Best Hausa Novels

Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: LAYLERH MALEEK.txt

Chapter 6 of 65

*Chapter 13*

Hannu Abbou Jaheed yasa ya dafa kafaɗanta, cikin kulawa haɗi da muryarsa da tayi sanyi yaƙira sunanta, saboda kukan nata ya farayin yawa, wanda hakan kuma zai iya haifar mata da ciwon kai me tsanani.
Jin yanda Abbou yaƙira sunanta asanyaye ne yasa ta soma ƙoƙarin daidaita nutsuwarta, tare kuma da ƙoƙarin shanye kukan da takeyi ɗin, saidai duk yanda taso tsaida kukan nata hakan yaci tura, domin kuwa kukan ya riga da yaci ƙarfinta,wanda har hakan ke ƙoƙarin fallasa sirrin dake cikin zuciyarta.
sheshsheƙan kukan da take sakewa ne yasa Abbou Jaheed ɗin miƙo mata bottle water me sanyi, ayanda takejin ƙirjinta nayi mata ƙuna, yasa batajin zata iya ƙin amsan ruwan, hannunta dake rawa tasa ta karɓi goran ruwan, yayinda shi dakansa ya buɗe mata murfin goran, takai ruwan bakinta. Sosai ta shiga tuttulawa cikinta ruwa, har saida tasha fiye da rabin goran, ganin yawan shan ruwan zai iya kawo mata wani abu na daban, ko ma ta iya ƙwarewa ne yasa Abbou Jaheed ya karɓi bottle water'n daga hannunta. Ajiyar zuciya ta shiga sauƙewa akai akai yayinda takejin zuciyarta ta sakeyi mata nauyi, gaba ɗaya haka taji komai na duniyar ya daina yi mata daɗi, yayinda taji wani abu me nauyi ya tokare mata aƙirjinta, still ga kuma wani irin ciwon kai da takeji, wanda har ta kai ga tanajin kannata na sarawa, miƙewa tsaye tayi tare da lumshe kyawawan idanunta wanda sukayi jajur, suka kuma bayyanar da zallan abun dake cikin zuciyarta, wato haƙiƙanin gaskiyar da ita kanta batasan da cewar tana kwance acikin zuciyarta ba.
Kallonta Abbou Jaheed yayi cikin tausasa murya haÉ—i da tausayinta yace. "Ina zakije, bayan kuma bakici abinci ba?."
ÆŠan buÉ—e runannun idanunta da suka soma lumshewa tayi, cikin sanyi da kuma muryarta daya soma dashewa tace. "Bacci nakeji Abbou, zanje É—aki ne na kwanta."
ÆŠan jim yayi, kana cikin yarda da abun da tafaÉ—a É—in ya jinjina mata kai alaman "Taje ta kwanta."
Batajin zata iya sake ɗaga idanu ta kalli wani daga cikinsu, saboda haka asanyaye ta juya ta nufi hanyar sauƙa daga step na dining area'n.
Da kallo Abbou Jaheed ya bita yana mejin wani abu na yawo acikin ransa, hakanan yakejin kamar kukan da ta keyi, bana haka kawai bane yana ɗauke ne da ma'anoni guda biyu, wanda kuma yakasa fahimtar haƙiƙanin ma'anar hakan, saidai wata zuciyar tana nusar dashi cewar bawai tana kukane saboda batason zaɓin da yayi mata ba, tana kukane saboda al'amarin yazo mata abazata, kasancewar har yanzu ita yarinyace. Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da ɗan yin shiru, kana ya daina cin abincin da yakeyi.
Aɗaya daga cikin ɓari na zuciyarsa sam bayajin cewa zaɓawa Laylerh miji da yayi, kawo nakasu ne acikin rayuwarta, domin yayi imani cewa Najeeb zai kula da Laylerh sosai. haka zalika bazai taɓa barinta tayi kukan maraici ba, saidai kuma ya rasa me yasa wata zuciyar tasa ke so da ƙoƙarin kawo masa wani tunani na daban adangane da hakan, wanda kuma ya tabbatar cewa tunanin hakan bazai amfanar dashi da komai ba, ganin da yayi damuwa na ƙoƙarin shiga zuciyarsa ne ya sashi share duk wani tunani ya cigaba da cin abincinsa, aransa yana me fatan hakan da yayi ya zamanto Alkhairi agaba ɗaya rayuwarsu.

Maleek.
Dake tafiya yana gauraya hanya, kamar yanda ya baro cikin falon baya iya ganin gabansa sosai, haka ma har yanzu dishi dishi yake gani a idanunsa, ahaka ya ƙaraso cikin tamfatsetsen bedroom ɗinsa wanda ke cike da kayan alfarma. Hannunsa dake rawa ya ɗaura akan handle ɗin ƙofar, tare da maida ita ya rufe, ahankali ya jingina bayansa da jikin ƙofar tare da rumtse jajayen idanunsa masu kama da garwashin wuta, zuciya da ƙirjinsa ne keyi masa wani irin zafi da suka, yayinda wani irin ɗaci ke mamaye maƙoshinsa, ƙwaƙwalwarsa ce ke ƙoƙarin zautar dashi, ta hanyar dawo masa da maganganun Laylerh'n cikin kunnensa. *"NA AMINCE"* wannan kalmar da ta faɗa tafi komai haukata tunaninsa,domin jin sauƙarta yayi acikin kunnensa tamkar diran aradu, kwata kwata bayajin zai iya jurewa, wani abu me kama da fargaba ne ke neman daƙushe tunaninsa, hakanne kuma ke sa zuciyarsa tsananta bugawa, har takai ga yana iya jin faɗuwar gaba da kuma wani yanayi na daban, sam bai saba da irin wannan yanayin da yakejin kansa aciki ba, wanda hakanne yasa bayajin zai iya jurewa.
Asanyaye ya buɗe idanunsa wanda suka sake runewa, yayinda kansa ke masa wani irin ciwo, irin wanda bai taɓa jiba, ahankali ya shiga taka ƙafafunsa da suke gab da kasa ɗaukar nauyinsa, saboda yanda gaba ɗaya jikinsa yayi weak, ƙarasawa gaban tsayayye kuma babban mirror'n dake manne agefen drawer'nsa yayi. Jajayen Idanunsa ya sauƙe akan madubin, wanda hakan yabashi daman kallon hoton bayyananniyar surar jikinsa, tun daga kan ƙafarsa har zuwa kansa, akaro na farko kenan daya taɓa zubawa kansa idanu ta cikin madubi, hakanan yaji gaba ɗaya zuciyarsa tayi rauni, wanda har hakan ya bayyana acikin idanunsa. "RAUNI!" Ya faɗa cikin wata irin murya, tare da rumtse idanunsa ƙam, domin itace kalmar daya fi tsana arayuwarsa, sanin cewa itace take ta wasa da zuciya haɗi da Ƙaddaransa.
Hannunsa dake adunƙule yasa ya bugi daidai saitin zuciyarsa, still cikin wata murya me ɗauke da wani irin amo dake son bayyana jajircewarsa yace. *"I am not a LOSER, and i will never be LOSER."*
Ɓuɗe idanunsa da suke a rumtse yayi tare da jingina bayansa da jikin bango, tabbas ayanzu shi kaɗai yasan me yakeji acikin zuciyarsa, duk da cewar yanajin zafi da raɗaɗi azuciyarsa, amma bayaso ya zamanto RAGO, aƙidarsa ce kuma fatansa ne, akullum yasan cewar shiba Rago bane, har yanzu kuwa yanaji ajikinsa cewa har abada bazai taɓa zama rago ba, duk da kuwa yasan cewar Ƙaddaransa nada rauni, amma hakan bazai sashi zama me kasawa ba, yanaji ajikinsa cewar kalmar LOSER bazata ci gaba da yawo acikin jininsu shida abokinsa SOORAJ ba, duk da kuwa cewar yasan SOORAJ yayi nasara na samun abun da yakeso, amma shi wata zuciyar bata gaya masa cewar zaiyi nasara.

Acan falo kuwa Najeeb da gaba ɗaya kukan Laylerh'n ya gama ɗaga masa hankali, ɗan jingina bayansa da jikin kujeran da yake kai yayi tare da lumshe idanunsa. Tabbas yasan cewa yana cikin farinciki ayau, domin samun Laylerh ba ƙaramar sa'a bace ga kowanni Ɗa Namiji, saidai kuma kukan dayaga tanayi ya matuƙar taɓa masa zuciya, duk kuwa da yanda ya zurfafa tunaninsa ya kasa tantance wa da kuma gano kukan nata na miyene, saboda zuciyarsa bata kawo masa cewar akan aurensa take wannan kukan ba, domin ya yarda cewa shi namiji ne da kowacce mace zatayi fatan samu, why Laylerh zatayi kuka akan maganar aurensa da ita?. Wani irin killer smile ya sake tare da ɗan soma jujjuya kujeran da yake kai, bayajin zai damu da koma meye, saboda yaji ajikinsa cewa Laylerh mallakinsa ce.
Momy kuwa da jin batun auren Laylerh da Najeeb, yasa ta aikin saƙawa da kuncewa acikin zuciyarta, samun mafita da tayi yasa ta saki murmushi me ɗauke da ma'anoni daban daban, cikin nuna kulawa da kuma son auren tace.
"Masha Allah Najeeb angon Laylerh, gaskiya wannan bikin na Æ´an gata ne, saboda haka ya kamata mu fara shiri tunda wuri, congratulation na ta yaka murna."
Murmushi Najeeb ɗin yayi tare da yin ƙasa da kansa, Abbou Jaheed da Alhaji Ahmad Rufae ma murmushin sukayi, domin sun riga da sunsan me suka shirya, Abbou Jaheed ne ya dubeta, cikin kulawa yace. "Karki damu very soon za'ayi biki Insha Allah, maybe ma nanda 3 to 4 weeks."
Cike da mamakin kusancin abun Momy taÉ—an zaro idanunta, wani abu kuma da ta tunane ya sata sakin murmushi. Tare da cewa. "Allah Ya kaimu."
"Ameen." suka faɗa atare daga haka kuma babu wanda yasake cewa komai acikinsu suka ci gaba da cin abinci, zuciyar Abbou Jaheed fari tas, domin gashi da yardar Allah Zai cika alƙawarin daya ɗaukarwa Amininsa, saidai kuma har yanzu idan ya tuna wani abu sai yanajin fargaba da kuma faɗuwar gaba na ziyartarsa, sanin cewa sharrin shaiɗan nada yawa ne ya sashi soma faɗin "A'uzubillahi!." acikin zuciyarsa, dan yasan da hakane kaɗai zai samu tsira daga abun da yakeji, wanda har yake zargin kansa da rashin aikata daidai.

Laylerh da tun barin dining ɗin, ta nufi ɗakinta ahankali take iya taka ƙafafunta, komai bayayi mata dadi, duniyar kanta dama abubuwan dake cikinta, jin zuciyarta takeyi acunkushe, yayinda tunani da nutsuwarta ke ƙoƙarin yin rauni, kamar yanda bugun zuciyarta ayanzu ta raunana.
Ahankali ta maida ƙofar ɗakin nata ta rufe, duk jikinta rawa yake har ta ƙafafunta kuwa, ƙarasawa gaban gadonta tayi, tare da zuba guiwowinta aƙasa, wasu irin hawaye masu zafin gaske ne suka silalo daga cikin idanun nata wanda hakan yasa ta lumshe su, akaron farko kenan da ta fara samun kanta cikin irin wannan yanayin, yanayin daya zamanto barazana ga bugawar zuciyarta, ita kanta batasan me takeji ba, bata kuma san me takeyiwa kuka ba, hasalima amsa take nema domin tana da buƙatar sanin me takeyiwa kuka, kukan zaɓin da Abbou Jaheed yayi mata ne kokuma me?, hannu tasa ta share hawayen da suka zubo mata, tare da sadda kanta ƙasa, tasani tabbas Abbou Jaheed Ubane agareta, kuma koda sau ɗaya bata taɓa masa kallon wani na daban agareta ba, Abbou shine gaba ɗaya duk wani gatan ta, ya riƙeta alokacin da tafi kowa buƙatar hakan, ya bata gata alokacin da duk wasu masu bata gata su ka bar duniya, saboda ita kawai ya bar kasuwancinsa na Dubai ya dawo Nigeria, ko yaushe burinsa shine ya sama mata farinciki, wannan kaɗai yasa bai cancanci butulci awajenta ba, domin bai kasance me musguna mata ba, ta yaya zata ƙi amincewa da zaɓinsa? tayaya zata watsa masa ƙasa a idanunsa? tayaya zata dubi mutum me girma kamarsa tace bata amince da zaɓinsa ba? tsawon shekaru da dama kenan da yake riƙonta bai kuma taɓa neman wata alfarma awajenta ba sai akan wannan, shi me iya bata umarni ne ako da yaushe, amma ayanzu sai yabata zaɓi, me yasa zata ƙi amsan zaɓi da kuma umarninsa na farko? ba zata iya ba, saboda ta yarda cewa aduniya babu wani Namiji bayan UBA haka kuma babu wata mace bayan UWA mahaifiya, tayi imani kuma cewa ita me karɓan zaɓin Abbou ne koda kuwa wani daban zai kawo yace ta aura zata amince masa.

Ɗan zamewa tayi tare da jingina kanta ajikin gado, kuka ne me sauti ya ƙwace mata, hakan yasa ta ƙanƙame jikinta waje ɗaya, tare da soma rera kukan, gaba ɗaya zuciyarta tayi rauni, wani irin matsanancin tausayi haɗi da wani abu me kama da bege takeji na mamaye duk zuciyarta, yayinda bugun zuciyarta ke harbawa da wani abu na musamman adangane dashi, wanda hakanne kuma yake daɗa sata kuka, tabbas ita me matsanancin Rauni ce akansa. *M.Jay* shi kaɗaine ke yawo acikin jiki da jininta, shi kaɗaine ke yawo acikin tunaninta, haka zalika kuma shi kaɗaine ke yawo acikin gaba ɗaya Rayuwarta, batasan da me zata ƙira abun da takeji akansa ba, saidai koma meyene tayi imani mai tsananin zafi da suka ne agareta, sake ƙanƙame jikinta tayi waje ɗaya, tare da sanya hannu ta dafe kanta dake masifar sarawa, wanda har hakan yasa jiri me ƙarfi ke ɗibanta, ganin duniyar na juya mata ne yasa ta haurawa saman gadon ta kwanta, blanket taja ta rufe jikinta dake ta faman ɓari, saboda yanda zazzaɓi me zafi ya sauƙar mata lokaci ɗaya.
Duk yanda taso ta tsaida zuciyarta waje ɗaya ta kasa yin hakan, domin kuwa hoton fuskarsa da kuma idanunsa ne ke yawo acikin nata idanun, lokaci ɗaya duk wata nutsuwa tata tasoma ƙaura daga jikinta, batasan me ta aikata ba, wanda har yasa takejin ba daidai azuciyarta ba, ba abun da take fata da buri awannan lokacin kamar bacci, saidai kuma duk yanda taso da yin hakan batajin zata iya.
Haƙiƙa idan zuciyoyi biyu suka kasance manne da juna, kuma akan abu ɗaya lallai ne kuma tilas yanayinsu ya kasance iri ɗaya, ba iya buri da fatan Laylerh Maleek bane ke cikin rauni, har ma da zallan Ƙaddaransu dake neman juya rayuwar su zuwa cikin wata sabuwar shafi mai ɗauke da manyan darussa.

*M.Jay*
Sama da 30 minute kenan daya ɗauka atsaye ruwan shower'n daya kunna na dukan jikinsa, wanda amatsayinsa na cikakken Namiji me motsa jiki haka kuma soldier yasa sam baiji ajikinsa cewa ya gaji da tsayuwan ba, yanayin yanda ruwan ke dukan jiki da kuma kansa kaɗai ya isa bayyana maka cewar lallai ba'a cikin tunaninsa yake ba, domin duk yanda yaso da yayi zeroying mind ɗinsa abun yaci tura, ahankali yakai hannunsa ya kashe shower'n, tare da ɗaukan wata kakkauran bathrobe din dake gefensa ya sanya ajikinsa, ba tare kuma daya tsaya tsane gashin kansa ba ya nufi ƙofar fita daga cikin bathroom ɗin, hannunsa ya ɗaura akan handle ɗin ƙofar ya buɗe, yayinda yakejin ƙirjinsa na amsawa aduk wani taku ɗaya da zaiyi.
A irin yanayin da yake ciki yasa sam bayajin zai iya tsane gashin kansa dake É—igar ruwa, wani dogon trouser kaÉ—ai ya saka batare da ya sanya riga ajikinsa ba, duk da kuwa cewar ana busa sanyi sosai agarin ga kuma sanyin A/C'n daya cika É—akin.

Ƙarasawa gaban windown ɗakin nasa yayi, wanda daganan inda yake yana iya hango compound ɗin gidan. Har yanzu zuciyarsa zafi takeyi masa, yayinda wani irin ɗaci yake daɗa mamaye maƙoshinsa, idanunsa da suke alumshe ya ware, saboda bayajin zai iya jurewa gizon da sukeyi masa, ayanzu baya buƙatar komai domin brain ɗinsa gab take da juyewa, wanda hakanne kuma yayi sanadiyar hautsunewar tunaninsa, yayinda har yanzu maganganunta ke masa yawo acikin kunnensa, kalamar "Na'amince!" da ta faɗa itace mafari acikin sabuwar shafin ƙaddaransu da ta buɗe ayau ɗin. haka kuma yakejin kalmar na neman tarwatsa masa ƙwaƙwalwa da zuciyars, kallonsa ya maida ga wata ƴar ƙaramar drawer dake cikin ɗakin nasa wanda aka rufeta da pin cord, ahankali ya soma takawa har ya ƙarasa gaban ƴar drawer'n.
Tare da ɗan durƙusawa agaban drawer'n. L73M75 shine pin ɗin buɗe drawer'n, wanda anan ciki yake aje duk wani abu me mahimmanci daya shafi sirrinsa, yana gama sa pin ɗin kuwa take drawer'n ta buɗe da kanta, yayinda murfin farko na drawer'n ke ɗauke da wasu manya manyan Diary's guda biyu, sai kuma wani farin abu kaman gari da aka killacesa acikin wani haɗaɗɗen leda. Idanu ya zubawa garin da ajikin ledan aka rubuta Cocaine da manyan baƙi, duk kuwa da cewar yanajin zuciyarsa na bugawa akai akai, amma bashi da wani zaɓi wanda ya wuce hakan. Ledan cocaine ɗin ya ɗauƙo tare da maida drawer ɗin ya kuma sanya pin ɗin ya rufe.
Idanunsa akan ledan dake hannunsa haka ya ƙarasa gaban kujeran dake gefen gadonsa ya zauna, ahankali ya jawo wani ɗan ƙaramin table ya ajiye agabansa, bayajin zai tsaya sauraran shawaran da zuciyarsa ke ƙoƙarin basa, domin brain ɗinsa ta ɗauki cajin da idan ya bata cikakkun 20 minute zata iya samun matsala, zuciyarsa kuwa ko tantama bayayi zata iya bugawa.
Hannayensa na rawa haka ya fasa ledan cocaine din tare da juye garin akan haÉ—aÉ—É—en glass table É—in dake gabansa.
Kamar yanda hannunsa ke rawa haka ma duk jikinsa, cikin zaucewa ya matso da fuskarsa kan table ɗin, tare da yiwa Cocaine ɗin wani irin shaƙa, wanda hakan yasa tatafi har zuwa cikin kansa.
Haka ya ɗauki sama da 13 minute yana shaƙan cocaine ɗin, ahankali ya ɗago da kansa yana me jan wani irin numfashi, tare da ɗan soma jujjuyawa kansa, domin cikin abun da bai wuce 18 minute ba har ya fara samun kansa acikin wata duniya ta daban, duniyar da bakomai acikinta sai gushewar hankali, kafun 10 minute tuni ya fara ganin abubuwa na zame masa bibbiyu, yayinda yake ganin komai adisashe.

*30/November/2020*
1/19/21, 8:11 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting By*
fatymasardauna

*(This book is mainly for those that pay, if you know you did'nt pay please do'nt read it. Here is the account number for people that are willing to pay 0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank. Whatsapp number 07017879464)*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.