Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 32 of 64
BABI NA TALATIN DA TAKWAS.
"Hammah" hannun shi ya kai kan bakina, tare da lumshe idanun shi. Yana jin cikar kwalla a kwayar idanun shi.
"Ki daina firgita ni, tsorata ni kike. Kina razana ni matukar tsoro nake ji, idan har akwai abinda zaki fada min ya bani tsoro kalmar mutuwa zaki yi! Kina son nayi kuka ne?" Girgiza mishi kai nayi sannan ya shafa gashin gaban goshina yana faÉ—in.
"Masha Allah good Girl, karki kuma fadar haka ina son ganin ki cikin farin ciki."
     Hannuna na zagaye a jikin shi ina jin wani irin yanayi, tare da saukar kwalla daga idanuna.
"Hammah je t'aime" (wato i love You, ina sonka da France)
"Moi aussi Moonah!" (Me too Moonah, nima haka)
"Zan iya samun damar shiga kowani hali amma idan na tuna da ƙaddara ta sai naji kamar ban dace da kai ba, Hammah kai ne kawai kasan yadda nake ji, Hammah kirjina zafi. Hammah zan yi sallah nayi wanka. Ina son ka fitar dani yawo"
Mikewa yayi tare da duba wayar shi, ya nemi Number Khausar, suka yi magana can sai gata da wasu Nurse biyu, ina jingine da jikin shi, suka shigo.
"Matar Hammah Mohan, ko zaki tashi su rike ki." D'ago kai nayi ina kallonta, kafin na maida na rufe idanuna.
"Hammah na zai kai ni ban daki idan yaso sai su min wankan" kallon shi tayi tana kallon Moonah da take kara kifa kanta a kirjin shi. Alama yayi mata da hannun, suka fita da kanshi ya kai ni ban daki. Zai fita na rike hannun shi.
" Ka tayani warware gashin nan yana tsami."
   A hankali ya zauna ya warware min gashin sannan ya fara wanke min a hankali. Na tuna lokacin da Innata take wanke min gashin har ruwan kanwa take zuba min, domin ya karkarye yadda ba za a fahimci mace ce ni ba, yau gashi ana wanke min shi. Buga kofar aka yi yayi gyaran murya. Gashin ba wai ya fita bane, amma ganin yadda suka uzura ya fito ya sani koran shi, suka samu kan yake wanke min, taimaka min suka yi na yi wanka bayan gama suka bani towel na rufe kaina, muka fito waje na samu har sun fita. Doguwar riga na saka, sannan na kalli inda suka ajiye min abin sallah, sallah nayi musamman wanda na sani, Hammah na shigowa ina sallama.
"Kwana nawa nayi ina kwance?"
"Kwana uku da wunin yau hudu.". Dama nayi na jiya da yau. kawai na kawo kwanakin da ban yi su ba, tare da niman gafaran Ubangiji, sannan na shiga addu'a Allah ya bayyana min iyayena idan suna raye, idan sun mutu kuma ya jikan su, idan na mu tazo ta kyautatta tamu bayan su.
  Ina cikin addu'o'in kuka ya kwace min domin sai lokacin nake jin kome yana zuwa min, haka na zauna na cusa kaina a cikin cinyoyina, zama yayi a taburman yana kallona, sai da na gama kukan ya mika min ruwan sanyi na karba hannuna yana rawa, sha nayi sannan na kalle shi.
"Ya isa haka! An jima zamu tafi yin hoton zuciyar ki, sabida kin fara tarin jini kuma ba son haka yana da illah." Ajiye kofin nayi sannan na ce mishi.
"Toh"
Abinci ya diba min da ruwan tea, na fara sha, ina amsar abincin yana kuma bani labarun ban dariya, sai dariya nake, muna gamawa na kwantar da kaina a kafad'ar shi, ina sauke ajiyar zuciya. Shafa hannun yayi yana jin kamar ya boye ni a kirjin shi.
    Bubbuga bayana yaƙe yana bani labarin ban dariya, wani nayi shiru, wani nayi dariya haka dai har yanzu lokacin da aka ce mu shirya a min hoton, shi da kan shi ya kai ni, yana rike da hannuna, har inda za yi hoton. Duk da mun sami mutane. Ganin mu da Dr Khausar yasa aka ce mu shiga kasancewar an san yar Shugaban kasa ce kuma bata damu da matsayin Ubanta ba, tana aikin ta. Uwa uba an san waye mijinta, haka bai saka ta jin wata ce ita, bayan mun gama muka fito, ina jingine a jikin shi.
      Kwana na bakwai aka sallame ni, gidan Khausar ya kai ni, na zauna na kara jin dadin jikina. Sannan ya kawo min kome da yayi min har da wani apartment na shi da yake cikin gari, koda muka je apartment din yayi min kyau, ya shirya kome a cikin gidan, juyawa nayi tare da kallon shi.
"Duk nawa ne?"
Lumshe idanun shi yayi sannan ya bude min, dariya nayi domin haka ya sani farin ciki.
"Hammah Nagode"
"Tu mérites mieux" (you deserve more, kin cancanci hakan) Kamar wacce aka samin battery, haka nayi ta mazari a gaban shi, kafin ya tako gaba, ya rungume ni. Murmushi nayi domin abinda nake son yi ne, na kasa shi kuma mutum ne da yake saurin d'ago ka.
"Bana tunanin banza a kanki, sabida ke Uwar Yarana ce, kullum burina taya zan mallake ki, taya zan samu nutsuwa idan na mallake ki, dan haka bani tab'a saka tunanin wani abinki a raina, ke nake so ba kayan jikinki ba. Ko kin manta ke mata maza ce" mintsinin shi nayi ina me ture shi.
"Auchewww, yarinyar nan kin zama kura wannan mintsin fa? Gaskiya sai na rama," fara zagaye falon muke ina dariya, yana bina ina zille mishi. Kafin na gaji na zube a saman sofa ina ajiyar zuciya.
   "Beauty! Zaki fara aiki a babban Kotun koli na kasar nan, ni dai don Allah ki rufawa zuciyata asiri domin na ganki da wani wallahi." Hannuna na kai bakin shi ina kallon kwayar idanun shi.
"Insha Allah babu abinda zai faru, ina tare da kai ne saboda ina raye, idan babu kai tabbas ni matacciya ce, ba zan tsallake dokarka ba"Â hannun shi ya daura a kafadana yana kallon yadda nake, tab'e baki. Goshina ya sumbata. Tare da shafa bakina yana faÉ—in.
"Insha Allah ina nan zuwa kan ku"
Dukar kirjin shi nayi ina dariya.
"Hammah Allah ya yaye maka," na fada ina dariya, kitchen ya nuna min, ba laifi kome gidan yayi min, gyada kai nake ina dariya sannan nace mishi.
"Amma gaskiya gidan yayi kyau amma yayi min girma, ko zaka iya nima min roommate" jan hancina yayi yana faÉ—in..
"A yadda duniya ta lalace salon na dauko miki yar iska ta lalata min ke? Tab ba dani ba.". Rike hannun rigar shi nayi ina kallon shi.
"Don Allah fa" na fada kamar zan yi kuka.
"Wallahi Maimoon ki fita idona, babu wanda zan kawo miki ku zauna tare, gidan bai miki bane na sauya miki?"
"Hammah yayi min, amma idan da wani a kusa dani, zan ji dadi da nutsuwa ace babu kowa a cikin gidan, sannan ka duba da kyau bani da lafiya zuciya ta tana ciwo idan ciwon ya tashi waye zai taimaka min kafin wani ya sani? Amma tunda kace ga yadda kake so haka za ayi" na fada a hankali.
"Shikenan, zan duba miki koda dattijuwa ce"
Washe bakina nayi ina kallon shi.
"Nagode sosai" sumbatar goshina yayi yana faÉ—in.
"Tant pis" (wato Never mind, karki damu" haka ya shiga kitchen tare da daura afro, ina kallon shi, ya ciro kaza a frij. Yana kallona yana murmushi ya shiga aikin shi,
  Bayan awa daya zuwa biyu, ya kammala girkin, sai had'iye yawun nake, ina lashe bakina.
"Hammah Abincin nan zai yi dad'i wallahi."
"Gashi ba zan iya bawa mai kwadayi ba"
"Ayya Hammah na, dan sammin dan kadan mana?" Na mika mishi flet, saka ludayi yayi a miyar ya dangwalo miyar ya saka min a saman flet É—in. Yana murmushi.
"Hammah na, wannan ba halin mutanen kirki bane, samin don Allah wallahi yawuna ya gama tsinkewa."
"Toh daure shi tunda ya tsinke" ya faÉ—a yana murmushin jin dadi.
"Kayi hakuri kaji, ka ciyar dani kamar yadda tantabara yake ciyar da matar shi." Na fada ina wani tsuma,
Takowa yayi yana kallon cikin idanuna, kafin ya dauki flet din.
"Zan ciyar dake sama da yadda tantabara yake ciyar da iyalin shi, zan gina miki sheka kamar yadda tantabara yake gina shekar matar shi, zan kula da ke kamar yadda tantabara yake kula da matar shi, ki yarda dani a Duk lokacin da ƙaddara ta shigo mana kiyi min kyakyawan Fahimta, ki yarda dani, kiyi min adalci. Ki Fahimce ni, karki yarda shaidan da shaidanun mutane da aljanun su rabamu. Kin ji" gyada mishi kai nayi ina jin kwalla na zubo min. Share kwallar nai ina kallon shi. Amsar flet din yayi ya zuba min macaroni da miyar kazar, zuba min ya dauko ruwa ya ajiye min, sannan ya ciyar dani da hannun shi. Ina koshi na dauki cokalin zan fara bashi ya amsa, tare da cewa.
"Babu ruwanki dani," haka ya zubo na shi ina kallon shi yaci ya koshi sannan ya shiga min hira, kafin yaja hannuna zuwa ban daki yace min.
"Kiyi alola zan tafi masalaci, gidan nan akwai mutane masu haya, kasan shi shaguna ne, sai kuma ko kula da kanki akwai babban falo inda ake hira, ban da shiga harkan kowa. Babu ruwanki da su, kowa yayi harkan gaban shi. Ban hana gaisuwa ki Barka ba, kece kawai bana son ana shigo miki, kuma ban ce ki shigar musu ba, halin dan Adam da wuya karki shiga su sa miki damuwa."
"Insha Allah" na fada ina kallon shi, ban daki na shiga ya fita. Sai da nayi wanka da alola sannan na fito ina kallon yadda aka gyara min dakin, a hankali na taka na bude wardrob din da na gani a d'akin. Ikon Allah, gefen dogayen riguna daban, gefen riga da zani dabam sai riga da skirt, sai kananun kaya, masu kyau da inganci. Daukar doguwar riga na saka, tare da wata hijab a naga gefen su daban, abin sallah na dauka na gabatar da sallah azhar.
 Sannan na shiga addu'o'in, ina idarwa na sha magani, kafin na kwanta. Ina nazarin abinda ya hana shi dawowa.
***
A can kuwa fadar shugaban kasa, jarida aka buga shafin Farko hoton Hammah Mohan da Maimunari, abin mamaki magana dai masu matukar zafi aka rubuta.
*SHIN ME ZAMU CE DANGANE DA MAJOR GENERAL MOHAN MAMMAN NASIR? ITA WANNAN WACECE MISHI DA YA KE RIKE DA ITA? SHIN ME YA HANA SHI AURE YANA RAYUWAR DA TAYI MISHI*
A cikin shafi na biyar na jaridar aka sake saka hoton shi da na Maimunari, wanda suka yi a Dubai tana sanye da kananun kaya musamman ranar da suka shiga club É—in nan.
'''AN CE MANA BAI DA LAFIYA ASHE MUTUM KAWAI WATSEWAR SHI YAKE ABIN SHI TOH ITA YARINYAR YAR WAYE? KUMA IYAYEN TA SUMA SUNA INA?'''
Kallon su Primer minister yayi yana faÉ—in..
"Allah ya kyauta, amma ban ga abin yayatawa ba, sannan kuma ministen labarai zamu tuntubar da wannan abun tunda."
Shiru yayi sannan ya kuma kallon su yace musu.
"Ku bar zance kawai, Allah ya rufa asiri." Daga haka ya sallame su. Kiran Mohan yayi, can kuwa sai gashi. Zama yayi bayan ya gaishe shi. Tura mishi hoton yayi.
Murmushi yayi sannan yace mishi.
"Abbu hoton yayi kyau sosai, wannan ne banji dadin ganin shi ba, kuma ban san me zance ba, amma itace Almamoon da tayi jinyata." Ya fada yana sunkuyar da kan shi.
"Kana Sonta ne?" Da sauri ya d'ago kan shi.
"Eh Abbuna"
"Haddir da Salman sun min magana, sai Khausar itama tayi min magana akan na tausassan Mahaifiyar ku, akan ka. Insha Allah zan yi yadda ya dace." Shiru yayi tare da jan fasali kafin ya cigaba da cewa.
"Ita Hanan fa?"
"Insha Allah zan ji da kome"
   "Allah yayi muku albarka."
"Amin Ya Allah, Abbu!" Sannan ya fita.
*
Yana fita ofishin Baban shi, wayar Hajiya lateefa na shigo mishi, cikin diriricewa ya dauka.
"Ina son ganinka."
"Toh Ammyn"
A rikice ya nufi gidan, kai jama'a. Ruwan bala'i ya sha na masifa, haka ya zuba tagumi kafin ya ninke ta baibai.
"Wallahi Ammyn ni da dud duniya bani da masoyi ya irin Hanan. Daga yau dan na fita da ita har sai anyi baikon mu, ya ga Yar dangi xan kula bare. Ina yar dangina nake so"
Anan ya cinye ta da baki, yayi ta rarrashinta, sannan ya mike zai tafi tace mishi.
"Abincin ka fa"
"Ammyn a kawo min part dina."
  **
Tun ina saka ran ganin shi, har na cire rai, washi gari sai ga drive yazo ya kai ni babban kotun kasar, anan nayi kome. Sannan na gama zan tafi naga sunan jikin Katsina MAIMUNARI I UMAR WODAADABE, shiru nayi kafin na sake murmushi, sannan na fara gabatar da abinda ya kawo ni.
  "Don Allah nace ba?" D'ago kai tayi sannan tace min.
"Ina jinki"
"Suna na Maimunari I Umar wodaadabe."
Murmushi tayi sannan tace min .
"Rukayya Husain Adam, auta."
Mika mata hannu nayi sannan ta mika min nata.
"Ofishin justice aka turani, kuma Ni bakuwa ce"
Mikewa tayi zata rakani. "Ok tun wancan satin na fara aiki anan nuna turo ni aka yi daga Agadaz, muje na nuna miki"
"Yan mata ji mana? Ina niman barista Maimunari" ya fada daga bayana.
"Karki kula shi muje niman magana yake."
"Kinga kawar mu, ki kulani indai da gaske ne" juyawa nayi a fusace, katon teddy bear na gani, dai dai misali a hannun shi.
"Sorry" ya fada min, dauke kai nayi ina kallon shi.
"Fiancée dinki ne?"
"Kyale shi karki kula shi"
"Kiyi hakuri kin sha magani? Kin karya?"
Amsar dolin nayi tare da maka mishi ina kuka.
"Kasan yadda zuciyata ta kwana da son sanin wani hali kake? Ko kirana baka yi ba, ban sani ba karka kuma zuwa nan dube shi katon mutum kawai, muje Kinji Kawata."
"Lallai kaci duka gobe maka kara."
"Toh duk wannan fushin name? Da bance zan yi sabuwar budurwa ba" cak na tsaya, tare da juyawa na kalle shi, kamar na rufe shi da dukka, haka na share shi. Bin bayan mu yayi. Har ofishin alkali, muna zuwa muka samu masijan shi, ya shiga ya gaya mishi. Kafin mu shiga Hammah Mohan ya tare kofar, tare da shiga cikin Office din ya rufe, yana ta rubutu. Jan kujeran yayi tare da zama, sannan ya cigaba da kallon shi.
"Mai girma alkali!" D'ago manyan idanun shi yayi tare da kallon shi. Yana son tuna inda yasan fuskar shi amma ya manta,
"Suna na Mohan Mamman Nasir Aghali, yarinya ta zata zo sanin makamar aiki, toh naji ance baka tab'a aure bane, shine nazo da kaina muyi magana daya, yarinyar a karkashin da'irata take, kai kuma a karkashin da'iran mahaifina kake, ban san yadda zaka dauki batuna ba, amma tabbas zan iya kome akan Beauty. Dan haka zata shigo ayi kome cikin mutunttaka, ba sai na gaya maka ina haukar sonta ba, amma toh gargadi ne ba Shawara ba." Ya fada bayan ya mike tare da bude kofar, shigowa tayi bayan ta, buga mishi dolin tana faɗin.
"Kayi min laifi amma haka bai saka ka fahimtar yadda nake ji ba, me yasa jiya baka dawo ba, kasa barci nayi fa. Har sai da nasha magani!" Bude min hannun shi nayi.
"Hammah na, ina sonka karka manta dani, idan baso kake na mutu ba......
#Mai_Dambu
8/19/21, 6:53 PM - My Mtn Number: https://www.wattpad.com/1109846382?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=5APA6mJ8v7GgHSCkDwtNb1XXK%2BVFjYD5JoQuwsUbL%2BoIhl%2B1ELBymj3sVefZSm9hx7T5VudtIwohWKCgDupKfRkENVHC3lkDkAPKgEM%2Fi1YU6rlaxusjnrm2Wbfeg0Md
ðŸ‚ðŸ‚BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
_Merci beaucoup, surtout mes compatriotes nigérs qui parlent français. Merci. Merci. Incha Allah. Nagode sosai â¤ï¸ðŸ˜ðŸ’“😘ðŸ‘_
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.