Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: LAYLERH MALEEK.txt
Chapter 11 of 65
*Chapter 19*
Tunda suka É—au hanyan super market É—in yake satan kallonta lokaci zuwa lokaci, yayinda kuma ya maida gaba É—aya hankali da nutsuwarsa zuwa gareta, wanda asanadiyar hakanne ya fahimci cewa akwai damuwa me tarin yawa dake kwance acikin zuciyarta wanda ta kasa furtashi ga kowa, duk kuwa da yanda zuciyarsa ke cike da son sanin damuwar tata haka ya share, domin kwata kwata bayason abun da zai hargitsa tunaninsa.
Isowarsu bakin babban katafaren shoprite ɗinne ya sashi kashe motar, ahankali ya ɗan jingina bayansa da jikin kujeran motar, cikin yanayin kasalan daya sauƙar masa lokaci ɗaya yaƙira sunanta.
Duk da cewar idanunta alumshe suke kana kuma tayi nisa cikin duniyar tunanin da take, hakan baisa ta kasa jiyo sautin muryarsa da ya ƙira sunanta da ita ba.
Ahankali ta kallesa da idanunta wanda suka sanja launi zuwa yanayin bacci.
Shi din ma kallonta yake saidai kuma yanayin nasa nasa kallon ya banbanta da irin wanda take masa, domin kuwa shi irin kallon nan me matuƙar kashe jiki yakeyi mata. Kasancewar kwata kwata bata saba da jefa idanunta acikin idanun wani namiji ba, hakan yasa bazata iya jure yanayin kallon nasa da yakeyi mata ba, ahankali ta ɗauke kanta daga gareshi, tare da kai dubanta zuwa babban ƙofar shiga katafaren Shoprite ɗin, gaba ɗaya har acikin zuciyarta batason irin kallon da Najeeb din keyi mata, saboda yanayin kallon nasa yakansa taji wani iri ajikinta.
Shi kuwa ganin ta ɗauke kai daga garesa ne, yasashi sauƙe ajiyar zuciya, ahankali kuma ya buɗe murfin motar, ta ɓangaren da yake, kana kuma cikin tone ɗin muryarsa data sanja amo saboda kasalan daya sauƙar masa lokaci ɗaya yace. "Muje ko."
Jin abun daya faɗane yasata buɗe murfin motar, ahankali ta zuro da kyawawan fararen ƙafafunta waje, wanda suke sanye cikin wasu haɗaɗɗun baƙaƙen flat shoe masu kyaun gaske, koda ta gama fitowa daga cikin motar, ahankali ta gyara zaman ɗan siririn mayafin dake jikinta, saboda kwata kwata bata fiye son tafiya ana kallon jikinta.
Najeeb kuwa ganin ta fito ne yasashi É—an soma takawa, wanda hakan yasa ta rufa masa baya.
Ahaka suka shiga cikin shoprite din yana gaba tana biye dashi abaya, yayinda kuma atsakaninsu ya kasance babu wani tazara sosai.
Kaitsaye sashin womens clothing ya nufa yayinda take biye dashi abaya, wasu manyan super market trolley ya É—auka tare da É—an juyowa ya kalleta. murmushi É—auke akan fuskarsa yace. "Muje ki tayani sayyayya, then duk abun da kikaga ya miki ki É—auka." Ya faÉ—i maganar yana me tura mata trolley É—aya gabanta,
Kai taɗan jinjina tare da mai da dubanta ga wata haɗaɗɗiyar abaya wanda tun shigowarsu wajen ita tafara ɗaukar hankalinta, domin kuwa rigar ta haɗu sosai saidai sanin cewa rigar zatayi tsada ne yasa ko kusa bata kawo tunanin ɗaukarta ba, idanu ta soma bazawa tana me ƙarewa haɗaɗɗun kayayyakin dake wajen kallo, domin kuwa kayane masu kyau haɗi da burgewa aka zuba awajen.
Kasancewar kwata kwata bata saba da irin hakan bane yasa ta kasa ɗaukan komai dake wajen, domin kuwa wannan shine zuwanta shooping na farko da wani daban wanda ba Abbou Jaheed ba, saboda sometimes idan zata zo shooping da Abbou Jaheed ɗin suke zuwa, yanayin rashin sabon da tayi da hakanne kuwa yasa takasa ɗaukan komai dake wajen, sanin cewa bazata iya ɗaukan komai dake wajen bane yasa ta tsayawa tare da juyowa zuwa ɓangaren da Najeeb din yake, ganin yanda yake ta kwasan kaya, dangin su abayas da kuma straight gown, haɗi da boubou ne yasa ta zuba masa ido, tana me mamakin yanda yaketa jidan kaya masu uban yawa kaman bada kudi zai biya ba.
Najeb kuwa ganin basket É—in nasa ya kusa cikane, yasa shi É—an dakatawa haÉ—e da juyowa ya fuskanci Laylerhn, wanda har zuwa yanzu ba abun da ta É—auka.
Ganin da tayi yana kallonta ne yasa ta sauƙe idanunta ƙasa, tare da kama ƙasan vail ɗinta ta soma wasa dashi.
Ɗan lumshe idanunsa dake cike da mayen ƙaunarta yayi, domin yanayin yanda tayi acting ɗin ne yasa yaji wani irin sanyin ƙaunarta ya ratsa sa, ahankali ya ɗan tura keken hannunsa wanda ke cike da kaya, kaitsaye ya nufo inda take.
Koda ya ƙaraso tsaida idanunsa akanta yayi cikin kulawa yace. "Meyasa baki ɗauki komai ba, ko babu abun daya miki ne?."
Kai ta girgiza masa alaman
"babu"
"Why?." Yafaɗa cikin yin ƙasa da murya tare kuma da sanya hannunsa ya ɗan ɗago haɓarta, wanda hakan ya bawa kyakkyawar fuskarta daman bayyana.
Idanunsa É—aya ya kashe mata tare da cewa. "Biyoni muje."
Yanayin yanda yayi maganar yana ɗan tafiyane yasa bata jira komai ba ta rufa masa baya, kaitsaye ɓangaren takalma suka nufa, nan ma kamar yanda sukayi aɓangaren abayas haka sukayi anan ɗin ma, dan shikaɗai ya dinga jidan takalma masu kyau da tsada. Ita dai duk inda yayi da idanu kawai take binsa, gaba ɗaya ta kasa ganin makusa ajikinsa, ganin kuma yanda yake mata wani irin kallo na alaman bazaki ɗauki komai ba ko, yasa ta ɗauki wani pink sneakers shoe me kyau.
Haka dai ya dinga janta suna kutsawa duk inda wani kyan ƙyale ƙyalen mata suke, ita dai idanu kawai ta zuba masa.
Saida yayi sayayya sosai kafun suka ƙarasa wajen da ake biyan kudi, ganin da yayi kamar tagaji ne yasashi ɗauko wata kujera ya ajiye mata batare daya kalleta ba yace.
"Please zauna ki jirani anan inazuwa yanzu."
Baijirayi me zatace masa ba ya juya, ya nufi part É—in da ake saida su chocolate da kuma kayan sweets.
Binsa tayi da kallo har saida ya ɓacewa ganinta, kafun ta sauƙe ajiyar zuciya, haɗe da dawo da kallonta ga mutanen dake ta hada hada awajen, yayinda kuma duk wanda yazo wucewa sai ya kalleta, musamman ma maza da suke mata ƙuri da ido kaman zasu cinyeta, wanda kuma hakanne yasa duk taji ta ƙosa da zaman wajen, saboda irin yanayin kallon da suke mata ne yasa taji ta kamar wata baƙuwar halitta wanda mutane basu saba gani ba.
Najeeb kuwa aƙalla saida ya share sama da 15 minute kafun ya dawo wajen, again trolley ne ahannunsa wanda ya sake cikasa da kaya.
Ƙin kallonsa tayi, domin kusan karo na uku kenan da yake kamata tana kallonsa, wannan yasa ayanzu taƙi ɗago kanta ta kallesa.
Gane manufarta ne yasashi sakin murmushin, domin kome take yana lure da ita, yasan sarai taƙi kallonsa ne saboda batason ya kamata akaro na hudu.
Yana tsaye kuwa aka gama yi masa lissafin kuɗinsa ya biya, tabbas ba ƙaramin kuɗi ya kashe a sayayyan nasa ba, saidai kuma ko ajikinsa baiji cewar ya kashe kuɗi ba,, saboda kuɗin akwaisu har ma ba asan iyaka adidinsu ba.
Nan cikin wasu ƙattin ledodi aka zuba musu kayayyakin tare kuma dasa wasu daga cikin ma'aikatan wajen suka kai musu mota.
Koda suka fito daga cikin shoprite ɗin, bayan motar Najeeb ya buɗe wa ma'aikatan suka zuba musu kayayyakin aciki, kasancewar shi me yawan kyauta ne yasashi zaro kuɗi a aljihunsa wanda shi kansa baisan ko nawa bane, ya bawa waƴanda suka kawo masa kayan, batare kuma daya saurari godiyarsu ba ya buɗe murfin motar ya shiga, Laylerh dake tsaye ganin ya shiga cikin motar ne yasa itama ta buɗe murfin motar ta shiga, akaron farko kenan da taji Najeeb din ya burgeta saboda kyautan da yayi, tabbas arayuwarta tanason mutum mai tausayin na ƙasa dashi, haɗe da mutum mai taimakon mutane masu rauni.
Tana gama daidaita zamanta ta jawo murfin motar ta rufe, ahankali ta maida idanunta ta rufe, tare da sauƙe ajiyar zuciya, haka takejin wani irin daddaɗan sanyi na ratsa duk jikinta, yayinda sabon shauƙin sa ke ratsa zuciya da ƙwaƙwalwarta, sanadin hakanne kuma yasa duk taji kasala ya sauƙar mata.
Sanin cewa baya kusa da ita ne yasa idanunta suka cika da tsumayin ganinsa.
Sanyi da kuma tsananin shauƙin dake ratsata ne yasa taji ajikinta cewa, "Inama da ace shine azaune akusa da ita ba Najeeba ba, inama da ace shine ke buɗe baki yana mata magana kamar yanda Najeeb ke mata, ina ma da ace shine keyi mata irin kallon da Najeeb ke mata." tabbas da ace zai zamanto gaba ɗaya duniyarta da har abada ta kasance acikin farinciki, kyawawan idanunsa ne suka shiga yi mata gizo aciki na idanun, lokaci ɗaya ta saki sahirtaccen murmushin daya ƙarawa fuskarta kyau, tabbas tanason komai nasa, musamman ma yanayin cikin kyawawan idanunsa, jajayen laɓɓansa, da kuma lafiyayyen sajen dake kwance akan ƙuncinsa, tabbas yana da tsari me matuƙar burgewa, wanda ako da yaushe yakesawa taji tana matuƙar son kallonsa, saidai kuma awani sashi na zuciyarta, shiɗin ya kasance kamar wani abun tsorone agareta.
Najeeb dake ƙoƙarin murza steering motar ne, ya zuba mata idanu cike da mamakin yanda yaga murmushi bayyane akan fuskarta, kasancewarsa mai saurin fahimtar yanayi da kuma halayyar ɗan adam ne yasa shi gane cewar tanajin daɗin tunanin da takeyi, duk da cewar baisan tunanin me take ba, amma kwata kwata bayason katseta daga yanayin nata, saboda murmushin da tayi ya matuƙar ƙarawa fuskarta kyau.
Ahankali ya murzawa motar key haɗe dayin reverse, kaitsaye ya fice daga farfajiyan shoprite ɗin, cike da ƙwarewa ya cilla motar tashi kan titi. wanda kuma sanadin hakanne ya sa Laylerh dawowa cikin hankalinta.
Ganin da yayi ta bude idanunta ne yasa shi cewa.
"Tunanin mekikeyi haka da ya miki dadi har kike murmushi?"
Idanunta ta ɗan lumshe, saboda kwata kwata bata taɓa tunanin cewa zai tambayeta game da tunanin da takeyi ɗin ba, mekenan zata ce masa? tace masa tunanin Ya M.jay ɗinta take, ko kuwa ta faɗa masa cewa tafara zargin kanta da cewar idan abun da takeji acikin zuciarta, shi ake ƙira So, to ta fara son Ya.M.jay.?
kanta taɗan girgiza, domin ita kanta bata yarda da cewar son Ya M.Jay din take ba, saboda kwata kwata ma batasan ya ake gane haƙiƙanin so na gaskiya ba.
Ganin tayi shiru ne yasa shi share maganar, saboda bayason matsa mata akan abun da take ɓoyewa acikin zuciyarta, kansa ya ɗan girgiza tare da sakin wani murmushi me ɗauke da ma'anoni daban daban, kana kuma cikin nutsuwa yaci gaba da tuƙinsa, yayinda kuma kusan rabin hankalinsa ya maidashi zuwa gareta.
Ganin tana hammane yasashi gane cewar bacci takeji, hakanne yasa shi ƙara gudun motar tasa, sai gashi kuwa cikin mintuna ƙalilan sun iso gida.
Laylerh da bacci ya soma ɗaukarta jin tsayuwar motar da kuma ƙaran horn ne yasa ta buɗe idanunta, ganin su a ƙofar gida ne yasata sauƙe ajiyar zuciya, domin dama duk jin kanta take atakure.
Ƙaran horn din motar nasu ne kuwa yasa maigadi tahowa cikin hanzari ya wangale musu gate din, anutse ya tura hancin motar nasa ciki, sai kuma da ya ƙarasa babban parking space ɗin gidan sannan ya daidaita parking ɗin motar.
ÆŠagowa yayi ya kalleta cikin sigar tsokana yace.
"Miss sleep wakeup mun iso gida."
Jin abun daya faɗane yasa ta ɗan sake ware idanunta, tare da turo ɗan ƙaramin bakinta gaba, cikin yanayin shagwaɓan da batasan tanayi ba tace. "Nifa ba bacci nakeyi ba." Murmushin daya bayyana fararen haƙwaransa yayi, cikin yin ƙasa da murya yace. "Really?."
Kai ta jinjina masa alaman ''Eh." Idanunsa ya ɗan lumshe saboda sosai yanayin shagwaɓan nata ya burgesa.
Ganin yanda ya zuba mata idone yasa ahankali ta soma ƙoƙarin buɗe murfin motar.
Akasalance yaƙira sunanta cikin wani irin murya, wanda jin amo da kuma sautin fitar muryar tasa ne yasata dakatawa, daga fitan da take ƙoƙarin yi tare da juyowa ta kalleshi.
Ganin ta juyo garesa ne yasa shi tura hannunsa acikin aljihun wandonsa, inda ya ciro wani haɗaɗɗen ɗan ƙaramin box me masifar kyau, irin dai box ɗinnan da ake sanya zobe ko sarƙa aciki, sosai aka ƙawata jikinsa, wanda kuma hakan alama ne dake nuna cewar zobe ko sarkan dake cikinsa me tsadane sosai, ahankali ya buɗe murfin box ɗin wanda hakan yabawa haɗaɗɗen diamond ring ɗin dake ciki daman bayyana, ring ne me kyaun gaske wanda aƙalla kuɗinsa zai iya kaiwa 500k, yanayin tsadan zoben da kuma kyaunsa ne, yasa yake wani irin shining, musamman ma duwatsun da akayi masa ado dashi, dan sunfi komai dake jikinsa ɗaukar hankali, ciro zoben daga ma'ajiyinsa yayi tare da ɗagowa ya kalleta, ganin ta zubawa zoben idanu ne yasa shi ɗan lumshe nasa idanun tare da sauƙe ajiyar zuciya, hannunsa ɗaya ya miƙa mata tare dayi mata alama akan tabashi hannunta.
Gane abun dayake nufi ne yasa tayi ƙasa da kanta, tare da soma wasa da ƴan yatsun hannunta, haka takejin kamar bazata iya sa hannunta acikin nasa ba.
Ganin tayi ƙasa da kanta ne yasa cikin wata irin kasallaliyar murya ya sake ƙiran sunanta.
Awannan karon kam bazata iya jurewa yanda amon muryarsa ke fita ba, gashi kuma duk ta ƙosa ta tafi, hakanne yasa ta miƙa masa hannun nata, kamar yanda ya buƙata.
Sauƙan lallausan fatar hannunta akan nasa ne, yayi sanadiyar miƙewar tsikar jikinsa, take yaji ƙofofin sadarwar tunaninsa sun tsaya, yayinda taushi da kuma laushin hannunta suka birkita masa tunani lokaci ɗaya suka kuma sauƙar masa da nannauyan kasala, idanunsa da suka ɗan soma marairaicewa ya zubawa kyawawan ƴan yatsun hannunta, wanda suke ɗauke da shining nails masu kyau, ahankali ya sauƙe ganinsa akan hafaɗɗen zoben dake sanye cikin ƙaramar ƴar yatsan hannunta wanda aka rubuta, *L.M* asamansa da manyan baƙi.
*L.M* ya maimaita kalman da aka rubuta ajikin zoben, wanda kuma haruffan da aka rubuta ɗinne suka ƙara ƙawata zoben, ƙurawa zoben idanu yayi, domin kuwa ya tabbatar cewa zoben ba gama gari bane, bakuma irin zoben nanne da ake zuwa super market asaya ba, zobe ne da idan mutum yanaso musamman ake haɗa masa a company, kuma ba ƙaramin kuɗi zoben ke dashi ba, musamman duba da irin yanayi da kuma tsarin zoben, wanda aƙalla kuɗinsa zai iya kaiwa 1.5 million. Ɗago shanyayyun idanunsa yayi, cikin sanyin murya yace.
"Waya saya miki wannan zoben?." Jin tambayar tasa ne yasa ta É—an É—ago ta kalleshi, sanin cewa bata da amsar da zata bashi shiyasa tayi shiru, domin azahirance itama batasan waya siya ko ya bata zoben ba, saboda itama kawai ganin ring É—in tayi ahannunta, wanda kuma har yau takasa ciresa daga yatsanta duk da kuwa cewar ayanzu ring É—in yaÉ—an matse hannunta.
Ganin tayi shiru ne yasashi sauƙe ajiyar zuciya, lokaci ɗaya yasoma ƙoƙarin yaƙi da mummunan tunanin dake son shiga zuciyarsa, ƴar yatsan hannunta na tsakiya ya kama, ahankali ya zura mata haɗaɗɗen zoben dake hannunsa.
"Happy Engagement!" yafaɗa adaidai lokacin da yagama zura mata zoben a yatsarta, wanda ya zauna ɗas kana ya kuma ƙarawa hannun nata kyau. "Engagement!." Ta maimaita kalmar acikin zuciyarta, dan kuwa hakanan taji kalmar tayi mata ban baraƙwai abakinta, gefe guda kuwa yanayin yanda ya riƙe hannunta ne yasa duk taji ta takura, ƙoƙarin janye hannuta daga cikin nasa tayi, saidai yanayin irin riƙon da yayi mata ne yasa bazata iya ƙwace hannun nata ba, har sai in dan kanshi ya sake mata, kwaɓe fuska tayi haɗe da ɗan karyar da wuyanta gefe, cikin muryarta dake ɗauke da zallan shagwaɓa tace. "Please ni zanje nayi bacci."
Sassauta riƙon hannun nata yayi, cikin kasalalliyar murya yace.
"Okay please ki kulamin da kanki sosai, sannan kiyi bacci me daɗi kinji, good night and sweet dreams my beautyful girl!." ya ƙare maganar yana me kissing ɗin soft hand skin ɗinta.
Cikin sauri ta janye hannunta tare da buɗe murfin motar ta fice, batare kuma da ta tsaya sauraran wani abu da zaice ba kaitsaye ta nufi ƙofar babban falon gidan.
Idanunsa da sukayi matuƙar ƙaɗawa kana sukayi ja ya rumtse, cikin wani irin zafin zuciya da kuma raɗaɗin daya keji ya dunƙule hannayensa tare da naushin glsss ɗin window'n, wanda hakan yasa gaba ɗaya glass ɗin amsawa, saidai kasancewar glass ɗin me ƙarfin gaskene yasa bai wani fashe wa sosai ba, akaro na farko kenan da tun tsayuwarsa awajen ya zame, inda ya zauna akan guiwowinsa, wanda kusan sama da 40 minute ya ɗauka a tsaye yana jiran dawowarsu, yanayin yanda yakejin ƙuna acikin ransa ne yasashi dafe ƙirjinsa daidai saitin zuciyarsa dake bugawa, komai kuwa daya faru atsakanin Laylerh da Najeeb din akan idanunsa, amatuƙar zafafe yakejin ƙirjinsa nayi masa suka, yayinda yakejin wani irin fushi ya cika zuciyarsa, haka yakeji kaman ya tashi yaje ya kakkarya Laylerh'n gida biyu, domin kuwa wani irin haushi da takaicin sune ya cika ƙirjinsa, babbar abun dayake sukan zuciyarsa kuwa shine, yanda yaga Laylerh'n ta miƙawa Najeeb hannunta, tabbas ganin da yayi musu yasa gaba ɗaya duniyar ta daina yi masa daɗi, yayinda baƙin ciki da ƙuna suka maye gurbin nutsuwarsa, bakomai yafi ƙona masa zuciya ba kuwa face kissing hannun Laylerh'n da yaga Najeeb ɗin yayi, wanda hakan ya zamanto tamkar sauƙan mashi ne akan ƙahon zuciyarsa, idanunsa ya kuma rumtsewa da ƙarfi, yayinda yakejin kansa na wani irin juyawa, sanadin hakanne kuwa yasa take memories din baya suka soma dawowa cikin ƙwaƙwalwarsa, wanda hakan ya sashi ƙara birkicewa, kunnuwansa ne suka soma dawo masa da gunjin kukanta, inda yakejin siririyar muryarta dake cikin matsanancin neman taimako na dukan zuciya da kuma hautsuna masa ƙwaƙwalwa, ahankali yanayin daya wuce ya soma wanzuwa acikin idanunsa, hakan yasa shi jin tamkar alokacinne abun ke faruwa. Lokaci ɗaya gaba ɗaya jijiyoyin kansa suka amsa da wani irin azababben ciwo, yayinda kuma gashin jikinsa suka mimmiƙe, still kuka da sautin muryarta yakeji suna tashi acikin kunnuwan sa, wanda hakan yasa amatuƙar zauce ya soma buga kansa da jikin bango, kwata kwata bayason jin ihun nata dake ƙoƙarin mai dashi mahaukaci, kana kuma bayason ganin moment ɗin daya riga ya wuce acikin idanunsa.
Cikin 10 minute gaba ɗaya ya fita hayyacinsa tare da zaucewa, da ƙyar ya iya tashi ya ƙarasa gaban drawer'n da anan ciki yake ajiye cocaine ɗinsa, ɗeɓo cocaine ɗin yayi ya zuba akan tiles din dake malale ƙasan ɗakin, kwanciya yayi aƙasan wajen kana cikin yanayin zaucewa ya shiga shaƙan cocaine din azafafe, yanayin yanda yake zuƙanta kaman mahaukaci ne yasa take hankalinsa ya soma gushewa, sanadin hakanne kuma yasa duk wani tunani dake cikin ransa ya kau, lokaci ɗaya ya samu kansa cikin wata sabuwar duniya.
Ahankali ya buɗe idanunsa wanda suka rikiɗe suka sake yin ja, saman ɗakin nasa dayake ganin yana juya masa ya ƙurawa ido, saboda haka yake gani kamar ba acikin duniya yake ba, cikin abun da bai wuce 14 minute ba ya sake samun kansa cikin wata duniyar, wanda take kama da bacci, suma, da kuma fitar hankali. Idanunsa ne suka rufe yayinda gaba ɗaya jikinsa ya daina motsi.
ÆÂangaren Laylerh kuwa koda ta Æ™asara cikin falon, bata iske kowa ba hakan yasa kaitsaye ta wuce É—akinta, kasancewar amatuÆ™ar gajiye take hakan yasa doguwar rigar dake jikinta kawai ta cire, kana ta wuce toilet ta É—auro alwala, baccine sosai ya cika idanunta hakan yasa tana fitowa daga toilet É—in ta faÉ—a saman gadonta, cike da mayen bacci tayi addu'a, cikin abun da baiwuce mintuna 15 ba kuwa bacci ya É—auketa.
Najeeb kuwa zuciyarsa cike da tarin tunani haɗi da saƙe saƙe kala kala ya wuce masauƙinsa, babu abun daya tsaya masa arai kamar kalmomi biyun da yagani ajikin zoben dake hannun Laylerh'n, gaba ɗaya zuciyarsa taƙi nutsuwa masa da hakan, baisan meyasa akaron farko yaji faɗuwar gaba ta ziyarcesa ba.
haka dai yayita juyi akan gadon, zuciyarsa cike da tunani kala kala bacci ɓarawo ya ɗaukesa.
Washegari.
Kasancewar ranan yau takasance ranan weekend, hakan yasa Laylerh koda ta tashi tayi sallan asuba wani sabon bacci ta sake komawa, ba ita ta farka ba kuwa sai kusan 9 am, tun tashinta taji gaba ɗaya gidan nasu ya cika da hayaniyar mutane, kaitsaye toilet ta wuce tayi wanka, koda ta fito mai kawai ta shafa ajikinta sai normal tpowder da taɗan murza akan fuskarta, wata doguwar rigan abaya me kyau tasaka ajikinta, tare da yane kanta da ɗan kwalin kayan, kasancewar tun tashinta takejin cikinta na kukan yunwa ne yasa ta zura takalmin flat shoe aƙafanta, kaitsaye ta nufi falo duk da kuwa kasancewar yau din tun tashinta takejin faɗuwar gaba haɗe kuma da tsinkewar zuciya na ziyartarta, sanin cewa bata da makama sai addu'a ne, yasa ta shiga karanro addu'a haɗi da ambaton sunan Allah azuciyarta, tunkaro falon da tayine yasa tasoma jiyo ɗan surutan mutane wanda kuma da dukkan alamu Momy ce da ƙawayenta, ƙarasowanta cikin falonne yasa idanunta suka sauƙa akan wasu haɗaɗɗun akwatunan da suka cike tsakiyan falon, wanda aƙalla yawansu zasu kai goma sha huɗu, akwatuna ne different colours masu kyau da kuma burgewa, hakanne yasa ma ta zubawa akwatunan ido.
"Gaskiya Hajiya Suwaeba kayan aure sunyi kyau Laylerh tayi goshi, saura kuma afara yi mata gyaran amarya, tun da dai biki ya matso kusa."
Ɗaya daga cikin ƙawayen Momy tafaɗa, tana me ɗaga wani tsadadden lace ɗin dake hannunta, wanda yake ɗaya ne daga cikin kayan auren.
Maganganun da ƙawar Momyn ke faɗa ne yasa zuciyar Laylerh tayi wani irin bugawa.
(note edit)
1/19/21, 8:13 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Writting by*
fatymasardauna
*(This book is mainly for those that pay, if you know you did'nt pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay-0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz bank. Whatsapp number 07017879464. )*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.