Best Hausa Novels

Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: LAYLERH MALEEK.txt

Chapter 7 of 65

*Chapter 14*

Lumshe idanunsa yayi tare da shaƙan wani dogon numfashi, ahankali yakejin mood ɗinsa na sanjawa, yayinda mayen cocaine ɗin ke ƙara ratsa cikin brain ɗinsa, sake maida kansa ƙasa yayi tare da ci gaba da shaƙan cocaine ɗin son ransa, wanda hakan yasa zuga ɗaya kwata kwata yayi mata ta ƙare, ɗan ɗgowa yayi tare da jingina bayansa da jikin kujeran da yake kai, ahankali yakejin kansa na juyawa, yayinda yakejin ita kanta duniyar nayi masa wata iri, kasancewar ya shaƙi cocaine ɗin sosai ne yasa take tasoma yi masa aiki, domin kuwa cocaine din nada ƙarfi sosai, sannu sannu hankalinsa ke ƙoƙarin gushewa.
Ganin yana shirin manta duniyar da yake ne ya sashi miƙewa tsaye daga zaunen da yake, wani irin hajijiyan daya ɗaukesa ne ya sashi saurin dafe bango, tare da soma ɗan girgiza kansa, dan ko gani sosai bayayi, adaddafe haka ya ƙarasa jikin makeken gadonsa wanda yaji farin bedsheet na alfarma, faɗawa saman gadon yayi, batare kuma daya kula ba dan ya fara fita hayyacinsa ya kwanta akan ciwon nasa, take kuwa ciwon ya fame, wanda hakan kuma yasa jini ya ɗan soma fita daga jikinsa.
Kasancewar baya cikin hayyacinsa yasa bai wani ji zafin fame ciwon nasa sosai ba.
Idanunsa dake abude ya mayar ya rufe, saboda yanda yaga gaba ɗaya duniyar na juya mai, ahankali yaji nauyin da zuciyarsa tayi yana raguwa, yayinda mind ɗinsa ke ƙoƙarin yin zeroying, take duniyar ta soma ƙoƙarin zame masa sabuwa wanda babu ɗigon damuwa acikinta, duk da kasancewar shi ba ma'abocin shaye shayen ƙwayoyi da kuma alcoholic bane, amma time to time yakan shan cocaine dan tana rage masa damuwar dake ransa, musamman ma idan kansa ya ɗau tension, duk da kuwa yasan hakan ba abu bane me kyau, saidai kuma watarana yakan kasa controlling kansa akan shan cocaine ɗin. Ahankali samun nutsuwa da kuma sanyin zuciyar da ya samu yasa shi, faɗawa cikin wani baƙon yanayi, yayinda yakejin wani irin hot feeling na ratsa duk jikinsa, cikin yanayin fitar hayyacin daya samu kansa aciki ne, ya sashi soma ganin kyakkyawar fuskarta nayi masa gizo, wanda sanadin hakanne kuma ke ƙara hura masa wutar zallan feeling din da yakeji, har takai ga kowacce gashi dake jikinsa mimmiƙewa,, yawancin lokuta baisan meyasa yake yawan jin hot feelings akan ta ba, yanayin da yake ji akanta me ƙarfi ne sosai, sometimes yakanji kamar bazai iya controlling kansa ba, wanda izuwa yanzu kuwa har hakan ya riga daya zame masa sabo, dan ayanzu feeling ɗinta ya zama kamar jini ne da yake gudana acikin jikinsa.
pillow'n dake gefensa ya ɗauka tare da yin hugging pillow'n nasa tight, sannu ahankali zuciyarsa ke saƙa masa abubuwa da yawa, yayinda kuma gaba ɗaya tunanin nasa ba acikin hankalinsa yakeyinsu ba, idanunsa dake a lumshe ya buɗe, tare da jawo wayarsa da ke aje saman wani ɗan madaidaicin stool ɗin dake gefen gadon.
Kunna wayar tasa yayi tare da ƙurawa hoton dake mamaye kan saman screen ɗin wayar idanu, ɗan ƙaramin bakin yarinyar da hoton ta ke jikin screen ɗin wayar ya ƙurawa idanu, sama da 14 minute ya ɗauka yana kallon hoton kyakkyawar yarinyar, kafun daga bisani ya ɗan lumshe idanunsa dake ɗauke da zallan maye, da kuma yanayin bacci, cikin wata irin kasalalliyar muryar sa dake ɗauke da wani irin amo yace.
"No one like you AYSH! I love your smile, your voice and your eyes, I love your ......" shiru yayi tare da kasa ƙarasa maganar dake cikin rai da kuma zuciyarsa, ɗaura wayar tasa yayi akan ƙirjinsa, tare da ƙurawa zanen pop'n dake cikin ɗakin idanu, yanayin yanda mood ɗinsa ya sanja lokaci ɗaya ne yasa ƙarara zaka iya fahimtar cewa, akwai wani abu dake kwance acikin zuciyarsa, wanda yake jin tsoron furtawa, tabbas yayarda cewa akwai wani abu dake sukan zuciyarsa, wanda kuma asannu hakan ke neman haukata tunani da nutsuwarsa, jin tunani na neman fasa masa ƙwaƙwalwarsa ne, ya sashi ɗan soma jujjuya kansa, baiwani ɗau lokaci ahaka ba kuwa, bacci ɓarawo ya ɗaukesa.

Laylerh.

Juyi kawae take tayi akan ɗan madaidaicin gadonta, duk kuwa ga yanda taso bacci ya ɗauketa hakan ya ci tura, domin kuwa da zaran ta lumshe idanunta, hoton fuskar Maleek ne keyi mata gizo, wanda hakan ke ƙara narkar mata da zuciya, yayinda wani irin sassanyar ƙauna haɗi da shauƙinsa ke mamaye gaba ɗaya illahirin jikinta, lallai ta yarda da cewar akwai wani abu adangane dashi, dake shumfuɗe acikin zuciyarta, wanda take da fata da kuma burin sanin ko menene shi, sake gyara kwanciyarta tayi tare da yin hugging ɗin pillow'n da take kai.duk yanda kuwa taso ta saki zuciyarta hakan ya faskara, kasancewar damuwa da kuma fargaba sun riga da sunyi tasiri acikin tunaninta, dalilin haka kuwa yasa taji komai na duniyar baya yi mata dadi, lumshe idanunta da suka ɗan kumbura tayi tare da sakin ajiyar zuciya me ƙarfi, ƙoƙarin tsaida duk wani tunani dake cikin ƙwaƙwalwarta tayi, duk da cewar yin hakan abune me wuya, amma dole ne tayi hakan matuƙar tanaso ta rumtsa. har yanzu ita yarinyace, dalilin haka yasa brain ɗinta bazata iya ɗaukar wata damuwa me nauyi ba.
Haka ta dinga juyi akan gadon, dicikin sa'a kuwa ko 15 minute bata É—auka ba bacci me nauyi ya É—auketa.

Washe gari.

7:00 am daidai ta farka daga nannauyan baccin daya É—auketa daren jiya, Kasancewar kuma bata samu baccin da wuri ba, shiyasa ta É—an makara yau É—in.
Ahankali ta buɗe idanunta wanda suka yi luhu luhu saboda kukan da tasha jiya, duk da cewar bata wani jin kuzari me ƙarfi ajikinta amma ahaka ta daure ta nufi toilet, koda ta ƙarasa toilet ɗin kayan jikinta ta rage tare da haɗa ruwan ɗumi tayi wanka, tana gama wankan kuwa ta zura wata ƴar baby pink bathrobe ajikinta tare dayin brush kana kuma ta ɗauro alwala, ganin tagama gudanar da abun da zatayi acikin toilet ɗinne, yasa batare da ta jira komae ba ta fice daga cikin bathroom ɗin.
Cikin yanayin hanzari da kuma gudun kada ta makara zuwa makaranta, ta shumfuɗa sallaya tare da tada sallah'n asuba, duk da cewar ma tasan ta makara, koda ta idar da sallan kuwa bata tsaya yin wani ƙyale ƙyale ba, versiline kawai ta shafa ajikinta sai kuma wata haɗɗɗiyar powder silk da ta shafa akan fuskarta, sai kuma peach colour lip stick da ta shafa sama sama akan laɓɓanta, wanda hakan ya ƙara fitar da asalin kalan shape da kuma kyawun bakinta. Ƙarasawa gaban drawer'nta tayi aɗan hanzarce ta ciro kayan uniform ɗin ta, ɗan madaidaicin sket na uniform din ta fara sawa, kafun ta saka rigar uniform ɗin, ko da yaushe uniform ɗin nata ƙara yi mata kyau suke, yayinda komai nata ke sake bayyana gwanin ban sha'awa, dan sosai uniform ɗin nata ke bayyana zallan ƙuruciyarta, saboda zamowarta me kyaun jiki dana sura ne, yasa ko cikin shigar uniform ɗin shape ɗinta kasa ɓoye kansa yake, wanda kuma hakanne kejan hankalin maza dayawa zuwa gareta.
Ahanzarce ta saka white socks aƙafanta tare da goya ƙatuwar school bag ɗinta akan shoulder nta, duk da cewar simple meckup tayi, amma hakan bai hana cute face ɗinta bayyana ba, musamman ma shining lips ɗinta da yasha oil lipstick, mathematical text book ɗinta ta ɗauka cikin ɗan hanzari ta nufi hanyar fita daga ɗakin, kasancewar 20 minute kaɗai ya rage mata.

Acan Falo kuwa Abbou Jaheed ne zaune kan ɗaya daga cikin haɗaɗɗun kujerun falon, hannunsa riƙe da jaridan Daily Trust.
Gefensa kaÉ—an kuwa Momy ce ke tsugune tana haÉ—a masa black coffee, sanin cewar bata da wata dama na sanya kokwanto acikin zuciyar Abbou'n sama da wannan lokacin ne yasa, ta É—an É—ago da kanta ta kallesa, cikin son nusar da manufarta da kuma sauya salon magana tace. "Alhajina inason magana dakai."

Jin abun da ta faÉ—a ne yasa Abbou Jaheed É—agowa ya dubeta, cikin kulawa yace.
"Inajinki."
Ganin daman da take buri da fatan samu na shirin samuwa alokaci ɗaya ne yasata gyara zama, tare da duban Abbou Jaheed ɗin, cikin ƙasa da murya tace.
"Akan maganan auren Laylerh da Najeeb ne, duk da nasan cewa bani ce na haifeta ba, amma sai nake ganin yana da kyau nasan duk wani plan da kake shiryawa akanta, saboda kamar ƴa haka na ɗauke ta, sannan kuma ina ganin kamar babu dacewa acikin haɗin auren Laylerh da kuma Najeeb da kake ƙoƙarin yi, baka tunanin cewa ko akwai wani wanda Laylerh keso ba Najeeb ba daya kasance zaɓinka."
Da katawa da karatun jaridan Abbou Jaheed yayi, tare da zubawa Momy idanu, mamaki da kuma shayin kalamanta ne suka shiga yi masa yawo acikin ƙwaƙwalwarsa, lokaci ɗaya yaji yanaso ya fahimci wani abu daga cikin kalaman ta, hakanne kuwa ya sashi ɗan gyara zama tare da numfasawa, cikin yanayin sa na dattako yace. "Bana tunanin na aikata ba daidai ba akan maganar auren Laylerh da Najeeb, kuma har abada banajin zanyi dana sanin haɗa wannan auratayyan danayi, kuma alƙawari ne na ɗaukawa kaina cewar matuƙar ina darai da numfashi Laylerh bata da wani miji sai Najeeb."

ÆŠan numfasawa yayi tare da gyara zamansa.
Daidai lokacin ne kuma Laylerh ta ƙaraso cikin falon, wanda shigowarta cikin falon ne yasa Abbou Jaheed dakatawa daga abun da yakeson faɗa, tare da zuba mata idanu, har ta ƙaraso inda yake, ɗan durƙusawa tayi, cikin yanayin girmamawa tace. "Barka da sapia Abbou." Murmushi Abbou Jaheed ɗin yayi mata tare da jinjina mata kai, cikin kulawa yace. "Yauwa Laylerh barka, fatan kin tashi lapia?."
Murmushin daya bayyana kyawawan fararen haƙoranta tayi, cikin sanyi tace. "Lapia ƙalau."
Murmushi Abbou Jaheed ɗin ma yayi, saboda ganin murmushin ta da yayi a yanzu yasa shi jin wani irin ƙwarin guiwa, wanda acikin ƴan sakannin da suka wuce yanzun ya soma ƙoƙarin rasa su, saidai ganin yanda fuskarta ke asake ya sashi jin dadi acikin zuciyarsa, tare da sake tabbatar wa aransa cewa Laylerh bata da wani miji sai Najeeb.

Laylerh kuwa maida kallonta wajen da Momy ke zaune tayi, cikin sanyin da ya zame mata sabo tace.
"Good morning Momy!."
ɗan ɓata fuska Momy'n tayi, cikin rashin kulawa tace.
"Morning!."
Bata damu da yanda momyn ta amsa mata gaisuwan nata ba, because idan da sabo ta saba da irin halayyan Momyn.
miƙewa tsaye tayi tare da ɗan gyara zaman jakar dake rataye akan kafaɗanta, kallonta Abbou Jaheed yayi tare da ƙiran sunanta. Wanda hakan yasata ɗan juyowa ta kalleshi, tare da cewa "Na'am Abbou." jaridar sa dake aje agefe ya ɗauka, cikin kulawa yace.
"Je ki ƙiramin Yayanki Maleek!." Ambatan sunan Maleek ɗin da yayi ne yasanya taji ƙirjinta ya buga, yayinda hakanan taji zuciyarta ta tsinke, ɗan lumshe idanunta tayi tare da haɗiyan wani wahalallen yawu da lokaci ɗaya ya tsaya mata amaƙoshi.
Jakar makarantar nata ta ajiye anan kan kujera, cikin takunta na nutsuwa ta nufi sashin M.Jay É—in.
Ahankali ta ɗan murda handle ɗin ƙofar da zai sada ta da babban falonsa, cikin sa'a kuwa tana tura ƙofar ciki ta buɗe, wanda hakan ke nuna cewa dama bai rufe ƙofar da kyau ba.
Ƙamshi da kuma daddaɗan sanyin A/C ne suka daki hancinta, wanda hakan yasa ta shaƙi wani dogon numfashi me dadi, yayinda ta ɗaura ƙafanta akan lallausan carpet ɗin dake malale nan bakin ƙofar, aje ƙafarta akan carpet ɗin yasa take ƴan yatsun ƙafarta suka soma nutsewa acikin carpet ɗin, idanunta da ta lumshe taɗan ware tare da soma bin ko'ina dake cikin falon da kallo, komai akimtse yake yayinda sassanyan ƙamshi ke tashi, wanda sanadin hakan yasa duk wanda ya samu kansa acikin falon bazai so ya fita ba. Ganin babu alamarsa acikin falon ne yasa ta ɗan sauƙe ajiyar zuciya, karo na biyu kenan da ta shigo cikin ɗakin tun dawowarsa, soma takawa tayi ahankali ta ƙaraso cikin falon, idanunta ta tsayar akan ƙofar bedroom ɗinsa, hakanan take ɗanjin zuciyarta na tsananta bugawa, yayinda wani abu me kama da tsoro yake ƙoƙarin mamaye duk wani kuzarinta. Cikin dauriya haka ta ƙarasa jikin ƙofar, ahankali takai hannunta ta ɗanyi knocking ƙofar, shirun da taji ne ya sata sake yin knocking door ɗin, still nan ma bataji alaman za'a buɗe ƙofar ba, rumtse idanunta tayi tare da ɗaura hannunta akan handle ɗin ƙofar, duk da kuwa yanda zuciyarta ke bugawa amma bata da wani zaɓi wanda ya wuce shigarta cikin ɗakin. Tura ƙofar tayi tare da ɗan kutsa kanta ciki, again wani fitinannen ƙamshi ne ya kawowa hancinta ziyara, ƙamshin da tafi so, yafi kuma kowanne ƙamshi yi mata daɗi adunia, wannan ƙamshin nasa na dabanne, domin shaƙansa kaɗai acikin hancinta yana sama mata nutsuwa.
Hangosa da tayi akan gado ne yasa ta maida ƙofar ahankali ta rufe, kyawawan idanunta ta ƙura masa, musamman ganin irin kwanciyan da yayi, gaba ɗaya ƙafafunsa aƙasa suke, kuma da dukkan alama bacci yake da gasken gaske, irin kuma baccin nan da ke nuna mutum baya cikin nutsuwarsa.
Ƙarasawa jikin gadon nasa tayi, tare da sauƙe idanunta akan naked skin ɗin bayansa wanda yaji zanen tattoo, haka nan taji wani iri ajikinta, lokaci ɗaya kuma taji zuciyarta ta karye, ƙasa tayi da idanunta tare da kama ƴan yatsun hannunta ta shiga murzawa, take kuwa ƙwalla ya cika idanunta. wani dogon numfashi taja tare da soma ƙoƙarin shanye hawayen ta, cikin sassanyar muryarta dake cracked taƙira sunansa.
Jin shiru bai amsa mata bane yasa ta ɗan ɗago kanta ta kalleshi, still har yanzu yana nan ayanda yake ko motsawa baiyi ba. *"Ya M.jay"* ta ƙara ƙiran sunansa ashagwaɓe tare da ɗan taɓa ƙafarsa, har yanzu baiyi motsi ba, balle tasa ran zai buɗe idanunsa, hannunta dake rawa tasa ta ɗanja yatsar ƙafarsa, ɗagowan da zatayi ne kuwa idanunta suka sauƙa akan white bedsheet ɗin daya ke kai wanda ke ɗauke da jini, daidai inda ya kwantar da cikinsa, amatuƙar ruɗe ta zaro idanunta waje lokaci ɗaya jikinta ya soma ɓari, sam tama manta da me yakawo ta ɗakin, cikin sauri ta haye saman gadon tare da ƙarasawa ta tallafo kansa, gaba ɗaya ƙarfinta ta tarrara ta shiga ƙoƙarin juyasa ta yanda zataga daga ina jinin ke fitowa ajikinsa, wani abun mamaki kuwa ko motsawa baiyi ba duk kuwa ga yanda ta saka gaba ɗaya ƙarfinta wajen juyasa, wani irin nauyi yake dashi wanda hakan yasa ƙarfinta bazai taɓa iya matsar dashi daga inda yake ba, ganin ta kasa matsar dashi gefe ne yasa taja wani irin dogon numfashi, tare da sakin wani wahalallen nishi, zama tayi akan gadon tare da tanƙwashe ƙafafunta, ahankali ta ɗago kansa ta ɗaura akan cinyarta, wanda hakanne ya bawa kyakkyawar fuskarsa daman bayyana, idanunta da suka ciko da ƙwalla ta sauƙe akansa, tare da ɗaukan hannunta dake ta faman ɓari ta ɗaura adaidai kan kumatunsa, cikin muryar kuka tace. "Please Ya M.Jay ka buɗe idanunka kaji! Katashi please!!..."

Daidai lokacin kuwa aka turo ƙofar ɗakin aka shigo.

*fatymasardauna*
1/19/21, 8:11 PM - Ummi Tandama: *LAYLERH MALEEK*

*Writting by*
fatymasardauna

*(This book is mainly for those that pay, if you know you did'nt pay please don't read it. Here is the account number for people that are willing to pay-0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank. Whatsapp number 07017879464)*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.