Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 25 of 64
BABI NA TALATIN.
Har malam Umaru yazo ya wuce Mohan yana jikin motar shi kayan yana gaban shi, bai saka yayi fush ba, haka yana tsaye har dare yayi sosai yana tsaye a gurin.
    .....
Bayan Baba Ya dawo, bata gaya mishi ba, kuma bata nuna mishi wani abu ya faru ba, domin ta gargadi ni da babban murya, ina kallon su suka kwanta,wato suka shiga dakin su, nasan yana kofar gidan bai tafi ba, dan haka na tashi a hankali na fito tare da dauko wani abu na saka a jikin katangar gidan mu, na haura katangar na diro. Sannan na kwasa da gudu, sai gurin shi.
Ina zuwa na fada a jikin shi ina kuka.
Bude min hannun shi yayi tare da shiga cikin jikin shi.
"Hammah kayi hakuri, ka tafi"
D'ago kaina yayi tare da kallon yadda nake kuka. Sake maida kaina yayi, yana shafa bayana.
  "Ina nan har sai Innah ta barni nayi magana da ita." Ya fada tare da dauke kan shi. Kallon shi nayi da gaske yake fa.
  Dan haka na gyara tsayuwa na a jikin shi.
"Hammah"
"Hmm! Mamoon"
"Hammah"
"Na'am My Golden Boy" ya faÉ—a tare da shafa kaina.
Bayan ya riko hannuna, ya nufi kofar gidan mu dani.
  "Don Allah karka buga musu kofar zata zane ni ne, don Allah karka bari tasan na fito ta katanga, please Hammah Mohan" bai saurare ni ba, ya
buga kofar yayi dakyar aka bude. Baba ne ya bude. A hankali ya ciro ni daga bayan shi.
"Maza shiga ka kwanta, ina nan har gobe."
Ya fada yana tura ni cikin gidan, tsoron Allah da tsoron Innah yasa Ni jin fitsarin tsoro, haka Baba ya kalle shi tare da cewa.
"Nagode!"
"Baba kar a dake shi don Allah."
  "Idan aka dake shi zaka karya mu ne kamar yadda kayiwa Wancan Yaron?" Bai ce kome ba, ya tsaya a gurin har suka rufe kofar gidan, zama yayi a kofar gidan bayan ya ciro ƙaramar bindigar shi, ya gyara kunamarta.
   Ganin yadda ina take niman abin dukana yasa Baba ya sha gabanta.
"Ya isa haka! Meye laifin shi, Kinga dukar nan da takurawa, wallahi shi zai lalata miki shi, tunda na dawo kika ki gaya min abinda ya faru nace miki wani abu ya faru ne? Kika ce min a'a, amma a can inda nake zaune aka gaya min Shago ya hadu da wanda ya fi karfinshi inda yabi Almamoon, na nuna miki na sani? Toh bari na gaya miki matukar Shago yana unguwar nan wallahil azim abinda kike boyewa zai fitar miki dashi domin ba dan Allah ya kawo shi ba sunan tattalin ki na shekaru sha takwas zai tashi a banza tsanani baya gyara sai lalatawa ba yau na fara gaya miki ba.
  Sabida ina son auna girman abinda yake faruwa ne, dan haka karki sake Almamoon ya fahimci dalilin ki na hana shi abinda yake so domin kuwa goben sa zai lalata da hannun shi. Ya ga yadda zakiyi, kai kuma wuce ka bani guri."
   -- Haka muka kwana zuciyar kowa babu dad'i, Allah Sarki. Hammah Mohan anan kofar gidan ya kwana. Da asuba suka nufi masalaci da Baba, sannan suka yi hira bayan ya fadi abinda ya kawo shi da abinda ya faru a baya, malam yayi godiya sannan yace mishi.
"Mun gode, sai dai kawai abar aikin nan idan hankali ya kwanta za a yi miahi kaga mahaifiyar shi hankalinta yake s tashi, sannan ina son Yaron ya koma makaranta sabida kwazon shi don Allah kayi hakuri zan kula da kome, ina son Rayuwar Almamoon ya bunkasa sosai."
"Insha Allah Baba nayi mata alkawarin ba zan kuma takura mishi ba, Yaron yayi jinya na, dan haka zan kula dashi sosai kamar kanina, kabawa Innah hakuri ba zan lalata mata Dan ta ba, wannan kudin shi da kayan shi ba zan iya kome dashi ba, ka bashi Don Allah."
"A'a yaro"
"Baba ka É—auke ni d'anka ne, idan ba zaka nuna min iya Almamoon ka haifa ba" amsa Malam Umaru yayi yana mishi godiya da saka Albarka,
   Sannan ya shiga cikin gidan,, ina kwance ya d'aga labulen tare da cewa.
"Kaje yana son zai tafi yanzun."
  A hankali na mike tare da fitowa waje, na same shi yana tsaye dake garin bai gama wayewa ba, a hankali na tsaya a gaban shi. Ina wasa da hannuna.
"Zaka dawo school ko? Domin ina son zan tafi wani course na shekara daya da rabi lokacin ka gama karatun ina ga zaka attechmen lokacin."
D'ago kai nayi ina kallon shi, kafin na sunkuyar da kaina.
"Innah tace ba zan koma ba" d'ago kai na yayi yana share min kwalla,
"Zata bari idan bana tare da kai zaka yi karatun ka cikin salama, idan kuma muna tare ba zan iya hakuri ba."
Gyada mishi kai nayi ina wasa da hannuna.
"Amma me yasa zaka tafi?"
"Baka son na tafi ne?" Ya fada yana bude min hannun shi, a hankali na shiga tare da lumshe idanuna, kwallan yana zuba min.
"Hammah na"
"Mamoona, kayi karatu me kyau zan baka kyauta ranar da ka gama karatu da attechmen."
Hannun naji akan lips, da sauri na bude idanun na, sai cikin nashi.
Sumbatar goshina yayi, sannan ya cire ni jikin shi bayan ya bar Ni tsaye ina me jin sassanyar lips din shi a goshina, har zuwa lokacin ban bude idanuna ba, domin ina jin shi kamar an kunna min wuta ne a jikina, tashin motar shi yasa ni bude ido ina kallon yadda ya figeta a guje..
 Yasan idan ba haka ya gaya mishi ba, Almamoon ba zai yi karatu ba, yayi danasanin koya mishi sabo da shi, yasan yaron tunda ya iya dira ta kantagar gidan babu makawa next abinda zai faru ba zai yi kyau ba, amma bari ya gani ko zai iya hakuri na shekara daya da dari bai saka shi a ido ba kai ma wata daya ma tukun. Amma babu inda zashi yana Nijar kuma yana nan yana kare Kayan shi.
  ***
Anyi gwagwarmayar kamar za'a tashi sama kafin Inna ta amince na koma makaranta bayan ta gama ja min kunne, na dawo makaranta bayan nayi wani irin laushi kamar bani ba.. kawai karatu na saka a gabana.
  Malam Ansar yana taimaka min sosai, gashi ya tattara duk kulawar shi a kaina, wata na daya da kwana ashirin sai ga Hammah Mohan a makaranta.
Sanye da unifoam, murza Idanuna nayi tare da kallon shi, yazo a cikin motar lamborghini aventador. Kasa magana nayi ina kallon shi, bude min motar yayi da sauri na nufi inda ya bude min na shiga, sannan ya dauke ni muka wuce.
   Yana tuki yana murmushi..
"Hammah Mohan yaushe ka dawo" jan hancina yayi tare da mai maida hankali akan tukin da yake.
    Wani gida muka nufa a cikin Barrack din gidan ya hadu, gashi da alamar an ware gidan yafi na sauran sojojin kyau, bude min yayi, tare da cewa.
"Ina zuwa, ka shiga."
  A hankali na nufi cikin gidan, tare da bude kofar, babu haske a cikin falon shiga cikin gidan nayi tare da lallubar inda makunin gidan yake, ina kunna wutar wani karamin sauti na wakar.
"Happy Birthday to you" yana tashi falon, ga wani abu da ya fashe yana fidda wasu yan kyali, an saka katon baloon na 19, sai wasu cake guda biyu, daya Blue And Pink daya kuma fari ne. Juyawa nayi tare da kallon shi. Yana jingine da kofar. takowa yayi tare da kallona.
"Barka da cika shekara goma sha tara."
"Taya kasani?"
"Takardun ka na makaranta da wasu abubuwan suka gaya min haka."
"Hammah Mohan!" Na kira sunan shi.
"Ina jin ka Mamoon"
"Nagode"
  A hankali ma'aikata suka shiga fitowa tare da shirya mana falon, haka muka ci abincin tare, muka yi game. Kai na kuma jin farin cikin tun bayan dawowar mu daga Dubai, kaina na kafad'ar shi .
   "Ina son xan gaya maka wata magana amma ban san ya zaka dauke shi ba, sai dai idan na samu lokaci zan gaya maka" jan hancina yayi yana faɗin.
"Anan zaka zauna, ina kai kaa makaranta akwai su Hurayyah zasu kasance da kai. Bana son kana zama a can domin naji an ce min Ansar yana kulawa da kai. Ni ba zan yi faÉ—a akan ka ba, amma zan nisanta kowani dan isa akan ka."
   Murmushi nayi domin ina jin dadin yadda yake nuna min kome nawa special ne, haka muka sha hiran mu, da dare ya nuna min d'akina, na kwanta naga ya saya min kome.
  ***
Tunda suka fita yake bibiyar layin Almamoon, amma babu alamar zai dawo, dan haka ya mai da hankalin shi kan abinda yake amma kuma Toh.
.....
Zama na a gidan Hammah Mohan ya kuma kara mana shakuwar mu, shi yake kai ni makaranta idan na tashi zai zo daukana, karshen wata da kan shi ya ke kawo ni Damagaram ya sauke ni a wajen gari na shiga cikin gari a wata motar..
Tattalin duniyar nan ya dauka min, tunda nake dashi bai tab'a kawowa min wata manufa ba, bai tab'a min wani abu da zai sani cewa yana niman wani abu a jikina ne, asalima babu wannan tunanin a ranshi.
 ***
Bayan shekara daya
Yau muka gama jarabawar mu ta wanda daga shi sai zuwa horon da zanyi na dawo na karasa wata shidan da ya rage ina da shekara ashirin.
   A hankali na fito ina kallon makarantar, ina fitowa na hango Hammah daga min hannu yayi, na nufe shi da sauri.
"Mamoon!" Naji muryan Benazir,
Kallonta nayi.
"Nagode sosai, ba dan kai ba da an kore ni"
Murmushi nayi mata, sannan na mika mata hannu.
"Kinga ni kamar kanwa nake jinki dan haka ki daina biyewa yaran nan basu da hankali."
   Sannan na wuce ta, tare da nufar gurin Hammah Mohan, bude min mota yayi na zauna, sannan na kalle shi.
"Kace min congratulations"
"Ba zan fada ba"
"Toh kuwa zan fita a motar."
"Ok" ya faÉ—a bayan ya shiga.
  A hankali na maida kai na jikin kujeran, ba yau ba ina son muyi magana da Hammah Mohan, ina son na gaya mishi gaskiyar kaina, ina son nayi rayuwa kamar kowa ina son Yancina. A dame na kalle shi.
"Hammah Mohan, ina son muyi magana da kai ban san yadda zaka dauka ba."
  Kura min ido yayi sannan yace min.
"Idan ba zaka iya fada ba toh dole ne?"
"Eh dole ne"
Tab'e baki yayi na rasa gane yadda zan gaya mishi.
"Nifa lafiya ta lau, kuma yadda kake gani na ba haka nake ba."
"Dama na ce ina son sanin yadda kake mata maza"
"Hammah ka daina mai da zancen wasa mana"
"Ok na na mai da shi babba."
Baki daya ya ki saurarona, ni kuma ba kome bane yasa nake son gaya mishi halin da nake ciki ba sai fadar da muka yi da Hurayyah, ta kuma sha alwashin sai ta haÉ—a ni dashi. Toh ina son na gaya mishi amma da kuma abu me muhimmanci akai na.
 Bayan mun isa gida na wuce dakin nayi abunda zanyi na fito, gabana ne ya fadi lokacin da naga sun zura min ido har da shi.
"WALLAHI tallahi Azim, mace ce Almamoon ba namiji bane." Kura min ido yayi tare da niman sanin ba'asi.
   Ranshi ya kai kololowar baci, domin na kasa magana, jikina yana rawa.
"Yallabai shekaranjiya na shiga ban daki na ga audugar jinin, sannan na sami wannan bra din a ban dakin, idona idon Mamoon mace ce kuma idan nayi karya gata nan ka tambaye ta."
   Kallona yayi tare da niman me zance,
"Meye gaskiyar abinda ta faÉ—a?"
"Hammah Mohan!"
"Gaskiya zaki gaya min?" Ya daka min tsawa.
"Abinda nake son gaya maka."
Bai saurarre ni ba, ya fita da wani e sauri, bin bayan shi nayi. Ko kafin na isa ya shiga mota tare da fita a haukace, haka nayi ta bin shi da mugun gudu. Na rasa gane dalilin da yasa yaji haushina.
Numfashi na sauke ina kallon motar, domin nasan ba zai tab'a saurarona ba.
Ina shiga cikin gidan naga ma'aikatan gidan suna min dariya, naji babu dad'i dan haka na koma daki na zauna ina nazarin su.
  Sam ban san meye na tsare musu ba, baki daya sun tsane ni sun tsani alaƙar mu, karo na farko da naji bana mubaya'a da boye min jinsina da Innah take koma me zata yi ba zan cigaba da boye kaina ba.
   ..... Har dare ban ga Hammah ba,asalima kin shigowa yayi sai da yaga alamar nayi barci ya shigo. Haka ma washi gari yayi fucewar shi. Gashi ina son tafiya gida, dole tasa na hakura da abinda nake so na jira shi.
  Haka kwanaki ya tafi babu shi babu alamar, karshe na tattara na koma gida.
  Da tarin tambayoyi a bakina.
**
Niamey
Kallon shi ÆŠan Ba'are yayi dariya ce ta cika mishi ciki, amma sanin bai da daraja yanzun zai kafta mishi rashin daraja yasa shi kura mishi ido. Yau kwana goma tunda yazo ya kasa gaya mishi gaskiyar abinda ya kawo shi sai dai ya zauna yayi ta busa shisha. Ya sha kamar ba gobe.
  "Amma dai ƙasan ina da abun yi ka tarani a gaban ka kamar mai daukar darasi"
     Ajiye bututun shishar yayi tare da saka hannun shi a tsakanin cibiyiar shi kamar mara gaskiya, ya sunkuyar dai kai.
"Mohan bana ciki da Bura Uba, zaka gaya min meye ke damun ka saka Ni a gaba kamar me niman gafara."
Shiru yayi yana kallon Dan Ba'are, kafin ya kura mishi idanun shi da suke maiko alamar ruwa ce ta taru a cikin shi tace mishi.
"Kasan Yaron nan ya ninke mu ne baibai" Ya faÉ—a yana jin karin b'acin rai sama da na kullum, kafin yace mishi.
"Kamar Ya?"
"Kamar yadda ka sani!" Na fada a zafaffe,
"Toh Ni ban san kome ba?"
"Allah yasa karka san kome dan Ubanka, dan iska Yaron nan dai." Shiru yayi yana kallon shi. Ya ma rasa yadda zai da ranshi. Sai jingina kan shi yayi da jikin kujeran, kan shi yana kallon sama.
   **
Damagaram.
Lokacin da na koma gida zunzurutun tsoron Allah da tsoron Innah kasa tambayar ta kome nayi, sai wani mugun shakkar ta ya kuma kama ni, dan haka na hadiye kome nayi shiru, har yanzun bani da zarran tunkarar Innah, har yau bani da kwarin gwiwar mata magana kai tsaye sai na nime taimakon Baba, shi yasa na ajiye batun bayyana kaina.
..haka nayi ta kome suku suku, na turawa Hammah Mohan sako yafi sau dari bai dawo min da shi ba, na kira shi bai kirani ba, karshe ma kin daukar kiran nawa yayi, na rasa meke min dad'i.
   **
Yau ma kamar jiya yana son gaya mishi abinda ya faru amma ya saka bude baki.
"Wai kai dan iskan ina ne? Meye ya had'aka da Mamoon? Nayi imani da Allah da za a gwada jininka sai an samu ya kai dari uku meye yake damun ka haka."
    Sake jan bargon yayi tare da lumshe idanun shi, yana kara jin takaici na murkusa shi.
   Kasancewar likita ya zo har gidan ne yake duba shi, yasa Dan Ba'are rufe shi da masifa, bayan likitan ya gama auna shi, ya rubuta musu magani tare da mishi gargadin.
"Yallabai ka kula da kanka jininka yayi mugun hawa,.....
#Mai_Dambu
8/19/21, 6:53 PM - My Mtn Number: https://www.wattpad.com/1107772644?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=bf4OKGFXFm%2BbTBcRYFtIWwkeTpAjYWx%2Ft%2B8piwgYnGj%2BHz02%2BCq8Olw61eWGNCGWLrWoWOYkU9DLRDRLwKRvQ2vFDZM4QGfJKL8gnNicMhI2rfKBsb98bQg%2Fv%2BXS7kmh
ðŸ‚ðŸ‚BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.