure.
Bayan ya gama kintsa kansa ne ya tashi tsaye, inda kaitsaye ya nufi saman makeken gadonsa, light off É—in wutan É—akin yayi, sannan ahankali ya haye saman gadon, É—an lumshe idanunsa yayi akaro na barkatai, tare da sakin bayyananniyar ajiyar zuciya, har yanzu yanajin ransa ba daÉ—i, ga kuma zuciyarsa da ke acunkushe, sam kuma baisan meyasa yakejin hakan ba.
Tuno da mood ɗinta na ɗazu, da kuma sautin kukanta da yayi ne ya sashi sake maida idanunsa ya rufe, hannunsa ya ɗaura adaidai saitin zuciyarsa yana me sauraran, yanda zuciyar tasa ke bugawa, wani abu da ya tuna ne ya sanyashi ɗan cije lips ɗinsa, tare da sakin murmushi har saida laɓɓan bakinsa suka ɗan motsa, wayarsa dake yashe akan gadon ya ɗauka tare da kunnata, hoton wata kyakykyawar yarinya ne ya bayyana akan screen ɗin wayar, wanda duka dukanta bazata wuce 9 years ba, yayinda yarinyar ke sanye da riga da wando, fuskarta ɗauke yake da murmushi, wanda hakan ya ƙara ƙawata kyawun fuskarta. Idanunsa ya zubawa hoton dake mamaye akan screen ɗin wayar, ahankali yakejin wani irin shauƙi na ratsa duk illahirin jikinsa, matso da fuskar wayar tasa yayi, ahankali yaɗaura bakinsa akan screen ɗin wayar. Cikin wata irin sassanyar murya me ɗauke da daddaɗan amo yace.
"My Baby Boo!!."
manna wayar tasa yayi akan faffaɗan ƙirjinsa, tare da lumshe kyawawan idanunsa, yayi imani cewa wannan yarinyar itace bugun zuciyarsa, haka kuma ƙaddaransa natafiya ne dai dai da rayuwarta.
Najeeb..
Da tunani kala kala acikin ransa, ya ƙaraso gaban babban pharmacy ɗin, cikin ɗan hanzari ya shiga ciki, magungunan da Dr. Ishaq ya rubuta wa Laylerh'n ya sayo, koda ya fito daga pharmacy'n kaitsaye wani supermarket ya wuce, kayan ciye ciye ya sayawa Laylerh'n dangin su choculate da dai sauransu.
Daga supermarket din kuwa gida ya nufa.
Koda ya shigo compound É—in gidan, yana gama daidaita parking É—in motarsa ya fito tare da nufar hanyar da zata sadashi da falon gidan kaitsaye.
Yana ƙarasawa falon kuwa ya tarar da su Abbu Jaheed da kuma mahaifinsa suna hira.
Ganin Najeeb É—inne yasa Abbu sakin murmushi cikin kulawa yace. "Najeeb kadawo."
Kai Najeeb din ya jinjina tare da ƙarasowa cikin falon.
Wrist watch É—in dake É—aure a tsintsiyar hannunsa ya kalla, cikin yanayin nuna damuwarsa ga Laylerh'n yace.
"Eh nadawo Abbu, ga magungunan, dan ya kamata ace tatashi tasha, saboda shima zai taimaka mata ƙwarai wajen rage raɗaɗin ciwon."
Kai Abbu Ya jinjina cikin gamsuwa yace.
"Ƙwarai hakan zai taimaka, amma yanzu nasan ana tashinta da kuka zata tashi."
Jin abun da Abbun ya faɗa yasa, Najeeb lumshe idanunsa, ƙwarai yanason sake ganinta, saboda baya so ace ya kwana batare daya sake sanya idanunsa acikin nata ba.
Ɗan sake duba agogon dake ɗaure a hannunsa yayi, cikin nutsuwa yace. "Bari naje nagwada lallaɓata ko zata tashi tasha maganin."
Murmushi Abbu yayi tare dabin Najeeb É—in da ido, wanda tuni ya kama hanyar dayake hasashen cewa lallai nanne É—akin Laylerh'n.
Kallon Alhaji Ahmad Rufa'e Abbu yayi, shiɗin ma Alhaji Ahmad ɗin da ya bi Najeeb da kallo, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da dawo da kallonsa ga Abbu, murmushi kawai sukayi juna tare da jinjina kansu.
Lokaci ɗaya kowannensu ya soma ancen zuci, yayinda kowannensu da abun da yake saƙawa acikin zuciyarsa.
Laylerh.
tun da Momy ta kaita ɗaki take bacci, har zuwa yanzu kuwa baccin take, sai dai kuma kallo ɗaya zaka mata kaji tausayinta, duba da yanayin yanda take baccin kasan cewa ba tanayinsa bane acikin daɗin rai, duba da irin yanda take ta faman sakin sheshsheƙan kuka duk da cewa baccin takeyi, kwance take akan ɗan gadonta yayinda gaba ɗaya fararen legs ɗinta suka bayyana.
Tsayawa yayi agaban ƙofar da yake tunanin cewa itace ƙofar ɗakin nata, ɗaura hannunsa yayi akan handle ɗin ƙofar, tare da tura ƙofar ciki, ahankali ya kutsa kansa cikin ɗakin.
Tashin farko idanunsa suka sauƙa akanta.
Murmushi yayi sakamakon yanda yaga ta duƙunƙune jikinta waje ɗaya. Maida ƙofar ɗakin yayi ya rufe, tare da ƙarasowa cikin ɗakin, kaitsaye ya nufi jikin gadon da take kwance. Ledan magungunan dake hannunsa ya ajiye, ahankali yaɗan ranƙwafo inda ya zuba mata idanunsa, sannu ahankali yake ƙarewa kyakkyawar fuskarta kallo, sauƙe ganinsa yayi akan zara zaran eye lashes dinta wanda suke ɗauke da danshin ruwan hawaye, ƙasa yayi da idanunsa har zuwa kan ƴan ƙananan jajayen shining lips ɗinta masu kyau, wani yawu ya haɗiya, wanda ya tsaya masa amaƙoshinsa, ahankali yaɗan lashi lips ɗinsa.
Cikin wata silent voice yace.
"Kina da kyau sosai."
Yayi maganar tasa abayyane, still cikin yanayin shauƙin daya samu kansa aciki, hannunsa yakai kan fuskarta, ahankali cikin sanyin murya yaƙira sunanta.
"Laylerh!."
ko motsawa batayi ba balle yasa ran cewa zata buɗe idanunta. Hannunsa yakai yaɗan ja hancinta, cikin sanyi ya kuma ƙiran sunanta. Laylerh wanda acikin baccinta tasoma jiyo sautin bakuwar murya acikin kunnuwanta, ahankali ta soma bude sleeping eyes ɗinta, cikin zallan shagawaɓa ta soma ƙoƙarin yin kuka. Hannunsa ya ɗaura akan bakinsa, cikin kulawa yace.
"Shii karkiyi kuka kinji, tashi kisha magani."
Akasalance ta ƙarasa buɗe idanunta, ganinsa akanta yasa tayi saurin tashi zaune tare da sanya hannayenta duka biyu ta kare ƙirjinta, idanunta ta soma ɗan mutsutstsekewa, tare da turo bakinta gaba.
Murmushi kawai Najeeb yayi tare da soma ɓare magungunan dake hannunsa.
Ganin yana ɓare magunguna ne yasa ta ɓata fuska, cikin zallan shagwaɓa tace.
"Ni dai Aa bazan sha ba." ÆŠago idanunsa yayi ya watsa mata. Hakan yasa tayi saurin É—auke idanunta akansa, dan batajin zata iya jurewa mayataccen kallonsa.
Murmushi ya sakar mata again tare da tashi daga tsugunon da yayi. Kan bedside drawer ɗin dake gefen gadon ya zauna, magungunan dake cikin hannunsa ya miƙo mata haɗe da goran ruwan swan, cikin kulawa yace.
"Karɓa kisha."
Yi tayi kamar bazata karɓa ba, saidai ganin yanda ya kafeta da idanu yasa bisa dole ta sa hannu ta amshi maganin, wajen karɓan goran ruwan ne hannunta da nasa suka ɗan gogi juna, cikin sauri ta zame hannunta, tare dayin ƙasa da idanunta, magungunan ta saka abakinta tare da kai goran ruwan bakinta, jin ɗacin magungunan acikin maƙoshinta ne yasata rumtse idanu tare da ɓata fuska.
Murmushi yayi, dan hakan da tayi ba ƙaramin ƙara fito da kyaun fuskarta yayi ba, hannu ya miƙa mata alaman tabasa goran ruwan, babu musu kuwa ta miƙa masa, ƙarɓa yayi tare da tashi tsaye, anan kan bedside drawer ɗin ya ajiye goran, ƴar madaidaiciyar ledan dake ɗauke da kayan choculate da ya saya ya ajiye mata anan kan bedside din, kallonta yayi, hakan yasa itama ta ɗago ta kalleshi, wanda hakan yasa idanunsu haɗewa waje ɗaya. murmushi yayi mata cikin kulawa yace.
"Gut night." Yana faÉ—in hakan ya kashe mata hasken wutan da ya mamaye É—akin, anutse yasa kai yafice daga cikin É—akin.
Idanu ta tsurawa bayansa har ya gama ficewa daga cikin ɗakin, ahankali ta saki ajiyar zuciya tare da komawa ta kwanta, lumshe idanunta tayi, cikin jiki da kuma zuciyarta takejin inama da ace Ya M.Jay ɗinta ne shi ɗin, inama da ace shi tagani acikin wannan yanayin nata, take lokaci ɗaya taji wani irin kasala haɗi da baƙon yanayi sun ziyarceta, ɗan ƙaramin pillown dake gefenta ta rungume, tare da ɗan karyar da kanta, batasan tayaya kuma ta ina zata fara siffanta haɗuwa da kuma matsayin kyawunsa ba, saidai koma yaya tayi imani cewa yana da wani baiwar kyau wanda dayawan maza basu dashi, M.J shidin na dabanne. Hannu tasa ta dafe kanta wanda takejin ya mata nauyi, ga kuma idanunta da suke ta faman lumshewa, da alama magungunan da Najeeb ɗin ya bata suna sa bacci, ji tayi gaba ɗaya jikinta yayi weak, shiru tayi tare da zurfafa tunaninta akan M.Jay ɗin, ko cikakken mintuna 20 kuwa batayi ba, bacci ya ɗauketa.
ÆÂangaren Najeeb kuwa yana fita daga cikin É—akin nata, kai tsaye cikin falon ya koma, har zuwa yanzu kuwa Abbu da kuma Alhaji Ahmad suna zaune, ganinsa ne yasa Abbu cikin kulawa yace. "Bata tashi bako?." Murmushi yayi tare da girgiza kai, É—an juyawa yayi ya kalli Æ™ofar É—akin nata, anutse yace. "Ta tashi, kuma na bata maganin tasha."
Ajiyar zuciya Abbu ya sauƙe tare da jinjina kansa.
Alhaji Ahmad ne ya dubi É—an nasa, cikin kulawa yace.
"Dama kai nake jira naga dare ya somayi kasan gobe jirgin 6 zanbi zuwa Kaduna, ya kamata mu wuce masauƙin mu."
Kai Najeeb ɗin ya jinjina tare da cewa. "Yeah nima bacci nakeji." Kasancewar ko wanni zuwa da Alhaji Ahmad ɗin keyi agidan na Abbu yake sauƙa, wanda musamman Abbu ya gina wani haɗaɗɗen part acikin gidan wanda yayisa ne musamman dan tarban amininsa Alhaji Ahmad idan ya shigo Nigeria, ko yazo garin na Abuja, hakanne yasa duk zuwan Alhaji Ahmad da yakeyi baya sauƙa a hotel anan cikin gidan yake sauƙa. Kusan atare suka miƙe dukansu, Abbu da kansa ya shiga taka musu har zuwa masauƙin nasu, wanda tuntuni Momy tasa an gyarasa. Ɗakuna uku ne acikin babban falon, wanda kuma kowannensu akwai furnitures masu kyau aciki.
Ɗaya daga cikin ɗakin wanda shine na farko Najeeb ya sauƙa, yayinda Alhaji Ahmad kuwa ya sauƙa aɗayan ɗakin.
Koda Najeeb ya shiga ɗakin murzawa ƙofar key yayi, cikin nutsuwa ya soma rage kayan jikinsa tare da ɗaura wani towel ya shiga wanka, baiwani jimaba ya fito daga wankan sanye da farar bathrobe ɗin wanka ajikinsa.
Tabbas Najeeb kyakkyawane, duk da cewar bashi da yalwatacciyar murɗaɗɗiyar surar jiki, amma kuma yana da ɗan faffaɗan chest, sannan akan fuskarsa yana da dogon hanci tare kuma da manya manyan idanu, ga kuma wani haɗaɗɗen sajen daya kwanta luf agefen fuskarsa, sannan kuma yana da yalwar gashi asaman kansa, yayinda laɓɓan bakinsa keda kalan light pink, tabbas Najeeb yana da salon irin nasa kyau'n, kuma yana da abubuwan burgewa da dama ajikinsa, wanda dayawan mata ke buri da fatan samu, saidai kuma dama duk yanda mutum yakai ga abu, kyau, ilimi, ko wayewa akwae wanda yafishi, wannan yasa tsakanin MALEEK da Najeeb ya zama da banbanci, kama daga yanayi harma kuma da tsarin halitta, domin Maleek shi ɗayane babu na biyunsa, saidai kuma dukka ninsu gwanaye ne wajen kyau, sannan acikin dukansu babu me makusa ɗaya wanda zaisa mace ta ƙisu.
Shirya kansa yayi cikin wasu fararen riga da wando, zuciyarsa cike da tarin tunanin Laylerh ya haye saman haÉ—aÉ—É—en gadon dake cikin É—akin. Koda ya kwanta ya rufe idanunsa, fuskar Laylerh'nce keyi masa gizo, tuno da santala santalan legs É—inta da yayi ne ya sashi sakin murmushi haÉ—i da ajiyar zuciya, tabbas duk da cewa Laylerh'n bata da wani girma sosai amma tana da tsarin halitta me kyau da kuma ban sha'awa, musamman yanda shape É—inta yake, Allah yayi mata body structure me kyau, wannan yasa idan yana kallonta bayason É—auke idanunsa daga gareta, tabbas yanaji ajikinsa cewa Laylerh zata zama wani yanki na rayuwarsa, domin yanaji ajikinsa cewa zai rayu da ita, har ma ya samu mafaka ajikinta.
Da tunani iri iri haka bacci ɓarawo ya ɗaukesa.
Washe gari.
Kamar yanda ta saba tashi ƙarfe 6 daidai akowacce rana, to yau ɗinma hakan ne ya kasance, saidai tashin nata na yau ya banbanta dana ko yaushe, dan kuwa da wani irin tashin zuciya haɗi da amai ta tashi, hakanan duk takejin yanayin nata ba daɗi, kyawawan ƙafafunta tazuro ƙasa daga kan gadon, tare da miƙewa tsaye, duk da cewa tanajin jiri amma haka ta daure.
ƙarasawa toilet tayi inda ta ɗauro alwala, bayan ta idar da alwalan ne ta ɗan ɗago tare da lumshe idanunta, sakamakon wani abu me ɗumi da taji ya na ƙoƙarin bin jikinta, ɗan shagwaɓe fuska tayi, dan bataso ace abun da take zargine, sake komawa tayi ta wanke jikinta, ganin cewa da gaske period ɗinta ne yazo yasa ta sake kwaɓe fuska take idanunta suka cika da hawaye,, duk da cewa wannan shine karo na biyu da farawanta amma sam batason abun, saboda yanda yake sawa takejin kanta atakure, tuno da cewa awancan karon Teemah ta bata kyautan Sanitary pads ne yasa ta sakin ajiyar zuciya, dan idan da ace Teemah bata taimaka ta bata ba, da yanzu batasan ya zatayi ba wanka tayi tare da kimtsa kanta. Kasancewar garin ana ɗan yanayin sanyi yasa koda ta sanya uniform ɗinta, wani kakkauran safa ta saka akafafunta wanda tsawonsa ya kawo har kan guiwowinta.
Koda ta saka rigar makarantar ɗas ta mata, kasancewar idan tana period breast ɗinta na ƙara girma shiyasa rigar uniform ɗin nata ta zauna ajikinta sosai.
Wani haɗaɗɗen combat shoe tasaka aƙafanta, wanda kuma zasu taimaka ƙwarai wajen rage mata sanyin da takeji.
Kallon agogon dake saƙale ajikin bangon ɗakin tayi. 7:13 am daidai, school bag ɗinta ta goya, tare da zura ɗan ƙaramin hijab ɗin makarantar ajikinta, extra pad guda biyu ta ɗauka inda ta buɗe zip ɗin dake bayan school bag ɗinta ta saka pad ɗin aciki, ganin ta gama kimtsa kanta ne yasa kaitsaye ta nufi falo.
(Am sorry yau ba editing, naso page É—in yayi tsawo amma bani da time.)
*Comment nd Vote.*
*fatymasardauna*
1/19/21, 8:11 PM - Ummi Tandama: ðŸÂ‡ðŸÂ‡ðŸÂ‡ðŸÂ‡ðŸÂ‡ðŸÂ‡ðŸÂ‡ðŸÂ‡ðŸÂ‡ðŸÂ‡
  *LAYLERH MALEEK*
*Writting By*
Phatymasardauna
        *Wattpad*
    @fatymasardauna
#Destiny
*(Alhamdulillah! Tabbas ina godiya agareku masoyana, musamman yanda kuke nunamin ƙauna kuma kuke nunawa labaraina, haƙiƙa inajin daɗin hakan, bani da abun ce muku sai godiya, sannan ayau inason sanar daku cewa littafin LAYLERH MALEEK ya tashi daga free book ya dawo na kuɗi, daga wannan pagen kuwa zan dakata da baku free pages, duk wacce takeson samun cigabansa tofa saita biya, inaso kusan banyi hakan dan na ɓata muku rai ko kuma kuga kaman nayi rashin adalci ba, no bahaka bane Laylerh Maleek mallakina ne kuma ina ƙaunar baku duk wani labarina amatsayin free, saidai tanadin danayiwa Laylerh Maleek yasa bazan iya ci gaba da sakinsa free ba, saboda haka am sorry to say, ga waƴanda suke buƙatar cigabansa 300 ne kacal, sannan zaku iya turamin kuɗin ta hanyar account number, ko kuma katin MTN na 300. Ga wacce ta turamin kuɗin ta account number saita min screenshot dan nagani na tabbatar zaku iya tuntuɓana ta Whatsapp Number na 07017879464. Ga kuma Account Number na kamar haka. 0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Ja'iz Bank Kada ku manta na faɗa muku cewa salon Laylerh Maleek daban yake, duk yanda kuke tunanin chakwakiyar cikin littafin ya wuce nan, haka zalika labarin ya shallakewa tunaninku. Nagode sosai duk wacce tabiya 300 ina tabbatar muku da cewa zata samu cigaban labarin Laylerh Maleek. Gare ku mutanen dake zaune a Niger zaku iya tura katinku ga wannan number'n. +227 90899076)*
         *CHAPTER 10*
Sako da Æ™afarta cikin falon yayi dae dae da buÉ—e Æ™ofar part É—insa da akayi. ÂÂ
Ganin haka ne yasa tayi saurin komawa baya, cikin hanzari ta lafe ajikin É—an bangon da tasan wanda ke cikin falon bazae ganta ba.
Cikin isa da kuma izza yake takunsa, sanye yake cikin full shigar uniform ɗinsa na soldiers, wanda sukayi matuƙar yi masa kyau, kana suka bayyana zallan kwarjini da cikar halittarsa, yanayin yanda kayan sukayi matuƙar yi masa kyau ne yasa Laylerh da ta ɗan ɗago kanta tana leƙensa ne ta kafeshi da idanunta, ganin shigar dake jikinsa ne yasata sakin baki da hanci tana kallonsa, tundaga kan ƙafarsa dake sanye cikin wasu haɗaɗɗun baƙaƙen takalma, sosai uniform ɗin suka zauna ajikinsa, yayinda ya ɗaura facing cap wanda yake shima na soldiers ɗinne akansa, sanadin hakanne kuwa yasa rumfar facing cap ɗin ya ɗan rufe idanunsa, ƙawataccen sajen dake kwance akan fuskarsa ne ke wani irin shining, gefe guda kuwa red shining lips ɗinsa ne keta walwalali, wanda hakan shike ƙara ƙawata kyawun fuskarsa, tabbas Maleek kyakkyawane, kuma tsayayyen Namiji me ɗauke da tarin kwarjini da kuma abubuwan burgewa.
Tabbas Batajin zata iya ɗauke kanta daga kallon kyakkyawan Namiji na musamman irinsa, wanda zata iya rantsuwa cewa babu wani namijin da uniform ɗin soldiers ya taɓa karɓansa kamar sa.
Ɗan lumshe idanunta tayi tare da lasan siraran laɓɓanta, duk da cewar basa kusa da juna amma gaba ɗaya ƙamshin daddaɗan turarensa ya cika falon, har takai ga ya ziyarci hancinta, numfashin dake ɗauke da daddaɗan ƙamshin turarensa ta shaƙa, tare da lumshe idanunta, acikin jiki da zuciyarta takejin wani abu nayi mata yawo, kamar yanda jini ke gudana ajikinta haka takejin wani abu na musamman adangane dashi, ganin ya nufi dining area ne yasa ta ɗauke idanunta akansa, har zuwa lokacin kuwa bata rufe bakinta dake a wangale ba, kwarjini da tsantsar haɗuwarsa ne suka mamaye zuciya da gangar jikinta, wanda hakan ya haifar mata da wani irin zazzafan shauƙi me ratsa gangar jiki.
Sake sakin ajiyar zuciya tayi akaro na barkatai, yayinda tayi imani cewa ganinsa da tayi ne sanadiyar rugurgujewan nutsuwarta.ÂÂ
Ɗan ƙara leƙa dinning area'n ɗin tayi, wanda tuni har ya ƙarasa ya zauna, yayinda ya bawa cikin falon baya, gefe guda kuwa su Abbu ne zaune,ciki kuwa harda Alhaji Ahmad Rufa'e wanda saboda wani babban dalili ya kashe zuwansa Kaduna da zaiyi yau ɗin.
Hannu tasa ta gyara hijab ɗin jikinta, tare da ƙoƙarin samawa kanta nutsuwa.
Cikin yanayin sanyi ta fito daga inda ta ɓoye, tare da ƙarasowa cikin falon, kaitsaye dinning area ɗin ta nufa.
Abbu na ganinta ya saki murmushi cikin kulawa yace.
"Good Morning Laylatu." ÂÂ
(Laylatu shine sunan da Abbu ke Æ™iranta idan yana cikin yanayin nishaÉ—i.)  Ɗan murmushin daya bayyana kyawawan haÆ™oranta tayi, cikin yanayin ta na sanyi tace. ÂÂ
"Am sorry Abbu Good Morning!."  ÂÂ
Murmushi Abbu yayi tare da cewa. "Morning my daughter, ya jikin naki?."
"Da sauƙi sosai." Tafaɗa tana me gyara zaman school bag ɗin dake goye abayanta.
Kallonta ta mayar ga Alhaji Ahmad Rufa'e, cikin girmamawa tace.ÂÂ
"Abba Ina kwana."
Murmushi Alhaji Ahmad É—in yayi, kasancewar tana kusa dashi yasashi É—an dafa kanta, cike da kulawa yace.
"Lafiya ƙalau Laylerh, ya jikin naki?."
Murmushi tayi tare da cewa.ÂÂ
"Da sauƙi."
Kai Alhaji Ahmad É—in ya jinjina tare da cewa. ÂÂ
"Allah Yaƙara sauƙi!."
Da "Ameen." Ta amsa tare da É—ago kanta, É—an satan kallon inda Najeeb yake tayi, kasancewar kallonta yake yasa idanunsu faÉ—awa cikin na juna, da sauri tayi Æ™asa da idanunta, hannayenta ta haÉ—e waje É—aya tare da soma wasa da Æ´an yatsunta, samun kanta tayi cikin wani irin yanayi, bakinta taÉ—an turo gaba ashagwaÉ“e tace.  "Ina Kwana." ÂÂ
Bai amsa mata ba saima cigaba da kallonta da yayi, baƙaramin kyau ƙananan laɓɓanta sukayi masa ba, musamman ma da tana maganan, wani irin hot feeling ɗinta yaji na ratsa duk jikinsa, lumshe idanunsa yayi tare da ɗan lashe lips ɗinsa, shikaɗai yasan me yakeji agame da Laylerh'n, lallai Laylerh macece wanda da kalma ɗaya kawai zata iya haukata nutsuwa da hankalin lafiyayyen ɗa Namiji.
Jin bai amsata bane yasa taÉ—an murgaÉ—a baki, cikin ranta tace.ÂÂ
"Dan kasamu ma angaisheka, bazan sake gaisheka ba to."
"Me yasa bazaki sake gaisheni ba to?." ÂÂ
Ya faÉ—a yana me yawo da idanunsa akanta.
Kyawawan idanunta taÉ—an zaro waje, domin a iya saninta ita da zuciyarta ne kaÉ—ai suke maganan, saboda haka bata tunanin cewa wani zaiji ta.
Kansa ya jinjina tare da É—age mata giransa É—aya alaman "Kina mamaki ne?."
Ƙasa tayi da kanta dan batasan me zata ce masa ba, sauƙe idanunta tayi akan ƙafafun M.JAY wanda suke sanye cikin baƙaƙen takalma, tabbas tana kwaɗayi da kuma son sake ɗaura idanunta akansa, ɗan ɗago kanta tayi tare da kai dubanta inda yake zaune, yayinda ya duƙar da kansa ƙasa yana me latsa wayarsa dake riƙe ahannunsa, saboda facing cap ɗin dake kansa ne yasa bata iya ganin full face ɗinsa.
Yatsun hannunta ta cigaba da cakuɗawa waje ɗaya, ahankali ta soma mamul mamul da bakinta, abun dake cikin zuciyarta shi take ƙoƙarin furtawa amma gaba ɗaya laɓɓanta sunyi mata nauyi, ƙirji da kuma zuciyarta ne ke bugawa, hakanan ta samu kanta da rasa duk wani ƙwarin guiwarta.
Ɗan rumtse idanunta tayi, tare da soma ƙoƙarin bawa zuciyarta confidence, kamar yanda bakinta ke rawa haka ma abun da takeson faɗi ɗin ke neman ƙwace mata.
Cikin sassanyar muryarta dake cracking tace. ÂÂ
"Gud Morning Ya... M....JAY....!" TafaÉ—a cikin dauriya tare da fisgo maganan nata.  ÂÂ
Sauƙan muryar ta acikin kunnuwansa ne yasa shi lumshe idanunsa dake abuɗe tare da tsaida dukkan abun da yakeyi, fararen teeth ɗinsa yasa tare da ɗan cizon laɓɓansa.
Wani irin abune yaji ya tsaya a ƙirjinsa, wanda hakan yasashi kasa ɗago kansa, hakanan yaji komai na ƙoƙarin ƙwace masa.
Jin shiru bai amsa ta bane, yasa taji gaba ɗaya jikinta yayi wani iri, lokaci ɗaya taji rauni na ƙoƙarin maye duk kan sassan jikinta, idanunta dake alumshe ne suka ciko da ƙwalla.
Batare da ta yarda ta sake kai idanunta garesa ba, ta ja É—aya daga cikin kujerun falon ta zauna.
Najeeb ne ya ɗago kansa tare da kallon Maleek ɗin, na ƴan wasu sakanni, dawo da kallonsa ga Laylerh yayi, wacce ta duƙar da kanta ƙasa, har yanzu wasa take da yatsun hannunta, yayinda idanunta ke cike da ƙwalla, duk da cewar bata yarda ta ɗago kanta kowa ya ga hakan ba.
Tsura mata ido yayi, lokaci É—aya yaji ba daÉ—i acikin ransa.
Plate É—in soyayyan dankali da ketchup É—in dake gabansa ya tura mata, cikin wani irin yanayin dake bayyana zallar abun dake cikin zuciyarsa yace.ÂÂ
"7:30 am ya kusa, kiyi sauri idan bahaka ba zakiyi latti!."
Jin abun daya faɗane yasa ta ɗan ɗago kai ta saci kallonsa, lokaci ɗaya ta soma ƙoƙarin shanye hawayen dake kwance acikin idonta, saidai duk yanda zata kai ga ɓoye hawayen nata dole idan mutum ya kalleta saiya gane.
Sanin haka yasa bata yarda ta haɗa idanu da Najeeb ɗin ba, bakuma zata iya ƙauracewa tayin abincinsa da yayi mata ba, domin gaba ɗaya zuciyarta tayi rauni, haka zalika tunaninta na ƙoƙarin tafiya ne wani waje daban.
A al'adarta bata fiye cin abinci da spoon ba hakan yasa ta sanya hannunta asanyaye ta soma cin abincin.
Lumshe idanu Najeeb yayi haka yakejin kaman ya sata ajikinsa ya bata abincin abaki, wani irin shauƙinta yakeji.
Maleek da haryanzu kansa ke ƙasa miƙewa tsaye yayi, batare daya sanya ko loman abincin dake gabansa abakinsa ba, ya soma ƙoƙarin barin dining area'n.
Hakanne yasa Abbu dasu Najeeb É—agowa duka suka kalleshi.
Cikin yanayin mamaki Abbu Jaheed yace.
"Aa Maleek ina zakaje kuma bayan bakaci abincin ba?."
Tsayawa daga tafiyan da yakeyi yayi, batare daya juyo ya kalli kowannensu ba yace.
"Naƙoshi."
Baijira me Abbun zaice ba yasa kai ya bar wajen, kaitsaye ya nufi É—akinsa.
Da idanu duk su Abbun suka bishi, banda Laylerh wanda takasa É—ago kanta.
Kai Kawai Abbu ya girgiza tare da cigaba da cin abincinsa.
Tanajin motsin rufe ƙofarsa alaman ya shiga part ɗinsa ne, ta ture plate din abincin dake gabanta, tare da miƙewa tsaye school bag ɗinta ta ɗauka ta rataya.
Abbu ne ya É—ago kai ya dubeta, cikin kulawa yace.ÂÂ
"Kema kin Æ™oshi ko?."  ÂÂ
Kai ta jinjina masa alaman "Eh."  Kallon plate ɗin abincin nata Abbu yayi wanda ko rabin rabi bataci ba.
Kansa kawai ya girgiza tare daɗan sakin mumushi, dama yasan hakan zata faru, ya jima da fahimtar cewa LAYLERH da MALEEK abu ɗaya ne, zuciya da ruhinsu duk iri ɗaya ne. Gyara zamansa yayi kana yace.  "Kije driver ya kaiki."
Kamar daman jiran hakan take cikin sauri tace "To." ahanzarce ta juya ta nufi hanyar fita daga falon.
Miƙewa Najeeb yayi cikin kulawa yace.
"Nima fita zanyi zan sauƙeta amakarantar idan yaso sai driver ya ɗauko ta."
Jinjina masa kai su Abbu sukayi tare da ci gaba da cin abincinsu.
M.Jay
Yana shiga part É—in nasa kaitsaye bedroom É—insa ya wuce.
Maida ƙofar yayi ya rufe, ahankali ya ƙarasa jikin window'n dake cikin ɗakin nasa, wanda daga nan wajen kana iya hango duk abun da ke faruwa a compound ɗin gidan.
Idanunsa wanda suka sanja launi daga farare zuwa jajaye ya ware, tare da fesar da wani irin numfashi me zafi, duka hannayensa biyu ya zura acikin aljihun wandonsa, tare da maida ganinsa zuwa ga compound É—in gidan, daidai lokacin ne kuma Laylerh ta fito.
Najeeb na biye da ita abaya.
Ganin Laylerh da Najeeb ne ya sashi dunƙule hannunsa dake cikin aljihun wandonsa.
Idanu ya tsurawa Laylerh'n, yanajin abubuwa da yawa na yawo acikin jikinsa, tabbas LAYLERH ƙaddarar sa ce, wacce akullum akuma koda yaushe take yawo acikin jininsa, ako da yaushe akuma kowacce rana wani abu na SIRRI daya ɓoye ƙoƙarin bayyanar da kansa yake, tabbas yanaji ajikinsa cewa acikin BIYU za ayi ƊAYA.
Laylerh da jin takun mutum abayanta yasata juyawa, ganin Najeeb agab da ita ne yasa ta ɗan tsaya tare da matsawa gefe, kana ta sadda kanta ƙasa.
Wucewa gaba yayi tare da cewa. "Kibiyoni mota na sauƙeki a school."
Bin bayansa tayi da ido har ya ƙarasa jikin motarsa.
Sai alokocin ta lura da shigan dake jikinsa, na wani haÉ—aÉ—É—en yadi me kalan coffee wanda hakan yasa farar fatarsa bayayyana, duk da cewa ma bashi da haske sosai, saidai kuma white colour É—insa is a natural.
Ayanayin da takejin kanta aciki yasa bata tunanin zata iya yi masa musu, asanyaye ta nufi wajen da motar tasa take.
Murfin motar ta buÉ—e, nan gefen me zaman banza ta shiga tare da jawo murfin motar ta rufe.
Ƙamshin turarensa daya cika motar ne yasata lumshe idanunta, tare da kwantar da kanta ajikin kujeran da take kai.
Key Najeeb yayiwa motar yayinda me gadi ya wangale musu gate É—in gidan suka fice.
Ganin ficewarsu daga gidan ne ya sashi juya baya, dan yaga komai da ya faru.
Wani irin abu me ɗacine yaji ya ziyarci maƙoshinsa, yayinda har yanzu hannayensa ke dunƙule.
Hakanan yakejin zuciyarsa na tafasa, lokaci É—aya mood É—insa ya sauya, idanunsa ne suka sakeyin ja. Cikin wani irin yanayi haka ya nufi hanyar fita daga É—akin.
Koda ya fito compound ɗin gidan ganinsa da full uniform yasa duk sojojinsa shiga hayyacinsu, yana shiga mota kuwa suma suka shiga tasu motar.
Yanayin yanda Abdoul yaga fuskar ogan nasu a murtuƙe ne yasashi jan motar a 360 suka fice daga cikin gidan, domin haka nan Abdul ya saba matuƙar yaga ran Captain ɗin aɓace to yasan abun zai iya shafansa matuƙar yayi tuƙi ahankali.
Gudu suke shararawa sosai akan titin hakanne yasa cutie É—insa dake bacci ta tashi, ganinsa da tayi ne yasa ta hayewa saman jikinsa.
Ɗago idanunsa da suka yi jajur yayi batare daya kalli cutie ɗin nasa ba ya hankaɗata gefe har saida ta buge da murfin motar, wani ƴar siririn ƙara ta saki tare da faɗuwa awajen.
Jin kukan magen ne yasa Abdul ƙara gudun motar, saboda yasan ba abu me sauƙi bane zaisa Captain ya yi wurgi da magensa, yasan M.J ɗin sarai kwata kwata bai iya ɓacin rai da hasala ba.
ÆÂangaren Laylerh kuwa tun da suka kama hanyar makarantar koda sau É—aya ne bata buÉ—e idanunta ba, gaba É—aya zuciyarta tayi nisa awajen tunanin Maleek.
Batasan meyasa take yawan jin rauni da kasala akan duk lamarin daya shafesa ba.
Aɓangaren Najeeb ma kuwa hakanne ya kasance kamar yanda zuciyarta tayi nisa atunanin wani abu daban, haka shima tasa zuciyar, saidai tunanin nasu ya kasance mabanbantan juna, saboda izuwa yanzu tunaninsa ya fara karkata ga abun da zuciyarsa ke raya masa akan Laylerh'n.
Ahaka suka ƙaraso bakin tamfatsetsen gate ɗin makarantar tasu.
Jin motar ta tsaya ne yasa ta bude idanunta ganin sun iso bakin makarantar ne yasa ta buÉ—e murfin motar ta fita.
Sam manta da cewar Najeeb É—inne ya kawota shiyasa ko waiwayowa batayi ta masa godiya ba.
Idanunsa ya zuba mata harta shige cikin makarantar.
Wani murmushi me ɗauke da ma'anoni daban daban yayi, tabbas ya hango abubuwa da yawa acikin idanun Laylerh, abu mafi girma daya gani acikin idanun nata kuwa shine RAUNI lallai dole da wannan raunin nata zaiyi amfani wajen biyan buƙata da kuma isar da shawarar zuciyarsa.
Cike da yiwa kansa fatan samun nasara yayiwa motarsa key kaitsaye yabar arean makarantar.
Laylerh.
Gaba ɗaya yau haka ta ƙare wuninta acikin school ɗin cikin rashin jin daɗin yanayin, abun da yafi damunta ma shine yanda take yawan jin faɗuwar gaba.
Duk yanda Teemah taso jan Laylerh'n ajiki hakan baisamu ba, dole ta ƙyaleta, dan yanayin damuwa ya bayyana ƙarara akan fuskarta.
Haka Teemah taje tayiyo tsokanar ta aka biyota har cikin aji aka dinga dambe da ita, yayinda ta kafe kai da fata cewar itace me gaskiya bayan kuma itace da tsokana, Laylerh kam kallonsu kawai takeyi, dan idan da sabo ta saba da neman faɗan Teemah kuma bata taro daidai da ita ƴan SS 3 take tsokanowa suzo ayitayi da ita gashi sam bakinta baya taɓa mutuwa koda kuwa za a dakata, to awannan karan ɗin ma dai Teemah taji ajikinta, saida waƴanda ta tsokano ɗin suka gaji da faɗan dan kansu suka tafi, kasancewar bakin Teemah'n kwata kwata yaƙi mutuwa.
Koda aka tashesu daga makarantar atare suka jero su dukansu suka fito bakin makarantar, Teemah sai masifa takewa Laylerh wae ae tana gani akazo har aji akaci zalinta bata kula ba, ita dai batace mata komai ba, dan tasan koda ma tafaɗa Teemah bazata taɓa sanja halinta ba.
Driver'n Abbu ne yafara zuwa É—aukar
Laylerh, kafun itama Teemah daga baya akazo aka É—auketa.
Har sukayi nisa a tafiyar tasu ta kasa daidaita nutsuwarta, still haka takejin heart ɗinta na bugawa da sauri. kwantar da bayanta tayi ajikin kujeran motar tare da ɗan lumshe idanunta, yayinda take saƙa abubuwa da yawa acikin ranta.
Ahaka har suka iso gida.
Tana fita a motar kaitsaye É—akinta ta wuce, yanayin yanda ake É—an busa sassanyar isaka agarin ne yasa koda ta cire uniform É—inta, wani kakkauran doguwar riga ta saka, yunwa takeji sosai shiyasa kaitsaye ta nufi kitchine dan samawa kanta abun da zataci.
Momy.
Zaune take abakin gado yayinda gaba ɗaya fari'a da kuma annurin fuskarta suka kau, gefenta kuwa Aunty Aina'u ce dake ta faman taunar cheewing gum, tana me karkaɗa ƙafanta.
Cikin yanayin fushi Momy tace.  "Banason Laylerh Aina'u, banason yarinyar nan, ban kuma taɓa jin tsanarta me tsanani acikin raina ba kamar yau danaji ƙudirin Alhaji akanta, ki bani mafita Aina'u dan narantse bazan taɓa bari abun dake zuciyar Alhaji ya bayyana har ya aiwatar da abun da yake so ba."
Murmushi Aunty Aina'u tayi tare da gyara zamanta cikin halin ko in kula da kuma bayyanar da zallan abun dake cikin zuciyarta tace. ÂÂ
"Dole saikin kashe Laylerh kafun ki samu ainihin haƙiƙanin abun da kikeso, saboda haka ki kasheta kawai!."
Murmushi Momy tayi tare da miƙewa tsaye, cike dajin daɗin shawarar da Aina'un ta bata tace.
"Tabbas zan kashe Laylerh Aina'u amma bada hannu na ba, Zan kashe Laylerh ne ta hanyar Captain M.J, najima da wani buri araina wanda nake buri da fatan cimmasa, tabbas Captain da kansa zai ruguza rayuwar Laylerh."
Murmushi sukayi su dukansu domin kowacce da abun da take saƙawa acikin ranta.
Acan falon Abbu kuwa Alhaji Ahmad ne da Abbu zaune, akan lallausan darduman da ya ƙawata tsakiyan falon.
Cikin nutsuwa Abbu ya É—ago kai ya dubi Alhaji Ahmad dake ta faman aikin duba wasu files dake gabansa.
Gyara zama Abbu yayi tare da sakin ajiyar zuciya.
Cikin muryarsa da tayi sanyi yace.ÂÂ
"Nasa ka auren Laylerh nan da 1 month."
ÆŠago kai Alhaji Ahmad yayi tare da É—an sakin murmushi,cikin halin dattako yace.
"Tabbas nasan da hakan Alhaji Jaheed, saidai bansan meyasa kaketa yawan maimaita hakan ba tun É—azu."
Ajiyar zuciya Abbu ya sauƙe tare da cewa.
"Bansan Ya Laylerh zata ɗauki abun ba, saboda har yanzu ita ɗin yarinyace, tabbas nasan ba zataƙi zaɓina ba, saidai kuma bansan me yasa nakejin faɗuwar gaba agame da hakan ba inajin kamar akwai wani gurbi daban cike ba."
Murmushi Alhaji Ahmad Rufa'e yayi tare da ɗan bubbuga kafaɗan Abokin nasa cikin kulawa tare dason basa ƙarfin guiwa yace.
"Insha Allah bakayiwa Laylerh zaɓen tumun dare ba, ina me tabbatar maka da cewar kamiƙa Laylerh a inda za'a kula da ita namaka alƙawari cewa Laylerh bazatayi kuka ba, kai Uba ne nagari kuma kayi abun daya dace."
Murmushi Abbu yayi tare da miƙewa tsaye yaɗan soma zagaye falon, cikin son ƙarfafawa kansa guiwa da kuma cika alƙawarin daya ɗauka yace.
"Insha Allah nima haka nake fata."
Maleek.
Shigowarsa cikin falon kenan, kaitsaye ya nufi dining area, kujera yaja ya zauna tare da cire facing cap din dake kansa, murfin bootle water'n dake hannunsa ya buÉ—e tare da juye ruwan dake cikin goran akansa, sanyin ruwan daya ratsa sa ne ya sashi kifa kansa akan table tare da sakin ajiyar zuciya.
Laylerh fitowarta daga kitchine É—in kenan hannunta É—auke da plate É—in indomie'n da ta dafa.
Kaitsaye danning area ta nufa, idanunta akan indomie'n nata har ta ƙaraso dinning ɗin.
Ƙamshin turarensa da tajine yasata ɗaga idanunta, take kuwa ta sauƙe ganinta akansa.
Kallonsa da tayi kuwa yayi daidai da É—ago kansa da yayi.
Akaron farko kenan da tafara sa idanunta acikin nasa kusa da kusa.
Wani irin matsanancin shock ne ya shigeta asakamakon hakan, lokaci ɗaya gaba ɗaya jikinta ya fara kakkarwa, kanta ta shiga girgizawa yayinda laɓɓan bakinta suka soma vibrating, ɗan jan jikinta baya tashiga yi, aruɗe ta saki plate ɗin dake hannunta, tare da sakin wani razanannen ƙara.
*(Menene buƙatar Najeeb akan Laylerh? sannan kuma me yakeso awajenta? wani buri yakeson cimmawa akanta? Aurenta yakeson ko kuwa wani abu yakeso awajenta na daban? WANENE MIJIN DA ABBU ya zaɓawa Laylerh? Me kuma Momy zata aikata akan Laylerh? Miye Laylerh ta gani akan fuskar Maleek daya ke ƙoƙarin fitar da ita a hayyacinta? Lallai Tabbas akwai wani abu, BURI ƊAYA ne ke yawo da kuma gudana acikin zuciyar Laylerh da kuma Maleek. Shin Laylerh Mallakin Wayene acikin MALEEK da NAJEEB? Kada ku manta tun da farko nafaɗa muku cewa ba irin yanda kuke tunani bane, cos ba amayi komai ba, ko wasan ma ba a fara ba.)*
*Karku manta game buƙata zata turo katin MTN na 300 ko kuma ta turo 300 ta account number.*
*Whatsapp number 07017879464*
*Account number 0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Ja'iz Bank.*
*Thank You*
   *fatymasardauna*
1/19/21, 8:11 PM - Ummi Tandama:  ðŸÂ‡ðŸÂ‡ðŸÂ‡ðŸÂ‡ðŸÂ‡ðŸÂ‡ðŸÂ‡ðŸÂ‡ðŸÂ‡ðŸÂ‡
    *LAYLERH MALEEK*
   *Writing By*
*fatymasardauna*
*(Wannan littafin na kuÉ—i ne, kada ki karanta idan kinsan baki biya ba, zaki iya turo kuÉ—inki 300 ta account number 0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna. Whatsapp nomber 07017879464)*
    *Chapter 11*
Hannayenta ta sanya tare da toshe kunnuwanta, wanda hakan yasa indomie'n dake cikin plate ɗin zubewa akan ƙafanta.
razanannen Æ™aran da ta saki ne yayi daidai da shigowar Abbu cikin falon.  ÂÂ
Yanayin yanda jikinta ke ta faman karkarwa ne yasa Æ™afafunta Æ™oÆ™arin kasa É—aukanta, take tatafi luu zata faÉ—i. ÂÂ
Cikin hanzari ya sanya hannunsa ya tallafota ta faÉ—a jikinsa, take wani irin shock ya shiga yawo ajikinsa, kyawawan idanunsa ya sauÆ™e akan cute face É—inta, tare da kai dubansa ga lips É—inta daketa faman É“ari.  ÂÂ
"Hey!." Ya faɗa cikin wata irin haɗaɗɗiyar lion voice ɗinsa, wanda dadin sauti da amonta ya ratsa cikin kunnuwanta.
Wani irin sassanyar iska ne ya shiga ratsa dukkan illahirin jikinta, sannu ahankali ta soma sakin numfashi, tare da É—an bude kyawawan idanunta wanda lokaci daya suka bayyana asali da kuma zallar kalansu na sexy eyes.
Adisashe ta soma ganin kyakkyawar fuskarsa, tare da jefa idanunta acikin nasa, lokaci daya taji kwakwalwarta na kokarin birkicewa, tabbas wayannan idanun da take gani ayanzu sune idanun da tajima tanaso da kuma burin gani agaba daya rayuwarta, wayannan idanun sune idanun da suka zama kaman abincin ruhinta, mafarkinta da kuma dukkan fatan ta.
Wani irin zubawa tsikar jikinta ya shiga yi, hakan yasa sexy eyes dinta soma lumshewa, take kuwa hawaye suka soma gangarowa daga cikin idanun nata.
Tabbas bazata iya jurewa yanayin da takejin kanta aciki ba, haka nan takejin duniyar na juya mata.
Narkakkun idanunsa masu oily ya zuba mata, domin ya lura da tana kokarin fita cikin hayyacinta ne.   Fuskarsa dake dauke da danshin ruwa ya hade, cikin husky voice dinsa yace.
"Ke what's wrong?". Shiru tayi tare da sake sakar masa jikinta, ganin da yayi cewar batayi motsi bane ya sashi zare hannunsa dake bayanta, wanda dama hannun nasa ne ke riƙe da ita.
Sakinta da yayine yasa tatafi luu zata faÉ—i.
"MALEEK!".ÂÂ
Abbou da tun É—azu yake tsaye yana kallonsu ya kira sunansa, jin muryar Abbou'n acikin kunnensa ne ya sashi saurin sake riÆ™ota, hakanne yasa bata kae ga faÉ—uwa Æ™asa ba.   ÂÂ
Ƙarasowa dining area ɗin Abbou Jaheed yayi, gaba daya fuskarsa babu alaman walwala.
Kallon Maleek ɗin yayi tare da kau da kansa gefe "Me kayi mata?" Ya tambayi Maleek ɗin yana me kallon Laylerh'n.
Kyawawan fararen idanunsa yadan zaro, tare da rolling dinsu alaman
"Me nayi mata kuma?."
Fuska Abbou ya haɗe tare da cewa. "Tabbas ruwa baya tsami banza, ni nasan cewa Laylerh bazata taɓa faɗuwa haka kawai ba, dole saidai wani abu tagani daga gareka.".       Jin hakane ya sashi sakin murmushin da shi kaɗai ya baiwa kansa sanin ma'arsa, ahankali ya ɗago ya kalli Abbou'n, kaman zaice wani Abu kuma sai ya kuma maida kansa kasa.
Laylerh da gaba daya ta Shiga shock din ganin idanunsa, jin muryan Abbou Jaheed akunnenta ne yasa ta fashewa da kuka, lokaci daya taji gaba daya zuciyarta tayi rauni.   ÂÂ
Ganin yanda ta fashe da kuka ne ya sashi lumshe idanunsa, lokaci daya yasa tafukan hannunsa ya rufe fuskarsa.
Hannun Laylerh'n Abbou ya kama tare da dagota tsaye cikin kulawa yace.
" Stop crying Laylerh, faÉ—amin me ya miki kike kuka?."
Kanta ta Dan shiga girgizawa tare da kokarin shanye hawayen dake idanun nata.
Hannunta Abbou ya kama tare da zaunar da ita akan daya daga cikin kujerun falon.
Kallon ƙafarta yayi wanda tuni fatar wajen ya somayin ja, saboda yanda zafin indomie'n ya kama fatar ta.
ÆŠago kai Abbou yayi ya kalli Maleek É—in, wanda har yanzu fuskarsa ke cikin tafin hanunsa.       ÂÂ
Kansa kawai ya girgiza, da kansa ya ɗauko ƙanƙara acikin fridge tare da ɗaurawa Laylerh'n asaman ƙafarta inda indomie din ya ƙona ta.
Dubanta Abbou yayi cikin kulawa yace."Kije É—aki ki kwanta kinji, nasan zuwa anjima ciwon zai daina miki zafi."
Kanta ta jinjina tare da É—an jan sheshshekan kuka.
Mikewa tsaye tayi haÉ—e da É—an É—aga Æ™afarta ta soma takawa ahankali, taku biyu kadai tayi ta tsaya da tafiyan tare da sakin yar siririyar kara, zafin da ta ji sosae ne yasata rumtse idanu, tare da cije laɓɓanta.   ÂÂ
Cikin zafi da kuma radadin da takeji tace "Abbu kafana zafi, bazan iya tafiya ba." Yanayin yanda tayi maganan tana me yarfa yan yatsun hannunta ne yasa Abbou jin tausayinta.
Kallon Maleek Abboun yayi cikin yanayin bada umarni yace.
"M.J ka mata ka kaita É—aki please bari zan kira Dr."
Jin abun da Abbou'n ya fada ne yasashi saurin dago kansa.
Kai Abbu dake kallonsa ya jinjina masa tare da haÉ—e fuska.
Bottle watern dake aje a gabansa ya zubawa ido, yayinda zuciyarsa ta Shiga saka masa abubuwa da yawa.  Ajiyar zuciya ya sauke tare da dagowa ya kalli inda Laylerh ke tsaye, wanda tsawon one minute kenan da take tsaye ta kasa tafiya.
Kujeran da yake zaune akai ya É—an baya tare da mikewa tsaye, ya nufi inda Laylerh'n ke tsaye, yayinda gaba É—aya idanunta suka kaÉ—a sukayi ja.   Hannunsa ya É—aura akan kafaÉ—arta, wanda hakan bisa dole ya tilasta mata juyowa, É—an ranÆ™wafawa yayi   batare da tunani ko tsammani ba kawai taji ya É—aga ta caÉ—ak.  ÂÂ
wani irin abu me kama da shocking ne ya shiga yawo ajikinta.
Idanunta ta rumtse da Æ™arfi, domin hakan ya zama wani baÆ™on yanayi na musamman agareta, akaron farko kenan da ta samu kusanci dashi har haka, daddaÉ—an Æ™amshin turarensa ne ya soma ratsa hancinta, tare da cakuÉ—ewa da numfashinta.   ÂÂ
Samun kanta ajikinsa da tayi, yasa bata da wani zaÉ“i daya wuce maÆ™ale wuyansa da hannayenta, Cikin nutsuwa ya nufi hanyar da zai sadashi da É—akinta, daga gefe guda kuwa irin yanayin riÆ™on da yayi mata ne yasa tsikar jikinsa mimmiÆ™ewa, lokaci É—aya brain É—insa ta soma ƙoÆ™arin juya tunaninsa zuwa wani waje daban. ÂÂ
Ƙarasowarsu bakin Æ™ofar É—akin nata ne yasa shi tura Æ™ofar da Æ™afarsa, wanda hakan yasa Æ™ofar buÉ—ewa da kanta. ÂÂ
Yana kutsa kansa cikin É—akin sassanyan Æ™amshin cool perfumed É—inta ne ya ratsa cikin hancinsa, hakanne ya sashi É—an lumshe idanunsa, shi mutum ne me tsananin son Æ™amshi wannan ne yasa hancinsa baya raina Æ™anshi aduk inda yake.     Ƙarasowa cikin É—akin yayi, sai kuma alokacin ne ya kai dubansa kan kyakkyawar fuskarta.        ÂÂ
Wanda har yanzu idanunta alumshe suke, yayinda zara zaran eye lashes ɗinta ke jiƙe da danshin ruwan hawaye, dawo da kallonsa kan ƙananan lips ɗinta yayi, wanda duk ta tattaune su da teeth ɗinta hakan yasa sukayi ja, take yaji wani irin abu na mamaye duk ilahirin jikinsa, wanda hakan ya sashi saurin ɗauke idanunsa akanta.
Æ™arasawa kan É—an madaidaicin gadon nata yayi, ahankali ya soma Æ™oÆ™arin zareta daga jikinsa, tare da kwantar da ita akan gadon. ÂÂ
Jin ya kwantar da ita akan gado ne yasa ta saurin juya masa baya tare da cusa kanta acikin pillow, tabbas da ace zai ga yanda Æ™irji da zuciyarta ke bugawa sanadin É—aukarta da yayi, to da bai É—auketa a daddaÉ—an jikinsa kamar yanda yayi ayanzun ba.  ÂÂ
ÆŠan lumshe idanunsa yayi tare kuma da buÉ—esu alokaci guda.
Akaro na biyu kenan da tun dawowansa ya tsura mata idanunsa masu rikitata.   ÂÂ
Kallon dogon dunƙulallen gashin kanta wanda ya baje akan pillown da ta ɗaura kanta sanadin juya masa bayan da tayi yayi, ahankali ya soma yawo da idanunsa akanta, har zuwa kan hips ɗinta da suka sake cikowa, ƙasa yayi da kansa ahankali ya ɗan soma jan jikinsa baya, tare da zuba hannayensa acikin aljihun wandon jeans ɗin dake jikinsa. Abu ɗaya ne ke yawo acikin zuciyarsa, wanda akullum kuma ako da yaushe ke sukan zuciyarsa, wanda hakan kuwa shi ya haifar masa da rauni me girma acikin rayuwarsa, bayajin zai iya jure kallonta,domin yayi imani cewa itace raunin zuciya da kuma rayuwarsa, sannan kuma ya jima da sanin cewa itace ƙaddara mafi girma agaresa, tabbas akwai wani abu dake kwance acikin ƙirjinsa, wanda yake azabtar da zuciyarsa akowacce rana. Baisan meyasa yazama haka ba, baisan kuma dalilin dayasa raunin zuciyarsa ke ƙara fallasa kansa akowacce rana ba, baya fatan wani lokaci yazo masa da zai kasa jure abun da yake ji.
Kansa ya soma girgizawa, sakamakon yanda yaji kasala na Æ™oÆ™arin sauÆ™ar masa, cikin sauri ya juya ya fice daga cikin É—akin.         ÂÂ
Jin alaman ficewarsa daga É—akin ne yasa Laylerh dake kwance buÉ—e idanunta, tare da juyowa tabi Æ™ofar É—aÆ™in da kallo, wani irin sanyi ne ke ratsa duk jikinta, yayinda daddaÉ—an Æ™amshinsa ya kama numfashinta.   Idanunta ta lumshe wanda hakan ya bawa hawayen dake cikin idanun nata daman gangarowa.  ÂÂ
Tabbas yau ranace ta musamman agareni, mutumin da nake gani acikin mafarkina ya bayyana, "Ya. M.Jay" tafaɗa cikin tsananin shauƙin da takejin kanta aciki.
Sam bata taɓa kawo cewa M.JAY shine mamallakin waƴannan kyawawan idanun da take gani acikin mafarkinta ba.
Hannu tasa tare da dafe daidai saitin zuciyarta dake ta faman bugawa da Æ™arfi.     ÂÂ
Tuno da yanayin da kuma zalla. kyawun eye balls dinsa da tayi ne, yasa ta Æ™anÆ™ame jikinta waje É—aya, pillown dake gefenta tayi rungume tare da É—an sakin murmushi.  ÂÂ
"Jikin ka akwai daÉ—i ya M.Jay, haka ma Æ™amshin ka komai naka akwai daÉ—i na tabbatar da hakan!."    TafaÉ—i hakan cikin yanayin dake bayyana zallar abun dake zuciyarta, take taji ta nemi duk wani zafin da Æ™afartata keyi mata ta rasa.     ÂÂ
ÆÂangaren Maleek kuwa yana fita daga cikin É—akin nata kai tsaye part É—insa ya wuce.  ÂÂ
Yana shiga cikin bedroom ya turo ƙofar dakin nasa ya rufe, tare da murzawa ƙofar key.
Ahankali ya É—an jingina bayansa da jikin Æ™ofar, tare da lumshe gajiyayyun idanunsa. ÂÂ
Bai tabbatar da abun da yakeji ba sai ayau É—in, Lallai ne akan Laylerh komai na musamman ne agareshi. BuÉ—e idanunsa yayi haÉ—e da Æ™arasowa cikin É—akin, kan wata haÉ—aÉ—É—iyar kujera ya zauna tare da sanya hannu ya dafe kansa, still ajiyar zuciya ya sauÆ™e, tare da É—an dafe Æ™irjinsa.    Abubuwa da yawa ne ke yawo acikin tunaninsa, ahankali ya soma É—an murza gold ring É—in dake hannunsa, daga gefe guda kuwa idanunsa ne suka kaÉ—a sukayi ja, tabbas tausayi da rauni sun riga da sunyi tasiri acikin rayuwarsa, wanda sanadin haka ako da yaushe yakanjin cewa ba akan daidai yake ba, ako da yaushe LAYLERH ce, kaman yanda jini ke gudana acikin jikinsa haka zanen Æ™addaranta ke bibiyan rayuwarsa.    Ƙaran wayarsa ne ya katsesa daga duniyar tunanin daya ke Æ™oÆ™arin faÉ—awa.  ÂÂ
Kallon wayar tasa yayi, ganin sunan Abbou Jaheed na yawo akan screen É—in wayar ne ya sashi É—agawa tare da kara wayar akan kunnensa.   ÂÂ
Abbou Jaheed dake zaune jin Maleek ya É—aga wayarne yasa shi cewa.  "Idan kayi sallan Isha kazo dinning area inason ganinka."   ÂÂ
"To." ya amsa cikin wata irin murya, dan lokaci É—aya yaji Æ™irjinsa na bugawa.  ÂÂ
Take Abbou Jaheed na gama jawabinsa ya kashe wayar. ÂÂ
Jin Abboun ya katse Æ™iran ne ya sashi aje tasa wayar shima, tare da miÆ™ewa tsaye ya shige bathroom.    ÂÂ
Ruwa ya sakarwa kansa saboda hakanne kaÉ—ai zai sama masa relief daga abun da yake ji a zuciyarsa.    ÂÂ
Najeeb..
tsawon mintuna 20 kenan da ya keta juyi akan makeken gadonsa, gaba É—aya tunanin Laylerh ya hanawa Æ™waÆ™walwarsa sukuni, wani irin hot feeling yakeji adangane da ita na ratsa duk ilahirin jikinsa, hakanne yasa yafara tunanin cewa abun daya É—auka da wasa zai iya fin Æ™arfin tunaninsa.  Jin ana Æ™iran sallan Isha ne ya sashi miÆ™ewa, ya shige toilet tare da É—auro alwala. Yana fitowa kaitsaye ya wuce masallaci. ÂÂ
7:30 pm daidai Abbou Jaheed da Alhaji Ahamad Rufae suka shigo cikin gidan, yayinda Najeeb ke biye dasu abaya, ahaka har suka Æ™araso cikin falon. Yayinda yau Momy da kanta ta shirya musu diner, bayan tasa Larai ta girka musu foods kala kala haÉ—i da drinks.   ÂÂ
Kujera Abbou Jaheed yaja ya zauna tare da duban Larai dake ta aikin mopping tiles É—in falon, yace ta kira masa Laylerh. Cikin girmamawa kuwa tace "To ranka shi dade."  Ahanzarce ta nufi É—akin Laylerhn.  ÂÂ
Laylerh dake kwance tayi hugging pillow,yayinda zuciyarta tayi nisa cikin tunanin Maleek wanda hakan yasa ita kaÉ—ai take ta sakin murmushi.  Jin ana knocking Æ™ofar É—akin tane yasa ta miÆ™ewa, ahankali take É—an taka kafarta wanda tuni ta ware ta daina yi mata zafi sosai. Ƙarasawa jikin Æ™ofar tayi tare da buÉ—ewa.    ÂÂ
Ganin Larai tsaye abakin Æ™ofarne yasata sakin murmushi, cikin son bawa Larai'n girmanta tace. "Inna Larai ki shigo mana." ÂÂ
Murmushi Larai tayi tare da cewa. "Aa ai bama sai na shigo ba, dama Alhaji ne yace na Æ™irawoki."  murmushi Laylerh tayi tare da cewa to gani nan zuwa.  ÂÂ
Komawa cikin É—akin tayi, kaitsaye drawer É—inta ta buÉ—e wani farin É—an Æ™aramin mayafi ta É—auka tare da yane kanta dashi, cikin nutsuwa ta nufi falon dan amsa Æ™iran da Abboun ke mata.   ÂÂ
Tana shigowa cikin falon tayi ido huɗu da Najeeb wanda dama tun zamansa awajen jiran fitowarta yake.   Kasa tayi da kanta tare da ƙarasowa dining area ɗin.
Kujera taja ta zauna, cikin salon shagwaÉ“an da sometimes bata sanin tanayi tace "Abbou gani."  Murmushi Abbou yayi sannan cikin kulawa yace. ÂÂ
"Ya ƙafan naki ta daina zafi ko?."  kai ta gyaɗa masa alaman.  "Eh."   Kanta yaɗan shafa cikin tausayi haɗi da ƙaunarta yace. "Good girl tashi kiyi seving ɗinmu to."   Murmushi ita ɗinma tayi, wanda har acikin ranta tanajin daɗin kulawan da Abbou Jaheed ke bata, tabbas tarasa uwa uba amma Abbou na iyaka ƙoƙarinsa wajen ganin batayi kukan maraici ba.
Cikin nutsuwa ta soma Æ™oÆ™arin seving É—insu. Daidai lokacin M.Jay ya shigo cikin falon. Ɗan Lumshe idanunta tayi tare da shaÆ™an daddaÉ—an Æ™amshin turarensa da ya kawowa hancinta ziyara, jin motsin Æ™arasowansa dining area dinne yasa tajin wani irin sanyi na ratsa jikinta, take ta kwaÉ—aitu da son É—aura idanunta akansa.  Jan kujera tayi ta zauna tare da É—an satan kallon gefen da yake, sosai yayi kyau cikin shigar white shirt, da kuma white trouser É—in dake jikinsa.  ÂÂ
Maida kanta Æ™asa tayi tare da jawo plate É—in abincinta gabanta, kasancewar yunwa takeji sosai yasanya bata jira komai ba ta fara cin abincin.  ÂÂ
Maleek kuwa tun isowarsa wajen bai É—aga kai ya kalli kowannen su ba, wani haÉ—aÉ—É—en cup ya É—auka tare da haÉ—awa kansa tea, komawa yayi ya zauna ahankali ya ke É—an sipping tea É—in yayinda rabin nutsuwarsa ke kan wayar dake hannun sa.   ÂÂ
ÆŠagowa Abbou Jaheed dake cin abinci yayi ya dubi kowannensu. ÂÂ
Tsaida cin abincin nasa yayi tare dayin É—an gyaran murya. ÂÂ
Cikin kulawa haÉ—i da nuna musu amfanin abun da yakeson faÉ—a yace. "Tabbas duk wani buri da kuma fatan uba nagari shine farinciki da kuma samun nasaran ƳaÆ´ansa." Ɗan jim yayi tare da sauÆ™e ajiyar zuciya, kallon Laylerh dake cin abinci yayi cikin kulawa haÉ—i da tsananin tausayinta yaÆ™ira sunanta.   "LAYLERH!."    ÂÂ
akaron farko kenan da taji Æ™iran sunanta da Abbou'n yayi ya tsinkar mata da zuciya, tsaida cin abincin nata tayi tare da É—ago kai ta kalli Abou'n.   ÂÂ
Hannunta ya kamo cikin kulawa yace.  "Laylerh ke Æ´ata ce da nakejin soyayyarki acikin raina, duk da nasan cewar banine na haifeki ba,amma koda sau É—aya ban taÉ“a kallonki amatsayin wacce ba jinina ba, haka zalika ako da yaushe matsayin Uba nake agareki, kuma nasan ina da haƙƙin da zanyi miki zaÉ“i na gari arayuwa, nayi imani cewa kamar yanda bazan iya cutar da yayanki Maleek ba haka kema bazan iya cutar dake ba, tabbas kina da matsayi me girma awajena Laylerh, wanda hakan yasa na yanke wani hukunci batare da nayi shawara da kowa ba, fatana da kuma burina ako da yaushe shine ki karÉ“i zaÉ“in da nayi miki hannu bibbiyu!."  Ɗan numfasawa yayi tare da sake riÆ™e hannunta Æ™am, idanunsa ne suka ciko da Æ™walla, saboda lokaci É—aya yaji Rasuwar Æ™aninsa Abbou Mahmoud ya dawo masa sabuwa, dan tabbas da ace yana nan ayau shine zaiyiwa Laylerh'n haka.   ÂÂ
Ganin Hawaye a idanun Abboun ne yasa Laylerh zaro idanunta, cikin tsananin mamaki haÉ—i da kaÉ—uwa ta soma girgiza kai, cikin muryarta dake ckracking tace. "Please Abbou dan Allah, Ka umarceni akan komai bazan taÉ“a saÉ“a maka ba, please Abbou dan Allah karka bari hawaye sufita daga cikin idanunka saboda ni!."  tayi maganar Æ™walla na saukowa daga cikin idanunta.   ÂÂ
Ganin hawaye akan fuskarta ne yasa Abbou shima ya girgiza kai, cikin sassanyar murya yace. "Kada ki sake barin hawaye su fita daga cikin idanunki Laylerh, burina ako da yaushe shine nafaranta miki, har abada ina fatan hakan da nayi bazai zamo cutarwa agareki ba."  tsagaitawa da maganan nasa yayi tare da É—an gyara zamansa cikeda kulawa yace. ÂÂ
"Nasan ke ƴace me biyayya agareni ako da yaushe, kamar kuma yanda yake alhakin kowani Uba ne ya zaɓawa ƴarsa miji nagari, nayi ƙoƙarin kamanta hakan, dan na zaɓa miki NAJEEB amatsayin mijin da zaki Aura.!!!."
*(Hmmm chab chakwakiya kenan Abbou ya zaɓawa Laylerh Miji, lallai akwai gurmi.)*
1/19/21, 8:11 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*This book is mainly for those that pay, if you know you did'nt pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay- 0002214625 Abubakar muhammed Sardauna Jaiz bank. Whatsapp Number 07017879464.*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.