Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: LAYLERH MALEEK.txt
Chapter 26 of 65
*Chapter 41*
“Pleaseee Laylerh!�
Yafad’i hakan cikin dashashshiyar muryarsa, dako fita da kyau batayi, hak’ik’a kuma kallo d’aya zakayi masa kafahimci cewa yakae wani matsaya wanda k’iris ya rage ya zauce, domin kuwa idanunsa k’ank’ance wasn’t sukayi tare dayin jajur kaman anwatsa musu garin barkono acikinsu, yayinda gaba d’aya hannayensa ke rawa, tabbas yaje wani level me tsananin wahala, saboda kallon surar Laylerh’n da yayi naked ba k’aramin wargaza masa lissafi yayi ba, duk dama iya saman k’irjinta kawae yake iya kallo amma hakan baihanashi zaucewa da rud’ewa ba.
Hak’ik’a tsoron dake kwance acikin zuciyarta ya bayyana akan fuskarta k’arara, domin da ace Najeeb d’in Zae dawo cikin nutsuwarsa yayi mata duban tsab to tabbas da yakaranci yanayin da take ciki, dan kuwa harta labb’an bakinta karkarwa suke saboda matsanancin tsoron da ya shigeta.
Sake k’ank’ame jikinta waje d’aya tayi, tare da had’e tafukan hannayenta waje d’aya, cikin yanayin firgici da kuma alaman rok’o, da muryarta dake matsanancin rawa tace.
“Dan Allah Kayi hakuri, kabarni tsoro nakeji!!� Yanayin yanda tak’are maganar tana me d’an janjikinta bayane, yasa Najeeb saurin rik’o hannunta yasaka acikin nasa, da idanunsa wanda sukayi luhu luhu ya kalleta, cikin sark’akk’iyar muryar yace.
“Please Laylerh help me, wallahi ni kad’ai nasan abunda nakeji acikin gangar jikina, ina matuk’ar buk’atar kulawanki Laylerh please Laylerh karki cemin a’a!�
Yanayin yanda ya k’are maganar cikin sigar dake bayyana rok’o agareta, da kuma bayyana gaskiar abunda ke ransa yasa, Laylerh soma d’an girgiza kanta, tare da cigaba dajan jikinta baya, tabbas har acikin ranta amatuk’ar firgice take dashi, tsoro da fargabane suka cika mata zuciya, wanda hakan yasa bazata tab’a iya control d’in kanta ba, hak’ik’a tanajin tsoron Najeeb d’in sosae, amma kuma har acikin zuciyarta tasan cewar hanasa hakk’insa tamkar sab’awa Ubangijinta ne, sannan kuma zata kwana mala’ikun Allah na tsine mata.
“Shin tayaya zata iya jure duk way’annan? Tayaya zata iya mallakawa Najeeb kai dama jikinta gaba d’aya? Hak’ik’a budurci shine abu mafi girma da kowacce y’a mace ke tink’aho dashi, burin kuma duk wata macece tabada budurcinta ga wanda ya dace sannan ya kuma cancanta, akuma guri d’aya ne idan kabada budurcinka baka da danasani, shine gidan aurenka da kuma masoyinka na gaskiya, wanda har abada bazaka tab’a danasanin hakan ba, tabbas Najeeb mijinta ne, amma kuma baizamo zab’in zuciyarta ba, shin zamowarsa mijinta kad’ai ya isa ya cancanci karb’an budurcinta?�
Tayiwa kanta duka tambayoyin alokacin guda batare kuma da tana da gamsasshiyar amsar da zata bawa kanta ba.
“Tabbas bawa Najeeb jikinta da zatayi ayanzu daidai yake da ruguza duk wani mafarkinta�
Wani yanki na zuciyarta ta tasanar da ita hakan.
Sanin bata da zab’i ne kuma yasata rumtse idanunta, tare da soma taune labb’anta, cikin zuciyarta tasoma ambatan sunan Allah Domin kuwa shikad’aine sarkin da zai taimaketa adaidai wannan lokacin.
Najeeb kuwa ganin yanda ta rumtse idanunta da kuma yanda take aikin taunan lips d’inta tamkar wata zautacciya ne yasashi matsowa kusa da ita sosae, idanunsa ya k’ura mata, take yaji wani irin matsanancin tausayin ta ya cika masa zuciya, lokaci d’aya yaji gaba d’aya guiwowin jikinsa sunyi sanyi, yayinda wani irin yanayi na daban ya sauk’ar masa, ahankali ya matso gareta cikin sabon yanayin daya samu kansa aciki kuwa ya kamo hannunta tare da jawota jikinsa yayi mata wani irin runguman da saida k’ashin jikinta yayi k’ara, idanunsa wanda sukayi jajur ya lumshe lokaci d’aya ya saki wani irin ajiyar zuciya me k’arfi.
Hab’arsa ya d’aura akan kafad’an Laylerh’n, wanda hakan ya bashi daman cigaba da shak’an daddad’an k’amshin dake fita ajikinta.
Akaron farko kenan da ya gano cewar zuciyarsa tayi nisa wajen tausayin Laylerhn, domin yanayin daya ganta aciki yanzu yasa gaba d’aya jikinsa yayi sanyi, sam koda wasa bai tab’a tunanin cewar zuciyarsa tayi k’arfi sosae har haka awajen tausayin Laylerh’n ba.
Hak’ik’a ya k’udurta aransa cewar yau zai tabbatarwa kansa da zama cikakken ango kuma Namiji, tabbas gangar jiki da zuciyarsa amatuk’ar buk’ace suke da Laylerh’n, amma kuma bayajin zai mata dole, domin bata hanyar k’arfi yakeson karb’an budurcinta ba, duba da irin k’ananan shekarunta yasa shi so da buk’atar amincewarta, domin rashin neman yardarta zai iya jawo komae, ayanzu da takasance matarsa soyayyarta yake buk’ata fiye da komai, yana da yak’inin zai samu hakanne kuma kad’ai tahanyar lallami da kuma rarrashinta, saboda yasan cewa ba abun dake jawo k’akk’arfan tsana kamar karb’an virgin d’in mace ta k’arfi, ko kuma ba’a bisa son ranta ba, bakuma yason hakan yafaru atsakaninsa da Laylerh’n, lallai dole zaiyi hak’uri adaren yau, saboda ya fahimci cewa akwae k’alubale dayawa agabansa, abu na farko kuma shine dole ne ya koyawa Laylerh’n zama tare dashi, son kasancewa dashi da kuma son yin magana dashi.
Ahankali yakai bakinsa daidai saitin kunnenta,cikin yanayin sanyi had’i da karkarwar da muryarsa keyi yace.
“Is okay Laylerh, i promised you bazan miki komae ba, ki daina kuka please, kawai dai nakasa control d’in kaina ne, amma Laylerh kimin alk’awarin cewa watarana zaki bani kanki cikin amincewa da kuma yarda, please Laylerh kimin wannan alk’awarin...� yakai k’arshen maganartasa yana me rumtse idanunsa da k’arfi saboda yanda yaji mararsa na murd’awa.
Tabbas maganganun nasa sunsa jikinta matuk’ar yin sanyi, take kuma tausayin kanta dana Najeeb d’in ya kamata, domin tasan cewa K’addara ce kawae ke bibiyan rayuwarsu, shi yana sonta ita da zuciyarta kuma suna son wani, tasani cewa Maleek bugun zuciya da numfashinta ne, amma kuma Najeeb Mijinta ne, kuma yana iko da komae najikinta.
Tambaya d’aya kawae take ta nanatawa azuciyarta shine ya zatayi?
Najeeb kuwa jin tayi shirune yasa ahankali ya janye jikinsa daga nata, tare da mirginawa gefe ya kwanta irin kwanciyar nan ta rubda ciki, hannunsa yasa ya dafe kan maransa dake masa wani irin ciwo, har wani zugi yakeji awajen.
Wasu irin hawaye ne suka silalo daga cikin idanunta, wanda kuma ita kanta batasan hawayen nata na meye bane, haryanzu tana neman hanyar da zaisa ta juri d’aukan duka way’annan nauyin akanta, ahankali ta sulale ta kwanta akan gadon tare da jawo rigarta da Najeeb din ya soma cire mata sama, dunk’ule jikinta waje d’aya tayi tare dajan tattausan wadataccen blanket d’in dake kan gadon ta rufe gaba d’aya jikinta dashi, ahankali take sakin wani irin numfashi, wanda yake fita da sautin sheshshek’an kuka.
Kasancewar kuma bata cikin mood me dad’ine yasa ko mintuna 15 batayi ba bacci ya d’auketa.
Duk da cewar baya cikin bargon amma yana iya jiyo sautin fitan numfashinta me had’e da sheshshek’a, yanayin yanda yaji fitan numfashinnata ne kuma yasa shi gane cewar bacci takeyi.
Ahankali ya bud’e idanunsa dake alumshe, tare da juyowa ya k’urawa Bayan Laylerhn idanu, haka yakejin wani irin abu na yawo acikin zuciyarsa.
Duk da cewar kuwa yanajin ciwon Mara me tsanani, amma haka dan dolensa ya daure, da Allah Yatashi taimakonsa kuwa baiwani jima ba bacci ya d’aukesa.
*Washegari*
9:30 am daidai k’aran alarm d’in dake gefen had’add’en gadon ya karad’e cikin d’akin, bugawan alarm din kuwa yayi daidai da shigowar k’iran wayan dake aje gefen alarm clock d’in.
K’aran daya karad’e kunnuwansanne yasa ahankali ya soma bud’e kyawawan idanunsa masu kalan maye wanda ke cike da bacci.
Cikin yanayin k’osawa da k’aran yakai hannunsa ya kashe alarm d’in, akasalance ya jawo wayartasa dake ta faman tsuwa, k’ok’arin kasheta gaba d’aya yasoma yi saidai kuma ganin sunan Abbou Jaheed da yayi rubuce akan screen din wayar ne yasashi fasa kashe wayar, swiping na wajen picking call d’in yayi tare da kara wayar akan kunnensa.
Abbou Jaheed kuwa jin Maleek d’in ya d’aga wayar batare da yatsaya yaji ta bakinsa ba yace.
“Mekake jira da har zuwa yanzu baka fito ba?.�
Jin tambayan da Abbou Jaheed d’in yayi masa ne yasashi d’an rumtse idanunsa, cikin muryarsa da ke d’auke da yanayin bacci yace.
“Bantashi abacci ba.�
“Badamuwata bane hakan, nabaka nan da 30 minute kazo kasameni afalona, dannayi alk’awari ba kuma zan zama mai sab’a alk’awari ba.� Cewar Abbou Jaheed ransa amatuk’ar b’ace, wanda jin yanayin yanda muryar Maleek d’in ya sanja, yasashi yin Tunanin ko wani abun mayen Maleek d’in ya sake sha, kashe wayartasa yayi tare da maida ita cikin aljihu, ya zauna zaman jiran zuwan Maleek d’in.
Jin Abbou Jaheed ya kasha k’iranne yasashi zare wayar akunnensa, Allah Yasani maganar auren da Abbou’n yace zaiyi masa ya matuk’ar d’aga masa hankali, wanda har yake fatan ace mafarki yake bawai gaske bane.
Ahankali ya yaye blanket d’in dake jikinsa tare da tashi zaune ya zuro da k’afafunsa k’asa daga kan gadon.
Hannayensa yasa ya d’an murza idanunsa, kana kuma cikin yanayin kasalan da yakejin kansa aciki ya mik’e tsaye.
Kamar kullum kuma kamar koda yaushe hotonta yasaba kallo Aduk sanda ya tashi daga bacci, to yanzun ma hakanne takasance, domin saida ya sauk’e idanunsa akan d’an k’aramin hotonta dake aje bisa bedside d’insa.
Idanunsa ya d’an lumshe tare da sauk’e sassanyar ajiyar zuciya, tabbas ya aminta cewa kallon kyakkyawar cute face d’inta yana sama masa nutsuwa, saidai kuma akoda yaushe idan ya tuna cewar ayanzu matsayin mata take ga waninsa sai yaji gaba d’aya komae na duniyar ya daena yi masa dad’i.
Cikin son kawar da duk wani tunani daga cikin zuciyarsa kaitsaye ya nufi toilet, yana shiga kuwa ya sakarwa kansa ruwa, wanka yayi tare da d’auro towel akan waist d’insa ya fito.
Sanin halin Abbou Jaheed ne yasashi goge jikinsa cikin hanzari ya shags mai ajikinsa, k’arasawa gaban drawer’nsa yayi tare da ciro kayan da zai saka.
Wani riga da wandon jeans masu d’an kauri yasanya ajikinsa, kasancewar ana d’an yanayin sanyi, sosae kuwa kayan suka amshi murd’add’iyar surar jikinsa, yayinda suka k’ara bayyana kyawunsa, kasancewar kuma kayannasa nada kalan dark blue ne yasashi saka wasu dark blue d’in takalma masu yanayi da sneakers shoe, dark blue d’in hulan facing cap ya saka akansa, tare da d’aura agogon Gucci ahannunsa.
Sassanyan perfumed d’insa ya fesa, tare da d’aukan wayarsa yasa acikin aljihunsa, duk da cewar kuwa bayajin dadi acikin ransa, amma dole haka ya daure tare da kokarin samawa kansa nutsuwa.
Yayinda acikin zuciyarsa kuwa yake mamakin cewar wae kamanshi Maleek za’ayiwa auren dole.
Wani murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa daidai lokacin da yake ficewa daga cikin dakin nasa, badan komae yayi murmushinba kuwa face ji da yayi ajikinsa cewar auren da Abbou Jaheed d’in keson d’aura masa bazae tab’a yiwuwa ba.
Locking k’ofar d’akinnasa yayi, tare dasa kansa direct b’angaren Abbou Jaheed ya wuce.
Yana zuwa kuwa ya samu Abbou Jaheed tsaye yana jiransa.
Ganinsa yasa Abbou Jaheed soma k’are masa kallo kamar zaice wani abu kuma saiya fasa, cikin had’e fuska yace.
“Muje.�
Haka suka fito daga sashin Abbou Jaheed d’in Maleek na biye dashi abaya.
Kaitsaye wajen da motar Abbou Jaheed d’in ke fake k’iran tundra suka nufa, gidan baya suka shiga dukansu, take kuwa driver’n Abbou Jaheed d’in yaja motar suka bar cikin gidan.
*(Am sorry Nagajine Wllhy😰)*
1/25/21, 9:16 AM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Writting By*
fatymasardauna
*Note edit*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.