Complete Hausa Novels

Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 62 of 64

BABI NA SABA'IN

*PAGE 70 NA KAMMALA ZANEN QADDARA TA, AMMA WANNAN KAMAR KUN TOFE NI😭🤣*
-----------------------------------------------
*Ina kuke matan alfarma muna da kayan ado da kawa... Musamman turaren kaya wanda zai yi awa ashirin da hudu a jikin kayan ki, muna da scentball wanda ake wurga shi a wardrob sannan muna da Oil mai dan karen kyau da dad'i! Ina uwar gidan ina Amarya, maza garzayo kar a baki labari kayan mu free order! Sannan ina uwaren gida da amare nesa tazo kusa, muna da kayan Mata ingantattun masu kyau, Muna da gumba mai kyau yar asali, muna da hadin kazar amare mai kyau yar asali sannan muna da Sha daka mai kyau na amare da uwargida! Akwai parkege na amare mace da ta yarda da kanta Hajiya taɓa Ni ta wannan Number:08130269841 sayan na gari mai da kudi gida*
Kaza
Tara bala'i-
Gumba bucket ƙarami-
Gari-
Hatsabibiyar zuma
Hatsabibin gari
Zobe-
Tsumi-,
Maina ya rikice
Zazzogau
HaÉ—in gigita shi
Maƙale mata

Sayan na gari mai da kudi gida..... Sai kun zo muna maraba da ku

________________________________

Kallon shi Innah tayi sannan ta maida idanun ta kan Yarinyar, da take kwance jikin Mommy.
"Zainabu mu tafi da ita gida." Bata rufe baki ba, Khalil ya isa tare da Abie.

"Zamu wuce da ita Germany, akwai likitan matsalar ta, sai dai zata iya daukar wata shida kafin yazo kanta, amma da mu zauna anan jiran gawon shanu gwara mu tafi can ko Allah zai saka ta tashi." Inji Abie, yana kallon Mohan,
"Duk yadda kace haka zamu ayi, amma ai shima Mohan din ba zai ki wannan shawaran ba, tunda abinda yake bukata kenan"

Kamar kurma haka ya zauna musu, ba tare da yace musu cikanku ba. Dafa shi Khalil yayi ya juya yana kallon Khalil.
"Idan hankalin ya b'ata hankali yake nima shi, don Allah kayi hakuri ka saka salama a zucuyarka karka damu Allah zai bata lafiya."

       Janye hannun shi yayi a kafad'ar shi.
"Ni nawa hankalin ya tafi ba tare da nasan ina ya tafi ba, hankalina ya b'ata a jikina tun daga d'azun da naga Maimunari wuka ya fito ta bayanta na fahimci hauka tuburan nake, dan haka ka kyale ni karka dame ni,"

Ya fada tare da saka hannun a bakin shi yana mishi alamar kar ya tashe ta, haka ya zauna yana kallonta, bani baki daya kome nashi ya tsaya cak, yana tare da ita ne, amma yayi imani da Allah ya mutu ya kai sau dari, kuma da za a tsaga jikin shi babu ruwa a cikin shi zunzurutun tashin hankali da fargaba, a kowacce dakika bugun zuciyar shi yake kara tsananta, ji yaƙe kamar kafin ya bude idanun shi na'urar da yake makale da ita zai daina aiki alamar ya cika, wani irin yanayi mara daɗi yana kara kusanto shi, ya tsani karar abu matukar ba numfashin ta ne, zai fita ba, asalima gani yake kamar kawai yaudarar shi ake shirin yi. Domin bai ga alamar tana numfashi ba,

"Zamu tafi da ita Germany da fatan zaka bamu hadinkai.".inji Khalil,cikin wata irin masifa ya juya kan Khalil.
"Matar ka ko matata? Karka yarda ka ce zaka min iyayi akan mata ta, wallahi ranka zai mugun b'aci, dalla matsa ka bani guri."

   Kura mishi ido suka yi baki daya ya fita hayacin shi, gani yake kamar cutar shi zasu yi, dan haka Abie da kan shi ya rike hannun shi tare da cewa.
"Karka zama mutumin da bai amsar ƙaddara mana, ka yarda dani babu abinda zai faru da Matar ka Insha Allah." Jikin shine ya shiga rawa tare da karkarwa, ya ce.
"Abie da gaske?" Ya tambaya hawaye na zuba mishi,  share mishi kwalla yayi tare da cewa.
"Insha Allah!"
"Don Allah Abie kar wani abu ya faru da ita!"
"Da izinin Ubangiji babu abinda ya gaggare shi. Ka yarda dani."

     Haka suka yi ta rarrashin sa, kwalla na zuba mishi,suka nufi airport aka gama kome, sannan suka dawo, a daren suka bar kasar,.sannan suka bar su Mommy da Innah da Beenah da suka shiga tattara kayansu zasu koma Nijar, inda zasu sauka a Niamey, gidan Abie.

Kallonta Innah tayi tare da amsar kayan hannunta tana ce mata.
"Sannun Zainabu! Dama baki da lafiya ne?"
"Uhmm" tace bayan ta ajiye kayan hannunta da sauri ta nufi ban daki,ta shiga kwara amai.
"Subhanallahi ikon Allah, Sannun amma ai baki ci kome ba naga yau tun farar safe, ban da ruwan zafi babu kome a cikinki."

       Wasu kwallar wahala ne suka zubo mata, wato idan ta fahimta, Abie jika mata aiki yayi, wayyo Allah wannan abin kunyar da me yayi kama? Ina zata shiga ne? Maimunari na haihuwa ga Benazir da tsohon ciki, itama haka zata jera da su, abin kunyar yayi ƙamari.

   "Sannun Mommy, tashi na wanke gurin" inji Benazir,
"A'a barshi na wanke ai kema ba dadin kike ji ba, taimaka mata ki kaita dakin ta."

     "A'a ba sai ta kaini d'akina ba, takai ni dakin shi, nafi son kamshin turaren shi." Ta fada a wahale,
"Ai haka ne? Toh Allah ya raba lafiya, rabo ajali." Ta fada tare da gyara ban dakin, murmushi Beenah take tana kallon Mommyn su. Tana kaita dakin ta riko rigar shi ta daura akan hancinta, wani irin yanayi me dad'i yana ratsa ta.
"Mommy ko na duba miki turaren shi ne, tunda kina son kamshin, idan yaso sai kina fesawa."

"A'a nafi son na jikin rigar shi" ta faÉ—a tare da kwanciya, idanunta a lumshe, fita Beenah tai ta barta a dakin suka ci-gaba da tattara gidan,

     Barci me nauyi ne ya dauke ta, haka tayi barcin da rigar shi a saman fuskarta.

  **
Wajen karfe biyar na yammacin washi gari.
Abie ya kira Mommy, bayan sun gaisa take tambayar shi.
"Ya jikinta dai?"
"Toh da sauki zamu ce, amma zamu dawo ni da Khalil, shi zai zauna da ita, idan yaso kafin ayi aikin zamu yi ta kokarin ganin mun zo dubata"

  "Toh amma kashe kudin ba zai yi yawa ba, kawai ku dawo din idan za a mata aiki sai ku je baki daya amma ayi ta sintiri a hanya akwai matsala"
"Toh shikenan, amma ya naji muryan ki kamar baki da lafiya?"
"Mura yake damuna"
"Allah ya baki lafiya"
"Amin Ya Allah Nagode"
"Ki kula da akanki da yaran Insha Allah jibi zamu shigo"
"Allah ya yarda" ta faÉ—a tare da zuba yawun a jikin wani abu.

    Sako kafarta tayi kasa, sannan ta mike a hankali,ta nufi hanyar ban daki tayi wanka sannan ta fito daure da towel, zama tayi sannan ta kira Yumnah, shigo tayi da sallama.
"Mommy gani"
"Yumnah, kice Beenah ta dauko min kayana zan yi sallah ne"
"Toh Mommy"
Ta juya da sauri,. Kwanciya tayi sai da yarinyar ta kawo mata kayan, sannan ta saka tace mata.
"Kicewa Beenah tazo dakin nan ta had'a kayan Abien ku."

      "Toh"
Ta fita da sauri, haka Beenah ta shigo ta had'a kayan tana sallah, tana idarwa tace mata.
"Benazir don Allah ki nima min abinda zanci yunwa nake ji"
"Toh Mommy me zaki ci?"
"Beenah duk abinda kika bani zanci."

    "Toh" fita tayi dake suna da garin kunun tsamiya, haka ta dama mata da Fanke ta kawo mata, haka tayi taci hannu baka hannu ƙwarya. Tana gamawa ta mike tare da yawo a dakin domin zata iya amai, wayarta ta dauka tare da kiran wani shagon magani ta gaya musu abinda take bukata ko awa daya baayi ba, sai ga shi an kawo mata maganin. Dake ta biya baki daya, sa hannu Beenah tai sannan ta kawo mata maganin.

      Bata sha ba gudun karta yi ama, sai da taji yunwa tasha. Da kunun.

    Baki daya kamar an mata iyaka da falo, suna ta had'a kayan tana kwance, kuma zasu yi waya da Abie amma bata gaya mishi ba, kuma ta hana a gaya mishi, kuma irin cikin nan ne mai shegen saka fitina domin ya sakata mugun jaraba,  ga laulayi ga fitin. Shi yasa bata son Fitina,. 

   Ranar da zasu dawo haka ta daure ta gyara jikinta, sannan ta kwanta a dakin, basu suka iso ba sai dare, a gajiye suka shigo gidan, shi kan Khalil daukar matar shi yayi suka tafi masaukin shi,

  Abie kuwa bayan yayi wanka ya fito ya ci abincin dan ya ganta a dakin da yace zai shiga da abinci dakin ta shiga mishi masifa, shine ya fito yaci a waje, yana kallon Kanwar shi da Yumnah.
"Wai meke damun ta?" Ya nuna musu kofar dakin shi,
"Abie bata da lafiya ne, kuma bata cin abincin sai kunu"

Mikewa Innah tayi ta nufi inda Mijinta yake, tana dariya.
"Allah ya bamu irin naku ai da mun ware!"
Shi da Yumnah suka ci-gaba da hira, bayan ya gama ta kwashe kayan takai kitchen a daren ta wanke sannan tazo ta zauna a kusa dashi.
"Abie ya jikin Addah Munah?"
"Da sauki karki manta idan kinyi sallah ki sakata a cikin Addu'arki."
"Insha Allah, Abiena" rungume ta yayi sannan ya sumbaci goshinta, ya rakata dakin sai da ta shiga ban daki tayi alola da kama ruwa , yana tsaye ta kwanta yayi mata addu'o'in, yana cikin yi tayi ta hamma sannan ya tofa mata, kafin ya fita. Tare da kashe mata wutar dakin,

     Dakin shi ya nufa a dan tsorace, bayan ya shiga ya same ta tana amai.
"Subhanallahi! Sannun" haka tay taimaka mata, ta fito ya wanke ko ina sannan ya shiga jera mata Sannun cikin jin haushi tace mishi.
"Zaka kyale ni da Sannun ka ko sai na fita a d'akin"

"A'a, Allah ya baki hakuri yi zaman ki, yan mata" ya fada tare da shiga ban dakin yayi wanka, ya a fitowa ya samu ta kashe wutar ɗakin, hango shi da tayi babu kaya ba karamin gigita mata lissafi yayi ba, dan Abie irin mazan nan ne masu kira mai kyau babu ko tumbin, kasancewar yana da tsawo, kuma zamani an Cigaba yana ƙoƙarin kula da lafiyar shi, ta hanyar motsa jiki, dirowa tayi a gadon ta fara rigima, shagwaɓa rikici.  Kamar Baby Yumnah, dan ma Innah ta tafi da Widad tana gurinta, domin Yarinyar ta makale mata, itama kuma yadda take son Uwar Yarinyar haka take kaunar Yarinyar.

     "Hammah don Allah!" Wani irin rikice mishi tayi, a sanin shi tunda aka daura auren, idan ya nime ta bata tab'a yarda tazo. Sai yara sun yi barci, musamman da suka dawo sam taki yarda ko hiran soyayya suna yi a gaban yara, kunyar Maimunari yasa basu sakewa, idan ma ta shigo dakin shi kamar daukar wuta ko mara gaskiya zai ga jikinta har rawa yake, dan haka ya zuba idanu yana kallonta.
"Zainah me kike bukata? Jikinki akwai zafi ko zamu je asibiti ne"
Yayi kokarin b'oye bukatar shi, cikin kuka me dauke da bukatar shi tace mishi.
"A'a kai nake so"
"Toh gani a gaban ki" fisge towel din tayi, lumshe idanun shi yayi..yana mamakin sauyin ta, matar da idan ya shiga d'akinta kamar yazo mata da alfasha, tayi ta kuka tana cewa ya rabata da abin kunya, dan haka tallafeta yayi tare da mata matsuguni a saman kirjin shi.
"Yau da kanki"
Gyada mishi kai tayi sannan, kwantar da ita yayi  tare da mata rumfa da faffadar kirjin shi.
(😂inji Ubaid yace dan Iya wannan sai dai yar iya)

        Ajiye kome yayi a gefe ya gurje soyayyar shi, domin ita ta kawo kanta, ya kuma tara mata gajiya sannan ya tashi ya had'a mata ruwan zafi, bayan ya taimaka mata ta shiga wanka.

      Ya gyara d'akin, bayan ta fito ta samu yana gyara gadon, zama tayi shima yayi nashi ta fito, tana kwance, kayan barci ya saka sannan ya rab'a gefenta, tare da shafa gashin kanta, juyowa tayi tana kallon shi. Janyota yayi jikin shi ina shafa bayanta, ta kuwa narke Mishi, ya gaji sosai dake ya dawo daga tafiya ne amma matar nan haka ta hana shi hutawa. Kallonta yayi idanunta babu barci.
"Me kike so?" Ya tambaye ta a gajiye,
"Kai"
"Toh Zainah" haka bawan Allah nan ya raba dare akan matan nan, sai da suka dauki lokaci kafin ta samu nutsuwa, wanka yayi da ruwan zafi ya zo ya kwanta,  karfe shida ya tashi yayi sallah asuba, sannan yayi nafilla da yake kafin sallah asuba. Yana idarwa ya tashe ta, bude idanunta tayi sannan ta zuro kafarta kasa, tare da ɗaukar towel dinta ta shiga wanka. Bayan ta idar ta fito ta gabatar da sallah asuba, sannan ta kwanta a gefen shi.
"Hammah barci kake ji?"
"Ke kuma rigima kike ji?"
"A'a kawai kai nake so"
"A'a kayana dai kike so"
"Kai Hammah meye haka" ta faɗa a shagwaɓe,
"Zainah na gaji wallahi, kuma ina son ma huta koda na awa biyar ne gaya min meye kika sha ne?" Ai kamar ya zage ta, ta fashe da kuka tana faÉ—a cewa.
"Idan ba lalura ba me zai saka na zama haka, ka hada ni da ciki me jaraba kace min ina rigima"

Tashi yayi zaune bakin shi dauke da sunan Allah, ya d'agota yana fadin.
"Alhamdulillahi! Kanin su Yumnah ne a jikin ki?"
Murmushi yayi tare da rufe fuskarta.
"A'a ai dole ayi ban ruwa, wannan kyakyawan dashen, Tabbas yana bukatar ruwa domin yayi yabanya"

    Ai kuwa bawan Allah nan ya dage tare da aikin Alkhairi da aikin lada.

   ....
Khalil ya gaji sosai, dan haka matar shi ta taimaka mishi yayi wanka sannan ta dauko kular da ta kawo mishi na abinci, sai da yaci ya koshi sannan ya zauna suna hira sama sama, ganin zata fara barci ya sashi dole ya taimaka

_Zaku yi hakuri a madadin three pages zai zauna a biyu, domin zan cigaba da typing É—in FREE Pages din kishi._
#Mai_Dambu
8/19/21, 6:54 PM - My Mtn Number: HAKKIN MALLAKATA
#wed-Aug-2021

BOROROJI

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.