Complete Hausa Novels

Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Baroroji Part 1 Complete Hausa Novel.txt

Chapter 58 of 64

BABI NA SITTTIN DA SHIDA
Ya tafi da ita bai tashi dawo da ita ba, sai da cikin shi haka yasa muka gudu, bayan rasuwar Mallam na dawo garin aka ce min suma.basu nan!"

Kukan Ammyn ne ya tsannanta, tace.
"Nahnah Yayanki ne ya dauke kakar Maimunari? Shi kuma Uban Maimunari ya dauke Zainabu, me yasa ban san tarihin mu na taya zanyi ta d'agawa."

"Baki ga kome ba, tunda gashi kin raba zumunci Allah ya haÉ—a kin raba, dake ke shaidaniya ce" inji Nahnah.

Addu'o'in aka yi tare da niman kariyar Ubangiji akan abinda ya faru Shekaru saba'in baya,
  Sannan Mohan tace.

"Don Allah ku taimaka min ku aura musu junan su, ko bayan sallah isha ne,"

Kallon suwaye aka mishi.
"Mommy da Abien mu."

   Kunyar haka yasa Mommy ta gudu, aikuwa bayan an tashi an rufe taro da addu'a,

Aka nufi masalaci, sallah magarib. Mohan ya tsaya waliyin Abie, Khalil ya tsayawa Mommy,

Haddir da Salman sune suka biya sadakin.aka daura aure cikin mutumtaka.
  A ranar kowa yasan matsayin shi, musamman Primer minister, da a daren ya ajiye aiki shi. Mohan kam bai iya magana ba, domin abin yazo mishi bazata, ta ko ina Maimunari yar uwar shi ce, kai ba zai ya jiran ya ganta ba, domin yasan zai bata mugun wahala. An kai amarya d'akinta, bayan watsewar abokan Ango.

   Wato ma'ana idan na leka gidan Amarya.  Duk wani abinda ake na al'ada sun yi (😂🤣🙄 BENAZIR bata san tsohon tuzuru ta aura ba, amma bari mu leka dakin ko🤨😜)

Wato shi tuwon girma miyar Nama ce,  domin kuwa Khalil ya gaya mata gaskiya (😎🤓 Alqur'an na rasa yadda zan rubuta kome)

Yar gidan Mommy da Marigayi ta zata auren shan minti ne, sai da aka gama tab'ayya, sannan ya zaro bayani daga karamar hukumar wandon shi, ya shiga zungure ta,....(na fecce bani da damuwa da ita)

  ***
Washi gari da safe, kiran Umma yayi kamar zai yi kuka.
"Umma don Allah kizo"

Haka ta nufi shashin su, daga bakin kofar kawai ta tsaya.
"Umma ki shigo mana".yana sanye da Jallabiya ruwan milk, tana shiga taga matasai a kasa, ga Beenah can a kuryan gado, ta makure, sai kuka take ta dunkule.
"Fita ka bani guri." Ta kore shi  ban daki ta shiga ta hada mata ruwa me shegen zafi. Sannan ta zo ta mika mata towel tace mata.
"Tashi kinjin" ta juya mata baya,a hankali ya zuro kafarta tana kuka, sannan ya daura towel din, da kifa akan gadon. "Kin gama daurawa"
"Eh " tace a raunane, sannan ta juya tare da taimaka mata suka shiga ban daki, sai da ta gasata sosai, ta gabata cire towel din, sannan ta fito ya same shi a falon fada tayi ya mishi tare da cewa
"Zan dauke ta, tunda baka da girma sai na jikinka. Kai ko kunya baka ji ba, ka saka yarinya a gaba kamar abinci, wallahi kaji kunyar ka, ina dalilin kasaka yarinya karama a gaba kamar ka samu babbar mace, toh ya kare dan ita ba tuwo bane da zaka saka a gaba kana ciki kamar ba zai kare ba, ce maka akayi haka rayuwar auren yaƙe? Dan haka kar na kuma jin labarin ka adabi rayuwar ta haka" kunya ya yasa shi sosa kanshi. Tana fita can sai gata da magani har zuwa dakin ta kaiwa Beenah,da tea mai kauri. Haka ta sata tasha. Dan ta same ta akan abin salla ne, tana sha  ta koma ta kwana, ita kuma ta fito ta same shi a falon yana zare ido, kwafa yayi mishi tare da shigewa ta barshi a gurin yana zare ido.

   Tana fita shima ya shiga dakin shi yayi wanka ya shirya tsaf, sannan ya fita tare da kiran Khalil suka tafi yawon gaida Surukai, sai wani sheki yake yana wani jim kanshi kamar akan shi aka fara aure (😎🤓 irin yaci sabon d....🤨😜) Ko kallo bai ishe Mohan ba, dan wani cin magani yaƙe.

...
Tunda aka daura auren Abie da Mommy, baki daya kowannen su yaki yarda ya hadu da wani, sai ma kara boye kansu suke, musamman Mommy, da take shashin Ummul Aiman, wani kunyar mutane take ji. Shi kuwa Abbu  ya sata a gaba yana zoyalarta.
"Malama idan zaki fito mu raka ki, toh dan ba zaki bar min dan uwa da kwanan kad'aici ba, ai son kai ne abin"
"Don Allah Hammah Mamman ka barni haka meye haka kake, wallahi zaka kore ni a gidanka"

     "A'a Malama bana son cutar kai idan zaki fito ki fito na raka ki, ina dalilin za a bar mutum shi daya a gida, da iyalin shi."

"Assalamun Alaikum!"
Mohan da Khalil suka yi sallama,
"Waalaikumun Salam," Mommy ta amsa musu cikin kunya domin dukkan su, surukanta ne.

"Mommy ina kwana!"
"Lafiya lau, ya kuke da fatan an tashi lafiya" sosai goshi Khalil yayi sannan ya damke cinyar Mohan cikin wani irin jin dad'i.
"Alhamdulillahi" inji Haddir ya amsa mata.
"Kai dan Ubanka sake ni, dan iska sake ni mara mutunci." Mohan ya buge mishi hannu, aikuwa ya kara damke shi. Kamar yara haka suka yi ta rigima Ita kam Mommy da Small Mom sai dariya suke, domin da ga Mohan har Khalil, basu rabuwa da abin fada.

Shigowata Ammyn ta zauna tana kallonsu. Domin an maida ita saniyar ware ba.
"Maman Maimunari, baku kira min ita ba, ko baki son naji muryan Kawata ce"
"Yaushe kika fara sonta haka?"
Sunkuyar da kai kowa yayi, domin tambayar da Abbu yayi mata kenan.
"Ina ruwanka tunda na kai na tambaya ba" tashi Small Mom tayi tabasu guri dan ta fahimci suna son magana a keb'ence.
Kiran layin Zurich din tayi bayan ta dauka tace mata.
"Ki bude data zamu yi magana dake kuma ina son ganin hoton me hancin karas"
"Toh Mommy kai, Widad din ce mai hancin karas ai irin naki ne, jiya Beenah take gaya min wai an daura auren ku."

Kashe wayar tayi tare da bude data, can kuwa Haddir ya dauko Laptop din shi tare da abubuwa connecter, aka had'a tana sanye da riga da wando. English wear. Sai karamin farin gyale da ta yane kanta.

    Murmushi nayi tare da cewa.
"Mommy an gama biki ni da Yumnah muka kewar ku, har da Widad. Please ku dawo" tayi wani maganar a shagwaɓe, kanshi a sunkuye yake bai san lokacin da tsigar jikin shi ya mike ba, tare da kura mata ido, yarinyar jego yayi mata kyau, kuma ta had'u iyaka, dauke kai yayi dan bata lura da shi ba.

"Ina me hancin karas?"
Dauko mata Widad nayi tana wani yatsuna fuska.
"Honey kaka tana miki magana kula ta ko zata ji dadi a ranta taga beautiful baby"
"Almamoon ya kake?" Hango Hammah Khalil nayi, na sake murmushi.
"Muna lafiya, ya kake kaima? Ya kanwata? Ya Umma da Jalilah."

"Alhamdulillahi tunda bata aure miki miji ba dole ki tambaye ta," murmushi nayi sannan na kauda zance haka muka yi ta gaisawa dasu, sannan aka had'a Ni da Ammyn hade rai nayi tare da dauke kai na nace mata.
"Ina wuni"

Daga haka na dauko abin saka yarinyar na ajiye ta na cigaba da aikina ita kuma, tana fama da jikarta suka hira wai.

"Ammyn ki kashe wayar haka baki ga yarinyar tayi barci ba, Mommy kiyi mata magana ta goyeta, tana bukatar dumin jikinta."

"Ai ba bayanka bane kuma baka saya ba balle kace ka saya ne dole a maka abinda kake so idan mutum bai fita rayuwar mu ba, wallahi zai sha wahala." Na fada ina murguda baki, na kashe kiran dan ban jira Abinda Mommy zata ce ba.

"Kayi hakuri Mohan, sai na sab'a mata Insha Allah, ai baa kanta aka fara rashin aure ba, mara kunyar banza zata ishe mutane bari ka isa Zurich din sai na mata duka.". Haka tayi ta faÉ—a suna bata hakuri, goggan naku sai wani murmushi yake irin matukar na kama yarinyar nan zata ji a jikinta.

  Bayan kwana uku.

Suka tattara suka dawo Zurich. Baba Mari kan tace bata bin su ko ina, gurin Yar uwata zata zauna. Haka suka tafi aka bar Beenah, wacce suke soyayyar kamar zasu cinye kansu, amma duk da haka bata yarda yace zai shiga aljanna (😎🤓)

***
Bayan sun dawo ne suka fahimci Maimunari ta dan sauya, yawan waya fita babu wani kwakwaran dalili, kawai aikin Ansar ne. Kuma bata dawowa akan lokaci haka Yarinyar zata gama kuka kamar ranta zai fita, ranar taga b'acin ran iyayenta, dan kamar zasu dake ta.

Ina jin su, suna fada ban kula su ba na dauki yarinyar ina hararanta. Ina shiga cikin dakin na dangwala ta a gado, sannan na wuce nayi alola, haka tayi ta kuka kamar zata shiÉ—e, koda na idar da sallah, na saka mata mama yarinyar nan taki karb'a. Ruwa na bata garin.daukar waya kawai na tunkud'a mata, yar mutane ta shiÉ—e. Baki daya ta kafe min.

"Wayyo Allah na, Mommy mi taimake yar mutane zata mutu," na fita a haukace karbanta Mommy tayi tare da gwada mata hikima amma fir taki dawowa, ina kuka kamar zan mutu,.haka muka nufi asibitin. Dakyar suka janyo ruwan da ya shiga hancinta, ana ja yana sake wata irin Marayan kuka, nima kukan nake. Likitan ne ya fito yayi ta faÉ—a tare da cewa sai an hada da hukuma domin wannan cin zarafin yara ne. Dakyar suka hakura tare da sallamar mu.

Tun a mota suke fada, Ni dai ban ce kome ba, ina rungume da Yarinyana a Kirjina.
"Ance min ana ganinki da wani waye shi? Wato dan bamu nan shine bari ko fara wani rashin hankali ko?"

"Abie ba kowa bane fa, Hisham Waadi Ansar ne, kuma naga babu kome a cikin alaƙar mu, sai abo.." tass Mommy ta wanke ni da mari.
"Kar na kuma ganin ki dashi, idan ba haka ba, zan miki Yaren da zaki Fahimta, wallhi" inji Abie, da yake tuki.
"Toh duk akan me? Haka kawai ban sami farin cikin rayuwa ba, dai da na hadu da shi  yanzun shima ace  za a rabani dashi."

Ran Mommy ya b'aci addu'a take Allah ya kai mu gida, dan haka muka isa ta rigani fita, ta amshi yar tare da mikawa Abie.
"Kyaleta mu shiga."

Amma ina ta hau dokin zuciya, ta rufe ta da duka, sosai domin ta gaji da Iskancin Maimunari ana cewa wai dan ba a sonta, sai da ta mata mugun duka, sannan ta shige ta barta a bakin kofar, taki shiga kuma taki karbar yarta, dan haka suka kyale ta, ransu kowa ya b'aci.

      Tunda Mommy ta shiga ɗakinta take kuka, sabida da ciwo a ce baka da iko akan d'anka, har kusan asuba ga yarinyar na ta kuka. Amma Maimunari tana waje, sai da Abie ya fita da belt ya bude mata ido ta dauki yar tare da shiga d'akinta ta, kwanta tana rarrashin Yarinyar.

Sam ban san me ya shiga kaina ba, nake jin haushin kowa har da Mohan, ina kwance maganar Ansar ya dawo min.
"Ke fa ba a damu dake ba, ƙawai ana damuwa dake ne sabida yar Mohan, ko yayya idan kika bari yarinyar nan wani abu ya same ta zaki ga yadda za a nuna baki da daraja, sai ita."

      Lumshe idanun nayi wato da gaske ne abinda ya gaya min, sabida ita yarinyar ta hanyar aure aka same ta, shi yasa ake damuwa da ita, Ni kuma Shegiya wacce aka haifa ta zina. Haka na sha kuka na more, da safe na tashi zan tafi makarantar na ajiye yarinyar bayan na shirya ta, na rubuta Musu.
*Ba zan dawo da wuri ba sai biyar*
Na saka a kasar rigar yarinyar, ina share kwalla. Koda Mommy ta shiga daukarta bayan na tafi ta ga sakona, ko karyawa ban yi ba, haka na bar musu abin su, ranta ya kuma b'aci dan haka ta kasa hakuri ya kira Mohan, ya gaya mishi abinda yake faruwa dauke wuta yayi....
#Mai_Dambu
8/19/21, 6:54 PM - My Mtn Number: https://www.wattpad.com/1116443174?utm_medium=link&utm_source=android&utm_content=share_published
HAKKIN MALLAKATA
#sun-Aug-2021

BOROROJI

~The Journey of Destiny💔~

Mai_Dambu

Sadaukarwa ga
Sajidah Nijar
Samirah Nijar
OumNass
Azizah Hamza....

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.