Complete Hausa Novels

Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 8 of 64

BABI NA SHA UKU..

Tun daga ranar da na shiga cikin gidan, nake fama da ciwon kai. Gashi Mutumin baya barina, idan ya kama ni niman hanyar cutar dani yake, amma Alhamdulillahi tunda duk abinda zai min Allah yana kawo min Malik akan lokaci.

        Yau kwana na tara da zuwa gidan, zuba min kaya yayi yana faɗin.
"Duba ka gani, sun maka?" Ya tambaye ni,
"Wallahi ba zan saka matsatsun kaya kamar dan iska ba, dube su fa, wannan duk gwiwar a yage?" Na fada ina kwalallo idanu waje.

       "Toh wallahi ban isa ba Yallabai dan Ba'are ne yasani na sayo maka duba har da kayan kwalliya irin na mu, koda yake dan kana yana yi da Mata ne yasa baka son."  Yadda ya ga na haɗe rai yasa shi jan bakin shi.

  D'aga kayan nayi, sai da tsigar jikina ya mike, idanuna suka cika da kwalla.
"Yanzun don Allah Ni ne zan saka su, gaskiya ba zan iya saka kayan ba"
"Toh kwashe ka kai dakin kasa, ka ajiye." Haka na kwashe kayan ina mita.
"Kawai dan kashe kudi za a wani tattaro min wasu kaya kamar dan iska"

  Kuma ban da jaraba wallahi babu muni a kayan kawai ban saba bane. A hankali na zuba kayan tare da shirya su. Ina kallon kayana, na shafa su. Kafin wani tunanin ya fado min a raina. Matse hannuna nayi ina me jin kwalla na ciko min idanuna.
"Kai Dan daudu, dalla fito mun yi baki daga  Niamey"

Da sauri ka sake kayan na fito a hankali, ina raba idanuna.
"Zo nan munafiki bakin munafiki, gaka baki ga bakin zuciya, wato dan Ba'are ya kawo ka? Ni Khalil Ibrahim zai ja dani?"
Ta nuna kanta. Sannan ta kalli Malik,
"Ai kaji abinda Firaminista ya faÉ—a? Dan haka kar na kuma ganin ka a cikin gidan nan,kai kuma duna muje"

      Haka ta sani a gaba har zuwa dakin shi ya farka daga barci, kifa mishi mari tayi cikin tsoro ya sauka a gadon, jikin shi yana rawa. Sake marin shi tayi, idanuna suka cika da kwalla dan ji nake kamar Ni take duka. Zata kuma na kare kanshi, da bayana tare da rungume fuskar shi.

"Don Allah ranki shi dade kiyi hakuri, wallahi bai da lafiya bai san meke damun shi ba." Na fada ina kuka.
"Guard" ta faÉ—a da karfi, cikina ne ya cika da ruwa, sautin tsoro.

Suna zuwa suka yakinceni ajikin shi, suka shiga takani tare da duka na, abin tausayi ya koma gefe can ya zauna yana kallon yadda suke duka na, kanshi a tsakanin cinyoyin shi. Sai da suka ga bana numfashi.sannan suka jani kamar kayan wanki suka watsoni ta step, nayi ta dungure ina fadowa har na iso kasa, dariya ma'aikatan gidan suka saka sannan kowa ya kama gaban shi.

            Tana gama abinda zata yi ta fito daga dakin shi, haka ta kira Hurayyah ta kawo mata ruwan sanyi, ina kwance suka zuba min ta kunne na, sai da na tashi zaune,  da gudu na haura sama, ina kai last step ya saka hannu ya turo ni, rike rigar shi nayi, ina kallon shi kafin ya ingizani na fado da baya, rayuwar duniyar nan cike take da al'ajabi, idan kana cikin talauci kace Allah ya kika? Idan kana cikin wadata fitinar zamani ta addabe ka, idan kana mulki rubabbun mutane su hana ka aikin kwarai.

   A hankali kai na ya daku step, daga nan ban kuma sanin me ya faru ba, sai bayan kwana biyu.

--- lokacin da suka gayawa juna magana da Dan Ba'are, ai tasan baya garin kuma tasan akan abotar shi da Mohan ba zai tab'a barin wani ua cutar dashi ba. Dan haka yana barin garin ta samu Mai girma Firaminista da zancen dan Ba'are ya kore masu aikin da suke kula da Mohan dan haka ya kira shi yayi mishi gargadi kuma zai je da kanshi.
A fusace ya ce mata.
"Ba na hanaki hada ni da wancan yaron ba? Dan haka zan kira Khalil din naci mutuncin shi da yasa kike hada wancan Mahaukacin."

Ya kira Dan Ba'are ya kafta mishi rashin mutinci, Kuma yace ya barwa Hajiya Safiya Aikin kula da Mohan. Hakuri yayi ta bashi sannan ya kashe wayar, bayan sun gama ne ta saka rana zata tafi Maradin.

      ***
A can inda yake aiki kuwa, cikin gaggawa ya kira Malik ya gaya mishi kome, sannan ya sallame shi. Bayan sun tsara kome.

  Dan haka lokacin da tazo babu wanda ya hana ta, sai dai daga Yadda da ta fara cutar da Mamoon ne yayi ta daukar abin a video yana turawa  dan Ba'are.

      ..... Tana gamawa ta kira wani layi, sannan ta shiga motar cikin wani yare na daban, take magana.kafin ta juya da cewa.
"Namiji ne ba mace ba, amma mun yi mishi bayani da Yaren da zai fahimta"

     Haka suka bar gidan, shi kuma Malik yazo ya dauke ni zuwa asibitin.  Inda aka min su ƙarin ruwa da allurai.

   A hankali na bude idanuna, baba larai na gani zaune.
"Sannun Kaji!" Lumshe idanuna nayi sakamakon kai na yayi nauyi,
"Malik" na kira sunan a gajiye,
"Na'am"
"Ina Yallabai?"
"Yana gida bai da lafiya"
Da sauri na dira a gadon ina ƙoƙarin tuge roban ruwan da a ka saka min.
"Dalla koma ka kwanta, akan shi ake niman rayuwarka, idan sun da mu dashi nima mishi magani zasu yi ba su barshi yana hauka ba, sannan haka kawai zasu dake ka ai ka  gama aikinsu"

"Zan cigaba da aikina "
Na fada a gatsale, "rashin mutunci zaka min?"
"Kai ka fara, wannan abun bai shafe ka na kake kokarin  shiga cikin shi."

Abinda ban tab'a yi ba,.shine fada da wani, yau gashi ina sa'in'sa da malam duk da tarin Alkhairin shi a gare. Ranar har dare ban yi barci ba, kuma ban san me ya hanani barci ba, amma tabbas ina cikin damuwa,  Washi gari da hatsin sai ga Dan Ba'are, ban ma san sun shi ba kenan.
..
"Kana ina Malik har haka ya faru? Taya zaka zuba ido su kashe dan mutane? Kai da kanka kwana É—aya da zuwa shi ka gaya min cewa yasan me yake yi, kuma kana ganin"

"Kayi hakuri yallabai." Ya fada, kallona dan Ba'are yayi sannan min.
"Mamoon ya jikinka?"
" Da sauki yallabai"
Sun jima sosai, kafin suka fita.
***
Gidan ya nufa, ranshi yayi zunzurutun b'aci dan haka yana shiga ya bada oda a ci uban masu aikin gidan, sannan ya nufi dakin da Mohan yake, ya riko kwalar rigar shi, cikin fushi ya zabga mishi naushi fuska, a fusace ya kalli Dan Ba'are.

"Ai kasan zafin duka?  Toh shima Yaron haka yaji lokacin da ake dukar ka,har kasa hannun kana ture shi daga sama uban waye ya baka izinin haka?" Ya fada da mugun karfi, sunkuyar da kai yayi kamar me hankali, bai iya kuma tari ba.
"Ba Mahaukaci ba kowani abu a duniya yasan me kyautatta mishi kai ne da bakin ka, ka tab'a gaya min haka?" Ya karshe maganar cikin kuka yana rungume shi, sabida yasan ba halin shi bane, kuma bai tab'a ganin shi yayi haka ba da lafiyar shi amma yaji matukar bakin cikin abinda yayiwa Mamoon.

   Jan shi yayi suka nufi asibitin, har dakin da Mamoon yake ya kaishi, kanshi a sunkuye.
"Almamoon ga Mohan nan yazo baka hakuri"

Tashi nayi da kyar ina rike wuyana nace mishi.
"Yallabai akan me zaka kawo shi ai zan koma"
"Ba zaka koma su kashe ka ba"
Da sauri na kalli Malam Ansar, "don Allah karka kirkiro mana abinda zai wargaza wannan tafiyar wallahi bai."
"Koma ka zauna, Idan Allah ya baka lafiya zaka koma"

"Wai ku me kuka dauki rayuwar shi ne?".wani mugun kallo Dan Ba'are yayi mishi tare da riko hannun Mohan.
"Nan Asibiti ne ka rike harshen ka" takowa yayi gaban su.
"Almamoon bazai koma ba"
"Wai malam me yasa kake haka ne"
"Kayi min shiru, ko ka manta waye kai ke? Kai din da kake tafe da jinsi iri-iri biyu"
"Malam Me ye haka ne?" Na tambaya cikin tashin hankali.
"Dan haka ka tattara mara lafiyanka zan cigaba da kula da my pumkim"

        Ran dan Ba'are ya b'aci sosai, dan haka ya rike hannun Mohan yayi tafiya shi.
"Yallabai karka bi na shi muje na karasa jinyar a gidan" na sauko a gadon,  tare da bin bayan su.
"Mamoon ka dawo" nayi banza dashi. Ina isa jikin motar, yana fincikar tare da watsa min kura, sauran sojojin suka rufa musu baya. Kurawa motar idanu nayi domin ban zaci haka daga gare shi ba.

   "Yallabai yaron nan bai da matsala, kuma a bakin shi na fara Fahimtar matsalar Yallabai Mohan bata Allah bace duk da nima na zargi haka, amma kuma a yadda ya fara kokarin niman abinda zai hada domin samun lafiyar shi ya min, wallahi Yallabai Mohan yana takura Yaron amma ko sau daya bai tab'a gajiyawa ba, yallabai karka barshi bamu san abinda Allah yayi a tare da shi ba"

    _Kayi min shiru, ko ka manta waye kai ke? Kai din da kake tafe da jinsi iri-iri biyu!_

Wannan ne abinda yake yawo akan shi da kunnen shi, ji yaƙe kome ya tsaya mishi, gaskiya domin Yaron ya shiga ranshi.

    "Sannan idan muka bar shi kamar mun bawa Malam Ansar damar cewa ya fimu karfin iko akan Mamoon(ikon Allah🙄😠 😏 yo ba dole ya fiku ba bana son munahunci da shiga tsakani) idan ka duba Yaron yana son aiki damu"

"Juya" yace shima a karan kanshi yana son Yaron ya zauna da Mohan, dan haka suka kuma sharan kwana da mugun gudu.

Tunda suka tafi nake tsaye, kuka ne ya kwace min. Na juya ina kallon Malam Ansar da shima yake jin kamar yayi kuka.
"Wai me yasa baka da kirki? Mutumin nan, jinya ce a jikin shi don Allah"

"Wallahi sai na gayawa Iyayen ka! Tunda baka jin maganar da nake maka wani irin taurin! Ai ashe kwadayin abin duniya yasa ka kake makale musu, tunda ka tazo gidan da ba a san arziki ba" rike bakina nayi ina kallon shi.
"Me yasa kake cin mutuncina? Meye nayi maka? Idan saboda Jinyar Hamma Mohan ne kayi hakuri, amma matukar zasu dawo tabbas zan bisu" na fada ina jin wani irin kwalla na zubo min. Saboda takaici.

Rike hannuna aka yi na juya. Share min kwalla yayi tare da nuna min kofar da aka buÉ—e min,
"Hamma Malik" murmushi yayi sannan yace min.
"Karka kuma kuka muna tare da kai"
Sai da ya kai ni har cikin motar, sannan ya dawo tare da kallon Malam Ansar.
"Ban san meye yasa kake kokarin shiga tsakanin mu da shi ba? Amma kuma yana da kyau ka fahimci abinda yaron yake so? Duk da na hango kishin yaron da soyayyar shi toh gaskiya kayi hakuri.koda zamu dawo maka da Yaron ka sai mun gadama, idan kuma ka sake ka kuma wani abu da zai saka Mamoon kuka sai na saka an kwab'e ka an maka dukar kawo wuka, gashi idan kana son ganin shi zaka iya zuwa any time, amma ban da É—aukar reni"

Ya juya tare da nufar motar, muka bar asibitin, tunda na shiga na kalli Mohan da yake zaune kamar mara gaskiya gefen fuskar shi tayi jajjur,
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, Hamma Mohan waye ya dake ka? Wayyo Allah"
"Hamma Malik ko zaka mai damu asibitin a duba shi." Yadda Mamoon ya rufe tare da gigita akan matsalar Mohan yayiwa Dan Ba'are dad'i. Dan haka ya gyara murya yana faÉ—in.
"Ni ne ba zabga mishi naushi"
"Hamma Dan Ba'are" yadda Almamoon ya kira sunan shi ba iya shi ba hatta Malik sai da ya juya ya kalle shi, shima dan Ba'aren haka.

  A sanyayye yake magana kamar me ciwon baki.
"Yanzun don Allah idan wani yace ka dake shi sai ka dake shi? Ban ji dadin abinda kayi ba, Hamma baka kyauta ba."

Na fada ina jan majina, murmusa min yayi bayan ya juyo yana kallona.
"Toh Sannun akan ka na make shi, amma tunda ban iya gwaninta ba, Malik kayi min sheda bani kuma shiga tsakanin su."

  Har muka isa gidan, tsokanar mu suke.
       Haka ya mai dani dakin dake kusa da na Mohan, tunda Hamma Malik ya koma bakin get kuma ya saka ido sosai akan mu, kwanan shi daya ya bar garin. Bayan ya ci Uban masu aikin gidan ya kuma kwace wayoyinsu su.

          Tunda Hamma Dan Ba'are ya zabga mishi naushi, tare da nuna mishi ni a kan aikin da nake mishi, sai ya zamana yana mugun tsoron tab'a ni. A hankali jikina yayi sauki dan haka na karb'i aikin mana girki, kuma Baga amfanin haka. Sai dai yadda nake ganin gidan kamar akwai matsala.

         Dan haka na fara karatun Alqur'an kullum zan saka shi a gaba, ina mishi karatun Alqur'an, wani lokaci ya fadi yayi ta burgima ko kuma yayi ta ihu. Bana wasa da lokacin da na samu, dan haka na shiga aiki gadan gadan gashi mun fara jarabawa.

     Ranar da na shiga makaranta da sojan da ya kai ni, dalibai da malamai sai n zame musu abin kallo, lokacin da na isa aji sai ga dayawa masu jin haushina sun zagaye ni.
"Dan baki kace likafa ta cigaba?" Ban kula su ba, sakamakon shigowar Malam Ansar, mik'ewa nayi tare da kallonshi.
"Ka same ni a Office" ya faÉ—a tare da barin hall É—in. Haka na mike tare da bin bayan shi, kowa na isa na same shi a tsaye.
"Gani Yallabai"
Wani irin rarruma yayi min, tare da matsane ni a kirjin shi, zuciyar shi na wani irin bugawa, ban ji kome akanshi ba, kuma ban tab'a ji ba, sai akan Hamma Mohan, tunanin halin da yake ciki nake, domin jiya da dare an kawo min wani farin abu wai idan yana niman duka na zuba watsa mishi, sai na abinci. Duk na amsa tare da zuba su a cikin bayi na tura musu ruwa suka tafi. Cire Ni yayi daga jikin shi yana faÉ—in.
"Nayi kewar ka My Puppu, kasan yadda nake jin ka kuwa?" Ya dauki hannuna ya saka a kirjin shi.
"Kullum da kai nake kwana nake tashi na zama zararre akan ka, kai baka tunanina".
Murmushi nayi domin karya da ciwo gyambo da wari.
"Idan Ina tare da Hamma Mohan, wallahi Mantawa ake da kowa da kome, amma idan ina tare da kai shi nake tunawa dan haka wallahi bayan shi bana jin kome akan wani dan adam sai shi. Kullum cikin nazari da tunanin yadda zan nima mishi lafiya nake. Ina matukar tausayin shi"

"Baka tausayina?"
"Eh a matsayin ka na musulmi ina tausayinka mana, amma ba irin nashi ba, wanda nake ji kamar na cire zuciyata na mika mishi."

Zama yayi yana kallona, kamar ya rufe ni da dukka haka yake ji, ban damu ba na tattara ba bar Office din shi, dan na gaji da zaman da babu cigaba. Bayan mun gama jarabawar ne aka zo daukata.
"Mamoon" juyawa nayi ina kallon shi.
"Baka tab'a jin kaunata a ranka ba?"
"Ko É—aya" na gaya mishi haka ina shiga motar. Shafa kanshi yayi yana kallon motar har ta bar makarantar tabbas dole yayi wani abu domin yana ji yana gani zasu rabashi da dan da ya gama wahala dashi, ya tashi tutar babu, kwafa yayi.

      Muna isa gidan na Fahimci, matar Ranar tazo, Allah sarki Yana zaune kamar wani mabaraci, ina shiga cikin gidan ya taso da sauri ya tsaya a bayana. Duk da nima a tsorace nake amma ba zan kuma barin a ci zalin shi ba.
"Zo nan, wallahi na tsane ka na tsani na bude ido na ji kana tare da Mohan, amma ba damuwa ina abin da na baka ka saka mishi idan ya tadda rigima?"

"Su...su ..su...suna.nan"
"Toh magani ce, kuma ka cigaba da aiki dashi, a yanzun kam zamu shirya da kai tunda na Fahimci baka da matsala, dan haka ga wasu ka kula dasu kana zuba mishi a cikin abincin shi duk magani ce, muna tafan lafiya ta samu ko ba yanzun ba."

    "Amin" na fada ta mike tare da cewa.
"Kayi min aiki me kyau nima zan maka me kyau, ga wannan ka rike ." Ta bani kudi me yawa, sannan suka fita, daukar kayan nayi na kai sama, yana bina kamar jela, dan gani yake kamar bata tafi ba. Nazo zan shiga ban daki naga ya bini.
"Kai juya ka koma ba abin mutum ban daki" na daka mishi tsawa ina zare ido. Kamar wani karamin yaro haka ya juya ya koma, na shiga tare da rufe kofar, a hankali na cire kayana, ina duba jikina. Murmushi nayi ina hasashen wata rana. Murmushi ne ya kwace Min.
Da sauri na gama wanka na shirya na fito yana zaune, sai kale kake yake, sallah nayi. Yana kallona, ina idarwa na kai shi ban daki nayi ta kokuwar yayi alola, dakyar yayi nazo na gwada mishi Sallah, hmm an sha dungure.

Bayan ya gama muka fito, kasa muka je na daura abinci tare, baya tab'a gajiya da tsayuwa. Har na gama na zuba mishi,  a Haukacd yake cin abincin, kwace abincin nayi na fara nuna mishi yadda zai ci, a hankali ya fara ci yana kallona, har ya gama muka mike tare, na kai shi ya wanke hannun shi muka dawo daki, duk inda zan saka kafa yana biye dani.

           Shakuwar mu tayi yawa, domin idan na tafi makaranta, rikice musu yake a gidan, ina dawowa kuwa, zai zo ya makale a gefena har yana sauke ajiyar zuciya. Kayan da ta bani ban yi amfani dashi ba.

Ranar da na cika wata daya aka bani kudi me yawan gaske, dan haka ranar da muka gama jarabawa, ban bi takan Ansar ba, na dawo gida na gayawa Hamma Malik zan tafi gida kwana É—aya zanyi, na mishi bayani da abinda Hajiya Safiya ta bani, bai hana Ni tafiya dashi ba, dan nace zan kaiwa Baba na ya gani. Washi gari da sassafe ina zaune a gaban shi bai tashi barci ba. Shafa kanshi nayi wanda yake cike da gashi me kyau, murmushi na sake sannan nace.
"Nasan zaka yi rigima, amma Insha Allah zan dawo gobe da wuri" sannan na mike a hankali, na bar dakin.

    Haka na bar gidan cikin nutsuwa, na nufi Damagaram. Karfe uku na yamma yayi min a kofar gidan mu, ina shiga na samu iyayena suna lafiya, amma matsin rayuwa yasa sun kara yamutsewa.

    Ajiyar zuciya na sauke ina kallon su bayan nayi sallama.
"Almamoon! Kai ne haka? Sannun da zuwa"

Innah ta shiga hidima dani, kafin kace me har ta rasa inda zata sani ga shi naga alamar babu abinci a gidan, mik'ewa nayi na nufi kasuwa, na mana sayayyan kayan masarufi masu yawan gaske wanda zai rike su wata biyu dan kuÉ—i ne me mugun yawa.

   Tunda na dawo da kaina na shiga kitchen nayi mana abincin, bayan na gama muna ci. Nake basu labarin aikin da nake, amma akwai matsala, nan dai muka sha hiran mu, sannan na mikawa Baba kayan, ya shiga dubawa nace mishi.
"Baba ka warke kamar ba kai ba"
"Eh wallahi gani nan na dawo kamar bani ba, amma waye ya baka wannan mugun aiki ?"

"Matar Uban Hamma Mohan, kasan shi ai dan shugabanan kasa ne, kuma babban jami'in sojan, toh ban san me yasa ba ina shiga gidan na fara gane gane, kuma an kawo min wasu na zubda wannan ne mace bari na kawo maka"

Gyada kai yayi sannan yace min.
"Insha Allah duk tsananin yana tare da sauki, bari muga zuwa gobe zan tsaya akan shi yau, Allah Sarki da ace Aminina yana nan da shi zai maka wannan aikin"

  "Allah Sarki, bari na huta. Inna wai meke damunki ne?" Na tambaye ta,
"Kawai tsoron yadda ka cusa kanka cikin tashin hankali ne ya sani shiru."
"Kai Innah kincika tsoro" na fada ina nufar dakina.

    ***
Washi gari.
Da sassafe baba ya bar gidan, Ni kuma na tashi nayi hidimar kome, muna yi muna hira da Innah, zama tayi tana kallon yadda nake aikin.
"Mamoon, kamar kana cikin farin ciki?"
"Innah Hamma Mohan nasan yanzun yana can yana rigima a kai shi gurina."

Murmushi tayi kafin ta kalle ni a razane.
"Dama namiji kake jinya?" Sai lokacin nasan bakina yayi subul da baka.
"Hmm." Na kalle ta.
"Tashi"
Ta daka min tsawa, tare da nuna min hanya dakina. Tunda mike da ita bata tab'a min abinda tayi yau ba, ban san lokacin da kuka ya kwace min ba, jikina har rawa yake, Innah bata kyale ni ba, sai da ta duba jikina tare da duba gabana ko wani abu ya same ni.

"Wallahi Innah ban tab'a aikata kome ba, na rantse miki da Allah, Inna don Allah karki duba gurin ki yarda dani"
.make santalelen bakin cinyata tayi nayi shiru tare da rintsa idanuna.
"Wallahi na sameka da aikata abinda bashi bane sai na yankakka na zubawa karannuka sucinye namar ka"
Shekaru goma sha takwas zuwa sha tara, wai Innah ke cewa zata yanka ni, amma dake a tsorace nake ban san lokacin da gyada mata kai ba, ina kara kame jikina. Kasa magana tayi tana kallon yadda duk na firgita. Komawa gefe tayi tana kuka.
Nima kukan nake ina bata hakuri.
"Wallahi ka sake wani yayi abu da kai, guduwa zanyi na Barka ka kame kanka"

Gyada mata kai nayi, sannan ta daka min tsawa na fita na karasa aikin, haka ne wuni suku suku.. duk tsoron ta kar wani abu ya same ni.

Da la'asar Baba ya dawo, sannan ya shiga hada min magani, bayan ya dauki allon karfe ya fara rubutu a cikin shi yana gaya min.
"Mutanen maraya basu san niman maganin kariya ba, su kawai akwai Allah, ai sai ka taimaki kanka Allah zai taimaka maka, idan baka taimakawa kanka ba waye zai taimaka maka, dan haka ka saka ido sosai akan shi, makiya ne a cikin rayuwar shi da ta iyayen shi, kuma shine Garkuwa Iyayen shi. Sannan akwai wani al'amarin da na kasa Fahimtar shi. Sai dai Allah ya kyauta kawai, iya ku da kuka tsaya mishi Allah ya tsaya muku."

"Amin Ya Allah'" dake na gaya mishi kome akan gidan shi yafi Innah fahimta kuma ya gane abinda nake nufi, wallahi har tsoron Innah nake musamman yadda ta wangale ni, yasa ni tsoron ta da ita, wallahi Innah jan wuya ce, yana gama hada maganin yace min.
"Gobe Insha ALLAH zaka tafi. A fara maganin amma dole zaka yi hakuri da halin da zaku tsinci kanku."

   "Ai ba haka ba, wallahi Malam ka kasa Almamoon ya fita idanuna, kuma namiji yake jinya ba mace ba, idan wani abu ya same shi Ya"
"Insha Allah  babu abinda zai faru" inji Baba,  wallahi Innah ta sani a gaba, domin har addu'a nake gobe na gudu, bata kuma gani na sai karshen wata. Haka kuwa ya faru, washi gari bayan ta gama min dogon nasiha sannan ta kara min da fada kamar zata dake ni, na samu dai muka rabu lafiya na bar gidan.

         Da kaya niki niki, zan tafi na cewa Baba.
"Baba ka nima mana wani gidan Insha Allah nan da wata uku zan zo da kudin gidan a saya mana ba sai mun cigaba da zama anan ba sabida sha'anin rayuwa"

Ya Amince kuwa yace min.
"Ka kula da kanka Insha Allah"

"Toh Baba" haka na tafi ina kallon Shege da Jama'ar shi na samu abin hawa na gudu, cizon bakin shi yayi yana kallona.

    ***
Da yamma likis muka isa, na nufi gidan a abin hawa, ina isa Sojojin suna kwashi kayan suka zuba a motar da aka ajiye dan ta kwana na shiga na zauna muna gaisawa.

   Ina shiga cikin gidan na ga ana tare tare da Hamma Mohan. Da sauri na fita a motar ina faɗin.
"Meye kake haka?" Cak ya tsaya tare da kallona, kafin ya juya ta koma cikin gidan, haka suka taimaka min da kwashe kayana,muka shiga cikin gidan.

   "Hamma Malik, ya na same ku?"
"Alhamdulillahi, ka tafi ka bar mu da rigima, tunda ka tafi yake mana rikici wallahi ba zai zauna ba ihu da masifa da barna babu wanda baya yi, yayi ta bude kofar daki yana hawa da sauka yana niman ka. Yaki cin abincin kowa fa yanzun haka da yunwa a jikin shi."

"Ya Rabb" na fada ina kara saurina har zuwa cikin gidan, na shiga kitchen na fara aikin shara da goge kome, ina kallon Hurayyah. Ta shigo kitchen É—in.
"Jinka zamu kyale ka kayi mana abinda yayi maka ne?"
"Toh idan baku kyale Ni ba, rawan nannaye zaku min?" Na fada ina aikina,
"Kai ka isa ka gaya min magana?"
"A'a banza irinki zan gayawa magana"
" Kai waye banza?"

"Ai na zata shashasha ce a gabana,ashe sakarya ce" na daura abincin ina aikina, kamar zata d'aga hannu sai ta fasa.
"Sai na baka mamaki"
"Kwantar da hankalinki, ni kullum a cikin bawa kowa mamaki nake"
Haka tafita. Tana fadin.
"Dan daudu"
"Maciya amana" na fada mata, haka na gama aikina Na hura sama, na samu ya kwanta, dakin ba laifi dan Hamma Malik yana kula dashi.  Takawa nayi gaban shi na tsaya tare da cewa.
"Ya hakuri tashi kaci abincin."
Tashi yayi na mika mishi ya fara ci, yana kallona.
Dauko maganin nayi na fara zubawa a dakin yana ci, ina aikin .ina gamawa na bashi ruwan addu'o'in wanda aka hada da saiwar itacce babu adadi, yasha baya ya gama cin abincin.

Faduwa yayi tare da girgizar da ta haifar da wata irin duhu, make ni akayi, kamar wani kwallon haka na hadu da bango.
    
Dakyar nace.
"Wash Allah na" na mike lokacin duhun dakin ya washe, hango shi nayi a kwance, da sauri na isa kanshi tare da d'aga shi muka dawo gefen gadon ina cewa.
"Sannun kaji" ajiyar zuciya ya sauke, haka na tattara sauran maganin na fita da shi.

     Tunda ta muka fara maganin nake ganin canji, wani lokaci yayi abu irin ta masu hankali wani lokaci kuma ya birkice min baki daya, har na rasa yadda zanyi dashi, ga shi An tura Hamma Malik wani aiki.

     ...... Tunda ya bada compliment card suka duba bayan sign din Malik, bude mishi kofar aka yi ya shiga, cikin nutsuwa yake bin gidan da mugu mugun mamaki, dole Almamoon ta makale Ashe yana inda wuta ma bai san ana dauke ta ba, kallon wasu mahaukatan mota yayi yana kara jinjina kanshi.

     Har ya shiga cikin gidan baki daya, a nan ya tsaya kallon wata karamar Bujr Arab, gyada kai yake kawai yana jinjina kudin da aka kashe a gurin.

     A hankali yayi parking motar shi sai yake ganin kamar motar shi irin wacce akayi yayin shi tun 1990 ne, (🙄😠 😏 saura a samu abin mana gori 🙄)  baki daya yaji kunyar kiran motar da sunan nashi ce ya kama, haka ya ja kafar shi har cikin gidan, ya tsaya tare da dannna kararrawan da zai gaya musu yana tsaye, budewa aka yi ya kalli Hurayyah.

  "Sannun kana niman waye?"
Ta tambaye shi,
"Almamoon!" Ya bata amsa,
"Shigo" ta bude mishi kofar, a hankali ya shiga, yana kara tabbatar da cewa. Tabbas Almamoon ya ga gurin zama dole ya guje shi, kallon falon yake me cike da haduwa da kasaita,  nuna mishi gurin zama tayi sannan ta haura sama.

   Ina tsaye tare da gyara zaman rigana ta danno d'akina a tsorace nace mata.
"Dalla dube ki kin shigo babu sallama"
"Ai gidan Ubanka ne da zan shiga da sallama"
"Ke baki gidan Uban?"
"Karka zage ni" ta hayayyako min,
"Akan me zan zagi duguli me duwawun roba" na fada ina watsa mata harara,

    "Kan Uban"
"Maso min ashar"
"Toh idan ka gama zagina kana da bako a waje."
Ta gaya min, ko takanta ban bi ba, na cigaba da abinda nake yi, ina gamawa na fito, daga saman step na hango shi, da sauri ka sauko tare da isowa gurin shi. Ina kallonshi nayi kewar shi na yan kwanaki amma ba wai ina kewar shi bane dan ina jin shi a raina. Kitchen na nufa na hado mishi ruwa da abin sha na ajiye mishi, kallon takalmin kafana yayi, wanda yake saka irin shi a matsayin na zuwa gurin aiki yau itace na zaman gida a kafar Almamoon shi. Tabbas canji yana da dad'i amma wannan canjin ya nisanta shi da abinda yake so ne.

"Almamoon"ya kira sunana a kasan makoshinsa,
"Hmm"
"Almamoon Isma'il Wodaadabe, alkawari bai ce haka ba, ina laifin da aka yi hutu ka tsaya mu yi sallama sai kayi tafiyar ka? Ai ki laifi na maka zaka tsaya na baka hakuri."

"Baka min kome ba" na fada kai na a sunkuye,
"A'a nayi maka laifi mana, tunda gashi ka sami inda ya fini"
"Malam me yasa kake min haka n?ranar ka gaya min maganar da ya hanani barci, yau kuma kana kara gaya min wannan zai sani tsanar kaina,, malam Hamma Mohan aiki ya dauke ni, duk da bai da lafiya bai san ni ba, amma ai musu ruwa da tsaki a rayuwar shi sun san dani."

"Eh mana tunda shi dan gidan Firaminista ne  ko? Amma ince haukar shi b'oyewa duniya ake dan kar aji labarin ya haukace?"

"Malam meye matsalar ka da mu ne?" Na tambaye shi murna yana rawa,
"Sabida ban da kudi da maka makan mota ai ko darajar Hamma ban samu ba, amma shi fa a cikin Haukar shi ya samu darajar Hamma! Ba shi ba hatta yan koran shi Hamma kake kiran su dashi? Wallahi ka sake wani ya tab'a min kai, sai na muku bayani da yaren da zaku Fahimta..... Wow 5k Words 😁🤣
8/19/21, 2:22 PM - My Mtn Number: 🐂🐂BOROROJI🫀🫀 
                   
~The Journey of Destiny💔~
  Mai_Dambu
BOOK ONE...

Sadaukarwa ga
  Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.