Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: LAYLERH MALEEK.txt
Chapter 20 of 65
*Chapter 35*
Ajiyar zuciya ta kuma sauƙe akaro na barkatae, tare da sake matse jikinta waje ɗaya, haƙiƙa awani ɓangare na sashin zuciyarta tausayin Najeeb ɗinne yayi kwance, wanda har hakan yasa takejin kamar akwai wani abu na rashin kyautawa da tayi masa, saidai kuma bata da wani zaɓi wanda ya wuce ta ƙyalesa, duk da kuwa ta lura da cewar yana cikin damuwa.
Ahankali kuma cikin yanayin sanyi takae hannu ta share hawayen dake tsiyaya ta gefen fuskarta, jin brain ɗinta na ƙoƙarin tuna mata kalaman da Oum Ayush ta faɗa mata ne yasa ahankali takai hannayenta ta toshe kunnuwanta, saboda tuna maganganun Oum Ayush ɗin zai ci gaba da sawa taji kaman bata aekata daedae ba, wannan yasa ta soma ƙoƙarin nutsar da kanta yanda bacci zai ɗauketa, kasancewar tun ɗazu takejin baccin, amma kwata kwata rashin samun gamsashshiyar nutsuwa ya hanata.
Najeeb, Kusan mintuna 15 ya ɗauka yana zaune akan kujeran, yayinda kuma har yanzu tafukan hannunsa ke kan fuskarsa, tunani daban daban ne ke yawo acikin ƙwaƙwalwarsa,yayinda wani tunanin yake kasancewa me daɗi, wani kuma akasin haka.
Ahankali ya fesar da wani numfashi me zafi ta bakinsa, haɗe da janye hannayensa dake kan fuskarsa, wata gauruwar ajiyar zuciya ya sauƙe, kana ya kuma sauƙe ganinsa akan Laylerh'n.
Kallon agogon dake maƙale aɗakin yayi.
Ƙarfe ɗaya 1:00 am dai dai ya gani, aransa da kuma zuciyarsa yace. "Sabuwar ƙaddara da kuma sabuwar rayuwa."
Sake dawo da kallonsa ga inda Laylerh'n ke kwance yayi, wanda zuwa yanzu yasan ta riga da tayi bacci, sannna kuma har yanzu sosae yakejin feelings ɗinta na ratsashi, musamman ma idan ya tuna da yanda ɗazun ya sauƙe lips ɗinsa akan soft skin ɗinta, me tsananin taushi da ƙamshi, haka yakejin tsikar jikinsa na zubawa, gefe guda kuwa ga mararsa dake ta faman murɗawa, saidai kuma sanin kansane babu yanda zaiyi dole haka zaiyi haƙuri ya ƙyaleta, saboda baisan me zai faru anan gaba, idan ya sake taɓata ba.
Ahankali ya miƙe tsaye daga zaunen da yake, cikin yanayin dake bayyana cewar gaba ɗaya jikinsa ya gamayin sanyi, ya ƙarasa gaban gadon da Laylerh'n ke kwance.
Ɗan sunkuyawa yayi ya leƙa fuskar Laylerh'n wanda ke ɗauke da danshin hawaye.
Murmushin daya ɗan bayyana ɓoyyayen dimples dinsa yayi, ahankali yakai hannunsa kan fuskarta, tare dasa ƴar yatsarsa ya lakato hawayen dake maƙale agefen idanunta.
"Wataƙila kuka baya bata wahala." Yafaɗi hakan azuciyarsa yana me shafa gefen fuskarta, wanda sili silin dogon gashinta suka kwanta awajen.
Jawo blanket É—in yayi ya rufa mata da kyau, tare da zagayawa ahankali ya hau kan gadon, gudun kuma kada ya tasheta abaccin da takeyi É—inne yasa shi yin komansa ahankali, inda yaja blanket É—in shima ya rufe rabin jikinsa, yanayin yanda ya kwanta É—inne yasa yana iya kallon bayanta, da kuma dogon gashinta da ya watse akan pillow.
Idanunsa wanda sukayi ja ya lumshe tare da shaƙan wani sassanyan numfashi, me ɗauke da fitinannen ƙamshin dake fita ajikin Laylerh'n, jin ƙamshin na ratsa hancinsa ne yasashi buɗe idanunsa ya tsurawa bayanta ido, take kuwa yaji wani irin sabon sha'awarta na sake shiga jikinsa, yayinda yake jin kamar ya juyo da ita ya haɗe bakinsu waje ɗaya, ko hakan zaisa yaji sassauci na daga abun da yakeji.
Ahankali yaɗan matso da jikinsa kusa da ita, saidai kuma hakan baisa ya zama suna kusanci da juna ba, saboda tsakaninsu akwae ɗan tazara kaɗan, alokacin da ƙamshin nata ya ci gaba da shiga hancinsa kuwa, lumshe idanunsa yayi tare da sakin wani irin numfashi me kama da nishi, asanyaye yasa hannunsa ya dafe mararsa da yakejin tanayi masa ciwo, haƙiƙa shi kansa baisan cewa ƙarfin sha'awan Laylerh'n da yakeyi yakai haka ba sae yau, dayake ganinta gashi gata, aɗaki ɗaya, kuma agado ɗaya, saidai kuma babu yanda za'ayi ya kawar da duk wata damuwar da ta dameshi ayau ɗin, duba da irin halin da Laylerh'n ke ciki, idan kuma har bazai tauyawa mata ayau ɗin ba, to haƙiƙa baicika masoyin gaskiya ba, duk da kuwa cewar yana matuƙar buƙatarta, akuma yanda yakejin kansa ayanzu, nutsuwa kawae yakeson samu daga gareta, tabbas da ace taɓata bazai zamo masa wani sabon case ba, to daya shiga jikinta yayi romancing ɗinta ko zaiji nutsuwar da zata sa ya iyayin bacci, saboda Allah Ma ya gani amatuƙar matse yake, ayanzu kuwa sosae yake buƙatar mace akusa dashi.
Sake dafe mararsa yayi da ƙarfi, saboda yanda yaji ta murɗa masa, tare kuma da rumtse idanunsa, ahankali ya sake matso da jikinsa kusa da Laylerh'n, tare da cusa fuskarsa acikin bajajjen gashin kanta dake fitar da ƙamshi, kasancewar turarukan gashi na musamman Oum Ayush ke bata tana shafawa.
Ahankali ya sake gyara kwanciyarsa, tare da ƙara kusanta gansa da ita, saidai kuma duk da haka baiyi yunƙurin taɓa jikinta ba, saboda yasan abu kiris ne zai iya tada ta daga baccin da takeyi.
Idanunsa ya lumshe, tare da sake dafe mararsa, ahankali yake fitar da wani irin numfashi, domin tabbas awannan lokacin shi kaÉ—ai yasan me yakeji.
Duk abun da yakeyi ɗin tanajinsa, saboda dama baccin nata bawae yayi wani nisa bane, tun hawansa kan gadon kuwa ta ɗan buɗe idanunta, saidai kasancewar bataso yagane cewar ta farka ɗinne yasa ta maeda idanunta ta rufe, tare da ƙinyin kyakykyawan motsi, duk da cewar kuwa hawansa kan gadon yasa taji faɗuwar gaba, saedae bisa dole ta daurewa duk wani fargaba da tsoronta, dan tayi imani awannan karon idan wancan mood ɗin ya dawo mata babu wani me cetonta,, jin kuma yanda ya matso bayanta ne yasa ta, soma ambaton sunan Allah acikin rae da zuciyarta, tare dayin fatan Allah Yasa bacci yakuma sake ɗaukarta, cikin ikon Allah kuwa ko 5 minute ba'ayi bacci me ɗan ƙarfi ya ɗauketa.
ÆÂangaren Najeeb É—inma dae rufe idanunsa yayi, tare da yiwa kansa fatan bacci, saboda ya tabbatar cewa nan da mintuna kaÉ—an idan bacci bae É—aukesa ba komae zai iya faruwa, domin feelings É—in nasa Æ™ara hawa yake, wanda kuma zuwa nanda Æ´an mintuna kaÉ—an yasan bazae taÉ“a iya control É—in kansa ba.
Jin kuma yanda sautin numfashin Laylerh'n ke fita ne ya sashi gane cewar baccinta ya ɗan soma nisa, wannan dalilin ya sashi sake matsowa jikinta, wanda kuma hakanne ya bashi daman jin feelings ɗin nasa naɗan sauƙa, take kuwa bacci ɓarawo ya ɗaukesa.
Maleek.
Yanayin yanda yake tuƙar motar tasa cikin yanayin sanyi ne yasa saida ya share wasu mintunoni kafun ya iso babban katafaren wajen da yake kamar night club, domin wajene dake ɗauke da yalwar mutane, duk kuwa da cewar dare ne amma wadataccen haske da kuma yawan mutanen dake wajen zaka ɗauka cewar rana ne, duba da irin yanda dayawan mutanen wajen keta hada hadansu, wanda kuma da yawansu samarine da ƴan mata, sannan kuma daga yanayin shigar jikinsu kaɗae zaka gane ko suɗin suwaye ne, domin babu wata mace ko ɗaya awajen da take sanye da shigar mutumci.
Yayinda da yawan mutanen dake wajen ke enjoying cool music É—in dake tashi awajen ta hanyar romancin junansu.
Haƙiƙa daga yanayin tsarin wajen kaɗai zai tabbatar maka da cewa bawajen zuwan kowa da kowa bane, saedae waƴanda suka jiƙe acikin nairori, musamman duba da irin tsala tsalan haɗaɗɗun maza da kuma ƴan matan dake wajen, saboda suɗin ba irin gama garin samari da ƴan matan nan bane.
Tun shigowarsa farfajiyan wajen, da idanunsa suka sauƙa akan tsirarun ƴan matan dake ta shawagi awajen, da kuma wasu dake cikin tabkeken swimming pool ɗin dake tsakiyar compound ɗin, ya yi ƙasa da idanunsa tare da kawar da kansa gefe.
Irin yanayin takun da yakeyi ne, cikin ƙasaitar da tabi jininsa, ya jawo hankalin Mutane da yawa dake wajen ya dawo kansa.
Kasancewar tun shigowarsa wajen hasken fata da kuma kyawun fuska, haÉ—i da murÉ—aÉ—É—iyar surar jikinsa ya É—auki hankalin mutane da yawa.
Shikuwa duk da yasan dayawan mutanen dake wajen kallonsa sukeyi amma sam baidamu ba, saboda idan da sabo yasaba da irin haka, wannan dalilin nema yasa baicika yawan shiga wajen taron jama'a ba.
Direct gurin da ya zama kamar nanne cikin glub É—in ya nufa.
ÆŠaya daga cikin haÉ—aÉ—É—un kujerun dake wajen yaja ya zauna, tare da zaro wayarsa dake aljihunsa ya ajiye anan kan É—an table É—in dake gabansa.
Ɗaya daga cikin masu aikin wajenne ya ƙaraso inda Maleek ɗin ke zaune, cikin rusunawa haɗi da girmamawa yace.
"Barka da zuwa ranka ya daÉ—e me za'a kawo ma?."
Maleek kuwa daya sunkuyar da kansa ƙasa jin muryar mutum akansa ne yasashi ɗagowa ya kalli mutumin, yanayin fuskarsa ne ta sanja, duk da kuwa bae taɓa zuwa wajen ba, wannanne karo na farko, amma yaga alaman cewa bazae samu abun da yake so ba, wani abun mamakin ma shine kwata kwata baisan dalilin daya kawosa wajen ba, hakanan dae ya samu kansa da shigowa wajen, duk da kuwa yasan cewa wajen holewa ne da yake tara isassun ƴan iska da yawa.
"kabani drinks." yafaɗa ataƙaice, domin bayaso ya tsawaita dogon magana.
Mutumin dake tsaye kuwa jin Maleek ɗin ya ambaci drinks ne, yasashi gane cewar kwata kwata Maleek din bae taɓa shigowa wajenba, ɗan rusunawa yayi tare da cewa. "I'am sorry sir, bamu da normal drinks saedae wanda akayi mix ɗinsa, sae kuma alcohol and wine non alcoholic."
Jin mutumin ya ambata masa alcohol ne yasashi saurin ɗago kae ya kalleshi, saboda tun da yake adunia bae taɓa shan giya ba, kuma bayajin akwae watarana da zae sha.
Kansa yaɗan girgiza, tare da kama Laɓɓan bakinsa yaɗan ciza, cikin muryarsa da bata fita sosae yace. "Kabani wine amma non alcoholic."
"Okay sir" mutumin ya faɗa tare da juyawa cikin sauri ya tafi dan kawowa Maleek ɗin wine kamar yanda ya buƙata.
Bajimawa kuwa mutumin ya dawo hannunsa É—auke da kwalbar wine da kuma wani glass cup me yanayin zinare.
Ajiye kwalban yayi agaban Maleek É—in, tare da juyawa ya tafi.
Maleek kuwa ɗaukan kwalban wine ɗin yayi batare kuma daya duba, ko wine ɗin non alcoholic bane, ya ɓalle murfin ya zuba wine ɗin acikin cup.
baikuma damu da yawan wine É—in da ya zuba acikin cup É—inba, ya kafa kofin abakinsa, bai kuma cire daga bakinsa ba har saida yaga ya shanye gaba É—aya wine É—in dake ciki,
Ahankali ya ɗauki wayarsa dake aje, tare da kunnata, kifa kansa akan table ɗin dake gabansa yayi, haɗe da tsurawa hoton Laylerh dake mamaye akan screen ɗin wayar idanu, wanda da ace zae tabbata yana kallo, to har abada bazae taɓa gajiyawa ba, domin sosae kallon hoton yake bawa zucia da ƙwaƙwalwarsa nutsuwa, idanunsa da suka sauƙa akan kyawawan lips ɗinta yaɗan lumshe, tare da fesar da wani irin numfashi me sanyi.
"I LOVE YOU!!!" ahankali ya faɗa ta hanyar motsa jajayen laɓɓansa, da suke ɗauke da danshin wine ɗin da yasha.
Kwantar da kansa akan table É—in yayi, saedae kuma ko mintuna 16 ba acika da shan wine din nasa ba, yaji kansa naÉ—an juyawa, yayinda idanunsa ke sake marairaicewa, tamkar wanda yakejin bacci haka yanayinsa ya dawo, musamman ma idanunsa da suka soma juyewa, haÉ—i da sanja launi.
Take kuma cikin mintuna kaɗan yaji duniyar na neman juya masa, ganin da yayi cewar da gaske yana neman fita acikin hayyacinsa ne yasashi miƙewa tsaye, tare da ɗaukan wayarsa, wallet ɗin dake cikin aljihunsa ya ciro tare da buɗewa batare kuma daya duba ba ya ciro fararen ƴan dubu dubu ya ajiye musu akan table ɗin.
Ahankali cikin yanayin da yakejin kansa ya fice daga cikin club É—in,
Koda ya fito farfajiyan club É—in kuwa, har zuwa yanzu mutane hada hadansu kawae sukeyi, yayinda wasu keta rawa.
Kansa yaÉ—an buga, saboda yanda yaji jiri na neman kada shi, acikin zuciarsa yake tambayan kansa shin ma meya kawosa wajen?, gashi sanadin zuwansa yasha abun da yake neman dagula masa lissafi.
Cikin É—an cijewa ya fito daga wajen gaba É—aya, inda ya ajiye motarsa ya nufa, yana zuwa kuwa ya bude murfin motar nasa ya shiga, da wani irin speed kuwa yacilla motar kan titi,
Duk da kuwa cewar baya cikin hayyacinsa, amma hakan bai hanashi, dagewa wajen ganin ya hana kansa, wrong driving ba.
Saidai kuma sanin dare ya raba sosae ne yasashi ƙarawa motar tasa gudu.
Kae tsaye ya nufi gida, sam baedamu da me zaije ya tarar agidan ba, duk da cewar bae taɓa raba dare haka awaje ba.
Isowarsa gaban makeken gate din gidan nasu ne yasashi soma danna wani irin horn, wanda kuma kwata kwata baedamu da waÆ´anda horn É—in nasa zae katsewa baccin ba.
Sama da 7 minute ya ɗauka yana ta faman danna horn ɗin, ganin da yayi kuma ba'a buɗe masa bane, yasashi ci gaba da dannawa, yayinda kuma ƙaran horn ɗinnasa kaɗae zakaji ka fahimci cewa baya cikin hayyacinsa.
Acan cikin gidan kuwa jin matsanancin ƙaran horn ɗin mota da yaƙici yaƙi cinyewane, yasa amatuƙar razane me gadin dake onduty ya farka daga nannauyan baccin daya ɗaukesa, fitowa daga ɗakinsa yayi, tare da zuwa jikin ƙofar gate ɗin yaɗan leƙa, ganin motar Maleek ɗinne keta danna horn yasa ahanzarce ya wangale masa gate ɗin.
Maleek kuwa da yakejin kansa asama, da wani irin gudu ya shiga cikin gidan.
Ko gama daedaeta parking É—in nasa da kyau kuwa baiyi ba, ya buÉ—e murfin motar nasa ya fito, kallo É—aya zaka masa kasan cewa baya hayyacinsa.
Maida murfin motar nasa yayi ya rufe yana juyowa kuwa ya sauke ganinsa akan Abbou Jaheed dake tsaye ya harÉ—e hannayensa, akan fuskarsa kuwa sam babu alaman fari'a.
*9/January/2021*
1/19/21, 8:28 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Writting By*
fatymasardauna
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.