Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: LAYLERH MALEEK.txt
Chapter 62 of 65
*Chapter 79*
Horn d’in motarsa ya danna adaidai lokacin daya iso gaban, tankamemen gate din gidannasu.
Cikin abunda bai wuce 4minute ba kuwa maigadi ya wangale masa gate d’in, anutse ya tura hancin motar tasa cikin gidan.
Saidai kuma sanin da yayi cewar bazae jima bane yasashi yin parking motar a tsakiyar compound din gidan, tare da bud’e murfin motar ya fito.
Cikin yanayin nutsuwa ya soma takawa, saidai bai wuce taku biyar yayi ba, ya tsaya tare da juyowa ya sauk’e idanunsa, akan part d’in da Laylerh da kuma Najeeb d’in sukayi rayuwa.
Idanunsa ya d’an lumshe ahankali, tare kuma da d’an cije jajayen labb’ansa, akaron farko kenan da yaji wani abu na rangwame acikin zuciyarsa.
D’auke kansa daga kallon part d’innasu yayi, lokaci d’aya kuma direct ya nufi b’angaren Oum Ayush.
Tsaye take agaban dinning table tana me harhad’a wasu had’add’un food flask acikin babban basket, k’aran knocking d’in falon da taji ne kuma yasa ta d’an dakatawa, tare da d’auko basket d’in ta rik’e ahannunta, dan a tunanin ta Abdoul ne, saboda tace masa yazo ya kaiwa su Laylerh’n kayan breakfast.
K’arasowa jikin k’ofar tayi tare dasa hannu ta bud’e k’ofar.
Idanu hud’u da sukayi da Maleek d’inne yasata dan bud’e baki, cikin kuma yanayin mamakin ganinsa tace.
“Maleek kaine da safe haka ina kabaromin Laylerh’n?�
Idanunsa ya d’an lumshe, batare kuma daya amsa mata tambayar da tayi masa d’inba, ya rab’a ta gefenta ya shige cikin falon.
Ganin hakan da tayi d’inne kuma yasata d’an tab’e baki, tare da maida kofar ta rufe, saboda dama tasan dole idan dai zasu had’u to sai ya nuna mata halinnasa na shariya, wanda kuma idan da sabo ta riga da ta saba da hakan.
“Good morning Oum Ayush.� Ya fad’a adaidai lokacin da ya k’arasa gaban, makeken fridge’n dake cikin falon, batare kuma daya jira amsawarta ba, ya bud’e murfin fridge’n ya d’auko bottle water maisanyi sosai.
Dawowa tsakiyar falon yayi tare da zama akan d’aya daga cikin kujerun falon, ahankali ya b’alle murfin bottle water’n, tare da d’aura goran abakinsa.
Only 8second kawai ya shanye rabin ruwan dake cikin goran, ahankali ya d’an janye kansa, tare da d’ago idanunsa ya kalli Oum Ayush da ta zuba masa ido.
Nuni yayi mata da goran ruwan, tare dayi mata alama akan ko zata sha.
“Bazan shaba, ko ce maka akayi ishin ruwa nakeji, da fari ka fara amsamin tambaya ta tukunna, ina kabaromin Laylerh, kodai barinta kayi awannan babban gidan ita d’aya?�
Ta fad’i hakan tana me harararsa tare da ajiye basket d’in dake rik’e a hannunta, kana ta zauna akan kujerar dake facing d’inshi.
Jin still Oum Ayush ta sake nanata masa tambayar ne kuma, yasashi d’an sake lumshe idanunsa, ahankali cikin kuma yanayin daya sabayin magana yace.
“Bata da lafiya tana bacci.�
“Bata da lafiya kuma Maleek? Meya sameta?�
Oum Ayush d’in ta fad’a ad’an rud’e, Domin abunda ya fara zuwa ranta, shine wannan ciwon marar da Laylerh’n keyi.
Kansa ya d’an sunkuyar kana cikin yanayin sanyin, dake bayyana tausayawarsa agareta yace.
“No bawani babban ciwo bane, fever ne kawai, kuma na saya mata pain relievers a pharmacy.�
Sassanyar ajiyar zuciya Oum Ayush d’in ta sauk’e, asakamakon jin abunda ya fad’a, lokaci d’aya kuma taji wani irin nutsuwa yazo mata, take kuma tunaninta ya bata cewar Lallai wani abu, ya faru atsakanin Laylerh da Maleek d’in, saboda haka kawai tasan cewa Laylerh’n bazata yi zazzab’i ba.
“Allah Yabata lafiya, ga breakfast nan dama ku Abdoul zai kaiwa, amma yanzu tunda kazo saika tafi dashi.� Tafad’i hakan cikin kulawa, sannan ga kuma wani sahirtaccen murmushi da ya bayyana akan fuskarta.
D’ago kai Maleek d’in yayi ya kalleta, tsawon minti d’aya kaman kuma zaice wani abu amma saiya fasa.
Mik’ewa tsaye yayi, tare da k’arasowa inda Oum Ayush d’in ke zaune.
Zama yayi agefenta tare kuma da juyowa ya fuskanceta, cikin yanayin daya tabbatar cewa zata fahimcesa yace.
“Me yasa Najeeb ya saki Laylerh?�
Oum Ayush kuwa saurin d’agowa tayi ta kalleshi, saboda jin tambayar nasa da tayi abazata.
Ganin kuma da tayi cewar shid’inma kallonta yakeyi ne ya sata d’auke kanta, tare da sauk’e ajiyar zuciya, kana asanyaye tace.
“Meyasa ka tambayeni hakan?�
“Saboda inason sani.� Ya bata amsa atak’aice, had’e da janye idanunsa gefe.
D’an Jim Oum Ayush d’in tayi acikin ranta tana me mamakin dalilin da yasa, Maleek d’in yayi mata wannan tambayar, saidai tasani koma meyene ayanzu bai kamata tak’i Gaya masa ba, saboda ta fahimci cewa ayanzu, shida Laylerh’n sun riga da sun zama abu d’aya, wanda kuma dama hakan shine burinsu gabaki d’aya.
D’an gyara zamanta tayi, tare kuma da juyowa ta fuskanci Maleek din.
Asanyaye tace.
“Saboda ya baku dama kuyi rayuwa tare, Domin ya fahimci hakan shi ne samun saukin zuciyoyinku, zuciyoyin da kullum suke awahale, Tabbas Najeeb bai saki Laylerh dan baya sonta ba Maleek, ya saketa ne kawai don samun sauk’in zuciyar da take gab da tarwatsewa, kaima kasani Maleek abune da yake abayyane, wanda kuma kowa ya fahimta, Domin ko zaka iya b’oye abundake cikin zuciyarka, bazaka tab’a iya b’oye wanda ke rubuce akan fuska da kuma cikin idanunka ba, Najeeb ya saki Laylerh ne saboda ya gano cewar kuna yiwa junanku tsananin so kai da ita, sannan mafarki dama duk wani burin dake cikin zuciyoyinku ahad’e suke, Lallaine kuma Allah ya tsara cewar dole duka ku biyun zakuyi zaman aure da ita, da farko Allah ya tsara mata zama da Najeeb, saidai bai k’addara zaman nasu zaiyi tsawo ba, ayanzu kuma gashi tana zaune ak’arkashin inuwarka, shin tayaya kake tunanin zai iya jure zama da Laylerh’n, da akullum sunanka ne cike acikin bakinta? Koda acikin bacci sunanka take k’ira masa, duk wani ciwonka kuwa acikin jiki da zuciyarta takeji, koda sau d’aya fa Maleek Laylerh bata tab’a bashi kulawar aure ba, kuma duk asaboda kai, safe, rana, dare duk bata da wani aiki sai tunaninka, ta ya ya zai jurewa hakan?
Tabbas akullum bamu iya sauya k’addarar mu Maleek, komai da Allah ya tsara mana, mai kyau ko marar kyau, bamu iya sanjawa ko guje masa, koda yaushe acikin k’addara da kuma jarrabawar Ubangiji muke rayuwa, saboda haka komai da ya faru rubutaccen al’amari ne, dan haka mu rungumeshi ayadda yazo mana, matuk’ar akwai Allah Kuma to kasani akwai zab’in alkhairi.�
Idanunsa dake alumshe ya bud’e tare da sakin wani irin ajiyar zuciya.
Tabbas kalaman Oum Ayush d’in sun shigesa, saidai kuma abun da zuciyarsa ke kokonto akai shine, dalilin dayasa Najeeb ya saki Laylerh batare da ya tab’a kusantarta ba.
Ahankali ya kifa tafukan hannayensa akan fuskarsa, tare da fesar da wani sassanyan numfashi, akaron farko kenan da ya fara jin wani abu na rangwame na ratsa zuciyarsa adangane da Najeeb d’in, saboda ada wani mummunan kallo yakeyi masa, Kallon wanda ya rabasa da duk wani Fata da Muradinsa, Kallon wani na daban, wanda yayiwa rayuwarsa kutse.
Jajayen idanunsa ya d’an ware, tare da mik’ewa tsaye ya zura duka hannayensa acikin aljihun wandon dake jikinsa.
Ahankali ya d’an soma zagaye tsakiyar falon, tamkar wanda ke son nazartar wani abu.
Ganin hakanne kuma yasa Oum Ayush ta zuba masa idanu, tare da shirin sauraran duk wani abu dazai fito daga bakinsa.
Almost 6 minute kuwa acikinsu babu wanda ya sake cewa komai.
Saima sunkuyawa da yayi ahankali ya d’auki basket d’in da Oum Ayush d’in ta ajiye atsakiyar falon, batare kuma daya sake kallonta ba yace.
“Zan tafi, but please idan kinsamu time kizo ki duba Laylerh.�
Kai ta jinjina masa alaman “To.�
Juyawa yayi cikin nutsuwa kuma ya nufi hanyar fita daga cikin falon.
Da kallo Oum Ayush ta bisa, ganin da tayi yakai bakin kofar fitane kuma yasa ahankali tace.
“Please Maleek kakula da Laylerh sosai, duk da nasan cewar tana da mahimmaci sosai agareka, amma kada ka matsa mata domin kasancewar itad’in har yanzu yarinyace, zaku ma ta taso ne akan duk wani abu daka d’aurata.�
Kansa ya jinjinawa Oum Ayush d’in, tare dayi mata alama akan cewar yaji duk abunda tace.
Hannunsa dake kan handle d’in kofar ya murd’a, take kuwa k’ofar falon ta bud’e ya fice.
Sassanyar ajiyar zuciya Oum Ayush ta sauk’e, tare da sakin murmushin jin dad’i, Lallai tayarda cewa akan komai Allah Ne ke ikonsa yanda yaso, domin duk da rashin sakewa irin ta Maleek d’in, hakan bai hanata hango zallan nutsuwa da kuma farinciki acikin k’wayoyin idanunsa ba.
Daga wani sashi na zuciyarta kuwa, tausayin Laylerh ne yayi mata tsaye, saboda batasan wani irin aika aikane Maleek d’in yayi mata ba, duk da tana da yak’ini akan cewar Maleek bazae tab’a cutar da Laylerh’n ba, amma tasan dole baza’a rasa wani d’an wahala da Laylerh’n tasha ba, saidai koma meye tayi alk’awari cewa da yamma zataje ta duba Laylerh’n.
Ab’angaren Maleek kuwa yana fitowa daga sashin Oum Ayush d’in, kaitsaye wajen motarsa ya nufa, bud’e bayan motar yayi ya saka babban basket d’in abincin dake hannunsa.
Yana gama rufe motar kuwa Abbou Jaheed da kuma Abbou Khareem suka shigo cikin gidan.
Ganin Maleek d’in da sukayine kuma yasasu fad’ad’a murmushi da kuma fari’ar dake kan fuskarsu.
Maleek kuwa Kamar yanda yasaba gaishe da mahaifin nasa, haka yayi yau ma, d’an durk’usawa yayi ya gaishe dasu dukansu.
Saidai gaba d’aya ya kashesu da mamakin ganin murmushi da sukayi kwance akan fuskarsa.
Wani irin sanyi Abbou Jaheed yaji acikin zuciyarsa, tare kuma da samun gamsasshiyar nutsuwa, Tabbas akaron farko yaji ajikinsa cewa, yayi abunda ya dace, sannan ya samawa y’ay’ayen nasa nutsuwa da kuma farinciki na har abada.
Haske da kuma annurin daya gani kwance akan fuskar Maleek, ya tabbatar masa da cewar zuciyar Maleek ta samu gamsuwa da kuma abunda takeso.
Hakika ya sake tabbatarwa kansa cewar, zuciyar Maleek dana Laylerh’n ahad’e suke, sannan kuma farincikin kowannensu shine rayuwa tare da d’an uwansa.
Sannan ada bawai ya nesanta Maleek da Laylerh’n saboda wani abu na daban bane, ya nesanta sune kawai saboda gujewa halin rayuwa da kuma biyewa zuciya.
Saboda abune daya jima da sani cewar, akwai soyayya mai k’arfi atsakanin Maleek da Laylerh’n, wanda kuma k’arfi da tasirin soyayyar kan iya haifar da faruwar komai atsakaninsu, Domin abune da ke abayyane, matuk’ar k’arfi da tasirin soyayya tayi yawa, takan iya makantar da idanun masu yinsa, har ya Kaisu ga kasa iya jurewa lokaci, ahaka ne kuma za’a samu makancewar zuci, ta yanda zasu mallakawa juna gangar jikinsu, batare kuma da tunanin girman zunubin da suka aikata ba, haka koda yaushe zasu kasance tamkar abu d’aya.
Wannan abun Abbou Jaheed yake matuk’ar gujewa, akullum shiyasa ada yake nesanta LaylerhMaleek d’in.
Abbou Khareem da bakinsa ya kasa rufuwa saboda farinciki ne kuma ya kalli Maleek d’in, tare da cewa.
“Maleek kaine haka da safe, to ina kabaromin y’artawa kuma?�
Jajayen labb’ansa yad’an cije, tare da Kallon Abbou Khareem d’in, cikin yanayin dake bayyana, gajiyarsa da tambayar Abbou Khareem d’in yace.
“Oum Ayush ma abunda ta tambaya kenan.�
Murmushi dukansu sukayi, saboda dama sunsan halinsa bai cika yawan son tambaya ba.
Kafad’ansa Abbou Jaheed yad’an bubbuga, cikin son dad’a basa k’arfin guiwa yace.
“Kayi maza ka koma gida, Allah Ubangiji ya baku zaman lafiya mai d’orewa, Insha Allah Muma zamu zo gidan naku mu duba ku.�
Idanunsa yad’an lumshe, tare kuma da jinjina kansa, hannun Abboun nasa ya kamo ahankali ya rik’e acikin nasa.
Cikin wata irin muryar dake bayyana rauni da kuma sanyin zuciyarsa yace.
“Thank you so much Abbou Jaheed!!�
Ya k’are maganar murya atausashe tare kuma da d’an karyar da wuyansa gefe.
Murmushin tsananin farinciki Abbou Jaheed d’in yayi, lokaci d’aya kuma yaji hawaye sun cika idanunsa, wanda suke bayyana tsananin tausayin Maleek d’in da yakeji.
Ahankali ya jinjinawa Maleek d’in kai, tare dayi masa alama da idanu akan ya tafi gida.
Hannunsa dake rik’e dana Abbou’n ya janye, tare kuma da bud’e murfin motarsa ya shiga.
Bayan yayiwa motar tasa key ne kuma ya soma yin reverse, ganin hakanne kuma yasa mai gadi ya wangale masa gate d’in gidan ya fice.
Da kallo su Abbou Jaheed sukabi motar tasa, kowannensu jin zuciyarsa yake tas, babu wani alama ko sauran damuwa.
Domin yau sunga farinciki, da kuma nutsuwar da suke so da fatan gani akan fuskar Maleek tsawon shekaru.
Kowannensu haka ya nufi sashinsa fuska d’auke da murmushi.
Saidai kuma ak’asan zuciyar Abbou Jaheed damuwa ce, damuwa mai d’auke da Rauni, da kuma tsananin tausayin Maleek da Laylerh, wanda suka amincewa rayuwa ayadda tazo musu, suka kuma yi imani da k’addararsu.
Tabbas ba’a tabbata acikin k’unci, Lallai watarana kowani mai damuwa damuwarsa zata yaye, farinciki zaizo koda kuwa acikin farincikin akwai nak’asu, hakan bazai tab’a hana zuciyar da ta wahala samun nutsuwa ba.
Maleek
Ahankali yake driving d’in motar tasa, Yayinda daga gidan nasu, kaitsaye juya akalar motar tasa yayi zuwa shoprite.
Kasancewar kuma daga inda yake zuwa shoprite din babu wani tafiya sosai ne, yasa cikin mintuna kadan ya iso.
Bayan ya gama daidaita Parking din motar tasa ne kuma, ya fito kaitsaye ya nufi cikin shoprite d’in.
Saidai kuma koda ya shiga baiwani jima ba ya fito, saboda mafiyawancin abunda ya saya chocolates ne, shiyasa bai wani b’ata lokaci ba.
Alokacin daya iso gaban tsararren gidannasa kuwa, horn d’aya kawai yayi maigadi ya bud’e masa gate.
Bayan kuma ya gama daidaita parking d’in motar nasa ne, ya bud’e ya fito, tare da d’aukan babban ledan da yayi sayayya aciki, da kuma basket d’in abincin da Oum Ayush ta bashi.
Ahankali ya tura k’ofar falon ya shiga, still kuma falon k’asan Yana nan kamar yanda ya barshi.
Sama ya haura direct, a zuciyarsa yana mai fata da kuma addu’ar Allah Yasa Laylerh’n bata tashi daga bacci ba.
Basket da kuma ledan dake hannunsa ya ajiye acikin falon, tare kuma da nufan bedroom d’innasu kai tsaye.
Ahankali ya murd’a handle d’in k’ofar ya shiga.
Sauk’e idanunsa da yayi akan gadonne kuma, yasa k’irjinsa wani irin bugawa...
*(I’m sorry nayi azumi shiyasa na makara wajen typing, insha Allah amma gobe zan baku update)*
*9:26 pm*
4/10/21, 7:32 AM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*
*Note editing*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.