Best Hausa Novels

Layleeh Maleek Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: LAYLERH MALEEK.txt

Chapter 1 of 65

‡

*Bismillahirrahamanirraheem*
*LAYLERH MALEEK*
*Written By*
Phatymasardauna

*Dedicated To My Blood Brother, My Happiness, My Sweetheart, nd My Heartbeat (AUWAL) I love you so so much my big bro, wish you quick recovery darling👏🏻.*

               *FOLLOW ME ON*
                           *Wattpad*
                      @fatymasardauna
#Firstlove.

*Friday 31/October/2020*

      *(📿Happy Jumma'at Mubarak To All Muslims Ummah, May Allah Bless You And Your Family.🕋)*

*CHAPTER ONE*

*(SOYAYYA wata irin ƙaddarace, da take ɗaure akan wuyan kowa, sannan kuma wata abace da ba'a iya ganin launinta da ido, hakanne ma yasa  ba'a iya sauyata, saidai idan taso takan tashi daga sunanta na SO ta koma ƘIYAYYA. Acikin  kowani rayuwar ɗan Adam akwai salon ƙaddarori masu tarin yawa, akowacce duniya akuma koda yaushe ƙaddara tana tafiya ne daidai da  rayuwa, haka kuma tana rayuwa da mu cikin  farinciki ko akasin haka, abu ɗayane yake tafiya acikin zuƙatanmu, shine MURADI, FATA, da kuma son samun ABUNDA ZUCIYA KESO. Sannan  kuma babu wani bawa wanda ke iya gujewa ƙaddaransa, Lallai ƙaddararmu tana gudana ajikinmu kamar jini, akowace rana abubuwa mabanbanta suna faruwa, to haka itama ƙaddara takan iya sauyawa ako da yaushe, wannan rayuwar daban take da saura, komai yana cikin zuciya da tunanin LAYLERH MALEEK.)*
  ***       *** ***
Cikin sauri take ƙoƙarin sanya uniform ɗin makarantar ta, sosai take sauri dan  tasan idan ta tsaya wasa zatayi latti, wanda zuwa yanzu  batasan da wani baki zata fara faɗan  excuse ɗinta ba, ga masu gadin makarantar, domin tasan zuwa yanzu suma sungaji da karɓan excuse ɗinta.
Ɗan madaidaicin sket ɗin makarantar nata tasanya, wanda yake da ɗan tattara ajikinsa,  wanda idan kasanya sa, zaka jawosa har saman cikinka, dan iyan high waist ɗinnan ne, bayan ta saka sket ɗinne.
Cikin sauri sauri ta zura wata farar rigan long sleeve ajikinta, ahanzarce ta tura rigar acikin sket ɗin, take ta zuge zip ɗin sket ɗin,  hakan da tayi ne kuma yasa ba'a ganin ƙasan rigar makarantar nata.
Sauri sauri ta maƙala aninayen dake jere agaban rigar,  farin safa ta sanya aƙafafunta, tare da ɗaukan  wani toms ɗinta me kalan baƙi ta sanya.
Dayake sket ɗin makarantar tata da kaɗan ya wuce guiwanta, hakan yasa safan da tasa aƙafanta yaɗan taimaka wajen suturta fatar ƙafanta.

Kyawawan fararen idanunta  ta ɗago, tare da  sauƙesu  akan agogon bangon dake saƙale jikin bangon ɗakin.  
8:15 am daidai ta gani, jitayi ƙirjinta yayi wani irin bugu, take taji zuciyarta ta karye, shikenan yau ma ta sakeyin latti kamar sauran ranakun,  by 8:00 am daidai ake kulle gate ɗin makarantar tasu,  da zaran an kulle kuwa babu me shiga, idan kazo late saidai ka koma gida,  duk da tasan cewar tana samun alfarmar shiga makarantar daga wajen masu gadi koda an kulle, saidai yau bata tunanin cewa zasu dubeta ma bare har su karɓi roƙonta.

Cikin azama ta zura  ɗan madaidaicin hijabin makarantar ajikinta, wanda duka tsayinsa baiwuce guiwan hannunta ba,  kallon kanta tayi amadubi, tare da kafe madubin da ido, kyakkyawar fuskarta take kallo ta cikin madubin, sannu ahankali idanunta suka ciko da hawaye, lumshe idanun nata tayi, wanda hakan ya bawa hawayen dake ciki daman gangarowa.
Da sauri ta share hawayen, ta  ɗauki ƙatuwar hand bag dinta ta goya. 
Text book ɗin ta da tayi assigment acikinsa jiya, wanda ta ɗaurasa bisa kan mirror ta ɗauka,  da sauri tafice daga cikin ɗakin.

Koda ta bude ƙofar ɗakin nata ta fito, nan cikin babban falon gidan, da kai tsaye za'a ƙirasa da aljannar duniya ta samu kanta, falo ne tankameme wanda tsarinsa da haɗuwarsa ya zarce misali, kallo ɗaya zakayiwa falon ka tabbatar da cewar mamallakansa ba ƙananan masu arziki bane,  saboda wasu irin haɗaɗɗun royal cushions masu uban kyau da tsada da aka ƙawata cikin falon dasu, adon jikin royal cushions ɗin ma kaɗai abun kallo ne,    tsakiyan falon kuwa wani irin haɗaɗɗen lallausan turkish carpet ne a malale, wanda kana takawa ƴan yatsun ƙafanka na lumewa aciki, tsabar laushi, ta cikin falon acan gefe kuwa wani irin ƙawataccen dinning area ne me azabar kyau da tsaruwa, an kewaye gaba ɗaya wajen da haɗaɗɗen decoration me kyau, wasu irin haɗaɗɗun labule kewaye da kowani ƙofa da window dake cikin falon, ga kuma wasu irin flowers masu kyau da aka saka akowani kusurwan falon, wanda sai shinning suke suna ɗaukar ido, still daga
cikin falon kuwa wani irin tangamemen tv plasma ne keta aikin ɓaɓatu shi kaɗai,  bayan plasman dake magana shi kaɗai babu wani halitta acikin falon, sai  sanyin A/C dake ta busawa.
Kan dinning area' n ta kalla, wayam haka taga saman table ɗin  babu ko cokali, bare kuma  food flask, da dukkan alama dai yau ɗinma ba'a rage mata break fast agidan ba.

Cikin rashin ƙarfin jiki ta murɗa handle din ƙofar falon ta fita zuwa babban compound ɗin gidan, wanda yayi matuƙar haɗuwa, kanta tsaye  ta nufi  hanyar babban gate ɗin gidan,  sunkuyar da kanta ƙasa tayi, tare da   sanya hannunta duka biyu ta riƙe jakar makarantar dake goye a bayanta.
Ɗahiru me gadi dake tsaye abakin gate ɗin gidan, ganinta yasashi ɗan sakin murmushi cikin kulawa yace.     " *LAYLERH* ƴan mata sarkin makara yau madai amakare za'aje makarantar kenan."
Idanunta ta É—an lumshe tare da jinjina masa kai alaman
"Eh."  
Murmushi ya kumayi tare da cewa.   "To Adawo lafiya Allah ya bada sa'a."   Cikin zazzaƙa kuma tattausan muryarta tace.  
"Ameen Malam Ɗahiru nagode."      

Buɗe ƴar ƙaramar ƙofar dake jikin gate din tayi ta fita.
Malam Ɗahiru kuwa binta yayi da kallo yana girgiza kai, cike da matsanancin tausayinta, dan yasan babu makawa yanzu haka ko karyawa batayi ba, kuma haka zata tafi makarantar,   ga kuma motocin da suke ajiye agidan basa aikin komai sunkai guda 7, amma daga cikinsu babu wanda ake bawa umarni ko izinin kai Laylerh'n makaranta, kullum saidai ta fita bakin titi tahau taxi , ranan da bata da kuɗi kuwa saidai ta taka akan sawayenta, wannan dalili yana daga cikin abunda yasa yake matuƙar tausayin yarinyar.

Cikin yanayi naɗan ɗaga ƙafa take tafiya, akan shumfufaɗaɗɗiyar hanyar da ta kewaye unguwar tasu, wanda kowani ƙofar gida akwai titi shumfuɗe agabansa, haka ƙa'idar unguwan tasu take, kasancewarta unguwar masu kuɗi shiyasa, saikayi tafiya me nisa aƙafa baka haɗu da wani ko wata ba, kowa na cikin gidansa akulle, idan ma zaka ga mutane tofa saidai acikin tsala tsalan motocinsu suna wucewa, musamman ma a irin wannan lokacin babu Ragowan ababen hawa akan titin unguwartasu, domin masu tafiya office da makaranta duk sun tafi.
Tafiya take sosai, sai cira ƙafa take burinta baiwuce taganta abbaban gate ɗin da zai fitar da ita daga unguwar tasu ba, dan ananne kaɗai zata iya samun abun hawa.
Sauri take sosai, duk da kasancewar ma babu wani abu na kirki da tasa acikinta tunjiya da dare, gashi yanzuma bata samu arzikin yin break fast ba ta fito.
Saurin da takeyine yasa bata wani ɓata lokaci ba, ta iso ƙofar gate ɗin, me gadin gate ɗinne ya bita da kallo dan idan da sabo ya saba da ganinta kusan kullum, matuƙar akwai makaranta to fa sai yaga wucewanta.
Ɗaga masa gaisuwa tayi sannan tabude ƙofar gate ɗin ta fice.
Samun kanta tayi akan wata sabuwar titi, wanda take akwai ragowan ababen hawa akanta, saidai kuma duk ba motocin haya bane ke kai da kawowa awajen.
Ahankali taɗan bubbuga ƙafafunta tare da ciza laɓɓanta, cikin wata irin murya me sanyi tace.     
"Ya Allah Ka taimakeni katuromin abun hawa, yauma na makara, bansan yazanyi ba, nayi missing  lectures, gashi by 9:00 muna da test."   

Yanayin yanda ta ƙare maganan tana ɗan rawar da idanunta ne yasa ƴan guntun ƙwallan da suka maƙale acikin idanunta suka samu daman gangarowa.
Daidai lokacin kuwa wata motar taxi tazo wucewa, da sauri ta sanya hannu tana taran taxi É—in, cikin sa'a kuwa ya tsaya.
Tana faÉ—a masa inda zai kaita, batare da tajira me zaice ba ta buÉ—e motar ta shiga, yayinda me taxi É—in yaja motar sukayi gaba.
Jakan dake goye abayanta ta ɗaura akan cinyarta, zage zip ɗin jakan nata tayi, ahankali ta sanya hannu acikin aljihun jakan ta zaro 1k wanda shine iya kuɗin da ya rage mata,  bayan shi kuwa bata da ko sisi.
Ɗan jingina bayanta tayi da jikin kujeran motar, ahankali ta sauƙe ajiyar zuciya me nauyi, tabbas idan naira dubu ɗayan nan ta ƙare batasan ya zatayi ba, dole ne ta fara takawa da ƙafa.
Ahankali taÉ—an lumshe kyawawan idanunta.
Tunani ne kwance acikin zuciyarta har suka iso bakin katafaren school É—in nasu batare da ta sani ba.
Jin taxi ɗin ya tsaya ne yasa ta buɗe idanunta, ganin sun iso bakin gate ɗin makarantar ne yasata fitowa daga cikin taxi ɗin bayan ta miƙa wa me taxi ɗin, 1k ya bata canji.
Ganin gate É—in makarantar tasu a rufe ne yasa taji gabanta yaÉ—an faÉ—i, dan tabbas tasan cewa tayi latti.
Ahankali ta ƙarasa jikin gate ɗin tare da ɗan  ƙwanƙwasawa.
Ɗaya daga cikin securities ɗin dake gadin gate ɗinne ya buɗe ƴar ƙaramar ƙofar dake jikin gate ɗin,   ganinta ya sashi zuba mata ido, tare da ɗaure fuskarsa, duk da cewa shi sabo ne awajen amma  tabbas ya shaida fuskarta saboda tana yawan zuwa late, cikin gurɓatacciyar hausan sa da bai gama iyawa ba yace. 
"Yarinya ki koma gida dan kinyi latti, kin san kuma bazan barki ki shiga ba, saboda yin hakan saɓawa aiki na ne." 
Idanunta da suka ɗan ciko da ƙwalla ta ɗago ta kalleshi, cikin sassanyar murya tace.
"Dan Allah kada ka hanani shiga, wallahi ban samu bus da wuri bane, please insha Allah zanna kiyayewa."    Kai ya girgiza  mata, tare da maida ƙofan ya soma ƙoƙarin rufewa, dan yasan idan har ya barta tashigo, muddin aka ganta akwai matsala, dan dokane na makarantar duk ɗalibin da baizoba har aka rufe gate to fa ko yazo saidai ya koma gida, idan kuwa aka kama ɗaya daga cikin  masu gadi da laifin buɗewa wani ɗalibi ko ɗaliba ƙofa to zai karɓi punishment me ƙarfi.

Saurin riƙe ƙofar tayi cikin yanayin roƙo tace.  
"Dan Allah Kamin alfarma koda sauÉ—aya ne, na yau kawai kabarni na shiga, 9 daidai muna da test kuma idan banyi ba zai iya kawomin nakasu please."

Kallon yanda idanunta suka ciko da ƙwalla gate man ɗin yayi,  hakanan yaji wani abu adangane da ita,  duk da cewa shi ba musulmi bane, amma yakanji wani irin nauyi aransa idan aka haɗasa da ALLAH.
Ɗan jinjina kansa yayi, cikin gurɓatacciyar hausan sa yace. 
"Zan barki ki wuce, amma ki kula kada wasu su ga shigowarki, saboda idan aka kamaki nima hakan zai shafeni."  
Dasauri ta jinjina kanta, cikin jin daÉ—i tace.
"Nagode sosai."  da sauri ta shige cikin makarantar, shi kuma ya maida ƙofar ya rufe.

Cikin hanzari take tafiya, har kafafunta suna harÉ—ewa, tsoro ne fal zuciyarta, addu'a take tayi Allah Yasa kada aganta.
Cikin ikon Allah kuwa har ta kawo bakin class É—insu bata taradda malami ko É—aya awaje ba, duka suna cikin aji suna gudanar da lectures, haka ma securities É—in da suke kula da makarantar basu taho ta wajen da take ba.
Ɗan leƙa ajin nasu tayi ta window, gabanta ne ya faɗi ganin tuni Maths teacher ɗin da zaiyi musu text ya shiga, har ya fara rubuta musu questions akan  board.
Jikinta ne ya soma rawa, dan sarai tasan  Teacher David baida mutunci ko kaɗan, yanzu sai yace bazata shiga ba.
Ɗan danne siraran laɓɓanta masu kalan pink tayi, ahankali ta ƙaraso bakin ƙofar ajin nasu ta tsaya.
Ƙarasowanta kuwa yayi daidai da ɗago da kansa, yakai duba zuwa bakin ƙofar.
Ganinta ya sashi ƙanƙance ƙananan idanunsa, cikin halin baƙin hali yace.
"you, from where?".
Yatsun hannunta ta soma ɗan murzawa, samun kanta tayi da kasa cewa komai, dan tasan sa kamar maye yake, daka masa ƙarya zai gane.
Kallonta yayi naɗan wasu daƙiƙu, wani yawu ya haɗiya tare da cewa.  "Oya come in."  
Jin haka yasa taji wani sanyi aranta, ƙarasowa cikin class ɗin tayi, hakan yasa idanun gaba ɗaya ƴan ajin ya dawo kanta, ɗan satan kallonta Teacher David yayi, can ƙasan maƙoshi yace.  
"Oya Go and sit down."  ai kuwa kamar jira take da sauri, ta nufi wani benci wanda bakowa akansa ta zauna.
Da sauri ta buÉ—e jakanta ta ciro paper da abun rubutu, sunanta ta rubuta ajikin papern sannan ta zubawa white board É—in nasu ido, cikin ranta take karanta questions É—in dake rubuce akan allon.
Daga  bayanta yaji anja hijab ɗinta ta ƙasa ,ƙin juyawa tayi dan tasan Teemah ce kaɗai zata mata haka.

Ɗan cije lips kyakkyawar matashiyar budurwan da ake ƙira da suna Teemah tayi, cike da takaicin rashin juyowan na LAYLERH,  ƙasa ƙasa tace.
"Wallahi Laylerh ke Æ´ar air ce, kina sane da cewar ban iya maths ba, me makon ki zauna akusa dani shine zakije ki zauna awani sit daban ko hmmm."
Ƙwafa tayi tare da hararan teacher david ƙasa ƙasa, cikin ranta tace.   "Banza tsohon maye, sai shegen son bada assigment da test, saikace an faɗa masa kowa ke gane darasin aljanu irin nasu, zaka gane wallahi kai da kunnuwan ƙwarangwal zan zana maka, sai injera maka sufuli aƙasansu."   Murmushi tayi tare da soma rubatawa takardan nata zero zero.

Laylerh kam da gangan taƙi juyowa, dan tasan da ta juyo Teemah bazata barta ba, sai tayi duk yanda tayi teacher David ya ƙwace musu takardan su.
Idanunta taɗan lumshe ahankali bayan tagama karanta questions ɗin, wani tunani ne yasoma shigowa ƙwaƙwalwarta, ahankali yanayinta ke sauyawa, zuciyarta ne ta fara bugawa da ƙarfi, yayinda numfashinta yasoma ƙoƙarin hautsunewa,  hannunta tasanya inda ta ƙanƙame jikinta, tare da sake rumtse idanunta,  gaba ɗaya jikinta ne ya ɗauki ɓari, wani irin zufa ne ya shiga keto mata.
Sannu ahankali  hoton haɗaɗɗun cikin idanunsa masu masifar kyau suka soma yawo acikin idanunta, laɓɓan bakinta ne suka soma rawa.
So take ta faÉ—i abun dake rai da kuma zuciyarta, kalma É—aya tak, ita takeson furtawa ako da yaushe, amma har yanzu takasa samun dama.
Tabbas tanason sa ni, tanason sanin wanene mamallakin wannan kyawawan idanun masu kyau da burgewa, meyasa yake shigowa cikin tunaninta akoda yaushe? batasan shi ba, batasan a ina zata ganshi ba, abu ɗaya kawai take iya fahimta amatsayinta na matashiyar budurwa, wanda ayanzune take ƙoƙarin mallakan hankalin kanta, wannan abu shine BUGUN ZUCIYA, tana da yaƙinin cewa lokuta da dama bada tunaninta take aiki ba, sannan kuma bugun zuciyarta na tafiya ne da abu guda.
Farinciki, ko akasinsa, tsoro, ko fargaba, rauni da kuma tarin ƙaddara, tayaya zata iya ɗaukan hakan, bata fatan zuciyarta ta tarwatse akan wannan dalilin.

(Kubiyoni, dan wannan labarin ba irin sauran bane, wannan daban yake da kowanne, kuyi comment da kuma votting  ɗina kamar yanda kuka saba, har ma fiye da haka, dan ta hakane kaɗai zan iya gane cewa lallai kuna enjoying labarina yanda ya kamata, sannan kuma karku manta ina alfahari daku akullum akuma koda yaushe, sannan ina neman Alfarma awajenku gaduk wani ko wata da ya karanta fejin nan, dan Allah kuyiwa YAYANA addu'a, akan  ALLAH yabasa lafiya😭. Then masoyana kuyi haƙuri da jinkirin dana samu na rashin kawo muku sabon labari da wuri, nagode sosai da nuna ƙaunarku agareni.🙏🏻)

      
       *Vote*
*and comment*

            

             *fatymasardauna*
1/19/21, 8:09 PM - Ummi Tandama: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*LAYLERH MALEEK*

*Writting by*
Phatymasardauna

*Wattpad*
@fatymasardauna

#Generalfiction

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.