Best Hausa Novels

Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: LAYLERH MALEEK.txt

Chapter 23 of 65

*Chapter 38*
Ganin Laylerhn da kuma gane cewar k'amshin Maleek d'in dake tashi daga jikinta yake fita ne yasa shi rumtse idanunsa k'am, yayinda take yaji wani irin abu me suka ya caki k'irjinsa, lokaci daya wani irin kishinta ya Kama sa.
Wanda har yakaisa ga cije labb'ansa, hakika shi kansa baisan cewar yana kishin Laylerh'n sosai har haka ba sae yau, saboda jin k'amshin Maleek ajikinta bak'aramin k'untata masa zuciya yayi ba.

Itakuwa Laylerh k'arasowanta dinning table d'in ganin su Abbou Jaheed da tayi ne yasa ta tsayawa tare da dan daidaita nutsuwarta, cikin yanayin sanyi ta k'araso dab dasu, hakan kuma ya farune saboda lura da tayi da irin Kallon da Abbou Jaheed ke mata.
"Good morning Abbou Jaheed."  Ta fad'a cikin yanayin nutsuwarta.

Abbou Jaheed kuwa dake goge bakinsa da tissue jin gaisuwar Laylerh'n ne yasa batare daya motsa bakinsa ba, ya jinjina mata kai alaman ya amsata.
Ganin hakanne kuma yasa jikin Laylerh K'arayin sanyi duk da kuwa batasan meye ma'anar hakan ke nufi ba.
D'ago Kanta tayi ta dubi Abbou Kareem tare da gaishesa, fuskarsa amatuk'ar sake kuwa ya amsa mata, tare da nuna mata kujeran dake facing ta Najeeb, alama yayi mata akan ta zauna, babu musu kuwa taja kujeran ta zauna tana me gaishe da Oum Ayush.
Murmushi Oum Ayush tayi cikin sakin fuska tace.    "Ina fata kindai tashi lafiya?."
"Lafiya lau." Tafad'a tana me gyara zamanta akan kujeran.
Plate d'in soyayyen chips da kuma plaintain Oum Ayush ta turo mata gabanta.
Abbou Jaheed kuwa kasancewar ya gama cin abincin nasa tuntuni mik'ewa tsaye yayi batare da yace da kowansu k'alaba yabar dining table d'in.
Murmushi me d'auke da ma'anoni daban daban Momy tayi domin koba komae manufarta ya isa inda takeson ya isa.
Jan kujeran da take kai baya tayi tare da mik'ewa tsaye ta rufawa Abbou Jaheed baya.
Ganin hakane kuma yasa Abbou Kareem ma mik'ewa tsaye dan dama dukansu sun kammala cin abincin nasu.
Kusan kuma atare suka mik'e tsaye shida Oum Ayush, dan itama tanaso tabawa Laylerh da Najeeb d'in waje, duk dama bataji dad'in zuwan da Laylerh'n tayi wajen Maleek ba, domin Sam bataso zargi ya fara shigowa tsakaninta da Najeeb.
Hakan yasa batare da sunce da kowannensu wani abuba suka nufi hanyar barin falon.
Ganin haka kuwa yasa Laylerh'n ta bisu da kallo har saida suka b'acewa ganinta, sassanyar ajiyar zuciya ta sauk'e tare da maida kallonta ga plate d'in abincin dake gabanta, fork d'in dake cikin abincin ta d'auka tare da tsakalo chips d'in takai bakinta.
Jin test d'in abincin daban da wanda ta saba cine yasa ta gane cewar girkin Oum Ayush ne bana laure me aiki ba. Batare da ta gama tauna abincin dake bakinta ba, ahankali ta d'ago kai ta kalli Najeeb dake zaune suna facing d'in juna, wanda kuma har yanzu bai d'ago kansa ya sake kallonta ba, tunkuwa kallon farko daya mata, ahankali yake d'an jujjuya spoon d'in dake hannunsa, domin hakanan yaji abincin yafita aransa duk da kuwa bawai wani sosae yaci ba.
D'auke idanunta tayi daga garesa, dan kwata kwata bata fahimci yanayin nasa ba.
Azahirin gaskia abincin takeci, yayinda acikin zuciyarta kuwa tunanin M.Jay ne yayi tasiri, kana kuma shi ya maye duk wani gurbin nutsuwarta, tuna yanda kyakkyawar fuskartasa take idan yana baccine yasa ta sakin murmushi me sauti tare da d'an lumshe idanunta.
Sauti da kuma amon murmushinta da yaji ne yasa shi d'ago kansa, tare da zuba mata idanunsa wanda suka d'anyi ja, kana kuma suke bayyana zallan abun dake zuciyarsa.
Murmushin kuma daya gani kwance akan fuskarta ne yasa shi sake jin wani abu ya tokare masa k'irji.
"Mekenan me hakan yake nufi? tana farinciki ne saboda wani abu daban, wani abu dake b'oye acikin zuciyarta, meyasa bata farinciki alokacin da take tare dashi sai akasin haka?" Yayiwa kansa tambayar yana me yawo da idanunsa akanta, tabbas wani abu me kama da zargine ke neman mamaye zuciya da tunaninsa, wanda kuma yarda da hakan zai iya lalata rayuwar aurensu, because aure da zargi haramunne.
K'ok'arin daure zuciyarsa yayi ta hanyar mik'ewa tsaye daga zaunen da yake, domin yasan zamansa awajen bazai k'ara masa komai ba sai zafin zuciya.
Jin alaman tashinsa ne kuma yasa Laylerh d'ago kai ta kalleshi.
Ganin yana k'ok'arin barin dining area d'inne yasa ta tsura masa ido, domin tuni ya d'auke idanunsa daga gareta.
Kansa tsaye kuwa ya nufi hanyar fita daga falon, batare dako waiwayenta yayi ba.
Laylerh kuwa har ya fice daga falon bata d'auke idanunta daga kallon hanyar da yabi d'in ba, hakanan duk taji ta tsargu da irin mood d'in da tagani akan fuskar kowannensu.
Saidai kuma rashin son tsanantawa Kanta damuwa yasa ta share duk wani tunani dake ranta, tare da maida hankalinta ga abincin dake gabanta.

Fitarta daga cikin d'akinne yasa shi bud'e idanunsa, wanda suka d'an k'ank'ance ahankali ya sauk'e wata sassanyar ajiyar zuciya, tare da fesar da wani sassanyan numfashi ta bakinsa, duk da kuwa cewar baya cikin mood maidad'i amma hakan bai hanasa bayyana wani k'awataccen murmushi akan fuskarsa ba, tare da shak'an daddad'an k'amshinta da ya cika d'akin.
Maganganun sakalcinta da tayi ta fad'a masane suka shiga dawowa cikin kunnuwansa, wanda hakan yasa shi d'an lumshe sexy eyes d'insa.
Cikin wata irin kasalalliyar muryar dake bayyana abunda ke cikin zuciyarsa yace.
"Yeah before zuwanki am not okay Laylerh, amma yanzu da kikazo am okay!"
Ya k'are maganar yana me yun k'urin tashi zaune, duk da kuwa yana jin jikinsa very weak,  hannunsa yakai ya shafi gefen wuyansa inda Laylerh'n ta tab'a.
Still murmushin da baizamo al'adarsa ba ya sakeyi, domin yasan da ace Laylerh'n tasan cewa baccinsa baiyi nisa ba da bazata tab'a sakin jiki dashi har haka ba, ganin tasaki jiki dinne kuma yasashi yin shiru tare dayin kamar bacci me nauyi ne ya d'aukesa, alhalin kuma duk abun da takeyi yana jinta.
Ahankali ya d'an yunk'ura ya mik'e tsaye, hannayensa duka biyu  yasa ya kama waist d'insa,
Kallon pillown da Laylerh'n ta ajiye masa yayi, maganarta da take cewa.  ya daina kwanciya ak'asa ne ya dawo masa, take kuwa sauti da amon zazzak'ar muryarta suka shiga dawo masa, tamkar alokacinne abubuwan ke faruwa, d'an murmusawa kawai yayi, ahankali ya soma rage kayan jikinsa, saida ya rage dagashi sai dogon wandon dake jikinsa kafun ya wuce bathroom dan watsa ruwa.

B'angaren Laylerh kuwa anutse ta kammala cin abincin nata, tare da d'aukan tissue ta goge bakinta.
Mik’ewa tsaye tayi tare da k’arasowa cikin falon nasu ta zauna, hankali da Kuma idanunta ta tsaida akan k’aton tv plasman dake cikin falon, tashar MBC Bollywood take kallo inda suke haska film d’in Force 2 na john abraham, kallon yanda murd’add’iyar surar JohnAbraham d’in yake ne yasa take Maleek ya fad’o mata saboda shima irin jikin John dinne dashi, saidai kuma fuskar Maleek d’inta yafi na John Abraham d’in kyau, samun kanta acikin sabon Shauk’i da tayi ne yasata lumshe idanunta tare da jingina bayanta da jikin kujeran da take kai, lokaci d’aya kuwa ta fad’a duniyar tunani.

Najeeb kuwa koda ya fita daga falon direct part d’insu ya koma, hakanan yakejin zuciyarsa duk ba dad’i shiyasa duk yaji zaman gidan ya ishesa, key d’in motarsa k’iran Benz ya d’auka kaitsaye ya fito daga part d’in nasu, babban parking space d’in dake gidan ya fito tare da bud’e motarsa ya shiga, ganinsa da maigadi yayi ne kuma yasashi wangale masa gate d’in gidan ya cilla hancin motar tasa waje, duk da kuwa cewar baiyi niyar fita yau d’inba amma dole haka zaije ya zaga gari ko hakan zaisa ya d’anji sanyi acikin zuciyarsa.

Asashin Maleek kuwa baiwani d’au lokuta masu tsawo acikin bathroom d’inba, koda ya fito towel ne d’aure akan waist d’insa, yayinda gaba d’aya jikinsa ke d’auke da danshin ruwa, Wanda kuma hakan yasa gargasan jikinsa kwanciya sukayi lub lub dasu, cikin takunsa me d’auke da nutsuwa ya k’araso gaban tabkeken dressing mirror d’insa Wanda yake wadace da kayan shafa kala kala.
Saida ya d’auki wani d’an k’aramin towel ya goge jikinsa, kafun ya murzawa jikinsa had’adden body lotion d’insa me dad’in k’amshi, kana kuma yabi fatar jikin nasa da turaren oud na jiki.
Handryer yajona tare dayin amfani dashi wajen busar da lallausan gashin kansa, bayan ya gama ne kuma kaitsaye yanufi wajen da drawer’nsa yake, direct b’angaren da yake ajiye Kayan training d’insa ya bud’e, kamar kuma yanda yasaba yawancin lokuta idan zaiyi training tracksuit yake sawa, yau d’inma hakance takasance domin tsab yagama shirya kansa cikin wani had’add’en riga da wandon tracksuit masu kalan red yasanya, yayinda ak’afansa kuwa yasa wasu fararen snickershoe masu ratsin ja, duk da kuwa cewar shid’in mai kyaune, amma shigar dake jikin nasa ya k’ara masa kyau Sosae.
Wayoyinsa dake aje akan bedside ya d’auka yasanya acikin aljihunsa, jakar da yake zuwa training da ita ya rataya akan kafad’arsa na dama, makullin motarsa ya d’auka cikin takunsa na nutsuwa ya fice daga cikin d’akin.
Kasancewar kuma bayason had’uwa da kowa ne yasashi zagayawa yabi ta k’ofar baya.
Koda ya fito compound d’in gidan part d’insu Oum Ayush ya kalla, dan sai alokacinnema ya tuna cewar tun zuwansu baije ya gaisheta ba, tuna hali da kuma kirkin OumAyush d’inne yasashi sakin murmushi, hakanan yaji zuciyarsa ta bashi umarni da zuwa b’angaren su Oum Ayush d’in, dama kuma yunwa yakeji, yasan kuma Bazai rasa abinci awajen Oum d’inba.
Cikin takunsa na nutsuwa yak’arasa bakin k’ofar da zata sadashi da babban falon dake part d’in.
Knocking k’ofar yayi saidai kuma jin ba’a amsa masa bane yasashi murd’a handle d’in k’ofar ya shiva bakinsa d’auke da sallama.
Shiru falon bakowa sai k’amshin turaren wuta dake dashi, k’arasowa cikin falon yayi tare da sauk’e jakan dake kafad’ansa, batare da damuwa kowani shakku ba ya k’arasa dining area d’in dake cikin falon.
D’aya daga cikin yankakkun apple d’in da aka jera akan wani plate ya d’auka tare da kaiwa bakinsa.
Oum Ayush dake cikin kitchine kuwa jin motsi afalon nata ne yasata tsayawa da abunda take yi tare da lek’owa dan ganin ko waye.
Saidai kuma rashin ganin mutum acikin falon yasa ta tsayawa tare da d’ansoma yin nazari, domin tabbas taji motsi acikin falon amma kuma gashi ta lek’o bataga kowa ba.
“Gani nan fa anan.� Cewar Maleek dake tsaye abayanta, kasancewar dama dining area d’innasu yashiga lungu shiyasa bata gansa ba.
Jin muryar Maleek d’inne yasa Oum Ayush sauk’e wata irin nannauyar ajiyar zuciya, saboda kafun yayi maganan ta d’an tsorita.
“Yadai kinji tsorone?.� Ya fad’a adaidai lokacin da yake sake gutsuran apple d’in dake hannunsa.
Kallo me kama da harara Oum Ayush ta watsa masa, cikin yanayin hasala tace. “Bansani ba.�
Murmushin daya bayyana kyawawan hak’oransa yayi cikin halinsa daya saba mata yace.
“I miss you so much.�
“Miss yo mata, koda yake ma ai idan da sabo nasaba da wannan halin naka, sai yau kaga daman dubani kenan?.�
Still murmushi yayi batare kuma da yace komae ba, yaja d’aya daga cikin kujerun dining table d’in ya zauna, kallon Oum Ayush d’in yayi, cikin yanayin d’an yamutsa fuska yace. “Am hungry, kuma zanfita training please Oum ki had’amin ko tea ne Nasha.�
Murmushi Oum Ayush tayi tare da k’arasowa dining table d’in, cikin sigar tsokana tace. “Ae dole dama kayita fama da yunwa, tunda har yau kakasa tsaida matar aure.� Tafad’a tana me k’ok’arin bud’e d’aya daga cikin kulolin dake saman table d’in.
Jin Oum Ayush d’in tayi masa batun aure ne, yasashi yin k’asa da kansa, cikin yanayi me kama da k’osawa yace.
“Please Oum Ayush ki had’amin Lokaci na k’urewa zantafi training ne.� Yafad’i hakan yana me kallon agogon dake d’aure atsintsiyar hannunsa, wanda kuma yayi hakanne dan son kawar da zancen da Oum Ayush d’in keyi.
Gane nufinsa ne kuma yasa Oum Ayush d’in ta saki murmushi, batare kuma da tasake cewa komae ba, ta zuba masa chicken pepper saup d’in da ta gama girkawa yanzun, tare da had’a masa tea, har gabansa kuwa ta kawo masa abincin ta ajiye, batare da ya tsaya b’ata lokaci ba kuwa ya soma cin abincin.
Anan gefensa Oum Ayush ta zauna tana kallon yanda yake cin abincin, wanda yanayin yanda yake d’iban abincin da kad’an kad’an ya tabbatar mata da cewar baya kulawa da kansa sosai, tausayinsu takeji Matuk’a shida Laylerh, saboda yanda rayuwarsu ke cike da maraici da kuma zallan kad’aici, Bazata ce Abbou Jaheed baya k’ok’arin kulawa dasu ba, saidai kuma ba kulawan Abbou Jaheed d’in kad’ai suke buk’ata ba, kulawan Uwa shi dukansu suke buk’ata acikin rayuwarsu, domin Uwa itace ginshik’in y’ay’anta.
Ahankali ya cire hannunsa daga cikin abincin, tare da d’aukan kofin tea d’in dake gefensa yakai bakinsa.
Batare kuma daya wani sha tea d’in sosae ba ya mik’e tsaye tare da d’aukan tissue ya goge bakinsa.
“Thank you� Ya fad’a cikin yin k’asa da murya tare dasa hannunsa acikin aljihun wandonsa ya ciro sweets guda biyu, b’are sweets d’in duka biyu yayi ya jefa d’aya abakinsa, kallon Oum Ayush yayi cikin sigar tsokana tace. “Bud’e bakinki nasa miki sweet.�
Jin abunda ya fad’a yasata watsa masa hararan wasa, cikin maganarta da baikai zuci ba tace. “Akan ina wasa dakai?�
Awannan karon kam murmushi maikama da dariya yayi, batare da Oum Ayush d’in tayi zato ko tsammani ba kuwa ya matso gab da’ita, bakinta ya bud’e ya jefa mata sweet d’in aciki, baijira me zata ce masa ba kuwa yayi saurin k’arasawa cikin falon ya d’au jakarsa, ahanzarce ya fice dan yayi latti sosae, kasancewar kuma yaud’in akwae soldiers d’in da yakeson horarwa ne, yasa yana fitowa daga part d’in Oum Ayush d’in motarsa ya fad’a, batare kuma da yanemi Abdoul ba da kansa yayi driving motar, maigadi na wangale masa gate d’in gidan ya cilla hancin motar tasa waje.

Jin k’aran tashin motarsa ne kuma yasa Oum Ayush sakin murmushi, sweet d’in daya sa mata abaki ta cire tare da d’aukan ledan sweet d’in daya zubar anan falon, sunan sweet d’in ta karanta tare da amfanin da yakewa mutum, ganin cewar sweet d’in na k’arawa mutum kuzari da kuma k’arfi ne yasata sake sakin murmushi abayyane tace. � Mai hali baya tab’a sanja halinsa, wato yabani sweet me k’ara kuzari nasha, dannayita jibgan aiki, d’an baccin rana dana sabayi ma bazan samu nayi ba to bazan shaba, dama aina sani Maleek baya kyauta haka kawae miskilin soja kawai.�
Ajiye mintin tayi akan table tare da mik’ewa ta shige d’aki dan so take tad’an huta.

Ab’angaren Laylerh kuwa sama da awa d’aya ta kwashe zaune acikin falon tana kallon film d’in da Bollywood ke haskawa, jin bacci yacika idanunta ne yasata tashi asanyaye ta nufi part d’insu zuciyarta cike da fatan kada Allah Ya had’ata da Najeeb.
Bak’aramin dad’i kuwa taji ba alokacin da tashiga part d’innasu ta tarar da Najeeb d’in bayanan, hayewa saman gado tayi cikin abunda baiwuce mintuna kad’anba kuwa bacci ya d’auketa.
Bacci sosai tayi domin ba ita ta farka ba sai k’arfe 2:56 pm, ganin kuma irin lokacin da ta d’auka tana baccin ne, yasa ta shiga mamaki, dan bata tab’a bacci me nauyi irin haka ba, ahanzarce ta wuce toilet ta d’auro alwala koda tafito kuwa sallaya ta shumfud’a tare da hawa kai ta tada sallah, koda ta idar da sallan bata tashi akan sallayanba saida ta sallame sallan la’asar, azkhar d’in yammaci tayi tare da mik’ewa tsaye ta soma rage kayan jikinta, bayan ta gama cire kayan nata ne kuma, ta wuce toilet wanka tayi tare da d’auro sabon alwala, koda ta fito ganin yamma tayi sosai ne yasa sama sama tashafa lotion ajikinta, powder da kuma lipstick wanda ya saje da kalan labb’anta ta shafa.
Ahanzarce ta k’arasa gaban sif d’in kayanta, kasancewar kuma bata fiye son kaya masu nauyi sosai bane yasa ta zaro d’aya daga cikin had’add’un dogin rigunan da Oum Ayush takawo mata tsarabarsu, duk da kuma kasancewar rigar nada d’an fad’i kad’an amma hakan bai hana had’add’iyar surar jikinta bayyana ba, yayinda kuma adon fararen duwatsun dake gaban rigar keta faman shining suna d’auke ido.
Anutse ta nad’a vail d’in rigar akanta kasancewar kuma vail d’in nada d’an girma kad’anne yasa ya sauk’o har kan k’irjinta, cool perfume ta shafa ajikinta tare da komawa kan gado ta zauna, d’an k’aramin handbag d’inta dake aje saman bedside ta jawo, wanda tun daren jiya da Oum Ayush ta ajiye mata shi bata sakebi takansa ba, zuge zip d’in jakan tayi, ganin kud’ad’e masu yawa acikin jakanne yasata d’an zaro idanunta, cike da yanayin mamaki kuwa ta sa hannu ta d’ebo kud’ad’en wanda bandir biyu na cikinsu suka kasance 2/2 hundred K, d’ayan bandir d’in kuma 100k ne.
D’an soma jujjya kud’ad’en tayi tare da sake lek’a cikin jakan ta zaro car key d’in da tagani aciki, sai kuma wayarta, maida kud’ad’en tayi tare dajan zip d’in jakan ta rufe, wayarta dake kashe ta kunna take kuwa sak’onnin Teemah suka fara shigowa, wanda dayawan sak’onnin kuma d’auke suke da zallan tsokana.
Share sak’onnin tayi batare da ta kulasuba ta somayin game dan shid’inne kad’ae zaihana k’wak’walwarta yin tunani marassa amfani.
Tana nan zaune kuwa har aka k’ira sallan magriba, sanin kuma da tayi cewar tana da alwala ne yasata shumfud’a sallaya ta tada sallah.
Tana nan zaune akan sallaya aka k’ira sallan Isha, bayan ta sallame sallan kuwa batawani tsaya yin dogon addu’aba ta mik’e tsaye saboda tun tashinta take jin cikinta na kukan yunwa.
Turare ta sake fesawa ajikinta tare da d’aukar wayarta tafice daga cikin d’akin, kaitsaye babban parlor’n gidan ta nufa, kasancewar tasan adaidai wannan lokacin ne sukeyin dinner.
Acan cikin falon kuwa zaune suke su dukansu ciki kuwa harda Maleek wanda ya maida gaba d’aya hankalinsa ga wayarsa dake rik’e ahannunsa.
Shigowarta cikin falonne kuma yasa Najeeb dake zaune ya d’ago kansa ya kalleta, hakan yafarune kuma saboda daddad’an k’amshinta da yaji ya ratsa cikin hancinsa.
Tabbas duk da cewar fushi yakeyi da’ita amma ganinta da yayi yanzun yasa shi jin zuciyarsa tayi masa sanyi, hakanan yaji ya nemi duk wani b’acin ransa ya rasa, kallon tsab yayi mata, tunawa kuma da abunda ke cikin zuciyarsa ne yasakashi sakin murmushi, domin alk’awari yayiwa kansa cewar ayau a kuma awannan daren babu abunda zai hanashi disvirgin d’inta.

Anutse ta k’araso dining table d’in, tare da d’agawa su Abbou Jaheed gaisuwa, saidai kuma wannan karon fuska asake Abbou Jaheed ya amsa mata.
Kujeran daya zamana shikad’aine awajen taja ta zauna, daidai lokacin kuwa idanunta suka Sauk’a akan Maleek wanda shigar jumper’n dake jikinsa tayi matuk’ar yimasa kyau.
Azahirance kuwa zaman nata, yayi daidai da mik’ewarsa tsaye, k’ok’arin barin dining area d’in yayi, domin matuk’ar Laylerh zata kasance akusa da Najeeb to bazae tab’a iya jurewa ba, saidai kuma k’iran sunansa da Abbou Jaheed yayi ne, yasashi tsayawa, batare kuma daya juyoba ya amsa k’iran Abbou Jaheed d’in.
Abbou Jaheed kuwa da ya tsaya dacin abincin da yakeyi, Sam baidamu darashin juyowan Maleek d’inba, cikin muryarsa da sam bata d’auke da alamar wasa yace.
“Kashirya gobe da safe za muje kaga matar dana zab’a maka, ma’ana wacce zaka aura, inason kasani kuma ba shawara bane umarni ne.�

*(Nasan dayawanku kunayiwa Abbou Jaheed kallon mutum meson kai, amma anan gaba kad’an zaku fahimci komae, then kada kuji haushi dan Abbou Jaheed yace zaiyiwa Maleek Aure, saboda saida wata hanyar k’addaran ake samun wani cikar burin, sannan kuma wata k’addara takan rikid’e tazamo alkhairi, please banaso kuyi saurin yanke hukunci domin bakusan wani future M.Jay da Laylerh kedashi agaba ba. Sannan ku k’ara hak’uri dani please danaso na bud’e WhatsApp dawani new sim saikuma naga abun bazaiyiwuba shiyasa na hak’ura har aka gyara wannan d’in.)*

*16/Jan/2021*
1/19/21, 9:09 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.