Complete Hausa Novels

Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 37 of 64

BABI NA ARAB'IN DA UKKU.

Ta bani tausayi. Amma a yadda nake hango tawa rayuwar taya zan fuskanci Mohan? Taya zan fahimtar dashi? Idan na gaya mishi zai yarda dani ko ba zai yarda dani ba? Yanzun na hango abinda Innah take nufi, yanzun na gane dalilin da yasa ta hanani zama a matsayin Mace, yanzun na Fahimci illar da take cikin rayuwar mata.

       Ina kallon su kamar masu yanci. Ashe basu da yanci, ina kallon su kamar masu farin ciki ashe kowani dakika na rayuwar su hatsari ne. A haife ka a mace matsala, ka rayu a mace matsala,  hawaye ne yake zuba min babu iyaka, dama tana tsoron kar wani mara imani ya min haka ne? Ashe dama can ƙaddara ta a tsare take, dama a shirya min kome nawa daki daki. Daga wannan ƙaddarar sai wata, sai wata.
"Hmm!" Naja wani iska mai zafi, sakamakon isowa wani Mahaukacin gida da zai iya cewa yana bayan gidan Mohan na can Jacader.
"Mommy ko fito" hannunta naji a samar nawa, juyawa nayi na kalle ta, kafin na bude kofar, ina takawa a hankali, sabida har zuwa lokacin gurin bai warke ba, muna shiga babban falon gidan, mutane ne. Yan gaisuwa, ana ganin Dr Zainab, suka rud'e da kuka musamman yan uwan mijinta. Dangin shi, haka ta zauna a cikin su. Zata yi kuka na matse hannunta a hankali ina murzawa. Jinjina min kai tayi alamar tayi shiru.

       "Addah muje daki, ki huta" inji Benazir, gyada mata kai nayi. Na bi bayanta muka shiga cikin gidan, dagaske masu ruwa sune da kifi, domin dakin Benazir kamar irin dakin ya'yan Barber's doll ne. Kome na dakin pink da light blue ne, ban daki ta nuna min. Bayan ya shiga ta hada min ruwan wanka, shiga nayi. Na tube kayana. Bayan na zauna cikin ruwan, zafin yana ratsa jikina. Lumshe idanuna nayi ina kara sake ajiyar zuciya, domin dadin da nake ji. Musamman a gabana, domin ji nake kamar an daure ni baki daya.

     Sai da na gasa kaina sannan nayi wanka da alola na fito, na samu ta ajiye min doguwar riga, dauka nayi na nufi ban daki, ina sakawa hawaye na zuba min, ina gamawa na fito nayi sallah, kusan kwana uku bana cika barci mai dadi, sai mafarkai. Haka ya tab'a min ciwo na, domin kuwa na fara jin ciwon kai da zazzaɓi, tare da nauyin kirji na. Haka na kwanta tare da kifa kirjina, akan matashin na samu barci mai daɗi.

    Kwanakin da suka biyo baya, bani da lafiya sosai, domin sai da aka danganani da asibiti, inda suka maza suka gano Matsalata. Ciwon zuciya ne ya tashi, gashi babu Number wani nawa da ta sani, domin bata bincika jaka na ba.
**
Niamey.
"Yallabai yaran nan kokari kare rayuwarka da ta iyalinka suka yi akan me zasu so kashe ka? WALLAHI daga Khalil har Mohan, babu wanda yake da nufin ya cutar da kai don Allah ka saka a janye batun kashe su da zaka yi don Allah"

Kallon Alkali yayi sannan yace mishi.
"Me nene shaidan ka?"
Laptop din shi ya bude bayan ya kunna mishi daukar da yayi na manyan mutanen da suke jikin shi, take ya gamsu tare da yarda da abinda ya faÉ—a, lokaci guda ya bada sanarwar ta hanyar mai yaÉ—a labarai na fadar shugaban jamhuriyar kasar Nijar, akan an wanke su Mohan, sannan kuma an saka duk inda aka samu manyan mutanen nan a kama bayan an sake videon su.

    Sannan ya sauke baki daya manyan sojojin kasar, akan za a tura da sunayen wasu. Da za a basu matsayin kuma matasa masu burin kawo cigaba. Sannan ministoci biyu da suka rasu ta jirgin sama za a kaiwa Iyalin su, gaisuwa.

*
Kallon Mohan yayi yana murmushi.
"Tunda kome ya kammala toh ni ba zan kuma binka muyi irin wannan kasadar ba, aure zanyi idan zan mutu na mutu ina da matar da zata min addu'a dan kutumar Ubanka"

    Kallon shi yayi ya watsar tare da lallubar wayar shi. Kira yayi cikin Sa'a ta shiga amma ba a dauka ba. Sake gwadawa yayi can aka dauka.

"Addah Mommy ta kaita asibiti tana ta aman jini, amma zasu dawo inji Addah Benazir!"
"Benazir!!?"
"Eh ai kamar su daya da Addana Munah kuma, kullum Addah Munah sai tayi ta kuka tana tari, shine rana  na gayawa Addah Benazir, Mommy ta kaita asibiti, sun barni Ni daya na, gashi Daddy baya nan an ce ya mutu a jirgin sama waye kai?"

"Mohan Mamman Nasir Aghali!"
"Wow, joli nom Où es-tu maintenant? "
(Wow, Nice name Where are you now?  Wow suna me dad'i, kana ina ne yanzun?"

   *Tabdijam yau na hadu da tsinkankiyya* ya faɗa a ranshi,
""Alors où est Niamey, C'est ton nom?" (Ina Niamey, kema ya sunanki
Cikin shagwaɓe ta marairaice murya yace mishi.
"Tout le monde s'appelle Addah, je m'appelle aussi Adda Yumnah"
(Kaga kowa Addah ake ce mishi Ni ma ka kirani da Adda Yumnah) dariya ce ta kama shi tace mata.
"Toh amma ni katoto ne! Amma zan saya miki chocolat, ina Addah Munah?"
"Sunan tafi asibiti" ta faÉ—a mishi,
" Wani gari?"
"Maradi"
"Gidan waye?"
"Dr Khalid Bashir"
"Ok baban kune Minister na lafiya" a sanyayye tace.
"Eh"
"Bani wayar nan, dama bincike kike yi mata? Sai na gayawa Mommy"
"WALLAHI ba bincike nake ba, wayar ne take ta kara, Sannun Addah Munah, wani ne ya kira."

   Amsar wayar tayi tare da cewa.
"Me yasa kika dauki wayar? Ince baki gaya mishi inda nake ba?"
"Kiyi hakuri na gaya mishi, kuma shima yana jin France"
Daka mata tsawa tayi, tare da cewa ta fita,, cillar da wayar tayi tare da jan tsaki.

Kashe wayar yayi yana kallon sunanta, mik'ewa yayi ba gobe ba, yau Insha Allah zai tafi Maradi. Bai tsaya na ya fita ai Dole Jelar shi ya bishi da gudu suka fita.

Karfe bakwai na dare suka shiga garin Maradi, da location na wayar ta, yayi ta bibiyarta har gidan, dakyar aka Barsu suka shiga dan sun ce ma sun zo ta'aziya ne.

       Kiran wayar yayi taki dauka, fita yayi zai shiga gidan Dan Ba'are ya rike shi.
"Tana cikin gidan zan shiga naji meye nayi mata"
"Kayi" banza yayi dashi ya nufi cikin gidan, da sallama ya shiga falon ya hango Benazir, a tsaye tana latsa waya. Dake masifa ya ciyo shi bai tsaya duba ba, kawai ya isa gabanta cikin fada yace mata.
"Gaya min meye nayi miki?" Ya fada da karfi, a razane ta kalle shi. Bakinta na rawa,
"Mohan Mamman Nasir Aghali, bani bace tana dakina bari na kirata, falon da mutane,
Sai lokacin wani mugun kunya ya kama shi, juyawa yayi tare da cewa.
"Kuyi hakuri don Allah"
Nuna mishi gurin zama Benazir tayi, ya je ya zauna sannan ta haura sama.
"Assalamu alaikum! Kamar Almamoon ko?" Murmushi nayi mata, sannan nace mata.
"Dama baki gane bane? Tun tuni na Fahimci kawar Almamoon ce ke ai abokiyar fada"
"Waw! Kizo Mohan Mamman Nasir Aghali ya zo?"
Murmushi nayi sannan nace mata.
"Kice ba zan zo ba, yayi tafiyar shi" na fada mata tare da gyara kwanciya na, kasa fita tayi tana kallona.
"Addah Munah!"
"Bana son jin maganarki don Allah fita"
Tana fita na mike da sauri zuwa ban dakin, ina shiga na dauke almashin da na gani a ban dakin na shiga yanke gashina mai mugun tsawo da kyau, na yanke shi kaf, sannan na dauki reza ina kuka sai da na kwashe gashin kaina, sannan na durkusa a gurin ina kuka, kamar raina zai fita. Zan koma gurin Innata, ina mai kama da maza sak. Buga kofar Dr Zainab take amma fir naki kula ta, ina jin ta bar dakin na fito, ashe yana tsaye. Har zan koma ya taso  da sauri, abinda ya faru tsakanina da Malik ya dawo min wani irin ihu na saka tare da zuɓewa kasa. A rud'e ya karaso tare da daukata, ya dauko dani, Lokacin dan Ba'are ya shigo gidan kenan, dan ya gaji da zama.
"Innalillahi wa'inna ilaihi rajioun, d'azun muka dawo asibiti da ita fa, yanzun kuma wani abu ne ya same ta?" Inji Dr Zainab a rud'e.
"Mohan kawota Mommy likita ce."
"Bani kayan aiki Benazir" sake rikicewa Dan Ba'are yayi jin sunan Benazir, da gudu ta haura zama can sai gata da kayan, ta shiga dubata, kafin tace musu.
"Ta firgita ne, zuciyar ta yana bugawa sama da yadda muka dawo, ka firgitatta ne?"
"Akan me zan firgitatta, yarinyar da nake kauna? A'a kawai tana ganin na nufeta ta yanki jiki ta fadi bayan ta kwala kara."

"Hmm" tace a kasan ranta kuwa tace.
*Allah kasa ba sanadin fyaden bane wannan abin ya same ba?*
"Dr baki ce kome ba?" Ya kuma tambayar ta,
"Akwai abinda ya firgitatta ne, amma babu Matsalar kome" rubutu tayi sannan ta mika mishi.
"Kayi hakuri, gashi ka sayo mana maganin da ruwa," ta ciro kudi a jakarta ta bashi.
Mikewa yayi sannan ya ce mata.
"A'a barshi kawai"
Ya fita daga shi har dan Ba'are, kuma zuwan su tare bai zama dole ba, abinda yasa yayi haka dan ya katse mishi kallon BENAZIR ne, kuma yayi dacen haka domin tunda suka fita yake auna mishi maganar banza.
"Dan bakincikin da Hassada ina kallon annurin zuciyata zaka ja hannuna."
"Kai dan Ubanka yar mutane ba zata iya daukar nauyin ka ba, wallahi yaga musu ita zaka yi"
"Allah ya isa tsakanina da kai, wallahi zata iya dauka na, don Allah karka fara."

Dariya abin ya bashi bai kuma kula shi ba, har suka sayi maganin a wani Babban kanti. Wayar shi ce tayi kara, ya saka a kunnen.
"Yallabai Nagode domin na san aikinka ne"
"Karka damu, Mahaifinka yana don magana da kai ka nime shi."
"Nagode sosai, Insha Allah zan Nime shi."
"Toh babu kome, kayi ƙoƙarin dai."
Daga haka suka yi sallama, lokacin da suka isa gidan ruwan aka saka mata a dakin Dr Zainab da yake kasa.

  Sai da safe suka mata, sannan suka wuce gidan Mohan da yake Jacader. Sun samu babu kowa. Dan haka suka shiga abin su, daga nan suka wuce cikin gidan.

***
Karfe biyar na asuba, ina jin motsin Dr Zainab tana ban daki, na mike tare da cire ruwan da yake hannuna, sannan na dauki biro da takarda, na tsaya ina kallon shi. Kuka ne ya tawo min haka na hadiye, ina jin zata fito na koma na kwanta.
Fitowa tayi, tare da fara gabatar da sallah nafillah, Ni kuma ba shiga ban daki, nayi alola da wanka.  Sannan na fito na bar dakin na haura zama, sai da na gama shiri tsaf na duba jakata babu kome a cikin shi. Ina saukowa kasa na hango jakarta ban tab'a sata ba, amma a karon farko dan nisanci Mohan, na bude jakar na dauki kudin mota da na shan ruwa, sannan na ajiye mata wasikar godiya da fatan Alkhairi tare da laifin da nayi mata na satar Kudinta ta yafe min zan tafi gida ne.

Ina isa bakin get na mikawa Baba shima nace mishi.
"Bba akwai wasu maza biyu zasu zo zaka ga dayan su kato ne ka bashi wannan wasikar" sannan na fita daga gidan.

Ina fita da sauri, babu ababen hawa, dakyar na sami abin hawa. Ya kai ni tasha, ina zuwa na samu mota amma saura mutane biyu, haka na sha zama har karfe bakwai saura, kafin Allah ya taimaka muka tashi. Ajiyar zuciya na sauke lokacin da na Fahimci mun hau kan hanya.

   Na tsani kome na rayuwa, tun banyi nisa ba, kome ya lalace min. Tun ban yi dogon tafiya ba. Na rasa mutuncina, ina kuma da  na matsa kaina, rayuwata zan rasa ba mutuncina ba, tir da wannan soyayyar da bata da riba, daga lokacin da na hadu da Mohan fara fuskar yadda rayuwa take, nagodewa Allah, Innah tana raye. Amma ba zan iya gaya mata wannan mugun labarin ba, domin Mohan zata daurawa......
UZURI💓
*Bai zama dole gobe ku ga Posting da safe ba. Domin wallahi ina jin barci kuma yara sun sami hutu dan haka idan kun gani toh Madalla idan baku gani ba! Sai dare Insha Allah idan ban zama Busy ba kuma sai jibi Insha Allah domin ina da uzuri gobe Insha Allah*
#Mai_Dambu
8/19/21, 6:53 PM - My Mtn Number: https://www.wattpad.com/1110763041?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Mai_Dambu&wp_originator=PYEroEpzcfPkMnsivXwBeeuxpzKGK0fkWNcFQtCIRTayJ6sMVuy4zCFcXax%2BjsXVmcWqYu7JpcasekmM2WVikzyWFlN%2FH2zr4nlW%2F5vRpIWR%2BVC4yv60%2F1T6BeQc23Yo
🐂🐂BOROROJI🫀🫀

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.