Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt
Chapter 36 of 64
BABI NA ARAB'IN DA BIYU.
Gurzawa yake cikin wani irin shauki me mugun dad'i, har yaji shi ya shige cikin jikinta kamar mahaukaci a zauce da ita, ya gigice domin bai tab'a kawowa zata kai mishi ba, dan haka lokaci guda yaji an shake mishi wuyar shi.
Ban san yadda zan kwatantata muku yadda nake ji ba, ban san wani irin yanayi nake ciki ba, sai dai duhun da na fahimta yana rufe min idanuna, karar da naji wanda ya tafi da jina da gani na baki daya, daga nan ban kuma sanin me ya faru ba, na ga dai ana tafiya dani da gudu, ina wuce wani irin haske. Sai muryan da ban san ta waye bana yana kirana can da nisa.
"Munnah!!!"
   Cikin wani irin faduwar gaba ta fito bayan ta gama sauya kayan ta, tana kallon abokan. Aikin da da suke mata magana, jin su take amma ba zata ce tana sane da abin da suke fada ba.
"Dr Zainab kina lafiya?"
Wani irin bugun zuciya taji lokacin da aka shigo da wata mara lafiya, mai da kallonta tayi kan yarinya domin a hannun wani mutum take yana niman agaji.
"Ku taimaka min don Allah," da sassarfa ta isa gabanshi. "Ku kawo min gadon dauka marasa lafiya." Ta fada da karfi, yana kawowa aka daura Maimunari, kallon Dr Zainab yayi tare da cewa.
"Don Allah ko nawa ne a duba lafiyar ta, don Allah" ya faÉ—a kamar ya cire ciwon a jikinta ya mai da nashi, da sauri suka wuce da ita d'akin tiyata, aka fara kokarin kunna wutar da zata iya haska inda ciwon yake, domin ta ga yadda mara lafiyan take.
    Domin zanin gado ce a jikinta, daga haka ya tabbatar mata da zargin da yake ranta, musamman da ta kwaye zanin da ya lulluba mata, kwalla ce ta shiga sauka daga idanunta. Tana kuka kasa kasa, kallon Nurse din dakin tayi tare da cewa.
"Kuje kawai ku kira min Dr Fadime da Dr Annah."
"Toh Dr" suka fita, a hankali ta mike tare da shafa kan Maimunari, kwalla na zuba mata, kwaso kayan aikin tayi tare da saka Safar hannun, ta fara duba ta sosai musamman gaban da ya fara alamar zai kumbura, yatsin ta gwada sakawa taga bai shiga dukka ba, da sauri ta cire tanadi mamakin yadda aka haka shigowar likitocin biyu ya sata kallon su . "Ban tab'a ganin irin wannan tashin hankali ba, ina ganin cases na Fyade, amma ban san yadda aka yi wannan case din ya tsaya min a rai ba."
 "Kai Dr meye na rashin hankali, wannan case din ba sabon abu bane, idan kika yi dubi da Yadda ake samun kananun yara ma ana musu fyade balle kuma babban budurwa kamar wannan.
  Ina ganin ba wani babban tashin hankali bane, kawai a dubata idan aiki ne sai mu hadu muyi mata, amma ki bar kuka haka." Inji Dr Annah.
Kallon su Dr Fadime tai sannan tace musu.
"Amma ai naga mutumin da ya kawo ta ya biya kome, idan ba ita ta kai kanta ba taya zai sami damar lalata mata rayuwa yan matan mu na yanzun basu da kamun kai, gashi nan ya kai ta ya baro ta. Idan aka gaya musu su kame kansu maza basu da amana su ga kamar karya kake musu gashi nan bata wuce ashirin ba amma dubi yadda namiji yayi mata fata fata, wallahi na fi tausayin Yara kananu da ake musu haka sama da yan matan da ake musu wannan aika aikan, meye amfanin zubda mutunci ne? Shi ba aurenki zai yi ba kin je kin bashi jikinki"
 "Akwai ƙaddara! Dr ki duba yarinyar mana, dubi fuskarta mana? Dubi yadda gefen fuskar ya kumbura sakamakon dukar da aka mata! Yarinya shekara ashirin, meye tayi mishi? Waye nata ya tab'a yar wani? Kisan yadda fyade yake da ciwo? Karki yi fatan haka ya faru da makiyinki ma balle masoyinki, karki yi fadan wannan mummunar yanayin ta faɗa kan wanda kika sani, wallahi akwai ciwo." Ta rushe da kuka, ta kasa aikata kome,."Dr Bawai muna zargin yarinyar bane, daga Yanayinta ya samu fahimtar halin da ta tsinci kanta amma kuma ai yan matan ne suka zama sai du'a'i,"
Gyada kai tayi zuciyarta yayi nauyi tace musu.
"Muna da y'aya mata, addu'a itace makamin mumuni, Allah ya kare mana su duk inda suke." Tana kallon su, suka gama aikin su tsaf, sannan suka mata sai da safe domin sun tashi aiki. Ita kuma ta Cigaba da lura da Yarinyar.
Sai da ta gama gyara gurin tare da rubuta magani sannan ta shafa mata wani cream kafin ta mike, faduwar da gabanta ya kuma ne yasa ta komawa ta zauna dabas, kuka ya tawo mata, sosai tayi kukan da rabonta da tayi tun ranar da ta rasa abinda ta haifa, mijinta abin alfahari ta, Uban Yaranta abin kaunarta. Kallon yarinyar da ta gama dubawa tayi, sannan ta mike, ta sanya mata ruwa da allurai. Ta gyara mata jikinta. Har lokacin kuka take.
Tausayin yarinyar da kaunar yarinya ya taru a ranta, har kusan uku na asuba, abun sallah ta shimfid'a a dakin da aka bawa Yarinyar, ta shiga gabatar da sallar nafilla. Tana gayawa Allah kukanta. Zata so ta ga iyayen yarinyar nan kuwa?
Waiwaye adon tafiya.
Wato masu iya magana suna cewa munafunci dodo ne, yakan ci ubangidan shi. Bari mu dawo tun daga lokacin da Almamoon ya fara aiki a gidan Mohan. Malik bai tab'a damuwa da shi ba, kuma bai tab'a kallon Almamoon da wata manufa ba zai da ANSAR , ko nace Hisham Waadi Ansar ya faÉ—a a gaban shi Almamoon mata maza ne, a da abin bai dame shi ba, sai dai yadda suka saba da Almamoon ya fara jin sha'awar shi, har ta kai yana kallon shi ina da zai same shi,duk da dama zaman da yake yana cikin mutanen da suke cutar da Mohan, ta hanyar saka mishi sihiri a cikin abincin shi da ruwan shan shi, zuwan Almamoon kuma sai ya kasa samun nasara akan Yaron, sai ya ma shiga taimaka mishi, a hankali kome ya canza, inda Ansar yayi ta cusa mishi kazaman kudi,. Suka fara abota har yana gaya mishi siririn Mohan.
   Sai gashi duk lokacin da Mohan zai yi wani abu kamar a kunnen Ansar, shi yasa bai damu ba, koda Maimunari ta bayyana kanta sai ya zuba ido ya ga gudun ruwan su, yana kuma bincike akan Familyn Mohan, a haka kuma ya samu labarin Hanan, dan haka ya mai da hankalin shi lallai sai sun yi wannan Game din, da taimakawan Malik.
     Lokacin da Malik ya tura mishi sakon Mohan yace ya maida Maimunari Damagaram. Tura mishi sakon yayi tare da cewa.
*Nawa zan baka ka kawo min ita Maradi?*
Dariya yayi sannan yace mishi.
_Toh nawa zaka bani?_
*CF Miliyan goma*
Tsaki yayi tare da tura mishi cewa.
_Ni na matsiyaci bane rike kudinka_
*Nawa kake bukata? Zan baka*
_CF miliyan Talatin, sabida abinda kake so ce idan bai maka ba kaje gidan Iyayenta ta_
*Shi kenan ciniki ya faÉ—a ga miliyan ashirin da biyar sauran idan na iso na dauke ta zan baka shi*
Suna gama cinikin ta, ya tafi kiran Mohan, yana zuwa ya mika key motar shi lafiyarta lau, amma suna barin Niamey, ya fara Surutun motar ta lalace, a hankali dai yayi ta jan abin kamar da gaske, har ya yanke shawarar su tafi Maradi su kwana, ya kuma san yadda ya sakata layinta ya daina aiki, koda suka iso, ya kira Ansar ya gaya mishi, sun iso bai yi tsammanin zai biyo daren yazo ba domin shi ya riga su, isowa garin.
  Shi kuma da iya iso kofar gidan, ya kira wayar shi bai dauka ba, ya kuma kira bai dauka ba, dan haka ya shiga cikin gidan, yana shiga ya hango abinda Malik yake shirin aikatawa, kawai yaja wayar da aka hada na receive ya fincika sai da ya watsar da kome na gurin kayan kallon sannan ya nufi dakin duka daya yayiwa Kofar, yana shiga bai tsaya wata wata ba, ya shiga zarga mishi wayar sai da ya nad'e wuyar shi tam tun yana motsi har ya daina motsi.
   Jan zanin gadon yayi tare da lullube ta, sannan ya dauke ta. Ranshi na kara b'aci, yana daukar ya koma gaban gawar Malik.
"Hukuncin ka kenan, duk wanda ya tab'a Munnah."
Kaita mota yayi sannan ya dawo ya kwashi kayanta har da wayarta, a yanzun kan babu amfanin tafiya da ita wani gurin, dan haka. Yana kai ta Asibitin ya basu kayanta akan su bata, sannan ya biya kudin kome, ya bar asibitin. Tare da gudun mafaka, domin yasan tabbas za a nime wanda yayi wannan aikin, shi yasa ya cire Maimunari cikin gida har da kome nata, kar case din ya faɗa kanta.
 **
Niamey.
Wani irin faduwar gaba ce ya same shi bayan ya gama shirya kome, dafe kirjin shi yayi, bayan ya gama daura hannun Fahad, kallon juna suka yi da Dan Ba'are.
"Ya dai?"
"Beauty tana cikin damuwa?"
"Ko?"
"A zuciyata nake ji!"
Shiru yayi sannan ya dauko ruwan sanyi wanda yayi kankara, ya jefa kafar Fahad a cikin ruwan. Kuka ya fara tare da girgiza kanshi yana mutsu mutsu.
"Yanke mishi wancan yar yatsar" Mohan ya gaya mishi, babu wani tausayi ko imani ya yanke yatsar kusa da ta babban, wani irin gurnani ya ke yana ihu, bayan sun toshe mishi bakin shi.
"Sake yanke ta karshen" inji Mohan, aikuwa Khalil ya yanke yatsar,
"Toh Yanzun gaya min su waye da waye"
"Dumm!!!" Garin Niamey ya dauki wani irin ƙarar me mugun karfi tare da daukewar wutar lantarki a garin baki daya, sakamakon faruwar fashewar.
"Duba ƙarar me?"
Da sauri ya fita, yaji garin yayi wani irin tsit, cire mishi tape din yayi tare da yanka mishi fuska da aska.
"Gaya min me kuka Shirya min?"
"Zan fada zan fada."
"Chief of Army Staff, Attorney general, Minister of defense, Inspector General of Police, tare da Minister of Information, sai Minister of affairs,sune suka shirya juyin mulki, yau Insha Allah. Sannan sun dakatar da babban kwamandan Sojojin sama, domin sun shirya kashe wasu ministocin Babanka, minister Lafiya, minister Ilimi."
Cikin tashin hankali ya kalle shi, bai san lokacin da ya caka mishi wuka ba.
"Wannan ƙarar fashewar jirgin ne?"
"Eh!" Ya fada a wahlarce,
"Shaidanun suna ina?"
"Suna ina?"
"Zasu kashe ka domin sun shirya maka" ya faÉ—a a wahale,
Bai kula shi ba, yayi waya kafin kace me. Har sun fita, kamar yadda suka zauna suka Shirya. Sharrin su haka suma, suka shiya musu, yayin da suka yi ta bin kowani dan banza suna kamewa, basu sami ministan harkokin waje ba ya gudu..
    Ba iya shi ba hatta manyan sojojin da suke da hannu akan abin sun gudu, dan haka suka nufi cikin gari bayan sun saka akan kama, munafukan take aka fitar da wani sanarwan me mugun tashin hankali. Akan duk inda aka samu Mohan da Dan Ba'are, a kashe su. Domin suna da hannun akan hatsarin jirgin sama da aka yi, da kashe ministan tsaron ta akayi, tare da mutuwar jami'in tsaro da aka samu gawar shi a Maradi.
 Domin sun yi kokarin yin juyin mulki ne sai sanarwan mutuwar Fasinjoji jirgin sama har da ministocin kasar biyu Dr Khalid Bashir da Dr Al-Amin Sahabi. Ba karamin tashin hankali dan Ba'are ya shiga ba.
"Kai kasan waye ya mutu?"
"Waye?"
"Malik"
"Ya aka yi kasani?"
"Idan bai tafi da Moonah Damagaram ba, Tabbas akwai hadin bakin da suke da ANSAR, kuma nasan zai iya kai mishi ita, abu daya nake tsoro kar ya aikata mata mugun abu, tsoron da nake ji kenan."
  "Babu abinda zai faru, Insha Allah."
  ***
Karfe bakwai na safe ranar da Nijar ta samu yancin kanta Yau ya zamewa wasu iyalan ranar bakin ciki, musamman inda jirgin ya fado, ya kashe mutane da dama bayan fasinjojin cikin dari da ashirin, a nan akayi ta sanarwan mutuwar.
   Fitowar Dr Zainab kenan, ta hango Benazir da Yumnah, tare da mai renon su. Da gudu suka tawo kanta.
"Mommy Daddy sun yi hatsarin jirgin sama." Kamar sauran aradu tashi maganar daga bakin su, kafatan ma'aikatan asibitin, suka sunkuyar da kansu, sabida sun ji labarin ita ce dai basu bari taji ba.
Kallon su take kamar wacce ta rasa tunanin ta, a hankali taji maranta yana murÉ—a mata, lumshe idanunta tayi sakamakon zafin da take ji har cikin ruhinta, mik'ewa take son yi amma ta kasa, haka Benazir ta d'ago ta. Amma ta kuma komawa sai ganin jini suka yi yana zuba daga tsakanin kafaffunta.
"Mommy!!!" Yumnah ta faɗa da karfi, baki daya suka rud'e, domin suma tayi. Haka likitocin asibitin da Nurses suka rufa akanta aka mai da ita dakin gaggawa. Inda aka shiga kokarin rike cikin jikinta.
  Amma ina ya rigada ya fita, shima yabi mahaifin shi. Dakyar suka samu ta farfaɗo. Bayan ta koma barci, sannan suka fita.
   Bayan kwana biyu.
Tun washi gari da abin ya faru dani na farka, sai dai bana magana da kowa, kasancewar babu wanda yake zuwa gurina. Na tsani kaina da kaina, duk da ina samun kulawa a gurin Nurses sosai, na bar haka da sunan taimako ne kawai.
  Ranar da na cika kwana takwas, aka sallame ni, ina shirya kayana. Ta shigo, kallo daya nayi mata na dauke kai domin Nurses din suna gaya min cewa.
"Inji Dr Zainab tana gaishe ki, jikinta babu kwari ne." Ban santa ba, amma kuma ina jin ta a raina, shigowa tayi tare da cewa.
"Maimoon" juyawa nayi na kalle ta, sannan na cigaba da had'a kayana na dauka, ina haki.
"Ajiye drive zai zo ya dauka zo mu tafi"
Kallonta nayi, sai gashi na kasa mata musu a hankali na isa gabanta, ina jan kuka. Jingina kaina nayi a kafadar ta, danne kukanta take amma tabbas akwai al'amari me girma akan Yarinyar.
  Haka suka fito sai suka ba da sani irin yanayi kamar yaya da kanwa, sabida dan tsayin su kusan daya ne, yanayin jikin su ma kusan iri daya ne banbancin Zainab fara ce kal, kallon su Benazir tayi da take gaban motar. Ta fito da sauri ta bude musu bayan suna shiga. Sai kallon Maimunari take, kamar tasan fuskarta ta. Haka suka zauna. Sai lokacin kukan Dr Zainab ya fito. Rike hannunta Maimunari tayi, sosai irin na rarrashin nan.
"Queen Bee, akwai kayan Addarki a dakin da ta kwanta ku kwaso keda Rabil"
  Cikin asibitin suka shiga tare da kwaso kayan suka fito, a bayan mota suka saka, sannan suka shiga.
   "Allah Nagode maka! Alhamdulillahi Ubangiji Nagode maka, Allah ka gafartawa Khalid." Ta fada tana kuka. Kamar ranta zai fita, mijinta abin kaunar ta, abin alfaharinta. Ya tafi ya barta da soyayyar shi.....
#Mai_Dambu
8/19/21, 6:53 PM - My Mtn Number: https://www.wattpad.com/1110873206?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=w9A2MuNtd%2B622l0%2BjIc2ASPfh3Zd6cFPBnC7ssNginYPPoEFUrAQ6F%2BPyB%2FEL3W27mCWwkzGM1DWmbWijxOkDE%2BgKcaqC15YNh%2Bfbe6kK1ewkr6qPiO5FQd5pOlySlZh
ðŸ‚ðŸ‚BOROROJI🫀🫀
~The Journey of Destiny💔~
Mai_Dambu
Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.