Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 46 of 64
BABI NA HAMSIN DA BIYU.
Dafe kirjin shi yayi tare da kurawa Zoben idanun, a hankali ya shafa bakin shi. Yana jin alamar maikon bakinta, sake juyawa yayi yaga babu ita babu alamar ta. Yason ya tashi amma ya kasa koda motsi ne, wayar shi ya janyo tare da kiran Dan Ba'are.
  "Khalil kazo" ya faɗa a wani irin murya, cikin rudrwa ya shiga tambayar shi kana ina ne? Ya gaya mishi inda yake, kafin ya katse kiran, saka zoben yayi a gaba, yana kallon shi. Har Khalil ya iso gurin shi. Bai tab'a sanin yana kaunar Maimunari ba sai yau da ya kasa bude baki ta bada labarin abinda ya faru,sai yau da yana ji yana ganin zuciyar shi tayi wani mugun nauyi. Sai yau da kome nashi ya tsaya cak.
  Yau yake danasani mara amfani.
"Mohan ka kirani kuma ka zubawa zoben idanun meye yake faruwa?"
"Ta rabu dani!" Ya fada a wani irin yanayi, idanun shi sunyi jajjur.
A wani irin kidima Khalil ya ja kujeran ya zauna yana kallon shi.
"Meye kayi mata? Wallahi haka kawai ba zata rabu da kai ba, ka gaya min meye kayiwa Yar mutane. Kafin na ci Ubanka dan iska kasan ba zaka iya hakuri da ita ba ka cutar a zuciyarta? Ka koya mata sonka? Karka manta kana da kane mata meye yasa baka da imani ne? Meye yasa baka tunanin kowa sai kanka? Toh shikenan Alhamdulillahi, Allah ta hada kowa da rabon sa, matsiyaci mara mutunci kawai."
  Tab'a wayar shi yayi tare da cilla mishi videon, dauke kan shi yayi tare da gaya mishi da wani abu daya da yasa shi sanyi sama da farko.
"Mohan! Kasan Allah idan har Ina son Beenah aka kawo min ita, tayi ciki an zubar dashi kai a sa ma taxo min da cikin kaunar da nake mata ba zai tab'a barina na duba cikin ba, fatana ita nake so. Kuma ko a gidan karuwai na ganta zan zauna da ita balle kai da ka dauki yar mutane har Dubai ka shiga da ita kuka kwana daki É—aya, baka lalata musu ita ba, ta zauna tayi jinyar ka, baka lalata ta ba. Sai yanzun da wani jahili ya turo maka hauka? Tun wuri ka kirata kuyi Magana"
Allah Sarki jikin shi yana rawa ya kira ta, tare da cewa.
"Moonah ki Fahimce mana, kin bar zuciyata cikin tashin hankali! Muna ina sonki dole nayi kishinki!"
"Mohammed Mamman Nasir, ina ga kamar mun wuce wannan yanayin ko? Amma ka tambaye ka! Shin da Ni da Budurcina wanne kake bukata?" Ta watsi mishi tambaya,
 "Munari dukkan ku ina sonku, dake da Budurcin ina sonku" ya faɗa a mugun tsora ce,
"Karya kenan, wallahi sai ka zab'e da ni da Budurcin wanne kake bukata?"
"Ina son dukkan!"
"Toh tunda kana bukatar dukka sai kayi hakuri da Maimunari kake bukata zan iya duba wani abu, amma dake Budurcin kake bukata kaje yana gurin Hanan ni nawa Malik ya rabani dashi kaje na maka tsana irinta k'iyayya da abokan gaba. Mara lissafi kawai. Kuma wallahi ka nime ni sai na illata rayuwarka kaje kaci yar da aka haifa yau ba gobe ba, mara imani da sanin ya kamata, tir da soyayyar da ta had'ani da kai, tir da zama da kai"
  Kashe wayar tai yana kallon Khalil kamar zai yi kuka, mik'ewa yayi tare da zuba hannun shi a aljuhun wandon shi yana faɗin.
"Fatan Alkhairi, idan ka sami damar kashe wutar da kishinka ya kunna ina nan ina jiranka, amma tsakanin ka da Allah, ba iya shi bane matsalar da zata iya hakuri meye ya faru?" Domin dai ba zai iya barin Mohan cikin takaici ba yayi tafiyar shi.
  "Muje shagon saloon din Uwani."
  Taimka mishi yayi suka fita bayan ya kai shi motar ya dawo ya biyan kudin abincin da suka saya, sannan ya tafi ya ja shi a motar shi, Mohan Mohan kuma ya kira driven Khausar mai suna Haliru yazo ya kai motar gidanta.
  .. Cikin bakin ciki ya ke sauraronta.
"Wallahi ban tab'a ganin mutane marasa imani irin Hajiya ba, kayi hakuri sunan ita ta haife ka, amma bata damu da abinda ke so ba, sannan ita Hanan din mahaifiyar ta, fadi tashi take sabida ita. Wai Hajiya Latifah ita kuma kashe D'anta take.. nan suka kira yarinyar bayan sun gama bincike akanta sannan suka saka aka dauko hoton iyayen ta, ta rabu da kai ko su kashe ta, haba iyaye ba abin wasa bane, ko kai ne autan maza wallahi na gama zama da kai sannan tayi mata gargadi akan karta bari ka sani ai yarinyar ta bani tausayi."
     "Mun gode sosai Uwani" inji Khalil, sai yanzun ya fahimci dalilin da abin yayiwa Munari yawa, ga na Mohan yana zargin ta ga Mahaifiyar shi da Kanwar ta suna kawo mata farmaki.
"Dole ko nice na rabu da kai, dole na nisanta kai na da kai, wallahi maimuna Yar halak ce, ta nuna maka ita bata da sama da Iyayenta kai kuma sauran naka ka tsaya kayiwa naka iyayen biyayya."
  Daga haka ya kawo shi gida, sannan ya kalle shi.
"Masu iya magana da larabci sunce Alhubbu fihi mararatin, so yana tare da bakin ciki da farin ciki, dan haka kayi hakuri zanen ƙaddarar ku ce, Allah ya baka hakuri rashin da kayi Ubangiji ya tabbatar maka da Hanan a matar ka ita kuwa Maimunari, Ubangiji ya bata wanda zai aure ta babu Budurcin ya zauna ta da ita haka!"
 Wani irin sanyi jikin shi yayi, a hankali yake d'aga kafa, sannan ya shiga falon ya samu duk suna cin Abinci, kallon Mahaifiyar shi yayi sannan ya tafi inda take ya ajiye mata zoben da Maimunari ta ta dawo mishi da shi, sannan yace mata.
"Ita Mahaifiyar Hanan sabida farin cikin Yarta take wannan hidimar, ke kuma sabida ki lalata min farin cikin na kike kome ko? Toh Alhamdulillahi, Maimunari ta fasa aurena, kuma na rantse da Ubangiji Rahama. Kuka hada ni da Hanan sai dai wata ba ita ba, dan zan kashe ta"
Ya fada tare da nufar hanyar part din shi, hango Mahnoor yayi da Hindu.
   Tausayi yaran suke bashi, tun daga lokacin da ya fahimci Hajiya Safiya ita ke mishi wani abu, haka ma Primer minister ya fahimci haka, shine ya kore ta a gidan yanzun haka bin abokan shi take tare da yan uwansa, akan a dawo da ita sharrin Oga shaidan ne.
  Ya tattara ta ya watsa gefe can, yanzun yaran an saka musu kahon zuga a cikin gidan musamman ma Hajiya Lateefah, shi yasa idan yana gidan suke zama a part din shi, yana son kanen shi. Kuma abinda yasa yake burin Auren Maimunari domin ya tattara Yaran su koma gaban shi. Kama hannun su yayi suka shiga part shi. Abincin gwangwani ya basu. Sannan ya koma uwar dakin shi ya kwanta, kamar wanda aka mintsina. Ya mike tare da surar key motar shi ta fita da sauri, gidansu Hanan ya nufa, tun a cikin motar ya zare belt din shi na aikin soja, yana shiga cikin gidan, ya same ta da Kawayen ta suna maimaita abinda suka yiwa Maimunari, tare da kiran mahaifiyar shi jaka.
Wato da bawan Allah nan ya zage yayi ta dukar su, yayi ta kwallon dasu sai da yayi musu kaca kaca, sannan ya nutsu ya juya yana nuna su da dan yatsa.
" Ki saka a ranki wannan wasan ba ayi kome ba, domin sai na miki wanda yafi haka." Sannan ta fita ya bar su a gidan domin Hajiya Karime tayi tafiya.
----
"Ban gane abinda Mohan ya faÉ—a ba! Kina nufin kin sami yarinyar ne domin ta fasa auren shi?" Inji Primer minister,
"A'a wallahi sharrin yarinyar ce kawai."
"Ammyn sharrin Munari kika ce? Bayan barazanar zaki kashe iyayenta meye na tsare miki da zafi ne haka?" Ya fada a mugun raunane.
  Dakatar dashi Primer minister yayi yana kallon shi, kafin tace mata.
"Ina jinki ko na kira a kawo min Hanan da Karime ne? Na saka a kira Uwani ne?"
"A'a Alhaji nayi domin yarinyar bata dace da Mohan ba, kuma ai yar matsiyata ce. Babu karya a cikin shi, waye ke daukar nauyin su banda shi." Yadda take maganar da kwarin gwiwar ta, san zata aikata dan haka ya kalli Mohan.
"Ka rabu da Maimunari, ka zauna da wanda Uwarka zata baka, Ni kuma zan yiwa Maimunari mijin ban mamaki." A firgice ya mike tare da dafe kirjin shi, sai zuɓewa yayi a kasa.
 Duk soyayyar da yake yiwa Mohan, amma yau yaji aranshi bari yabar shi da uwar shi taji yadda ake rayuwa, dan haka ya tsallake su tana ihu a taimaka mata, ya kuma buga kashedin kar a tab'a mishi motocin gidan shi, Mohan din ya mutu yana da wasu Yaran.
  Ihu da niman taimaka ta gigice, dan haka ta shiga kiran yan uwanta, tana cikin wannan yanayin Hajiyar Hanan ta zo da nata tijarar, ta kuma yi alkawarin sai ta illata Munari da Mohan. Karshe Hajiya Nuratu ta kira Mahaifiyar Khalil, ta gaya mata abinda yake faruwa. Dole ita da mijinta da Khalil suka zo gidan aka kai Mohan Asibiti. Abin tausayi kuka take tana faɗin.
"Don Allah ku taimaka min Yarona ya dawo daidai na amince ya auri Yarinyar indai itace rayuwar shi."
  Dr Khausar da tasan matsalar yayanta kallon mahaifiyar su tayi sannan tace mata.
"Ammyn dama farin cikin shi kika watsar shine har zuciyar shi take niman bugawa? Toh Alhamdulillahi. Ki duba d'anki wallahi ba zan duba shi karshe ki kuma wurga shi cikin tashin hankalin da yafi wannan ba. Kunga ku bar mata D'anta ta kula da lafiyar shi."
 Cak likitocin suka fito, tare da juyawa zasu tafi.
"Zuɓewa tayi akan gwiwar ta, na amince na Yarda, Ku duba shi don Allah wallahi da kaina zan tafi niman auren shi da ita don Allah ku rufa min asiri, na tuba nabi Allah da Manzon Allah. Ku duba min shi."
  "Dr Khausar! Don Allah!" Khalil da Mahaifiyar shi suka masu magana.
  Dakyar aka samu suka amince, tare da shiga cikin dakin, suka fara aikin su. Har kusan asuba suna tsaye kafin suka fito, zama Khausar tayi tare da fashewa da kuka. Dukkan su tunanin su ya Mutu ne, dan haka Hajiya Lateefah ta zauna dirshan ta fashe da wani irin kuka, tana kuma kara kuka. Shiga dakin Khalil yayi ya hango shi da wasu karafa, kirjin shi yana sama da kasa. Sai na'urar da suke aiki akan shi. Duk karfin zuciyar shi sai da kwalla ya zubo mishi, wani irin soyayya sukewa junan su haka, wata irin kauna ce haka.
  Soyayyar gaskiya ce, soyayyar gaskiya sukewa junan su, shi yasa kome nasu yake tafiya iri daya, rayuwar su ce ta banbanta amma kaddarata su tafiyarta daya ce.
"Ya mutu ne?"
"A'a, Umma sai dai a koda yaushe zai iya mutuwa, domin zuciyar shi tayi wani irin laushi har ta tsage, saboda kumburin da tayi lokaci guda. Idan ya cigaba da kasancewa a haka bakin ciki zasu iya masara rayuwar shi, ina ga gwara Ammyn tayi mishi fatan ya mutu kawai domin mutuwar zata iya zame mishi hutu ne a gare shi."
   Bayansu yi sallah asuba, Khalil da Hajiya Latifah, suka wuce Damagaram....
***
Ina barin gurin Mohan, gida na dawo na hada kayana ina son jin dumin Innata, dan haka na wuce Damagaram. Kome dare alƙawari ne a jikinta zan kwana, dan haka tafiyar dare muka yi bamu iso ba, sai karfe goma sha biyu na dare, dan haka na biya motar ya sauke ni har kofar gidan mu, sanan na buga kofar sosai, Baba yazo ya bude min.
"Maimunari kece a daren nan?"
"Eh Baba nice"
Amsar kayana yayi ya wuce dashi cikin gida, ni kuma na rufe gidan. Nabi bayan shi,
Har dakin Innah tana barci na shiga, a hankali na cire takalmi na, na haura bayan ta na kwanta tare da rungume ta.
"Waye ya gaya miki ban san kina kusa ba, kwanta ki huta."
"Banyi salollina bane."
"Tashi muje."
Haka ta raka ni nayi alola nazo na gabatar da sallar da suke kaina, sannan na kwanta a bayan ta, sai lokacin na fashe da kuka, na shiga bata labarin abinda ya faru.
   Shafa bayana take tana faɗin.
"Kwanta kiyi barci, ai kina son Mohan, yawan rikicin ku karfin soyayyar ku, yawan makiyan ku. Kafuwar kaunarku. Karki damu Insha Allah. Ubangiji zai daidaita ku kinji."
Koda na fara barci mafarkin Mohan nake a cikin mawuyacin hali, yana mika min hannun. Amma naki tare da juya mishi baya. Sai da wasu mutane suka zo tare da kama hannun shi suka saka a nawa.
Abu daya nayi ta nanatawa,.karshe barcin da ya ishe ni tashi nayi na Innah ta rakani nayi alola kuma, na gabatar da sallah nafilla, har asuba ni da Innah muna kan abin Sallah.
Wayata ce tayi kara na dauka.
"Abie ina kwana?"
"Lafiya lau. Ya kike?"
"Alhamdulillahi! Yau zaki shigo da wuri ne?"
"Kayya Abie gani a jikin Innata sai wata sati zan dawo, na tattara wasu bayanan na kai makaranta, tunda sati biyu zamu gama"
  "Toh babu damuwa ki gaida min Innarki da baban ki"
"Zasu ji Insha Allah" katse wayar yayi, nan nake bawa Innah labarin Abie, da irin taimakon da yake min...
"Allah ya saka mishi da Alkhairi"
  **
"Karka Kuskura ka bita zuwa Damagaram, wallahi fushina a ya haura kanka, kuma kika sake kika taka damagaram a bakin aurenki billahi azim. Shi kuma idan zai iya ya tashi domin rayuwa sai da faffutikar. Kaunar da Uwar shi take mishi ne, dan haka ya kwanta a gurin"
    "Abbu!" D'aga mishi hannu yayi tare da wuccewa, ya shiga motar shi, har zasu tafi yace a dakata.
Tare da bude kofar motar yace.
"Uwar me kake da ba zaku tawo aiki ba, wallahi idan ban ji labarin ka tafi aiki ba, sai na kore ku daga kai har shi din."
Sannan ya rufe kofar suka yi tafiyar su, haka Khalil ya koma gida ya nufi office din shi, kai Abbu ma bai da kirki, domin kuwa haka yayi ta sawa ana duba mishi ko Khalil yana nan.
Bayan ya gama abinda zai yi. Babban Aminin shi Professor Ibrahim Dan Ba'are, ne a gaban shi. Yana sosa kai.
"Jiya da na ritsa Khalil ya gaya min yarinyar da yake waya da ita har biyun dare, bai boye min ba ya gidan Marigayi Dr Khalid ce, dan haka na yi kokarin na bincika sai na samu yarinyar karama ce, shekaru shatakwas. Amma ina niman alfarma ka barni na nimawa Mohan auren Maimunari,.kayi hakuri tayi laifi ta tuba, kai kuma ka nimawa danka yarinyar can don Allah. Mun girma da yanzun ba da bane, da ake ganiyar samartaka. A duba Yanzun yaran Khausar uku. Yaran Muslima hudu(Kanwar Khalil tana zaune a Saudiya mijinta dan jakadar Nijar ne a Saudiya, daga ita har mijin Likitoci ne, domin tare suka taso da Khausar tare aka musu aure.. mijinta mai suna Miqdad....
*Yau kam babu three pages biyu ne Insha Allah... Masu cewa ko minti biyar basu yi page ya kare Sannun ku🤣🤷ðŸÂ¼â€Â♀ï¸Â�? 🙄 wato jiya dan dad'i har da cewa kuna jiran gud 9tyðŸ˜Â😒☹ï¸Â🤨 Toh indai ana son haka a fito a nuna min kaunar da ake fadan nan ta hanyar sayan book din Kishi a tsakanin zubda jini idan ba haka ba zan iya kiran Kaunar da Fake na karya ce 🙋ðŸÂ¾â€Â♂�? dari uku 300�? ne babu tsada sai Chakwakiyya 🤦ðŸÂ¼â€Â♀�? Hajiya naji alart ga Number na nan0472282105 Ramlat abdulrahman manga GT bank a Turo min shaidan ta nan 08130269641 idan da gaske ana yina naga truelove dinku ta nan 🤷ðŸÂ¼â€Â♀ï¸Â😒�?*
#Mai_Dambu
8/19/21, 6:54 PM - My Mtn Number: https://www.wattpad.com/1113306431?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=MylozxK1LL0LZmGH%2BFlqDRo0TQ1Q9yGEG9nFFLmRkE9c1Tezw88rwfc5nN0EYZgvek%2BtvlgPbqgF8xcCF0NBZoEs3rVxEEf5He91kHbbcO253bO6iKoETacuVt1pplyW
ðŸÂ‚ðŸÂ‚BOROROJI🫀🫀
~The Journey of DestinyðŸ’â€~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.