Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 13 of 64
BABI NA SHA TARA.
Da mugun gudu na danne kofar, tare da sake wata irin kara, me had'e da kuka.
"Ashhhhhh! Ohhhh Auwshhhhhhh" ya faɗa tare da banging kofar, sai da na kuma faduwa, ashe na rufe da hannun shi ne, ina jin ya bar jikin kofar na koma ban dakin na dauko kayana, na saka kafin na fito da sauri. Yana zaune tare da zubawa hannun idanu, zuɓewa nayi akan gwiwa ta, na sake wani irin kuka tare da jin nadamar me yasa na matse mishi hannu, riko hannun nayi tare da sakawa a bakina ina tsotsa su, can na kuma mik'ewa zuwa kitchen na dauko kankara na saka a cikin towel na nad'e shi sannan na shiga matse mishi hannun. Duk abinda nake idanun shi kumshe bai bude ba, sai leka fuskar nake jijjiyar goshinsa sun mike sosai.
Mik'ewa nayi ina kallon shi kafin na shiga inda first aid box yake na dauko na mishi dress din hannun sannan na koma na shiga duba hannun.
"Kayi Hakuri" sai lokacin ya bude idanun shi tarr akai na.
"Kayi hakuri kaji"
Lumshe dara daran idanun yayi, tare da gyara kwanciyar shi, haka nayi ta kula da hannun a binka da farin fata sai gashi gurin yayi jajjur bayan ya kumbura, shafa mishi man zafi zanyi yayi maza ya rike hannuna. Idanun shi har lokacin bai bude ba. Sai tauna bakin shi yake tare da lumshe idanun shi duk da a rufe suke, amma haka bai hana shi yin yadda zan Fahimci yana jin matsanancin zafi ba.
  "Kayi hakuri ka ji, nasan da zafi amma haka shine mafita domin zaka ji dadin hannun" a Sannun a hankali yake zare hannun, tare da kauda kanshi yana me jin kamar ya kurma ihu, domin shi kad'ai yasan yadda yake ji.
Shigowar Hammah Malik yaga halin da muke ciki.
"Subhanallahi taya haka ya faru"
"Eh wallahi garin garin garin" nayi ta maimaitawa sabida wani irin kallon da yayi min wanda ya sani jin saura kiris fitsari ya zubo a wandona, kai ban tab'a ganin mugun kallo irin na yau ba. Sannan ya juya ga Malik, ya zuba mishi ido. Shima kuma kamar mara gaskiya shan jinin jikin shi yayi tare da cewa.
"Sir ko zamu kai ka asibiti ne?"
"Ok bari na kawo mishi jacket din shi ya daura akan kayan zai fi kyau kam a kai shi asibitin."
 Â
    Da sauri na haura sama na dauko mishi rigar Black yayi mishi kyau sosai, ga gashin nan irinta buzayen asali ta wani nad'e akan shi, ba zaka tab'a kallon fuskar shi ka dauka bai da lafiya ba. Saboda kullum cike yake da kwarjini da kamala, haka muka nufi asibitin domin yaki bin Malik sai da nace mishi.
"Toh muje"
Haka ya saka kai ya biyo mu, baki daya ina walwala ne amma bani da nutsuwa domin kuwa ina tsoron malam Ansar sosai,haka aka gama duba mishi hannun shi, sannan muka dawo gida.
  Zuwa dare sabon zazzaɓi ya rufe mu dukkan mu, dakyar na shiga dakin shi tare da taimaka mishi yayi wanka, amma yana fitowa yanki jiki ya fadi, gashi tikeke, haka nayi ta jan shi.
"Ko zan kira Hammah Malik ne baka da lafiya" lumshe min idanu yayi yana kallon yadda nake son kuka nima zazzaɓi nake ji. A hankali ya dafe jikin gadon tare da rike Ni da karfi sai da na kusan faduwa, sannan ya mike dakyar ya faɗa gadon, tare da fisgo ni jikin shi. Hakoran shi suna haduwa da juna.
        A hankali na saka kafana na janyo bargon na lullube shi, sannan na gyara kwanciyar shi, kafin na fara ƙoƙarin zamewa a jikin shi, wasu irin kananun surutai yake tare da faɗin.
"Zasu harbe ni, karka bari su same mi."
Ya fada tare da matse ni a jikin shi, yana ƙoƙarin boye fuskar shi a jikina, tsoron kar ya cutar dani ya sani fara mishi addu'o'in, can naji yana sauke ajiyar zuciyar, sai barci me mugun karfi ya tafi dashi. A hankali na gyara mishi kwanciyar shi, kafin na fara ƙoƙarin saukowa a gadon ya rike hannuna, haka na dawo na kwanta a gaban gadon, hannun shi cikin nawa, haka nima barcin ya dauke ni.
  -.02:30am farkawa yayi yaji hannun shi da na Almamoon a sarkafe da juna, a hankali ya zare nashi tare da mik'ewa ya nufi ban daki yayi alola sannan yazo ya gabatar da sallah da yake kanshi, zama yayi yana addu'o'in wanda duk kusan rabin shi kuka yake hannun shi a sama, bayan ya idar yaji Almamoon yana nishi a hankali a hankali. Tare da kuka yana surutu shima. mik'ewa yayi tare da nad'e abin sallah.
  Yana ajiyewa ya nufi gaban gadon, a hankali ya durkusa zai dauke shi, bakin Almamoon ya sauka akan kuncin Mohan, tare da sauke mishi wani irin nishi me tab'a jiki da jini, sabar shi yaji sama yana kallon fuskar shi, musamman yadda ya daura kanshi a daidai kahon zuciyar shi, wannan ne first time da ya tab'a ɗaukar wani a hannun shi. Ko mace bai tab'a rikewa ba indai ba jarirai bane.
  A hankali ya haura gadon ya kwantar dashi, yana me gyara mishi kwanciyar shi,,.bayan ya ja mishi bargon shi, ya zo zai dai fuskar shi zai gyara mishi kwanciyar shi musamman wuyar shi da ya kwanta a karkace, sai ji yayi Almamoon ya kuma damke wuyar shi.
  A hankali ya kwace rikon ya gyara mishi kwanciyar shi ya fita daga dakin yana mamakin meye ya kawo mishi wani jikin shi? Yasan ya samu lafiya amma baya son koda wani a cikin gidan ya san lafiyar shi lau. A hankali yake takawa cikin wata irin kasalalliyar yanayi, ya fita daga dakin ya nufi dakin shi, ya zauna tare da dafe goshinsa yana jinjina karfin k'iyayyar da Hajiya Safeeya take mishi meye yayi mata da zafi haka? Ba dan Almamoon din ya zubda maganin ba tabbas da wani mara imanin ne zuba mishi maganin zai yi, meye ya tsarewa mutane da suke burin su kashe shi? A iya sanin shi dai bai da matsala da kowa amma meye ya kawo haka?
 Akwai dalilin da yasa Almamoon yazo ina Khalil da Malik? Amma ko yau kwana biyu yasan Khalil ya tafi amma zaman me yake a cikin gidan nan da yayi shi domin ya kawo matar shi gidan, wato wacce zata zama mallakin shi.
 ***
Tun da asuba na tashi jikina babu dad'i, dan haka na sauka a gadon na shiga ban daki ina mamakin taya aka yi na dawo sama gadon ni da na ke kwance a kasa. Lumshe idanuna nayi bayan nayi alola zan yi sallah ya shigo. Shima ina ga alolan yayi yazo tadda ni.
   Kallon yayi na wani lokaci kafin ya juya ya fita, rufe kofar nayi na gabatar da sallar, ina idarwa na mike tare da nufar kitchen na mana abun karyawa, ina gamawa na kawo zan ajiye, na hango shi zaune ya daura dogayen kafaffun shi a saman hadaddiyar center table din falon yana kallo.
"Hammah ina kwana?" Na dai fada ne amma ban sani ba ko zai amsa,
Bai kalle ni ba ya cigaba da abinda yake, mik'ewa nayi na nufi gurin shi da abincin, ya kawar da kanshi, Cigaba nayi da tsayuwa.
"Ga abincin ka ni tafiya makaranta zanyi" na fada ina tura mishi baki..share ni yayi ya cigaba da kallon shi.
"Wai ma waye ya kunna maka tv? Bana ce kayi ta kallon Tashoshin musulunci bane, na kuma ganin ka kunna labarai sai na cire kunnen ka" na fada ina zare mishi ido. Kallon Yaron yayi daga sama har ƙasa.
*Wannan Yaron akwai karfin hali!*
Ya fada tare da mik'ewa yana me nufar hanyar table din, sake baki nayi tare da nufar shi da abincin.
  "Ina wasa da kai ne? Wato zaka mai dani karamin mutum na kawo maka abincin ka taso ka bar ni dashi" na fada da karfi ina zare mishi ido sannan na cigaba da cewa.
"Sai na gayawa Hammah Khalil dan na lura kafu shakkar shi, tunda ka rena ni"
*Kan Uba! Wato Dan Ba'are ya gaya mishi ina shakkar shi kenan dan Uban shi? Lallai zan ci kaniyar ku daga kai har dan Ba'aren*Â ya faÉ—a tare da bin Almamoon da wani mugun kallo kasa kasa.
  "Maza dauki cokali kaci abinci." Na fada a ikonce, irin nice gaba da shi.
*Wai Ni dan abun nan yake min ihu? Abinda bai fi nayi loma daya da shi ba! Zan kama dan Ba'are sai naci Uban shi dan banza mara mutunci*
Babu musu ya dauka ya fara ci yana kallon fuskana, tari ya fara na bashi ruwa ya sha, sannan nima na dibe nawa na dawo falon ina ci, kad'an yaci sanan ina gamawa na nufi hanyar kitchen na ajiye kayan, a gurguje na gyara gidan, sannan na tawo tare da rike hannunshi muka haura sama, na bashi magani da addu'o'in da nake tofa mishi. Dakyar yasha yana niman kwara min amai.
       Ko ta kanshi ban bi ba, na dauki jakata na fita ina me shafa sumar kanshi na fita da sauri. Sabida na kusan makara.
  Lokacin da na iso makaranta, an kusan shiga aji dan haka ina isa bakin kofar shiga naga dalibai sun tsare hanyar.
"Lafiya kuka tsaya a tsatsaye kamar mama maza?" Na tambaye su ina nufar hanyar shiga aji..
"Ai har kai Almamoon malam Ansar zai nemi ya taimaka maka ka saka a mishi dukar kawo wuka?"
"Haka ya gaya muku?" Kallona suka yi tare da cewa.
"Idan na haka ba toh meye kayi mishi?"
"Tunda ku nan uwayen shi ne me zai hana ku rama mishi" ban tab'a zata zasu iya duka na ba, amma dai gashi sun rufe Ni da mugun duka.
   Dakyar aka kwace Ni na sha mugun bugu, kasa zama nayi domin abokan malam Ansar sun goyi bayan daliban, dan haka aka kore ni zuwa gida, kuka yana cina amma kuma na kasa yi,tafiya nake kamar wanda kwai ya fashe mishi a cikin shi. Ina isa bakin get na samu motar haya, ya kai ni gida, ina isa bakin get din farko aka dauke ni a wani motar zuwa cikin gidan, ina shiga gidan na hango shi yana tsaye ya zubawa dabbobin shi ido hannun shi a cikin aljuhun farin jeans din shi na kamfanin Next, sai bakar riga me kyau me dogon hannu, ya daura wata mara nauyi akan rigar cikin fari tass na saman.
   Hadaddiyar gashin kan shi ya dauka har keyar shi,
    Kwalla ne ya shiga zuba min ina jin kirjina yana bugawa da mugun gudu. Na shagala da kallon shi kwalla na zuba min.
   Yayi nisa gurin tunanin yanayin da ya tsinci kanshi, da yadda yake rayuwa babu lekowar iyaye. Lumshe idanun shi yayi lokacin da yaji kamar ana kallon shi, a hankali ya juyo tare da kallon yadda yake tsaye kamar an dasa shi a gurin. Takowa yayi har inda yake ya hango Bakin Almamoon a fashe. Kura mata ido yayi tare da kasa motsi sakamakon tawowa da Almamoon yaji ya wani rungumo shi yana kuka kamar ranshi zai fita.
"Hammah Mohan, don Allah ka mai dani ni gurin Innata, bata tab'a duka na ba, amma sabida malam Ansar na sha dukka sau biyu."
Na fada ina kuka tare da jin ko ina na jikina yana ciwo, janye ni yayi a hankali yana kallon yadda fuskana ya kumbura, sai jinin da yake fita ta hancina. Ga goshina da ya fashe, cire rigar saman yayi tare da saka min a bayana sabida yadda suka yaga min rigar jikina, ya lullube ni da shi, dake saman rigar ce, rike hannuna yayi tare da wucewa dani cikin gidan.
     Ruwan sanyi ya dauko ya bani na sha, na sauke ajiyar zuciya. Bai magana balle ya ce min nayi hakuri, haka ya zuba min ido, sosai sannan ya mike tare da nufa sama, can sai gashi ya kuma saukowa da kayan first aid box. Duk da hannun shi yana ciwo bai hana shi nutsuwa ya shafa min idean ba, lokacin da ya saka min spirit ne na shiga tsalle ina wash da rike hannun shi.
  "Don Allah ka barni na huta, idan na huta sai ka saka min" na fada ina matsar kwallan, bai saurare ni ba, ya kuma dangwala audugar ya manna min.
"Wayyo Allah na zaka kashe wallahi sai na huta kafin ka kuma saka min wayyo ni wayyo zafi don Allah ka saka min a hankali."
    Kamo ni yayi tare da juyar dani, ya matse ni yadda ba zan iya motsi ba, yana wanke min ciwon ni kuwa sai kuka nake da rikici. Shigowar Malik zai gaya min Ansar ya zo, ya tsaya baki sake yana raba idanun shi akan mu, d'ago kai Hammah Mohan yayi tare da d'aga mishi gira alamar lafiya.
    Cikin wani irin yanayi da ban mamaki ya kame guri guda ya sara mishi tare da cewa.
"Jami'an soja mai lamba C210 mai igiya uku Malik Moussa Abzin yake magana Yallabai"
  Lumshe idanun shi yayi yana jin wani abu yana yawo a jikin shi tun daga tafin kafar shi har tsakiyar kanshi, tsigar jikin shi sai mik'ewa yake, d'ago kai nayi ina kallon fuskar shi wacce take kara fidda wata irin kwarjini. Shagala nayi ina kallon shi.
  Bayana yana jingine da kirjin shi, hannun shi daya yana tsakanin cikina da kirjina, daya hannun shi kuma yana rike da almakashi.
  Jinjina kai yayi tare da kallon Malik irin ina jinka. Nutsuwa Malik yayi a karo na biyu ya fadi abinda ya kawo shi, da sauri na fara ƙoƙarin mik'ewa a jikin shi, kai hatta sunan malam Ansar tsoro yake bani, balle kuma nayi ido biyu da shi.
   Gyada kai yayi alamar ya shigo da shi. Yana makale dani, har lokacin bai barni na mike ba, fuskar nan ta kuma had'ewa shigowa malam Ansar yayi yana dingishi. Tun kafin ya idda sallamar shi kalmar ta makale a wuyar shi yana kallon ikon Allah.
  "Almamoon" ya faɗa a sanyayye, cikin wani azzababben kishi, ya tako da karfi ya manta da ciwon kafar shi, yana zuwa ya tsaya a gaban mu jikin shi yana kerma, kokarin fisgo ni yayi amma ya kasa.
"Tashi ka haura sama" a mugun kidime na juya ina kallon shi, fuskar ku kusan tana gogan juna, hancin shi har yana gogan goshina,  d'ago kai nayi ina kallon bakin da yayi magana, tare da kura mishi ido, ina jin sautin Muryan shi har cikin jinin jikina.
"Nace tashi" kara ware idanuna nayi ina kallon shi bakina cike da mamaki. Can kuma sai gashi ya daure fuskar sama da baya, da sauri na mike na haura sama. Nunawa malam Ansar guri yayi tare da kallon shi.
"Ba zama nazo yi ba, abinda na kawo na zo dauka"
  Cikin renin hankali irin ta namijin duniya yace mishi.
"I thought abinka yana jikinka" ya faÉ—a cikin wani irin isa, kamar ba shi yayi maganar ba.
"Poor" inji Malam Ansar.
Kamar bai ji abinda yace ba, ya kuma Cigaba da kallon yatsun hannun shi.
" Malam ka bani yaron can domin ni na mishi hanyar samun damar zama a cikin ku." Ya fada cikin karaje da fusata.
 Juyawa yayi tare da kallon inda zai ga yaron, bai ga kowa ba. Ya juya tare da tab'e baki yace mishi.
"Ban ga yaron ba, yana ina?" Ya fada yana kallon malam Ansar wanda ya cika kamar an watsa mishi yiest.
A fusace ya mike Mohan ya mike tare da sakala hannun shi dukka biyu a k'ugun shi, suran shi ta zaratan sojoji ta kuma bayyana sama da farko, ya fito giant din shi, ya tsaya a gaban Ansar duk da shima ba kad'an bane amma Mohan ya kere shi.
"Akan me yasa kake cutar da shi bayan kasan kana bukatar shi a tare da kai?"
  Wani irin duba yayiwa Mohan sama da kasa, kafin ya fashe da dariya. Mai karfi sosai sannan yace mishi.
"Ina son shi! Ina kaunar shi! Tun daga lokacin da na fahimci shi mata maza ne, na fara kaunar shi dan haka matsa min a hanya na dauko shi"
  Shiru yayi tare da matsa mishi a hanya ya wuce sama, bai hana shi ba, komawa yayi ya zauna yana tuno abinda ya faru jiya, ok dalilin da ya sa kenan ya datse mishi kofa a hannun? Lashe bakin shi yayi yana kallon yadda zasu kaya.
  Can kuwa sai gashi nan ya fito da Almamoon yana jan shi, shi kuwa sai kuka yake yana faɗin.
"Ni kam ba zan je ba, ka kyale ni"Â na fada mishi ina kuka.
"Ba zan ba zan cigaba da ganin ka cikin suffar maza ba muje idan ka ga gatar da na shirya maka iya ni da kai a duniyar mu sai kasha mamaki."
"Bana son" na fada da karfi ina kwace hannuna.
    Na nufi gurin Hammah Mohan, yana zaune ya aza daya kan daya yana jin mu,. Rike kafar shi nayi ina kuka.
"Don Allah karka bari ya tafi dani". Na fada ina kuka. Malam Ansar yana zuwa ya fisgo ni, tare da d'aga hannu zai mare ni, Ya rike hannun.
"Masoyin gaskiya ba tab'a dukar abinda yake so, manufar ka mai kyau ce, amma dukar ba zai iya canza kome ba. Kai kuma ka bishi ku tafi."
   Ya fada min yana kallon yadda na sake baki, jikina yayi mugun sanyi, haka ya nuna min hanya. Had'iye yawun da ya tsaya min a wuya. Ina kallon shi, na kasa magana, kawai saka kai nayi zan fita.
"Amma irin wannan al'amarin iyayen shi sun sani?" Ya tambaya yana kallon yadda Ansar yake jan hannuna. Cak muka tsaya, wasu irin kwalla ne suke zubo min, a hankali ya mike tare da takowa gaban mu. Ya zare hannun malam Ansar da ya rike hannuna. Sannan ya saka hannun shi ya riko k'uguna.
"Hatta kare idan yana tarayya da shi ba zan tab'a barin shi yayi haushi ba balle kuma shi Yaron ka koyi yadda ake martaba dan adam sai ka dawo na baka shi......
_Barka da Sallah! Na cika muku alkawari.......😘ðŸ˜saura kuma ku nuna min naku alkawarin.... Karku saka rai zaku samu update nan kusa domin sha'anin aikin sallah_
#Mai_Dambu...
8/19/21, 2:23 PM - My Mtn Number: ðŸ‚ðŸ‚BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.